BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 6

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA❤* *Arewapen@ayshadansabo*

©️Ayshat Ɗansabo lemu✍🏻

*Free page 6*

Yau da yake Surayyah ba tada zuwa catering class,sai bata tashi da wuri ba sai around 11am.Wanka tayi ta kintsa kanta kafin ta fito ta nufi ɓangaren Babansu,domin tasan Sunday rana ce da ya ware yake zama a gida ya huta.In ka ga ya fita to ba nisa zai yi ba,za ka ga ya dawo gida.Da sallama ta sanya kanta cikin falon nasa,ta samesu a zaune Shi da Mum.Hakan ya sa ta ƙarisawa gabansa ta gaidashi,ya amsa cike da kulawa yana faɗin,

"Auta sai yanzu kike tashi sabida yau ba class kenan,wai ma sati nawa ya rage ne ku gama class ɗin?"

Surayyah ta saki smile tana faɗin."Saura one week ya rage Baba."

"To masha Allah yau sai ki shiga kitchen ai ki min Dambu da sauce,irin wanda kika gwada yi kwanaki,ya yi mini daɗi."

Baban ya ƙare maganar yana murmushi,ƙaunar Surayyah yake sosai a cikin Yaransa domin tana da nutsuwa daidai gwargwado.Kuma tana da gudun zuciyara sosai.Dariya Surayyah tayi tana faɗin."Tuh Baba za a yi maka,yanzu ina gama karyawa ma zan fara aikin."

"To madallah Auta,Allah Ya yi albarka."

A tare suka amsa da, "Ameen." Ita da Mum.Surayyah ta miƙe domin zuwa ta nemi abin karya kumallo.Har ta kai bakin ƙofar fita Baban nata yayi kiranta,ta dawo da baya tana komawa ta zauna lokacin da yake faɗin,

"Kin ga na manta,ɗazu mukai magana da Safiya akan Aliyu.Ban da abinki Surayyah,ai da tun farko da muke damunki da magana a kansa sai ki sanar da Mahaifiyarki irin BURIN da ke ZUCIYARsa a kanki.Ba abinda za ki ji kunya kiyi shiru bane,kin ga da kin sanar ni da kaina zan yi masa iyaka da ke.Ina tsoran yadda lalacewar samarin zamanin nan kullum yake daɗa yin gaba,daga yanzu kada ki sake yin shuru,duk wanda yazo gareki matuƙar kin fahimci manufarshi a kanki ba alkhairy bane,uwarki zabki ma bayani.Ita kuma idan ta sanar min sai na ɗauki mataki kinji ko? Sannan ina sake miki nasiha da kiji tsoran Allah,ki cigaba da kare mutuncinki na ƴa mace Surayyah.Ka da ki sake shaiɗan da shaiɗanun Samari suyi galaba a kanki,Allah Ya yi muku zaɓi na alkhairy,l.Shi kuma Allah Ya shiryashi,miye amfanin yin auren sha'awa,sam ban zaci haka daga Aliyu ba,yadda nake masa kallon Yaro mai hankali da nutsuwa."

Surayyah ta sadda kai ƙasa tana faɗin. "In Sha Allah Baba zan cigaba da kiyayewa. "

"Hakan yafi,sannan kuma kada ki manta ina nan ina lissafe.Da zaran lokaci yayi baki fito da miji ba,ni da kaina zan zaɓo wanda na yaba hankali da ɗabi'unsa na haɗaku ko a cikin Yaran abokaina ne."

Cewar Alhaji Mahmud yana tsareta da idanunsa.Surayyah ta sake duƙar da kai kirjinta na bugawa.Ganin ta kasa cewa komi yasa Baban nasu sallamarta,ta fice cikin sauri tana ji zuciyarta na jagulewa da ruɗani mai yawa. Koda ta nufi kitchen ta zubo abinda za ta ci haka ta dinga juyashi ta kasa cin abin kirki,daga ƙarshe ruwan tea kawai ta shanye ta nufi ɗakinta.Zama tayi bisa resting chair dake ɗakin tana mai dafe kanta da hannuwa biyu,yayin da zuciyarta ta cigaba da kai-kawo,kunnuwarta na amsa kuwwa da maganar Babanta wanda daga yanayin yadda yake furta kalamansa tasan babu alamun wasa ko sassauci.Domin shi mutum ne da baya magana biyu,tayi imanin kamar yadda yace idan lokacin yayi bata fiddo mijin ba zai haɗata ne da wanda yaso.

