BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 5

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA❤* *Arewapen@ayshadansabo*

©️Ayshat D'ansabo lemu 🖊️

*Free page 5*

Yau a gajiye take tako layin zuwa bakin hanya domin samun abin hawa,ji take tamkar ta yadda hand bag ɗin hannunta haɗe da ledar da Anty Hauwa ta zuba musu abinda sukai ranar.Hakanan ta ƙariso bakin hanya ta ja ta tsaya,duk abin hawan da zai zo kuma sai ya zo a cike.Hakan yasa take ta sakin tsaki jefi-jefi,gashi sun tashi da wuri yau domin duka ƙarfe ɗaya ne na rana.Sosai garin ake ƙwalla rana,hakan ne ma yasa gajiyar ta ninka sabida ranar dake taɓata.Tana ji ana zabga mata horn amma ko kaɗan ba tayi yinƙurin ɗaga kai ba bare ta kalli mai yi,har sai da ta ji tsayuwar motar dab da ita sannan ta ɗago ido domin ganin wani mai karanbanin ne? Caraf idanunta suka faɗa kan Mubarak,ya kafeta da manyan idanunsa yana faɗin,"Ke ƴar ƙauye kina ji ana ta horn kinyi banza,ko kin sha masu tayawa ne ana jan musu aji,oya shigo mu je in sauke ki."

Babu musu ta buɗe gaban motar ta shiga fuskarta ɗauke da smile take faɗin."Ya Mubarak kenan,ashe dai maganar da nake ji ka dawo da gaske ne.Amma shine ko ka zo a gaisa,gaskiya zumuncin mu yana da rauni sosai.To ya ka dawo ɗan Cyprus?"

Surayyah ta ƙare maganar tana duban gefensa.Sosai ya yi wani irin fresh da jiki,kyawunsa ya sake fita sosai.Shi ma ita yake duba yana faɗin.

"Zumunci kam kuna da gyara sosai a kansa Surry,amma ni karki ɗaura min laifi tunda na dawo ban zauna ba ne shiyasa,sai yau na samu lokaci shiyasa ma na fito.Yanzu haka ma daga gidan kawu Lawal nake,nace bari dai in wuce gidan naku."

"Ok yayi kyau to,shikenan an kammala Master's sai mu fara shirin shan biki idan an darzo mana matan aure."

Cewar Surayyah cike da zolaya irin na abokan wasa.Mubarak ya saki smile yana kallon ta rabin hankalin sa naga tuki yake faɗin.

"Haka ma za ki ce,idan na darzo,to idan kuma ke zan darzan fa?"

Ya ƙare maganar yana sakin dariya ƙasa-ƙasa,yayin da Surayyah tayi saurin ɓata fuska.Cike da shagwaɓa take faɗin,

"Ai bama ni ɗin bace Bro,kawai abar maganar ma kar ta yi tsawo,kaga yadda ka zama wani lukuti ne gaskiya ƙasar ta amsheka sosai."

Ta ƙare maganar cike da son basar da waccan maganar.Murmushi kawai yayi domin sarai ya gane wancan maganar ne bata so,sai ya bita a yadda take so har suka ƙariso gidan nasu.Tare suka jera da juna har zuwa cikin gida,a falo suka tadda Mum tayi baƙuwa hakan yasa Surayyah yin gaba zuwa ɗakinta bayan ta gaida da baƙuwar.Shi kuma Mubarak ya zauna Mum na masa barka da zuwa.Surayyah bata jima da shiga ba ta fito,wannan karon ta cire hijab ɗin jikinta tana sanye cikin riga da skat ne da suka zauna a jikinta.Sosai atamfar ta amsheta,ɗinkin yayi mata kyau sosai. Kitchen ta nufa domin kawo ma Mubarak ɗin ɗan abin sha,idanunsa fes a kanta suke tunda ta fito har ta shige hanyar corridor da zai sada ta da kitchen ɗin.Bai san lokacin da ya sauke wani ɓoyayyen ajiyar zuciya ba,yana jin wani abu na tsarga masa tun daga yatsun ƙafarsa zuwa zuciyarsa. Haka Surry ta zama a tsayin shekaru biyu da ya yi bai ganta ba? Dama yasan Yarinyar akwai kyau da diri,amma wannan karon gani yayi kominta ya ƙaru.Koda Surayyah ta fito Mubarak sake zuba mata idanu yayi,yana sauke ganinsa akan ƙirjinta da ya fi ko'ina ɗaukar hankalinsa.Aje ƙaramin tray ɗin hannunta tayi a gabansa,mai ɗauke da lemun cway da cake,tana faɗin.

