JODAH

05

by @sadisakhna


 

_____👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

Na  

*Sadi-sakhna* 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

 

 

*HarÆ™a ta (5)*👑 

 

 

 

 

 

ÆŠaga mata kai tashiga yi kamar kaÉ—angare tana Æ™ara sautin kukanta mai haÉ—e da dariya. 

 

 

 

"Nice Joda nice Ummah ce,sannu kinji sannu.....nayi zaton na rasaki Joda......" 

 

 

 

Sambatun da takene yajawo hankalin baba yakub yayi magana daga waje domin yaji mai yake faruwa,a zatonsa ko ciwon kamaluddeen ne yayi tsamari. 

 

 

 

"Baba Yakub joda ce ta tashi,Joda ta tashi shigo ka gani harta Æ™ira sunana" 

 

 

 

Ƙarisawa yayi ciki jin tayi masa ido,a kwance yaga yarinyar akan cinyarta ta rirriÆ™eta tamkar zata maidata ciki,ita kuma kallo kawai take bin Aminatoun dashi. 

 

 

 

"Yarinya sannu kin farfaÉ—o ya jikin?" 

 

 

 

Tsayawa Aminatou tayi da jijjiga ta domin bata damar amsawa baba yakub É—in. Itama Joda a nata bangaren jin muryar mutum yasa ta juya inda yake tana Æ™are masa kallo cikin nutsuwa kamar ba yarinya,batace komai ba ta É—auke kanta tareda Nuna gogar Duma na ruwa dayake gefen Aminatou. 

 

 

 

Ta gane mai take nufi dan haka da sauri ta miÆ™o mata ruwan tareda É—an tayar da ita kaÉ—an ta fara sha. 

 

 

 

Ƙwat Æ™wat kwat saida ta shanyeshi tass kafin tasaki gorar,ajiyar zuciya tasake tareda sakin jikinta ta koma ta kwanta,cikin Æ™anÆ™anin lokaci bacci ya fizgeta normal bawai na suma ba. 

 

 

 

Ita dai ta baba Yakub ido kawai suka zuba mata har zuwa lokacin data sulale ta kwanta,Aminatou cema ta miÆ™a hannu da sauri zata É—agata amma yayi saurin dakatar da ita. 

 

 

 

"Ahah ki barta kada ki tasheta,ba doguwar suma ta koma ba wannan bacci ne. Har yanzu jikinta bai gama Farkawa ba,dan haka dole saita samu hutu sosai kafin komai ya daidaita. Na samo wani maganin bari zan saka masa kafin daga bisani da Asuba mu É—au hanyar Daular Songhay in Allah ya yarda" 

 

 

 

"To bakomai,nagode fah yanda kake É—awainiya damu Allah yabaka kaima mai maka nagode sosai gashi mu ba Æ´aya face bayi" 

 

 

 

"Karki damu musulmi ai É—an uwan musulmi ne,duniyar tamuce ta sauya,har ana ganin bawa kaman ba mutum É—aya bane da masu Æ´an ci."  

 

 

 

 

 

Koda ya isa inda kamaluddeen yake kwance,É—aurin da yayi masa a wajen ciwon yafara kwancewa,Æ™ofar da kibiyar ta huda yayi baÆ™iƙƙirin ya kumbura,jijjiga kai yayi cikin halin tausayawa domin da ganin ciwon kasan duk wanda yake a jikinsa to yanashan wuya. 

 

 

 

Saida ya goge ruwan daya fito kafin ya É—auko wani Dakyakykyen maganin dayazo dashi ya manna masa a wajen,wata Æ™ara ya saki yana numfarfashi,amma bai daina danna maganin ba har saida ya tabbatar ya ratsa ciwon kana ya maida wani sabon tsumman ya É—aure.  

 

 

 

Duk abinda suke Aminatou tana kallonsu amma ta gagara Æ™arisawa wajen,domin bazata iya gani ba,hawaye kawai take gogewa daga nesa. 

