BARRISTER SUHAIL

52

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️-----52

Cikin nutsuwa Suhail ya ci gaba da tuƙi, idanunsa na kan hanya amma zuciyarsa na wani waje dabam

a haka su ƙara sa gida 

Zeenah na zaune a falo hannun ta na fitar da jini jennifer na tsaye gefen ta ta ƙoƙarin yi mata dressing a ciwon da taji amman ta ƙi a haka suka shigo suka same ta tun daga valcony Suhail ya jiyo sautin kukan zeenah da sauri ya shigo Dakin suka same ta  a wannan yanayin 

ya kalli jennifer ya ce"miya sameta"
"Sir… na tarar da ita a kitchen tana ƙoƙarin yanke jijiyar hannunta da wuƙa Na yi ƙoƙarin ƙwace mata amma ta ƙi, har ma ta yanke ni a hannu"
ta ida fada tana nunawa Suhail ciwon da zeenah tayi mata 

hannun sa ya sa ya dafe inda jinin ke fita cikin idanun tausayi ya dubi zeena da Idanun ta har sun kumbura sakamakon kukan da ta wuni tana yi ya ce"miyasa da hankali zaki jima kanki ciwo"

fizge hannunta tayi ta ce"Suhail leave duk ma halin da na shiga ba kai kaja ba ko kashe kaina nayi wannan ruwa na ne kaje chan wajen matar da kafi so nima ka kyaleni"

Iman ta girgiza kai a zuciyarta Tana tausaya wa Zeenah fiye da yadda ta yi fushi da ita Ta fahimci cewa tsananin kishi da rashin kwanciyar hankali sun fara rinjayar rayuwarta Sai dai ta yi addu’a kada wannan ya kai ta ga aikata abin da za ta yi nadama ba shakka idan har ta cigaba da haka wata rana zata iya kashe kanta

Zeenah ta tuna da lokacin da Suhail ya shafe sama da wata biyu a ɗakinta bayan aurensu

A lokacin ba ta taɓa tunanin akwai ranar da zai sake kallon wata mace da irin kulawar da yake nuna wa Iman ba 

Suhail ya dubi jennifer ya ce"kawo min first aid box"

"okay sir"

ya kalli zeenah ya ce"ko kina fushi dani bazan zuba ido jini na fita daga jikin ki ba"

ta dago idanunta da sukayi jajir  ta ce"yanzu ka tuna dani"

bashi da abinda zai zai ce mata amsar akwatin yayi daga hannun jennifer ya so yi mata dressing din bayan ya gama wanke mata ciwon da sprit ya nade hannun da bandage 

ita kadai tasan azabar da take ji Suhail ya kai dubansa gare ta da Idanun tausayi yake kallon zeenah ganin yadda take ƙoƙarin halaka kanta akan kishi 

ya kalli jennifer ya ce"make sure kin bata magani ta sha idan jinin bai tsaya ba sai mu kaita Asibiti"

yana gama fadar haka ya nufi Dakin sa zeenah na binsa da kallo har bace

wani sabon kuka ya kwace mata

jennifer keta aikin lallashin ta bayan ta bata maganin ta sha ta maida 

iman na shiga daki ta soma cire kayan jikin ta wanka tayi ta ɗora alwala ta gabatar da Sallar la'asar 

hannu ta daga sama tayi wa suhail addu'a Allah ya bashi ikon gano mai laifin dan har ranta tana ji ba Amina tayi kisan nan ba 

suhail ma ta bangaren haka ne sallah yayi ya soma hada files din amina waje guda dan gobe laraba ne za'a cigaba da sauraren case din


Salisu ne zaune Dakin mahaifiyar sa yana busar taba kallo ɗaya zaka masa kasan baya cikin hayyacin sa gaba daya bashi da maraba da dan ta adda sanye yake da singlet hakan ya bayyanar da damtsen hannun sa dake kulle da laƴu yana shan tabar yana fitar da hayakin ransa a bace 

jaru wato mahaifiyar sa ta ce"Ulu yanzu ya kake ganin za'ayi,tun farko sai da na gargaɗe ka akan haka idan ma kayi hakuri duka kwana nawa ya rage wannan tsohon ya wuce amman da yake baka jin magana sai da ka aikata Abinda kayi niyyah"

