Rabin Raina

5. Bracelet

by @inkedbynadeerah

Najib na kau da kai, Maryama ta sauƙe ajiyar zuciya a hankali, irin wacce ko na kusa da ita zaiyi wuya ya ji. 


Ta shige motar ta zauna sannan ta rufe ƙofar motar. Nan da nan Najib ya taka motar, ya shiga murza steering wheel irin ta ƙwararru ya fice dasu daga rumfar motocin suka kama hanyar fita daga harabar gidan zuwa gate.


Wassu ‘yan mintuna suka shige, babu wanda yace da wani komai. Ƙarshe dai Maryama tayi ƙarfin hali tayi magana. 


"Umm..., gidan mu yana...." 


"Ummi ta faɗa min." Ya katse ta ba tare data ƙarasa maganar ta ba. 


Ta gyaɗa kai a hankali a lokacin da ta kai kallon ta gefe inda yake zaune, shima kallo ya kai mata kafin ya mayar da idanun sa kan hanya. 


Duk da babu haske sosai cikin motar, suna iya ganin gefen fuskar juna. Ido suka sake haɗawa na sakanni ƙalilan sannan Najib ya sake mayar da kallon sa kan hanya. Da haka har suka isa babu wanda ya sake cewa da wani komai. 


Da isarsu Najib yayi parking ba tare daya kashe motar ba. Maryama ta dube shi sannan tace, “Na gode sosai. Sai da safe." 


Cikin sakin fuska ya amsa. “Allah ya kaimu." 


Ta ɗauki handbag ɗinta dake ajiye kan cinyarta sannan ta fice daga motar ta kama hanyar shiga gida a lokacin da Najib yayi reverse shima ya fice daga harabar gidan. 


Tana shiga cikin gida ta sanar da iyayenta ta dawo, sannan ta wuce ɗaki ta shige bathroom ta dauro alwala tayi sallar isha. Tayi shirin bacci ta ɗale gadonta tare da jawo wayarta. Pictures ta shiga tana ƙara kallon hotunan da suka ɗauka. 


Tayi swiping zuwa wani hoton da aka ɗauke ta ita ɗaya. Hoton yayi kyau matuƙa. Kwalliyar ta ba mai yawa ba. Ɗaurin ɗankwalin ta yayi kyau sosai, sai dai mayafinta baya zagaye da kafaɗar ta a lokacin dalilin jiƙewa da yayi da ruwan coffee. 


Coffee... 


Ta dafe goshinta da tafin hannu tare da murmusawa a lokacin data tuna abinda ya faru tsakanin ta da Najib. Nan da nan fuskarta kuma sai ya canza yanayin nuna damuwa data tuna ƙunar data same shi a lokacin. 


Ta mayar da hankalinta kan hoton da take kallo. Cikin hoton ta hango golden  bracelet ɗinta data saka. 


Duk cikin bracelets ɗinta tafi ji dashi. Asali na mahaifiyar ta ne ta gada. Tana jin tamƙar tana da kusanci da ita dalilin wannan bracelet ɗin duk da bata taba ganin taba sakamakon rasa ranta datayi a lokacin zuwanta duniya. Tana da hotunan mahaifiyar ta da dama da take sanye da shi a hannun ta.


Ta ajiye wayar ta ɗauko Jakarta data rataye shi jikin bag rack. Ta buɗe ta shiga lalumar cikin jakar da ‘yan yatsun ta. Giran tane suka haɗe data ji babu alamar abinda take nema. 


Ta zazzage duk kayan cikin jakar a kan gado, babu bracelet babu labarin sa. Ta shiga duba kan side drower, dressing mirrow dasu ma'ajiyar jewelleries ɗinta, sai dai bata samu ba.


To ina ta ajiye? Tasan tabbas ta ɗauko shi daga ɗakin Hasina da zata tafi. Da zatayi alwalar magrib ne ta cire shi, tazo wanke hannu sai taji kamar ana mitsinin ta dalilin ja mata Ƙananun gashin hannunta da yakeyi.


Zata iya tabbatar wa tana tare da sarƙar hannun akan cinyar ta har isowar ta gida. 