 

 

 

Har baba yakub yazo zai fita sai kuma yace mata. 

 

 

 

"Kishirya muku kayanku dare yana rabawa biyu zamu fara tafiya,yakamata mu hanzarta,jinkirin mu zai iya sakawa dafin ya ratsa zuciyarsa,wannan makari ne nasaka masa ba lallai yaÉ—au dogon lokaci yana bashi kariya ba." 

 

 

 

Amsa masa tayi da to,da sauri kafin ta miÆ™e tafara haÉ—amusu kayansu.  

 

 

 

Har suka fito zuwa cikin jirgin ruwan Joda bata tashi ba,sai Aminatou ce ta É—auketa,shikuma yusha'u suka riÆ™o kamaluddeen shida baba yakub. 

 

 

 

Saida suka tabbatar sun gama É—aukar kayansu tass kafin suka since igiyar data riÆ™e jirgin a bakin ga'ba,kana suka nausa Arewa izuwa ga masarautar Songhay 

 

 

 

Sannu a hankali jirgin yafara tafiya a saman ruwan,saida suka É—anyi tafiya mai nisa sun daina ganin tsibirin da suka biyo kafin yafara Æ™ara gudu. 

 

 

 

Matsakaicin jirgi ne mai É—aki É—aya a tsakiya wanda zai É—auki mutum huÉ—u,sai kuma gefe da gefe inda mutane zasu zauna suyi fito idan igiyar ruwa tayi Æ™arfi. 

 

 

 

Joda da kamaluddeen ne a cikin É—akin,Aminatou tana tsaye a waje,yayinda su baba yakub ke Æ™oÆ™arin wajen ganin sun saka hancin jirgin a hanya. 

 

 

 

**Joda** 

 

 

 

Bude idona nayi,wannan karon banga rufin zana ba saidai na katako,kenan ba a inda nake É—azu ba nake a yanzu? Nayiwa kaina wannan tambayar. Tashi nayi zaune ina rarraba ido,jikina yamin nauyi dakyar yake bani haÉ—in kai wajen motsashi.waigawa gefena nayi na hango mutum a kwance a irin gadon katakon danake kai,kunnuwana suna jiyomin Æ™arar iska tana Æ™ugi irin wacce ake samu a kogi. Tashi nayi a hankali na nufi mutumin dayake kwancen Abah nane nagani,gefen kafaÉ—arsa a É—aure,mai ya sameshi haka? Bana tuno komai na rayuwata ta baya,fuska biyunnan kawai na tuna,Ummah da Abah. Wata Æ™ofa nagani hakan yasa naje nabuÉ—e,da tunanin kozai kaini waje inda wasu suke,domin idan kunne na ba Æ™arya yakemin ba ina jiyo alamar motsin mutane a wajen. 

 

 

 

Da farin sararin samaniya nayi arba,fararen tsuntsaye manya suna shawagi a cikinsa,gabana na kalla wanda bana ganin komai face zallan samaniyar wanda tayi kaman ta saƙƙo Æ™asa ta haÉ—u da ruwa. 

 

 

 

Toh mai muke a cikin kogi kuma,ban tuna inda muka fito ba,amma dai inaji a jikina cewar nayi wata rayuwar dole wacce ban tuna ba,tunda gani a tsaye kam ai dole saida nayi rayuwa kafin na iso yanda nake. 

 

 

 

Lissafi Æ™waÆ™walwata naji tana yi na yanayin sararin samaniyar,son gano wacce kusurwa iska take bi,sannan su kansu tsuntsayen dake shawagi wacce irin rayuwa suke gudanarwa,dannan wacce alÆ™ibla jirgin da muke ciki yakebi. Shin wannan wanne irin kwaÉ—ayine na neman ilimi danaji zuciyata da Æ™waÆ™walwata sun haÉ—u suna yi? 