"kinga tsohuwa nifa bazan zuba ido ina gani tsohon nan yana rayuwa ki duba kiga ya riƙe komai ba wanda zai kalle mu ya ce yaransa ne duk ya barmu talauci ya samu a gaba Yanzu da ya gilma zamu ci Dukiyar mu hankali kwace muji dadi har ma mu jiya ma wasu,ita ma wachan bussasar ta gama zaman gidan dan kanden ta fito mu  in aure ta dan ko an tashi rabon gado inaso ta fado a shiyata"

Salisu ya barke da dariyar mugunta

jaru ta ce"kai banda Rashin hankali ina ka taɓa ganin anyi rabon gado da matar uba"

"idan ma ba'ayi za'a fara ta kaina Ko shekaru nawa aka yanke mata, zan jira ta fito Ni zan aure ta, dukiyar gidan nan kuma ta dawo hannuna inci kare na babu babbaka"

anan jaru ta tashi ta barsa tana fita ta gamu da samaila kannen 
 salisu amman ba ita ta hafe sa mamar sa shi kadai ta haifa saba yana laɓe jikin taga yana sauraren gaba daya hirar da suke tana  sa ta koma ta kira Salisu yazo taga Sama'ila yana laɓe kuma tana da tabbacin yaji duk Abinda suke faɗa

da sauri ya saki sigarin dake hannun sa ya ce"jar uba yana ina Sama'ilan"

ta nuna masa hanyar da yabi salisu ya bi bayan sa da gudu amman cikin Rashin Sa'a ko mai kama dashi bai gani ba 

haka ya dawo yana haƙi ya zube a gaban Dakin jaru ya manta rabon da yayi irin wannan gudun a Rayuwar sa  

jaru ta ce"ka same sa kuwa"


"ina fa,ke da kika san shegen gudu irin na yaron nan Shiyasa bana so muna irin wannan zatuttukan a gidan nan ga irin ta nan yaron nan gaba daya yaji sirrin mu"

jaru ta ce"ulu zama ba naka ba naka bane ya zama dole kaje ka kawo Sama'ila a raye ko gawar sa "

tashi yayi ta sake fita a karo na biyu 

haka ya wuni yana zagayen garin tsauni har dare ba tare daya samu samaila ba har ya gaji ya dawo gida

daren Ranar yadda jaru da salisu suka ga dare haka suka ga Rana sun tabbatar da kashin su ya gama bushewa babu Abinda zai hana Sama'ila ya tona masu Asiri

dan daman gaba daya gidan basa kaunar sa shine mutun ɗaya daya  fitar da zakkah cikin ahalin Alhaji barau hakan yasa yake yawan jansa a jikin sa  tare da nuna masa duk wata kaddara daya Mallaka babu abinda Sama'ila bai sani game da Dukiyar mahaifinsa sabanin sauran yara da sai sata tamkar bera baida damar da zai shigo da kuɗi duk ƙankantar sai sun sace ba mazan ba matan ba 

hakan yasa jaru ko Abinci ta girka bata ba shi sai bayan auro Amina take zuba masa idan ta dafa hakan yasa yake jin ta a zuciyar sa ya shaku da ita fiye da kowa a gidan haka itama ta ɓangaren ta shi kadai ta isa dashi a gidan ko ta rasa dan aike sai ta jira Sama'ila ya dawo yana  kokarin bata girman a Matsayin ta na matar Mahaifin sa duk yawan shekarun daya bata dan Gaba Amina shekarun sha takwai a duniya shu kuma yafi Shekara Ashirin da ukku

kuma shi kadai yasan da zuwan ta asibiti dan ta faɗa masa shine ma ya bata kuɗi a kudin da Mahaifin sa ke bashi idan an tashi daga kasuwa ranar da aka kashe Alhaji barau yasan ba Amina bace tayi kisan amman bashi da wata hujja tun a ranar ya ƙudiri aniyar sai ya gano duk wani mai hannu a kisan mahaifinsa

tun daga ya saka ido a gidan ranar idan ulu ya shiga dakin Mahaifiyar sa yakan je ya laɓe yaji abinda suke tattauna har zuwa yau sa suka gansa 

yana fita bai zarce ko ina ba sai garin da mahaifiyarsa ke aure tafiya ce mai nisa tsakanin su da garin haka ya tafi a kafa dan baya son kowa yasan ina ya tafi 

gashi babu wanda yasan sa garin da take aure a yanzu bare ayi tunanin yana chan cikin Sa'a ya shiga Garin babu kowa kansacewar dare ya fara yi babu wanda yaga shigar sa



kuyi haƙuri da wannan idan na samu yadda nake so in sha Allah gobe zan maku page biyu 

like 
share 
comment