"Ya salam! "

Ta furta tana mai buɗe idanunta tare da miƙewa zuwa gaban mirror,sakamakon wayarta da ta jiyo tana vibrating.Ganin sunan Bro M yasa ta jan ƙaramin tsaki ta ɗaga call d'in.

Basu jima suna magana ba ta yanke wayar,ta hanyar sanar dashi cewa za ta shiga kitchen domin ɗaura ma Baba girki.Hakan yasa Mubarak haƙura ba don ransa ya so,ko ya gaji da jin sweet voice ɗinta ba.

Kitchen ta fice ta cidda Lami nata ƙoƙarin ɗaura girkin abincin rana,sosai ta ƙware a iya sarrafa girke-girke in ka ga Mum a kitchen to girkin Babansu za ta ɗaura.Shi ma idan Surayyah na skull ne,tunda ta gama ita ke yi sai yanzu da ta shiga catering class ne bata samun time ko da yaushe nayi masa,sai a ranakun da babu class ɗin wanda weekend ne kawai bata zuwa.

Cikin lokaci kaɗan Surayyah ta haɗa Dambun couscous ɗinta,wanda yaji zogale da gyaɗa.Ta zuba wadataccen kayan miya da albasa,ƙoƙarin haɗa sauce ɗin take inda za ta yi amfani da liver,Irish da kuma vegetables.Daga ƙarshe lemun pineapple ta haɗa da watermelon,sai ginger ta tace tare da zuba zuma bame yawa ba tasa a cikin fridge.Tuni kitchen ɗin ya gama cika da ƙamshi,har sai da Lami ta kasa daurewa ta shiga koɗa kyawun da dambun yayi tun a ido ma kafin akai baki.Ita dai Surayyah murmushi kawai take saki tana zubawa Baban a cikin kula.ɓangarensa takai komi ta shirya bisa table dake tsakiyar falon,Shi sam baya hawa dining yaci abinci shi yasa ma babu shi a ɗakin.Su ma sabo da cin abinci a ƙasa yasa dining ɗin dake ɗakin Mum ya zama hoto,domin basa hawa su ci abinci sai idan anyi baƙi masu ra'ayin hawa nan su ci abinci.

Albarka yake ta sa mata wanda hakan ya haifar mata da farin ciki sosai,koda ta koma ɗaki toilet ta shiga domin ɗauro alwalar Sallar Azuhur.Tana idar da Sallah kiran Busheera na shigowa wayarta,ta ɗauka tana faɗin.

"Sis ya kike? Wannan kira da tsakar rana haka."

Banji me Busheera ɗin tace ba,sai amsar da Surayyah ta bata tana faɗin. "Haka yace miki? To sai kin zo ɗin,ki zo min da abin daɗi ta wajena."

Daga haka ta yanke kiran tana sakin murmushi.

Busheera cousine sister ɗinta ce, Mamarta ciki ɗaya suka fito da Baban su Surayyah.

**********

Misalin ƙarfe hudu na yamma sai ga Busheera tazo gidan su Surryn,Surayyah ta fito suka rungume juna kafin ta ja hannun Busheera zuwa ɗakinta.Gidan ita kaɗai ce Mum ta fita wani suna ta dawo,zama Busheera tayi a bakin gado tana duban Surayyah take faɗin.

"Haba kice su Ya Mubarak anga kayan alatu na sake tunbatsa dole a rikice,a fara kurin cewa auren zumunci ake so.Kinga yadda kike sake wani kyau da fresh ne Sis,dama ashe skull ke hana aga fresh ɗinki kullum kana yawo a rana,amma yanzu kinga yadda kika koma Surry,gaskiya dole ki yi ta gwara kan ƴan maza hegu."