 

 

 

"Joda Mashaallah Joda kin tashi" 

 

 

 

Inda naji sautin sunana yana tashi na kallah,Ummah ce garinya ban kulada ita ba tunda na fito daga cikin É—akin. Hankalina gabaÉ—aya ya tafi ga son sanin abinda yake zagaye dani. 

 

 

 

Kallon hannayen ta nayi wanda tarike nawa gamm a cikinsu kaman wanda idan tabuÉ—e ido bazata sake gani na ba na bace. 

 

 

 

Daga yanayin kallonta alamar akwai abinda yafaru kenan,inaso na tambayeta ko kuma nayi magana,amma sam nagagara cewa komai,badan ban iya maganar ba sai domin yadda fatar bakina tayimin nauyi,kenan na É—au wani lokaci a kwance. 

 

 

 

"Baba yakub zoka dubata dan Allah kaddai bayan tabin Æ™waÆ™walwa kwanciyar da tayi yasakata daina magana....." 

 

 

 

Cikin murya mai rauni tayi maganar....tabin Æ™waÆ™walwa ohh dama banida hankali,ko shiyasa waÉ—annan lissafen suke shigowa cikin kaina kai. Wani dattijo ne ya nufo mu,wanda buÉ—e idona na farko na ganshi,ban taba ganinsa ba sai yanzu mai ya haÉ—asu dasu ummah,ko ban tuna ba amma wani yanki na cikin kaina yana gwadamin ba'a nan muke rayuwa ba da,domin wannan ne karo na farko danaga wajennan. 

 

 

 

Ƙarisowa yayi inda muke ya zubamin ido,ganin kallon har hanji yakeyimin yasa na É—auke kaina ina kallon wani waje daban,bayan kaman wani lokaci ya sauÆ™e ajiyar zuciya kafin yace. 

 

 

 

"Abin akwai É—aure kai,kada kiyi mamakin jawabina amma da alamun komai yasameta a jejinnan ya kwantar da ita doguwar suma to kuwa yayi mata maganin gefen Æ™waÆ™walwarta daya shanye,domin idanuwanta basa É—auke da wani abu waishi wauta,da alama hasashena ya zama gaskiya,doguwar suman data shiga Æ™waÆ™walwarta ce take jinyar warkewa daga shanyewar da tayi. Amma kada mu yanke hukunci da wuri mu bari lokaci ya nuna mana dakansa." 

 

 

 

Duk wannan bayanin dayakeyi babu wanda bangane ba,amma kuma daga kallon fuskar umma alamun bata ganeba ko kuma mamakin hakan yahana ta gasgata bayaninnasa. 

 

 

 

Wani Æ™ugi cikina yakeyi,jiri yafara É—ibata kaman zan faÉ—i,saurin kama hannun umma nayi ina riÆ™e kaina. Ganin haka yasa wani matashi a gefe shiga cikin É—akin dana fito ya É—auko irin gorar ruwan da suka bani a tashina na farko,sannan da wani abu a nannaÉ—e cikin ganye. BuÉ—ewa nayi ina kallon abun,nakiyace da akayi ta da soyayyan gari da ruwan rake,sai kamshi take tun kafin nakai bakina. 

 

 

 

Gutsira nafarayi da sauri sauri kaman wani zai Æ™wace har na cinye dukka,sannan na bita da ruwan da umma ta miÆ™omin. 

 

 

 

Sai a lokacin nafara ganinsu garau,ashe tun da yunwa ce tahanani gani da kyau,ko kuma ba komai nake gani ba sai yanzu,domin ji nayi kaman an yayemin wani baÆ™in mayafi daga idona. Kuma bakina yayi fayau zan iya buÉ—eshi ba kaman É—azu ba. 