Ko ta manta shi a motar da Najib ya dawo da ita, ko kuma ta yar bata sani ba garin fitowa daga motar. Cikin biyu za’ayi ɗaya. Da har zata fice daga daƙinta taje waje ta duba ko zata gani, sai tayi tunanin dare yayi kuma an kulle kofar mashigar gidan. Dole ta jira zuwa safiya sannan ta duba kafin masu shara su fara aikin su. Haka ta kwanta cikin tunanin har bacci yazo mata. 


****


Alhaji Bello mustafah shahararen mai kuɗi ne. Allah ya azurta shi da dukiya tuli bila adadin. Asalin sa ɗan masu arziƙi ne domin kuwa iyayen sa na ɗaya daga cikin masu kuɗin Nigeria ta Arewa. Allah ya azurta iyayensa da kakanninsa da albarkan kasuwanci. Arzikin sa bama anan ƙasar ya tsaya ba, yana ɗaya daga cikin mutanen da suke da manyan hotels a ƙasashen waje. Yana da ƙanne biyu, namiji da mace. Sune Alhaji Mukhtar Mustafa, sai Hajiya Saudatu Mustafah. Duk cikin su ukun nan kowa da nashi yalwataccen arziƙin da 'yaya masu albarka son kowa ƙin wanda ya rasa. 


Alhaji Bello Mustafah yana da 'yaya Uku. Biyu maza ɗaya mace. Na farkon shine Najib, na biyun kuma Ramadan, sai auta, Hasina. Kasancewar Hasina ce mace a cikin 'yayan gidan yasa ta zama 'yar lelen kowa. 


Duk da bata fiye zama tare da yayun taba dalilin yawan fita da zaman ƙasashen waje, hakan bai hana su creating solid bond ba a tsakanin su.


Mahaifiyar su itace Hajiya Bilkisu wanda suke ƙira da Ummi, mahaifin su kuma suna kiran shi da Abba.


Hajiya Bilkisu shuwa arab ce usil daga garin Maiduguri. Mata ce mai ɗumbin kirki da kulawa. Tana son 'yayanta kuma tana ji dasu sosai, bata so taga damuwa ko da kaɗan ne a tattare da na kusa da ita.


Kamar kullum yau ma masu aikin gidan sun gama haɗa komai na breakfast, sun jera kan royal dining table ɗin da zai ɗauki mutane takwas. Wadda ke supervising masu aikin tazo tayi inspection kamar yanda ta saba gudun kada a samu wani matsala. Ta duba agogon dake manne a bango taga karfe bakwai da rabi na safe. 


Basu kammala da wuri sosai ba kuma basu makara ba, kamar dai yanda masu gidan suke so. Masu aikin na iya ƙokarin su suga sun faranta wa masu gidan rai, domin kuwa suma ana sallamar su da kuɗaɗe ba kaɗan ba, ga kuma kirki da masu gidan ke nuna musu. 


Suka gama kintsa komai na buƙatar masu gidan sukayi tafiyarsu suma don suje su karya.


Misalin ƙarfe takwas Hasina ta sauƙo daga ɗakin ta. Tana isowa daf da dining table ɗin taja daya daga cikin kujerun ta zauna a inda ta saba zama kullum. Ta shiga latsa wayarta tana jiran fitowar sauran. Bayan wassu mintuna Alhaji Bello da matarsa Hajiya Bilkisu suka sauƙo suna tafe da juna cikin hira. 


Hasina ta sauƙa kan kujerar da take zaune ta ɗan duƙa ta gaishe da iyayen ta cikin ladabi, suka amsa cikin sakin fuska.


Bayan kowa ya zauna hajiya Bilkisu ta dubi 'yar ta. "Ina Najib? Ko yau ma bazai sauƙo ba?" Hasina tace, "Eh yau ma ina ganin ba zamuyi breakfast tare dashi ba. Mun haɗu a kitchen jiya da daddare na sauƙa shan ruwa, shi kuma he was making coffee. Da alama ya raba dare yayi aiki kamar yadda ya saba." 


Cikin damuwa hajiya Bilkisu ta dubi mijinta tace, "Ka gani ko? Yaron nan sai bawa kanshi wahala yake yi. Kaga yanzu ma daya dawo gida bai haƙura da aikin ba wai sai dai yasha coffee ya raba dare. kuma nasan idan ya koma Canada aikin da yake yi yana fin haka. Ni wallahi aure nake so yayi ko zai samu sauƙi da irin wannan rayuwar.” 