Yadda Busheera ta ƙarishe maganar cike da shaƙiyanci yasa Surayyah sakin dariya tana faɗin."Kai,Busheera wallahi baki da dama,amma wai tsaya. Shi Ya Mubarak ɗin ne ya fesa miki cewa yana sona?"

Busheera ta amsa da. "Yes Shi Ya sanar dani ɗazu da Ya je gidanmu,shine abin ya ban mamaki nace yaushe har kuka ƙulle daga dawowansa har ya fara san naki,bayan ke kuma nasan yadda kika tsani ayi miki zancen auren zumunci.Shi yasa nace bari in wanko ƙafata inzo inji gaskiyar zance,ko ɗan fresh ɗin da Ya yi ne ya sake zama ajebo ya ruɗeki?"

Sosai ta ba Surayyah dariya,ta shiga ƙyalƙyalashi,sai da tayi mai isarta kafin ta kaiwa Busheera maka tana faɗin. "Uban fresh ne shegiya mai abin dariya,wallahi Busheera Ya Mubarak shirmensa kawai yake."

Nan ta kwashe yadda suka yi jiya ta sanar mata,ta ƙare maganar da faɗin. "Wallahi Busheera bani son auren zumunci,ke ni gaba ɗaya ma maza tsoro suke bani da ita kanta soyayyar.Duk wanda yazo da zaran ka gama bashi Zuciyarka ya fahimci ka fara sonsa,daga ƙarshe sai ka gano ashe akwai BURIN da ya ɓoye a cikin zuciyarsa a kanka."

Ta ƙare kalamanta tana jan ƙaramin tsaki. Busheera ta gyara zama tana faɗin."Hmm! Ke dai bari ƴar Uwa,ni kaina soyayya ta fara fice min akai,duk rabin mazan dake tururuwa a kaina duk rabin su bada aure suke zuwa ba,suna da wani BURIN ZUCIYARsu ne na daban a kanka,a gida aita matsa maka kaƙi fidda miji alhali ba a san cakwakiyar fama da Samarin da kake,kana ƙoƙarin fidda na gari ka aura din ba.Wai nikam ina Aliyu ne Surry? Yadda ya mato a kanki wallahi har tausayi yake bani."

Busheera ta ƙare maganar tana jefa ma Surry harara.Surayyah ta kuma jan tsaki tana warware ma Busheera duk abinda ke tsakaninta da Aliyu,da irin BURIN ZUCIYARsa a kanta.Ta ƙare maganar da faɗin."Busheera Aliyu jikina yake so,duk wannan rawan ƙafar da yake nunawa a kaina ba saboda Allah bane,ko don yana mini so irin na aure na tsakani da Allah.Yana yi ne don ya cika BURIN ZUCIYARsa,shiyasa na daɗe da cireshi a cikin zuciyata.Shi da Nas na sosu Busheera, amma sai ya kasance duk abu ɗaya suke mawa jikina su ke so ba ni ba.Ko sun aureni auren kashe sha'awa ne za su yi domin cika BURINsu,duk Namijin da zai nuna yana son wani abu na jikinki tun a waje wallahi ba ke yake so ba,da zarar ya samu abinda yake so za ki sha mamaki.Shiyasa ba zan taɓa iya auren duk Namijin da ya fara nuna mini jikina yake so ba."

Surayyah ta ƙare maganar cikin rawan murya,sabida yadda abin ke matuƙar taɓa zuciyarta.Sosai take jin ciwon yadda maza da yawa da suka zo gareta,kuma duk BURIN ZUCIYARsu iri ɗaya ne a kanta.Busheera ta saki tsaki cike da takaici itama take faɗin,

"Allah dai ya cigaba da tsare mana mutuncinmu Sis,Ya yi mana zaɓi Nagari mafi alkhairy.Amma abin akwai ciwo,yanzu ni ina ga ki bawa Ya Mubarak dama,Shi kuma ki ga da wanne yazo? Idan har da gaske son ki yake tsakani da Allah,ina ga gara ki amshesa ku yi aurenku.Da a ce Baba ya zaɓo miki wanda baki sani ba ya haɗaku aure,Surry ni banga aibun auren zumunci ba sam.Matuƙar akwai kyakykyawar fahimta da haɗin kai na Iyaye,sannan kuma kune kuka haɗa kanku kuna son juna,amma ki zauna kiyi nazari dai."