 

 

 

"Umma ina ne nan,mai yasamu Abah na naganshi a kwance kaman baya motsi,É—azu naji kuna maganar nayi doguwar suma,shin mai ya sameni nafaÉ—a doguwar suma. Wacece ni dana kasa tuna komai a rayuwata ta baya,iya fuskarku kaÉ—ai nake tunawa banda haka bana tuna komai sai tashina É—azu da kuma tashina a yanzu" 

 

 

 

Sakin baki ummah tayi saÆ™ale tana kallona,saikuma taja da baya kaÉ—an da alamar razani a fuskarta. Kaman taga wata sabuwar halitta. Ganin hakan bazai kaita ba bubbuga fuskarta tayi sanann ta murza idonta. 

 

 

 

"Wai ba mafarki nake bane,Joda meyasami maganarki da yanayinki,badan da kamanninki akan fuskarki ba,da kuma mu mukayi ta dakonki a gadon bayanmu da zance na ajiyeki a wani wajen na É—auko wata daban. Ikon Allah tsarki ya tabbata ga ubangiji. Baba yakub tabbas maganarka gaskiya ce, yanayinta da kuma maganar ta gabaÉ—aya ya sauya daga yanda take baya, wannan Jodar tawa mai lafiyace,wacce baza'a zagemin ita ba,wacce baza'a cutarmin da ita ba,kullum addu'ata tazamo Æ´a kamar kowacce,mai hankali,tunani dakuma basira,ba wawiya mai tabin hankali ba,wacce takasance abar cutarwa ga kowa ba. Allah ya karbamin addu'a ta,wacce tafidda tsammani da zan sameta saidai idan Allah ya ajiyemin ita sai gobe kiyama,sai gashi ashe ya amsa yah Allah,yah Allah yah Allah...." 

 

 

 

Rushewa tayi da kuka tareda zubewa a wajen tayi sujjada tana cigaba da kukan fuskarta na kan goshinta. 

 

 

 

Jikina ne dukka yayi sanyi,shin mai ya farune,wacce irin rayuwa iyayena suka fuskanta haka, meyasa na gagara tuna komai a ciki?  Tsugunnawa nayi tareda dafa ta a bayanta,É—agowa tayi jin hannuna ta rungumeni tsam a jikinta,har sannan bata daina sheshshekar kuka ba.  

 

 

 

Baba yakub ne yayi gyaran murya tareda cewa. 

 

 

 

"Kamata ki kaita É—aki,idan ta nutsu hankalinta ya kwanta zata baki dukkan wani labari dakikeson ji. Ki shiga da ruwan dayake gefenki wataÆ™ila zata buÆ™aceshi,sannan kibita a hankali domin taga rayuwa sosai" 

 

 

 

ÆŠaga masa kai nayi alamar na fahimta kafin na rike hannunta muka shiga É—akin. 

 

 

 

 

Bayan tagama bani labarin zuyawa nayi na kalli inda mahaifina yake kwance,hawayen dayake ta zurara tun É—azu da aka fara labarin ban share ba,su na samu damar saka hannu na sharesu yanzun. Muryarta na tsinkayo ta cigaba da magana. 

 

 

 

"To kinji abubuwan dasuka faru,karkiji babu daÉ—i domin baki tuna ba,dama ba abun daÉ—i bane dazaki tunashi,duk da cewa yana daga cikin wani tsagi na jarrabawar rayuwarki. Bansan wacce irin godiya zanyiwa ubangiji ba danayi arba dake kin warke kina cikin hankalin ki kaman sauran kowanne É—an adam mai lafiya. Yanzu burina bai wuce Abanki ya tashi ba na sanar dashi wannan daddaÉ—an labari,nasan zaifi kowa farin ciki da jinsa" 

 

 

 

Har taÆ™are bayanin nata ban kalleta ba idanuwana suna kan Jarumin mahaifinnawa,wanda nakeji a raina babu tamkarsa,lallai nayi sa'ar iyaye wanda suka zabi kare rayuwata ta hanyar saka su tasu rayuwar a haÉ—ari. Ni banida wani buri daya wuce naga ya tashi yana rayuwa cikin farin ciki da Æ™oshin lafiya. Sannan kuma nasakashi yin alfahari dani wanda bayyi ba a baya. 

