Chapter 3️⃣
💦BARIKI TAFI GIDA💦
writer✍️
Aisha Yakub Ahmad
join my whatapp grouo via this link : ***
or join my arewapen via this link: https://www.arewapen.com/book?id=6a404d02013c3441d19e0400
Bismillahir rahmanir raheem
page 3️⃣
Tafiya take tana hasaso abubuwa da yawa da
suka faru a rayuwarta , tana tuna yadda
mahaifinta ya ke da son kuɗi , yadda baya
girmama mahaifiyar ta , yadda yake wulaƙanta
su , yadda yake dukan mahaifiyarta , kuka ta
sak i , se da tayi me isar ta sannan ta goge
hawaye , ta cigaba da tafiya , tun tana tafiya da
kuzari har ta soma gajiya , haka ta ci gaba da
tafiya , tana taku ɗai ɗai , dai dai san da zata
tsallaka titi , wata mota ta taho da gudu , ba ta
lura ba , se ƙarar horn taji a kanta wanda hakan
ya gigita ta kawai a afka gaban motar , hakam
ya bashi damar kaɗe ta.
Cikin sauri ya sakko daga motar lakacin mutane
sun fara taruwa yayin da jaririyar nan take ta
tsala kuka , kukan tane ya ankarar dashi har ya
ga yarinyar,a hankali ya dauki uwar ya saka a
mota sanna wani mutumi ya miƙo masa jaririyar.
Wani private hospital ya nufa dasu , a nutse ya
fito ya wuce ciki , tare da wasu nurses ya dawo ,
cikin sauri suka nufa ciki da ita taimakon
gaggawa suka fara bata , shi kuma yana riƙe da
jaririyar , nufar wata nurse yayi ya miƙa mata
jaririyar , wuce wa nurse din tayi da ita , yayin da
shi kuma ya koma reception yana zaune.
Waya yake dannan wa da bisani kuma se ya
kara wayar a kunne ; “ musaddiq “ naji ya furta
ina hospital kazo yanzu ka same ni , ban san me
aka ce daga ɗayan ɓangaren ba , gani nayi ya sauke wayar……………….💧
HAJ ATIKA POV … ……………..
“ ai se naga bayan sa kamar yadda na kori uwar
su ta barmin gida da wannan me idon magen ,
shima haka ze bar gidan nan “ shiru tayi banji
ma aka ce daga ɗayan ɓangaren bah , sake
cewa tayi “ ai ɗazu ina sane na saka aka yi faten
wake da safe saboda nasan ko yunwa zata
kashe shi baze ci bah, magana aka sake yi a
ɗayan bangaren , kwashe wa da dariya tayi tace
“ shi ya isa ya faɗa wa mahaifinsa abun da nake
masa ai soko ne kina ganin sa “ dariya ta sake
saki sannan tace “ indai wannan ne na miki
alƙawari Nimrah bata da mijin da ya wuce Aabid
in dai ina raye” sun daɗe sun tattauna sharrika
iri-iri sannan sukai wa juna sallama daga baya
………………..💧
wannan kenan
“ Ummiey ina addah Ash ta ke “ wata yarinya ta
fada wacca bazata wuce shekaru sha biyar bah,
duba na kai ga wacca aka kira Ummiey,
mahaifiyar Ashnahh ce , duba na sake kawai
kan yarinyar , tsananin kamar da suke yi da
Ashnahh ne ya saka na sake duban ta a karo na
biyu , kyakyawa ce dan har ta so tafi Ashnahh
kyau , tana da dan tsayi , saɓanin Ashnahh,
kuma wannan tafi Ashnah garin jiki , kuma
wanna fara ce sol , shiru Wacca ta kira da
Ummiey tayi mata , itama bata sake ce mata
komai ba kawai ta wuce ɗaki dan duba Ashnahh
, wata mace na hango a chan ƙuryar ɗakin …………………💧
ku biyo ni domin jin yadda zata kasance
Daga alƙalamin✍️
Aisha Yakubu Ahmad