"Ya Mubarak,Bismillah."

Ta ƙare maganar tana zama a kujerar dake kusa dashi.Baƙuwar Mum ce ta miƙe zata wuce sukai mata sai anjima,Mum ta bita domin yi mata rakiya.Sai falon ya zama sai su biyu,hakan yasa Mubarak duban Surayyah yana faɗin.

"Surry kin ga yadda kika sake wani mugun kyau da cika ne,gaskiya Allah yayi halitta a wajen nan, tabɗi! Aini kuma na samu matar aure a gida babu ruwana da nema a waje."

Ya ƙare maganar yana sake kafe ƙirjinta da kallon ƙurilla.Hakan yasa Surayyah jin ranta ya sosu,ta tsuke face tana faɗin.

"Don Allah Ya Mubarak kama daina wannan maganar,ni bana son auren zumunci kaje can ka samo matar aurenka ehe!"

Ta ƙare maganar tana hararansa,tare da zame ɗankwalin kanta ta warwareshi ta yafoshi ya rufe ƙirjinta da Mubarak ya kafe da kallo.Cup ɗin hannunsa ya aje yana jefa mata harara yake faɗin."To miye na wani rufe jiki duk abinki dai In Sha Allah ke ce rabona,maganar baki son auren zumunci kuma wannan ke ya shafa.A tuh! Ni dai na gani,kuma ina so."

Shigowar da Mum tayi ne ya hana Surayyah cewa komi,sai hirar ya koma tsakanin Mum da Mubarak ɗin.Surayyah sai ta koma ɗakinta domin kallon da Mubarak ke tsare ta dashi ya takurata,hakan da tayi yasa Mubarak yanke hirarsu da Mum ya miƙe yana faɗin zai wuce.Mum ce ta ƙwalama Surayyah kira ta fito sanye da ƙaramin hijab iya cinya,sallama ya yi ma Mum ɗin yana duban Surayyah yace.

"Sisi ni zan wuce,muje a takamin ko."

Surayyah kaman ta fasa ihu haka taji,amma don kar Mum ta fahimci wani abu yasa ta sakin murmushi tana faɗin. "To Bro,muje ba don halinka ba amma."

Maimakon yayi gaba sai yaƙi,sai da Surayyah tayi gaba sannan ya bita a baya idanunsa na yawo a jikinta.Sosai yake ƙarewa surarta kallo,yanayin takunta ya haifar masa da mutuwar jiki,sabida yadda mazaunanta ke juyawa.Ji yayi kamar da gayya take irin tafiyar,daga bakin gate ɗin ta ja ta tsaya tana dubansa cikin ido tace,

"To gashi na tako ma,a gaida gida,da su Gwoggon."

Ta kai ƙarshen maganar tana kauda face ɗinta,ganin irin kallon da yake jifan ta dashi kafin ya furta. "Za ta ji,yanzu dai ungo phone ɗina kisa min digits ɗinki Sisi,seriously naji kin gama rikitani Surryn Mum."

Amsar wayar Surayyah tayi ta sa masa number ɗinta,ta miƙa masa wayar tana faɗin."Bro don Allah tsokanar ya isa haka,ni ka ga tafiyata ka gaida gida."

Bata jira cewarsa ba ta juya domin komawa cikin gida.Sai da ta ɓacewa ganinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya yana ficewa daga gidan zuwa motarsa,ya tasheta yana ji zuciyarsa na kisima masa abubuwa masu yawa akan Surayyah.

********

Ƙarfe kusan 11pm har bacci ya fara ɗaukarta kiran Mubarak ya tada ita,ta kara wayar a kunni tana sauraran muryarsa.Cikin muryar bacci tayi magana a shagwaɓe tana faɗin.

"Ya Mubarak wallahi bacci nake ji,ka taimaka ka bari da safe mayi magana."

Daga ɓangaren Mubarak ya furta."No Baby please,ki barni naji wannan sweet voice ɗin naki.Surry ni fa da gaske kin yi min,wallahi Allah son ki ya kama zuciyata.Ki taimaka ki bani dama muyi auren zumunci,bakinmu alaikum please Sisi."

Ya ƙare maganar yana narke mata murya cikin wani irin salo,wanda ya yi matuƙar bama Surry mamaki.A cikin zuciyarta take faɗin,"Su dai maza duk haka suke sam basu da kunya sam." Muryarsa ta sake jiyowa yana faɗin. "Hello,Surry kina ji na?"

Ta sauke numfashi tare da lumshe idanunta tana faɗin."Ina jinka Bro,wallahi bacci ne kawai ke ɗawainiya dani."