Busheera ta ƙare maganar tana duban Surayyah cikin ido.Yayin da Surry ta sauke ajiyar zuciya maganganun Busheera na zama a cikin kanta sosai.Cikin sanyin murya ta furta, "Hakane kuma Sis,ke ma kin zo da magana abin dubawa.Zan yi tunani tare da bashi dama,da kuma yin gwaji a kansa.Amma ina so wannan maganar ya tsaya iya ni da ke,sam bani son asan da maganar Mubarak ya fara cewa yana so na.Shi ma kuma zan kwaɓeshi har zuwa lokacin da zan fahimci wani irin so yake min."

"Tabbas kina da gaskiya Surry,gara amma kiyi saurin kwaɓarsa,don sarai za ki ji maganar ya fara zaga dangi,wasu ma ɗauka za su yi cewa har kun daidaita kanku ne.Allah dai ya shige mana gaba."

Cewan Busheera. Surayyah ta amsa da, "Ameen. " Tana mai tashi ta nufi kitchen domin samowa Busheera ɗan abin kaiwa baka.Sai wajen ƙarfe shida Busheera tayi niyyar tafiya gida,Surayyah ta raka ta har bakin gate sukai sallama da juna.Ta juyo zuwa cikin gidan tana juya shawarar da Busheera ta bata a cikin zuciyarta,tare da jin ta gamsu da shawarar Busheerar sosai.

⚡⚡⚡⚡⚡

*KADUNA*

"Wai Abdallah har yanzu kana nufin baka cire Yarinyar nan a cikin ranka ba? Watanni kusan huɗu kenan fa amma har yau kace baka sake ganin koda mai kama da ita ba.Dallah! Mallam in za ka manta da ita ka zaɓi macen aure ka manta,ga mata nan birjik kuma haɗaɗɗun ƴan shila sai wacce ka darza.Za ka tsaya kana bulayin neman Yarinyar da kai wa gani ɗaya,tana can tana rayuwarta bata ma san kana yi..... "

"Enough! Rayyan,haba wannan irin zuba haka.Don Allah idan ba za ka min addu'a Allah sake haɗani da pretty ba,to gara kaja bakinka kai shuru.Ni ita na gani ina so,kuma itace BURIN ZUCIYAta.Don haka addu'a kawai nake so daga gareka."

Cewar Abdallah da ya katse Rayyan da tsubarararsa,Yana zabga masa harara.Hakan yasa Rayyan sakin dariya yana faɗin,"Afuwan ɗan gatan Hajiya."

Wani hararar Abdallah ya kuma aikawa Rayyan ɗin,yana maida hankalinsa kan system ɗin da yake aiki da ita.Hakan da Rayyan ya gani ya sashi miƙewa domin tafiya,don yasan tunda Abdallah Yai irin wannan ɗauke kan,to bazai kuma bi ta kansa ba.

"Afuwan na pretty ni zan wuce,Allah bayyana mana pretty mu sha biki."

Rayyan ya faɗi cike da neman magana,amma sai Abdallah Yai banza dashi ko ɗagowa ma ya dubi Rayyan ɗin bai yi ba.Hakan yasa Rayyan ficewa yana dariya,domin ya riga ya saba da halin mutumin nashi,miskili ne idan bai so magana ba.

Rayyan na fita bada jimawa ba ya rufe system ɗin ya shige bedroom ɗinsa,wanka ya shiga ya fito ya kintsa kansa cikin ƙananun kaya sai tashin ƙamshin mai daɗi yake.Wayoyinsa da mukullin motarsa ya kwasa,ya fito daga ɓangaren nasa bayan ya kulle ƙofar falonsa. Kai tsaye wajen rumfar adana motocin gidan ya nufa,motarsa ya shiga domin barin gidan.Kuma Mangal plaza nan ne wajen da zuciyarsa ke kwaɗaitar dashi ya fara zuwa,wai ko zai sake ganinta..........✍🏻