 

 

 

Dare na uku yashiga mana a babban kogin muna tafiya,duniyar tayi tsit babu wannan Æ™arar tsuntsayen dasuke shawagi akan mu kullum daga gari ya waye. Sai taurari wanda kowacce ke takara wajen ganin ta Æ™yalla nata hasken a duhun samaniyar. 

 

 

 

Nafi minti goma ina kallonsu,wanda wannan shine nima kwanana na uku ina zuba musu ido. A gefen mu kuma yusha'u ne da Ummah suke fifita Kurfoti zasu dafa mana shayi. Wanda a yanda na kula alamun sun É—an samu jituwa da ummantawa. A bangare É—aya yana mata kallon tamkar babbar yayarsa,itama kuma kallon Æ™ani takeyi masa,wani zubin kuma idan an kalla tamkar É—a. 

 

 

 

Tunda na tashi daga suman danaji ana cewa nayin na samu kaina da sabon halin da banida shi a baya. Hankalina yafi karkata da abubuwan da suke kewaye dani fiyeda shiga shirgin mutune ko yaushe,indai ba abu yazama dole na shiga ba to nakan koma gefene nayi nazarin wani abun daban. Ji nake kaman rayuwar cikin jirgin tayi min kaÉ—an,Æ™waÆ™walwata ji nake kaman tanaso ta fice daga cikin keji ta shiga duniya nemo wani abun da bansanshi ba.  Hakanne yasa naga kaman mutanen jirgin sunayimin kallon miskila,ko kuma a kalam mafi daidaito ace marar magana. 

 

 

 

Hankalina ha 'ilau tafiya yayi kan baba yakub wanda yasaka hannunsa guda biyu sama suka bada Æ™ofa a tsakiya,saita wata tauraruwa yayi dake arewancin duniya ta yanda zata shiga tsakiyar Æ™ofar daya bayar a . Karkata hannunasa yayi a hankali zuwa Gabas maso arewan,kaman na wasu daÆ™iÆ™u sai ya ajiye hannunsa yana wani nazari da hannunsa. 

 

 

 

Karisawa nayi gefensa a hankali nayi magana,wanda saida ya É—an zabura,domin tunda nake bantaba tunkarar sa nayi masa magana ba. Saidai idan ya tambaye ni na bashi amsa,ko kuma in yayi magana na É—aga kai alamar naji. 

 

 

 

"Baba yakub shin menene matsayin wannan tauraron dayake arewancin sararin samaniya,baya motsawa sosai har gari ya waye,ba ya karkata yamma ko gabas saidai ya É—anyi Æ™asa kaÉ—an, ko yayi sama. Sannan wasu taurari ma wanda suke a sunkushe waje guda,a duk lokacin dazaka karkata jirgi,ko kuma an daÉ—e ba'a tuÆ™ashi ba sai ka saka hannunka inda suke na wani lokaci daga bisani saika gyara jirgin. Yawwa akwai wani ma wancan mai haske sosai,daga haskensa ya dusashe Ko ya bace saika tashemu nida umma muyi sallahr asuba. Akwai abubuwa da dama dakakeyi harma auna lokaci da tafiyar rana da kakeyi da inuwar tsinke......shin zaka sanar dani wanne ilimine wannan sannan kuma mai kake karanta a tareda su kuma taya kake ganewa?" 

 

 

 

Ba iya baba yakub kaÉ—ai ba,harma dasu Aminatou dake gefe dasu kaÉ—an suka tsaya suna saurarena dasuka ji ina magana saida suka sake baki da ido suna kallona. Shuru nayi na sunkuyar da ido,duk sai naji na tsargu da kallon dasukemin. Ko saboda da bahaka nake bane shiyasa sukemin wannan kallon mamakin. 

