53
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
NOT EDITED❌❌❌
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----53
Cikin dare Sama’ila ya taka a hankali har ya isa ƙofar wani ƙaramin gida da aka yi da tubali
sai biyu ya bugi kofar daga cikin wata murya aka ce "waye" Sama'ila ya ce"ni ne mama" da sauri ta buɗe kofar jin murya danta
da ganin ta zaro ido "Sama'ila daga ina kake cikin daren nan"
mama salisu ne da jaru zasu kashe ni ki taimaka min
gabanta ya fadi
taja shi ciki Sannan ta rufe kofar ra zauna dashi a tsakar gida ta kawo masa ruwa sai da yakusa shanye kwarya gida ya ƙwaso ƙishi
sai ta jira ya nutsu ta ce"Sama'ila mi ka musu zasu kashe ka"
ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce"mama saboda naji sirrin su"
"sirri kuma"
kai ya gyada mata ya ce"mama ba Aunty Amina bace ta kashe baba salisu ne da baba jaru"
da sauri ta miƙe tsaye cikin firgici ta ce"me kake nufi"
"mama naji komai da kunnena"
nan ya soma labarta mata komai kamar yadda yaji tattaunawar jaru da salisu kalmomin na fita daga bakin sa daya bayan daya har sai ya ƙarshe
dafe kanta tayi tana furta"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un" cikin rawar murya
Sama'ila ya ce"baba jaru ta ganni lokacin da nake sauraren su shine ta sa Salisu ya biyo ni nima ya kashe ni"
da sauri ta rungume masa a cikin ta ce"baza ka kara komawa gidan nan ba tun farko ba'a san raina na barka sai dai ba yadda zanyi mahaifin yaƙi yarda ka biyo ni"
kallon ta yayi ya ce"Amman mama Amina fa ba ita ta kashe baba ba"
"na sani Sama'ila a yadda kake gaya min kirkin nasan bazata taɓa aika hakan ba"
Sama'ila ya ce"mama inaso na taimake ta"
kallon sa tayi ta ce"Sama'ila ina tsoro kawai ka bar maganar nan bana so ka tona masu asiri su kashe min kai tun kai kadai ne dan da Allah ya bani kana ganin har yanzu ban kara haihuwa ba ka rufa min Asiri kai kashiga komar su su hallaka min"
hawaye ya soma saukowa daga idanun ta Sama'ila ya fara share mata ya ce"in sha Allah mama ba Abinda suka isa sumin tunda babu wanda yasan inda nake a cikin su"
tashi tayi ta dauko masa tuwo a daki ta ajiye masa yana ci tana kallon sa ji take kamar ta bashi a baki a yadda take jin kaunar dan nata a haka har mijin ya dawo ya same su
yaji daɗin ganin Sama'ila jin sa yake tamkar dan da ya haifa,tun tuni yake so ya dawo wajen ya cigaba da kula dashi amman Alhaji barau ya hana
nan ya soma tambayar ba'asin Abinda ya kawo sa matarsa ta kwashe komai ta fada masa ya jima yana mamaki ko maganar
bayan ta gama ta roki alfarma ya bar Sama'ila har zuwa lokacin da komai zai daidata ya ce"bakomai shima Sama'ila ɗa ne a wajen sa"
Iman na zaune a daki waya take da Ammi cike da jindadi abinda suke tattauna Ammi ke fada an sa auren yaya Mubarak watani ukku masu zuwa
iman keta murna ko ranar da aka daura auren ta da Suhail batayi Wannan farin cikin ba
ta ce"Ammi Allah ya sanya Alkairi ya kaimu Lokacin"
har sha daya na dare suka kai suna waya da Ammi daga bisani tayi mata sallama ta kashe wayar
tayi kokarin kiran Mubarak amman taga dare yayi hakan yasa ta tura masa da massage na fatan Alkairi a cewar gobe zata kira sa
Washe gari tun kafin fitowar alfijir, Suhail ya gama shiryawa cikin bakar suit ɗinsa, ya ɗauki files ɗin Amina ya saka a cikin briefcase ya shirya komai ya fito
Yana fitowa daga ɗaki ya tarar da Iman ta riga ta shirya masa breakfast akan dining
murmushi iman ba ƙaramin mahimmanci ta baiwa case din Amina ba
serving dinsa tayi ya soma cin abinci bayan ya gama ta rako sa har ƙasa tare da masa fatan samun nasara a wannan case din
a daidai lokacin zeenah ke saukoa daga upstair hannunta daure da bandage Suhail gaba daya ya manta da ciwon da zeenah taji idanunta sun kumbura sakamakon kukan da ta kwana tana yi ga wani matsanancin ciwon mara daya dame ta kuma tayi kanta Alƙawarin baza ta kara neman Suhail ba matukar bashi ne ya nema taba dan ta lura Yawan neman sa ta take babu abinda yake karasa face raini
hakan yasa ta kwana tana juyi da shan lipton
Suhail ya dube ta
"zeenah ya jikin"
a sanyaye ta ce
"da sauki"
bai karawa cewa komai ba ya dauki makullin motar da ya fita
a wani bangare kuwa
dr hafiz ya kasa tsaye ya kasa zaune tun bayan barin Barrister suhail daga office din sa
wayar sa ce ta yi kara ganin ɓakuwar lamba yasa ya daga murya da yaji ta kara daga masa hankalin sa Barrister suhail da kyar suka gaisa
Suhail yayi murmushi ya ce"dr hafiz nasan warhaka hankalin na nan a tashe to ina so ka sani ni banzan tona naka asiri ba sai da zan baka shawara wannan hanyar da ka dauko tayi lalata da patient a Matsayin na Babban likita ba dabi'a bace mai kyau nasan kana da mata kana da ƙanwa bazaka so kayi a'wani yayi lalata dasu ba abu na gaba kuma flip na cctv already yana hannuna kar ka damu da taya na same sa dan zaka ba kanka wahala ne kawai abu na ƙarshen kuma iya abinda ya danganci case nan kawai zanyi representing a kotu naka video kuma already nasa a ciresa a ciii ka ƙiyaye gaba dr hafiz"
katse wayar yayi zufa ta ko ina ke ketowa dr hafiz bai taba jin kunyar abinda ya aikata irin yau ba ya saba da wannan badaƙalar Amman iya kunyar ta da yayi yau kadai ya isa ya tuba ya komaga Allah
handchiep yasa ya soma goge fuskar sa tabbas ya yarda da Suhail mutun kirki ne da hannun wani wannan clip ya faɗa ya tabbatar har Social media sai samu wanda ya kaisa madallah yayi ya gode wa Allah daya wannan gangarumin rufin asirin daya sake masa tabbas Allah mai rahama ne mai jin kan bawan sa duk Abinda ya jima yana aikatawa Allah ya cigaba da rufa masa asiri a hankali ya furta "astagafirrullah Allah na tuba"
Doctor Hafiz ya daɗe zaune a office ɗinsa yana kallon wayar hannunsa.
A karon farko cikin shekaru da dama, ya ji nauyin zunubin da yake aikatawa
Ya buɗe drawer ɗin teburinsa ya ciro kwalin sigari, ya ɗan kalle shi na wasu daƙiƙu kafin ya murƙushe shi ya jefa a kwandon shara
yayi wa kansa Alƙawarin daga yau duk wasu halaye marrasa kyau ya barranta kan sa dasu haƙiƙa Wannan dama da Allah ya bashi domin gyara halayensa sa
amman a yau yayi taubatan nasuha baizai kara jefa kansa cikin mummunan hali ba