"Shikenan Sisi yi baccin ki,amma ki sani da safe da wannan sweet voice ɗin naki zan fara yin breakfast."Murmushi kawai Surry tayi tana cutting call ɗin,tare da kashe wayar baki ɗaya ta maida kai ta kwanta zuciyarta na jin takaicin yadda daga dawowarsa zai ɓullo mata da wani sabon salon yana son ta.Bayan a duniya sam bata son auren zumunci ko kaɗan.Da ƙyar bacci ya sake ɗaukarta,cike da mafarkai barkatai.

⚡⚡⚡⚡⚡

*KADUNA*

A gajiye ya shigo gidan,kuma kai tsaye ɓangarensa ya nufa domin yin wanka ko zai ji daɗin jikinsa.Shigowar dare sukai sakamakon lalacewar da motarsu yayi a hanya,halin ƙarfen nasara da bashi da tabbas.Allah ya so ya yi dibarar sanar ma Hajiya,ba don haka ba yasan da yanzu tana nan hankalinta a tashe.Duk da a yanzu ɗin ma ya san tana nan ba tai bacci ba,sai ta ji dawowarsa.Shiyasa yana fitowa daga wanka ya sauya kayan jikinsa tare da yin sallah ya fito,kai tsaye sashin Hajiyan ya nufa.

Da sallama ya shiga cikin falon,tsit babu kowa da alama su Humaida an shige room domin kwanciya.Ɗakin Hajiya ya nufa kanshi tsaye,ya shiga bakinsa ɗauke da sallama.Kuma kamar yadda yayi tsammani tana zaune ba tai bacci ba,hannunta riƙe da carbi tana lazumi ga dukkanin alamu bata jima da idar da shafa'i da wuturi ba kenan.

Idanunta ta ɗago ta sauke a kansa tare da amsa sallamarsa, fuskarta na bayyanar da murmushi na jin daɗin ganin dawowarsa lafiya.Ya ƙarisa inda take zaune a kan sallaya ya zauna,yana faɗin,

"Barka da dare Hajiya da fatan mun sameku lafiya? Kin ganmu sai yanzu,halin ƙarfen nasara kenan."

"Lafiya lau Abdallah,sannunku da dawowa.Ai ƙarfen nasara bashi da tabbas kam."

Cewar Hajiya tana aje carbin hannunta,ta miƙe tana dubansa tace, "Tashi mu je falo ga abinci can nasa ai maka mara nauyi,da kuma jarababben shayin naka na fama."

Abdallah ya saki dariya yana faɗin."Godiya nake Hajiyata,Allah dai ya ja kwana."

"Ameen. " Hajiya ta furta tana yin gaba yana biye da bayanta har suka fito falon.Ya nufi ɓangaren dining ya zubo abinda zai ci ya dawo cikin falon,yana ci suna taɓa hira har ya gama.Mug ɗin shayin ya ɗauka ya yi mata saida safe ya fice,domin komawa sashinsa.

Sai da ya gama kammala duk abinda zai yi kafin yayi shirin kwanciya,ya nufi bed bayan ya maida hasken fitilar zuwa dump. Kwanciyarsa ke da wuya ya janyo wayarsa tare da tsurawa screen din ido tamkar ita ce a gabansa a zihiri,zanen fuskarta ne da ya zauna ya zana ya ɗauka a wayarsa ya zama shine screen wallpaper ɗin wayarsa.A kullum kwanan duniya soyayyarta sake ninkuwa yake a cikin zuciyarsa,bai kuma daina bibiyar Mangal Plaza ba akai-akai wai ko Allah zai sa ya sake cin karo da ita,amma ko mai kama da ita bai kuma gani ba.Addu'arsa kullum shi ne,Allah ya sake haɗasu,domin BURIN ZUCIYARsa bai wuce ace ya sake yin tozali da kyakykyawar fuskarta ba.A hankali yakai bakinsa ya shiga sunbatar fuskar wayar,tare da yin magana a fili yana faɗin.

"Ina kike ne Pretty,kika bar zuciyar Abdallah na azabtuwa da soyayyar ki? Pretty ke ce BURIN ZUCIYAta.Please ki sake bayyana kanki gareni..."

Ya gintse kalaman yana jin yadda zuciyarsa ke cigaba da azalzalarsa a kanta.Bai taɓa sanin haka so yake ba,domin bai taɓa bai wa ko wace diya mace fuska ba bare har ya kulata da sunan so.Duk da irin yadda yake fama da,ƴan matan da ke matowa akansa.

Da ƙyar bacci ya rinjayi idanunsa har ya aje wayar a gefensa,ya sake shigewa cikin duvet.Bada jimawa ba bacci mai nauyi ya tafi dashi,cike da mafarkinta wanda hakan har ya fara zame masa jiki.