 

 

 

Amma zancen ba haka bane,hatta yusha'u da tun yana Æ™arami baba yakub yake tafiya dashi acikin teku bai taba lura da yanayin taurari ko kuma yanda ake amfani dasu ba. Sai ita wacce gabaÉ—aya kwananta uku a cikin jirgin,har ta kulada waÉ—annan tarin ilimummuka haka. 

 

 

 

Ganin wajen yayi shuru kowa yana kallona yasa baba Yakub barin wajen zuwa can inda hancin jirgin ruwan yake ya zauna. Juyowa yayi yakalleni tareda nunamin gefensa nazo na zauna. Banyi musu ba naje na zauna inda yace É—in. 

 

 

 

Kallona yayi na wasu sakwanni kafin yamaida kallonsa izuwa sararin samaniyar. 

 

 

 

"A gabaÉ—aya tsawon rayuwata nayita ne akan ruwa fiyeda doron Æ™asa,nayi tafiya da mutane da dama acikin ruwa bayan mahaifina ya turani neman ilimin gane hanyoyin garuruwa ta hanyar amfani da taurari. Hakanne yasa na tafi Æ™asar Fararen fata wanda sukeda ruwa manya manya na koyo ilimin gane hanya akan ruwa. Wannan ilimi dana samo ya siyamin daraja sosai,ciki kuwa harda nemana da akayi tayi akan nazama matuÆ™in manyan jirage na Æ™asar Songhay. Amma firr sainaÆ™i amincewa,domin ni babu abinda nake sha'awa kuma nake mafarki kamar rayuwar Æ´anci, sunyi ta bibiyar É—an uwana ganin yakasa shawo kaina yasa suka haÆ™ura. Nasan zakiyimin tambayar meyasa naÆ™i amincewa da wannan babbar dama?" 

 

 

 

Hakan kuwa ne a cikin raina,sai ya tari numfashina yayimin tambayar shi da kansa. 

 

 

 

"Mutanen gidan sarauta masu Æ™arfin mulki da iko sunada wani hali guda É—aya. A duk lokacin dasuka kalli wata baiwa a gareka wadda zatayi musu amfani,to zasu bibiyeka suyita Æ™wadaita maka dukiya da matsayi domin su jaka zuwa jikinsu,daga lokacin da suka kalli bakada wata damar sai tasu,ko kuma abinda suke nema a wajenka babu shi,to zasu Æ™asÆ™antar dakai su koreka,wanda hakan zaisa zuciyarka ta karye ka kasa amfanar da kanka da komai harka koma ga mahaccinka. Hakan shine yafaru da mahaifinmu a dalilin fikirarsa da ilimin sanin magunguna. Labarin da tsayi bazan iya sanar dake a yanxu ba. Shiyasa nazabi nayi rayuwata ni kaÉ—ai,nayi amfani da fikirata na nemi abinda zan ciyarda iyalina. Banason cutar da kowa saannan nima banason wani ya cutar dani ko ya dunga juyani a Æ™arÆ™ashinsa. 

 

 

 

Wannan labarin na zabi bakishine saboda jikina yabani rayuwarki bazata tsaya a iya waje É—aya ba Joda,saboda duk wanda Allah ya bashi kaifin hankali irinnaki to lallai zai jarrabeshi da abubuwa kala kala. Dan haka ki kulada duk abinda zakiyi,karki bawa mutane komai naki batareda kinsan waye su ba. Mutum yanada kaifi sosai dayafi tsinin takobi,kada ki zauna akai batareda kinsan dabarun yanda zakiyi bazai sokeki ba. Sannan idan kinada goma ki boye biyar ki nuna biyar. Wannan biyar É—in da kika boye zata iya yimiki amfani da lokacin da shi mai goman bashida ko sisi. Nasan kin fahimci maganganuna,koda baki fahimta a yanzu ba ki haddacesu zaki fahimta a gaba "