Chapter 5️⃣
💦BARIKI TAFI GIDA💦
writer✍️
Aisha Yakubu Ahmad
join my whatapp group via this link : ***
or join my arewapen via this link: https://www.arewapen.com/book?id=6a404d02013c3441d19e0400
💦Ending of free pages💧
Bismillahir rahmanir raheem
Page5️⃣
Wata mota ce ta shigo harabar asibitin , wani
matashin baƙin saurayi ne ya sakko daga motar
aƙalla ze yi shekaru 28 zuwa da tara , sanye
yake da blue jeans da black t-shirt, sanye yake
da wata ɓakar p- cap , black beauty ne,
kyakyawa ne sosai , yana ƙananun idanu wanda
suka amshi fuskar sa sosai, cikin asibitin ya
dosa , a ƙofar shiga reception ya tsaya , yana
ƙoƙarin kiran Abid , se ya hango shi zaune ya
lumshe idanunsa , cikin sassarfa ya ƙarasa
wajen shi .
Zaune yake ya lula duniyar tunani , saukar
hannu yaji a kafaɗar shi wanda hakan ya sanya
shi sakin ajiyar zuciya tare da juyawa dan ganin
waye , haɗa ido yayi da Musaddiq , murmushi
musaddiq ya sakar masa , haɗi da tambayarsa ,
lafiyar sa , kamar mara son magana haka ya
shaida masa , abunda ya faru , waje ya samu ya
xauna , ba jima wa se ga nurse ta ƙaraso wajen
Aabid tace “ sir jaririyar na cin ƙoshin lafiya , se
dai tana ɓukatar abinci , kuma the mother is
unconcious ko za’a iya siyo madara ta yara se a
bata kafin maman tata ta farfaɗo.
Miƙewa yayi ya isa wajen Musaddiq magana
sukai sannan ya saka kai ya fice haraban
asibitin,mota ya shiga ya fice daga asibitin
………………💧
ASHNAHH POV………………..
Kwance take akan gadon asibiti , a hankali ta
fara buɗe idanun ta da sukai mata nauyi , nurse
ta gani a kanta , addu’a take a ranta , allah ya
sa, jaririyar nan ta mutu , dan bata san ina zata
nufa da yarinyar bahh , muryar nurse din ce ta
dawo da ita daga tunanin da taje “ baiwar allah
kin samu hatsari ne , kyma wanda ya kaɗe ki
shine ya kawo ki asibitu , yau kwanan ki huɗu ,
shi yake kula da ciyar wa yarki da take chan
gadon “ , ta faɗi tare da nuna mata gadon yar
tata, fitsari tace tana ji haka ya bata damar shiga
banɗaki, taji sayƙi sosai , bata jin komai a
jikinta,alwala ta dauro sannan ta fito tana ƙoƙarin
sako kanta ɗakin , shima a dai- dai lokacin ya
shigo , yana sanye da white jean da blue shirt ,
haɗa ido suka yi , saurin sauke kanta ƙasa tayi ,
ta shiga takowa a hankali , dakin ta ƙaraso , ta
zauna , gaida shi tayi , tsaya yayi yana kallonta ,
jin shiru ita kuma ya sa ta ɗago kanta ,
idanuwansu ne ya sarƙe ana juna , gaban ta ne
ya faɗi ras, da sauri ta dauke idonta a kansa ta
sake ƙasa da kai , samun kansa yayi da
murmushi sanan ya amsa ta da lpy, kujera ya ja
ya zauna , gyaran murya yayi ya fara magana “
baiwar allah bansan sunan ki ba , na daɗe ina
fatan allah ya tashi ka faɗun ki ko dan ki faɗa
gidan ku , sannan na maida ke “ yana fara
magana hawaye suka fara wanke mata fuska ,
cikin muryar kuka tace “ bani da kowa , bawan
allah na gode , allah ya saka da alkhairi , amma
zaka iya tafiya tunda har na tashi” , kuka take
sosaai, shiru ne ya ratsa tsakanin su , miƙewa
yayi yace kiyi sallah za muyi magana , be jira
cewarta ba ya saka kai ya fice a
ɗakin………………💧
ku biyo ni domin jin yadda zata kasance
free pages sun ƙare 💧
Daga alƙalamin✍️
Aisha Yakubu Ahmad