Ta ɗanyi jim tana tunani sannan taci gaba. “To wai meyasa bazaka dawo dashi ɗaya daga cikin branches ɗinka ba a nan Nigeria? Kullum yana cikin raba dare?... Ni wallahi abun yana damuna sosai.”


Alhaji Bello yayi ajiyar zuciya sannan ya dube ta. “Bilkisu, kada ki damu. Kinsan ya dawo gida yanzu shiyasa aikin zai masa yawa, dole ya rinƙa handling aikin daga nan idan ba haka ba there will be alot of problems. Kuma dai naga ke kika sashi dole ya daɗe idan ba haka ba da yayi kwanaki da barin ƙasar, kinga da aiki bazai taru ya masa yawa ba.


Maganar dawo dashi nan Nigeria kuma, ke zaki lallaɓa shi ya yarda tunda shi yace he prefers working out of the country." 


Ya sake duba ta da kyau a lokacin da yaga damuwar fuskar ta ya fara gushewa. "Yanzu ki kwantar da hankalin ki komai zaiyi dai dai da yardar Allah. Kuma nayi magana da Ramadan jiya a waya, nace shima ya ɗauki hutu yazo gida ko dana sati ɗaya ne. Naga gidan ya cika banda shi. Kinga shima idan ya dawo zakiji daɗi sosai." 


Hajiya Bilkisu ta murmusa. “Gaskiya kayi abu mai kyau Abban Hasina. Wallahi kamar kaga zuciya ta duk nabi na damu naga yaran nan a kusa dani.”


Hasina dake gefe tana kallon iyayeyen ta da idon so irin na 'yaya ga mahaifan su. A kullum tana ƙara godewa Allah daya bar mata iyayen ta cikin rai da lafiya tare da kulawa da junan su.


Zuciyar Hasina fal cike da farin cikin jin zata ga yayanta Ramadan kwana kusa. Tayi kusan rabin shekara bata ganshi jiki da jini ba, sai video calls da suke yi a lokutan da yaki free. Chatting kuma basu cika yi sosai ba saboda yana yawan busy. 


Sai dai kuma tasan zata sha takura. Ramadan bai cika biye mata tayi abin da take so ba duk da shima yana ji da ita a matsayin ƙanwar sa.


Cikin wannan yanayin na kwanciyar hankali da hamdala Hasina da mahaifanta suka yi breakfast.


****


Da fitowarta wanka ta tsane jikin ta da towel sannan ta shafa mai ta saka kaya irin wanda bazai takura mata ba. Bayan ta gama ta kwanta kan gado ta shiga tunanin shin wai ina sarƙar hannun nan zai kasance?


Da sassafe ta fita dubawa ko zata samu, amma abin ya gagara, sai ta sanar da masu share harabar gidan su duba mata. Har suka gama share sharen su basuyi tozali da sarƙar hannun ta ba. Dalilin hakan yasa ta kasa nutsuwa tayi breakfast kamar yanda ta saba.


Daga ƙarshe ta yanke shawarar kiran Hasina a waya. Ta miƙe daga kwanciyar da tayi tare da janyo wayarta dake kan drower inda ta saba ajiyewa kullum. Ta shiga dailing layin Hasina, cikin ringing na uku ta ɗauka.


"Hello Maryama," 


"Hasina, ya kike ya yau?" 


"I'm fine. Ya gida?" 


"Lafia ƙalau. Dama na kira ki ne na faɗa miki jiya na ɓatar da bracelet ɗina bayan mun rabu. Nayi ta dubawa ban gani ba. 


Ina ganin maybe na yar cikin motar da yayanki ya kawoni gida. Please ki tayani duba cikin motar ko Allah zaisa a dace." 


"Aiyya, that your lovely bracelet da kika sa jiya?" 


"Eh wallahi, shine. Kinsan na cire shi da zanyi alwala to kuma i'm sure ban barshi a ɗakinki ba. So ina kyautata zaton yana cikin motar.”


"Okay, to shikenan zan tayaki dubawa. Yanzu dai ya Najib yana bacci, idan ya tashi zanje ya bani key din motar sai na duba miki. Kada ki damu Inn shaa Allah it will be found." 


"To shikenan Hasina, thank you. Ki gaishe min da Ummi. Sai mun sake waya." 


"Ummi zata ji. Will talk to you soon, bye." 


Bayan sun gama wayar Maryama tayi addu'ar zuci Allah yasa a dace.