4. Fargaba
Sun tsinci kansu cikin wannan yanayi na ɗan lokaci. Maryama ta sake sauƙe kanta ƙasa tana ganin inda coffee ya zube a jikinsa.
"Don Allah kayi haƙuri... I'm sorry."
Ya buɗe idanunsa daga runtse su daya yi, ya ɗaga gira tare da numfasawa.
Raɗaɗin ƙuna sai ƙaruwa yakeyi domin coffee ɗin yayi zafi sosai. Ya buɗe baki da niyyar magana, amma ya rasa kalmar da zata fara fitowa.
"Ya Najib!"
Ya mayar da kallon sa zuwa gefe. Hasina ce ke tahowa inda suke da fuskar damuwa.
"Maryama! Subahanallahi, meya faru haka?"
Hasina ta janyo Maryama kusa da ita tare da riƙo gefen mayafin ta da ya ɓaci da ruwan coffee. Ta kalli yayanta taga shima yasha rabon ruwan coffee a ƙasan rigar sa, sannan ta kai duban ta inda mug da coffee ɗin suka tarwatse kasan floor.
"Maryama, are you okay?"
Maryama ta gyaɗa mata kai. "I am fine..."
"Calm down Hasina. No body is hurt. Karo mukayi da juna shine hakan ta faru." Najib yayi magana a karo na farko.
Ya salam!
Maryama taji kamar ta narke tabi ƙasa.
Muryar shi akwai nauyin ji,
low pitch,
so calm...
Najib ya sake duban Maryama dake kusa da Hasina.
"Kayi haƙuri, ban lura bane... I'm so sorry. You must be hurting."
Maryama ta sake bashi haƙuri a karo na biyu.
Tabbas tasan ya ji ciwo. Yanayin fuskarsa ya tabbatar mata da hakan a lokacin da coffee ɗin ya zuba a jikinsa.
Najib yace, "Ba komai, it was an accident."
Hasina ta kwala wa masu aikin dake kusa ƙira da su gyara gurin.
"Ya Najib, sorry about your coffee. Zan haɗo maka wani yanzu na kawo maka. Give me your shirt also. Ni zan wanke maka da kaina."
"Just leave it Hasina, bana jin sha kuma yanzu. Batun shirt ɗina kuma ki barshi. Karki damu i will take care if it."
Hasina ta ɗan tsaya kamar mai nazari sannan tace, "Toh shikenan ya Najib."
Ta kalli Maryama dake kusa da ita. Kunya da fargaban abin da ya faru ya rufe ta. Hasina ta riƙe hannun ta data gane yanayin da take ciki.
"Duk da dai it's a bad timing, ya Najib, I'm introducing you to my dear friend." Ta saki murmushi.
"Ya Najib, ka tuna Maryama da nake baka labarin ta a waya? Ai ita ce wannan.
Maryama, this is my one and only ya Najib da nake baki labarin shi a school. Wanted to introduce you two a wajen dinner, but dana duba ka ban ganka ba."
Mamaki ne ya sake nunawa a fuskar Maryama a lokacin da ta sake haɗa ido da Najib. Shima fuskan shi yaso ya nuna mamaki, amma cikin ƙanƙanin lokaci alamun ya bace.
Ashe sunan shi Najib?
Ashe yayan Hasina ne?
Ashe shi ne wanda ta daɗe tana jin labarin sa?
Maryama ta ɗanyi jim sannan tayi murmushi.
"Ina wuni ya Najib?"
Cikin sakin fuska ya amsa mata.
"Lafiya Maryama. Hasina tana yawan bani labarin ki."
Najib ya matsa daf inda wayar Maryama ta faɗi. Ya duƙa ya ɗauki wayar sannan ya miƙa mata. Cikin jin kunya Maryama ta karɓa.
"Thank you..." Maryama tace.
Idanun sa ya sauƙar cikin nata ba tare da ya furta komai ba. Ita ma kollon shi tayi na ƙanƙanin lokaci sannan ta duƙar da kai.
Duk abinda ke faruwa Hasina na tsaye a gurin.
Fuskar ta na ɗauke da murmushi haɗe da mamakin ganin yayanta na abu kamar bashi ba.
Hasina ta lumshe idanu, ta kai kallon ta gefe guda kamar mai nazari, tana son gano gaskiyar lamarin.
Najib ya mayar da kallon sa zuwa kan Hasina. "You should go. Kin bar mutane a ƙasa."
Hasina ta kalli Maryama.
"Kizo mu sauƙa." Maryama ta gyaɗa mata kai sannan suka tafi tare.
Najib ya kalli tafiyar su cikin sakan ƙalilan yana wani nazari sannan ya ƙarasa ɗakin sa.
Hasina ta ɗauki hotuna masu kyau da camera ɗinta data, sannan sukayi hotuna a wayar Maryama.