⚡⚡⚡⚡⚡

*Nnamdi Azikiwe International Airpot Abuja.*

Rash ce da Hisham cikin farar Land Crusher ɗinsa,shi ke tuƙa motar yayin da Rash ke kame a gaba.Tana sanye cikin English wear's Riga da Wando masu azabar kyau,ƙamshinta dake narkar da zuciyan maza a kanta ke tashi a jikinta.Face ɗinta cike yake da annuri sosai,tare da ɗokin zuwa ƙasar da ta jima tana Burin zuwa.Sai wannan karon da Hisham ya buƙaci rakiyarta sannan Allah ya yi zata halarci ƙasar.Anty Sameera ta sha zuwa tare da shi,a lokacin da suke ganiyar yawon horneey moon ɗinsu.Bayan ya faka motar tare da kasheta baki ɗaya ne,ya juyo da face ɗinsa zuwa gareta,tare da watsa mata manyan idanunsa.Cike da murmushi yake faɗin.

"To baby gaki a airport yau za ki bar Abuja zuwa Lagos,daga can kuma sai Dubai.Ina so ki kular min da kanki kafin na iso,da zarar kun sauka ki kira line ɗin Zaid.Shi zai zo ya kaiki hotel ɗin da na riga na kama mana,nima gobe zan taho In Sha Allah,sabida bana so muyi tafiya rana guda sabida gudun zargi.Oya give me my twins in ɗan shashsha su."

Bai jira cewarta ba ya janyota zuwa jikinsa baki ɗaya yana cusa kansa bisa ƙirjinta,ya jima yana morewa dukiyar fulanin kafin ya saketa suka fito tare domin yi mata rakiya.Saura mintuna sha biyar ya rage jirginsu ya ɗaga zuwa lagos,daga can kuma cikin dare zasu tashi zuwa Dubai.

Tuƙi yake bisa titi domin komawa gida,yana tafe yana faman mamakin kansa yadda lokaci guda Yarinyar ta gama rikita tunaninsa.Sosai yake jinta a cikin ransa fiye da matarsa Sameera,Rash ta gama birkita duk wani lissafinsa ta yadda yake ji babu abinda za ta nema ya gaza yi mata shi.Ba Dubai ba,duk ƙasar da ta nuna tana so yana jin zai iya kaita.A yanzu ita kaɗai ce ke juya duniyarsa,tunda ya lashi zumarta bai sake jin garɗin na sauran ƴan matan da yake tarayya da su ba.Ya rasa wani irin baiwa ke gareta,addu'arsa kullum shi ne,Allah ya cigaba da rufa musu asiri kada Sameera ta gano mummunar alakar da ke tsakaninsa da Rash ɗin.Ko za ta gano ɗin,ya zamana sai ya jima yana anfanuwa da baiwarta.Har ya kai gida,yana kisima abubuwa da yawa akan Rash ɗin da irin holewar da za su yi a ƙasar Dubai ɗin.

Koda ya shiga gida time ɗin magriba ya gabato,a ɗakinsa ya tadda Sameera ta fito daga toilet ɗaure da alwala.Murmushi ta jefa masa tana faɗin.

"Har ka sauketa ka dawo,Allah sarki Autar Mama,waya ga idanun Rash a Dubai.Kasan rawar kanta,ni wallahi na so ace tare za mu,amma tunda one week kaɗai za ta yi kuma ka haɗata da mutananka na can da sauƙi."

Ta ƙare maganar tana jifan shi da smile ɗin dake kashe mai jiki a da.Shibma murmushin ya jefeta da shi yana faɗin.

"Ai Rasheeda ɗokin wannan tafiyar take sosai,gara da muka barta ɗin,next time sai mu tafi mu duka mu huta.Nima gobe war haka ina cikin jirgi,sam tafiyar nan zuwa Spain na dole zanyi,domin na fara gajiya da yawan tafiye-tafiyen nan,kamata yayi ace na huta a cikin Iyalina.Gashi ke sam yanzu kin daina kishina,ɗan rakiyar da ake mini da ana kaf-kaf dani duk an daina,hankalinki na kan business ɗinki wife."

Sameera ta shagwaɓe murya tana faɗin."Sorry my luv,ba haka bane kai ma kasan tun farkona ba mai son yawan tafiya bace."

"Ok to ya isa,bari inyo alwalar nima.Idan munyi sallah ma sake tattauna maganar."

Ya ƙare maganar yana nufar hanyar toilet,ita kuma ta nufi inda pray mat ɗin yake.....✍🏻