Ana ta shagali ana jin daɗi, amma zuciyar Maryama sai yaudararta take yi da tunanin karon da tayi da Najib.
An gama birthday celebration kowa ya tafi sai ya rage saura Maryama. Hakan ya faru ne dalilin hanata tafiya da Hasina tayi da wuri.
Maryama tayi ƙoƙarin tafiya gida kafin magariba amma sai da Hasina ta shawo kanta da cewa ta tsaya tayi sallah kafin ta wuce gida.
"Tunda kinyi sallah kawai ki tsaya muci abinci sannan ki tafi." Hasina ce ke magana a lokacin da take faman goge makeup ɗin fuskarta da wipes a gaban dressing mirror a cikin ɗakin ta.
"Hasina akwai ki da wayo. Wasa wasa kinsa na daɗe ban tafi ba." Sukayi dariya.
"Ummi fa? Ban ganta ba tunda nazo."
Hasina ta ɗago kai. "Tana nan fa bata fito bane kawai don itama bata son hayaniya. Kinsan fa birthday ɗinnan da ƙyar suka yarda nayi? Basa so, tun ba ya Najib bama. Da ƙyar na samu ya barni."
Jin sunan Najib yasa ta kasa cewa komai. Har yanzu tana cikin mamakin yadda ta sake ganin shi.
"Ina zuwa, bari nayi alwala. Kafin ki tafi zamu je ki gaisa da ummi ai."
Hasina ta shige bathroom ta ɗauro alwala. Maryama ta kira gida kada suju shiru, tana nan tafe bada jimawa ba.
Tana gama wayan ta shiga dailing layin driver, amma bai shiga ba. Ta sake gwadawa sai taji ana ce mata not reachable. Haka ta sake gwadawa karo na uku kiran yaƙi tafiya. Sai ta yanke shawaran zata shiga taxi idan ta tashi komawa gida.
****
Bayan sun ci abinci Hasina ta kai Maryama suka gaisa da mahaifiyarta Hajiya Bilkisu, wanda ake kira da Ummi, sannan Maryama tace zata wuce gida kada dare ya mata sosai.
"Za'a zo ɗaukan ki ne?" Hasina ta tambaye ta.
"A'a, layin drivern baya shiga. Nayi ta trying ɗazu amma not reachable. So ina ganin zan shiga taxi kawai."
Hasina ta dube ta cikin rashin yarda. "Haba ke kuwa shine baki faɗamin ba?"
Maryama tace, "To ai ina ganin bazan samu wata matsala ba na neman taxi shiyasa ban sanar dake ba."
Hajiya Bilkisu tace da Maryama, "A'a haba Maryama. Ai da kin faɗa. Kafin ma ki fita asalin gate da zai fitar dake ai sai kin ɓata lokaci. Don haka bari a kira driver kawai ya kaiki."
Hasina tayi saurin cewa, "Eh Ummi hakan za'ayi. Bari na sauƙa na nemo shi yanzun nan." Maryama ta yarda da hakan don yafi mata sauƙi. Bayan wassu mintuna Hasina ta hauro sama ta same su.
"Ai Ummi driver baya nan. Wai ya shiga cikin gari ya saka mai a mota. Kuma yanzu if I call him kafin ya iso it will be a waste of time, Maryama tana ƙarayin dare."
Hajiya Bilkisu tace mata, "Ɗauki wayata akan dressing mirrow ki kiramin Najib. Idan baya wani abu yazo ya kai ta."
Maryama ta ɗan zaro idanu cikin sirri da jin hakan.
Hasina ta shiga kiran wayar Najib. Ba'a ɗauki lokaci ba ya amsa.
Hasina ta sanar dashi komai, suka gama magana sannan ta katse wayar. Ta dubi mahaifiyarta tace,
"Yace zai kai ta. Wai mu jira shi a waje yanzu zai sauƙo."
Hajiya Bilkisu tace, "Yauwa to madallah." Cikin sakin fuska tace da Maryama, "Ki gaida gida ko?"
"Ummi zasu ji da kyau. Sai da safe." Sannan Hasina ta raka ta waje. Basu wani daɗe ba suna 'yar hirarsu Najib ya ƙaraso sanye cikin wani shirt kalar grey.
Ɗaya daga cikin manyan motocin dake ajiye cikin rumfar parking tayi ƙara, alamun an buɗe ta da remote. Najib ya isa daidai ƙofar motar sannan yace,
"Ta shiga mu tafi." Ya shige ya tada motar a lokacin da fitillun motar suka haska.
Sukayi sallama da juna, Hasina ta wuce cikin gida Maryama kuma ta juya zata shiga motan.
Tana cikin fargaban kasancewa da shi ita ɗaya, amma kuma wani ɓangaren zuciyarta na son hakan.
Ta buɗe ƙofar seat dake gefen Najib. Tana kai kallonta inda yake zaune taci karo da idanun sa a kanta.