6
by @gureenjoh
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjoh6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
*SHAFI NA SHIDA*
Jagaban na parlor ta shigo ganin jini a White ɗinta ya ƙirata ta zo ta zauna da kanshi ya ɗinke wurin don ta yanku sossai amma tsabar taurin rai ko ɗarr bata yi ba don duk bayanta akwai yanka da wasu sassa na hannayenta duk akwai scar na yanka ta riga ta saba in da sabo.
Bayan ya gama ta yi ciki bacci tayi don ta sha Ice kan tayi faɗa wurin takwas a lokacin, ƙarfe Ɗaya da wani abu kuma ta farka ta shirya ta fito kai tsaye kitchen ta yi wurin hajjo.
"'Yar albarka kin fito? Akwai abin da kike buƙata ne?"
Ta ce
"No na zo na dubaki ne kwana biyu ba mu haɗu ba"
Murmushi kawai hajjo ta saki tana kallon Diva ɗin Allah ya gani saboda Diva ne kaɗai take zaune a wannan gida, kuma ta ɗauketa tamkar ɗiyar da ta haifa Dukda akwai tarin gyararraki da take son yi wa rayuwarta sai dai Diva ɗin bata ba da damar hakan ba, tana kula da hajjon kaman mahaifiyarta don kyautar kuɗi, tufafi, turaruka ba a rufa wata bata samu daga Diva ba.
"An kai abincin Pascal?"
"Eh Hajiya Shamsu 'Pabloo' ya zo ya ɗauka ya ce da machine hannunshi zai miƙa musu kawai"
Sai da ta ɗan shiga nazari kan ta tuna ashe fa sunan Pabloo na asali Shamsuddeen.
"Ki dafa min indomie guda biyu da kwai zan shiga wurin Shaly a kai min chan"
Tana kai nan ta fice tana tafiya ana miƙa mata gaisuwa wani ta amsa wani tayi kaman bata ji ba har ta shiga babban gidan hayan Baba da ke jikin gidan nasu, mutane ne ratata Dukda rana ne kowa ya tafi neman kuɗi amma akwai wasu da suke gida, gidan haya ne mai dakuna dayawa don za su iya yin talatin, amma kusan duka masu zaman kansu ne ciki.
Kai tsaye ɗakin Shaly ta shiga ta same su da zee-zee suna lido a tray.
"Barka da zuwa Diva"
"Sannunku"
Tana kai nan ta kwanta kan katifarta bata sake cewa komai ba sai ido da ta zuba musu har dai aka kawo mata indomie ta shiga ci, idan da sabo sun saba da halinta za ta iya yini a tare da su bata ce kanzil ba kawai dai ya kasance akwai motsin su kusa da ita, sai dai in ta gaji ta ɗan yi chat a wayanta wanda ba kasafai ba don ita ba ma'abociyar mayar da hankali kan waya ba ce.
Har dare suna tare kan mazan suka dawo suka fita zuwa gidan suka dasa hirarrakinsu.
Anan ne ma ta sake tana 'yar dariyar hirar Skipo dabin da suka yi tsakanin shi da wasu kwalawa(police) yau, Skipo Adaidaita yake ja amma yana amfani da shi ne backup asalin abin da yake yi distributing kayakin Jagaban ne, idan ya gama sai yayi ta daukar passenger.
Washegari da safe bayan Diva ta shirya ta fito as usual kayakin dai ba na kirki ba don ma wani bodycon ne jikinta duk wani siffanta a waje ta saka facing cap kawai dai tana da wani irin idon fashion ne, duk yadda tayi styling jikinta sai ya karɓeta kaman wata fashion star, da key ta fito a hannunta tana cewa Baaba dake parlor
"Mun tafi asibiti"
Ya amsa da Allah ya tsareta ta fice, duk suna nan don haka shiga kawai suka yi suka nufi asibitin don duba Aminu, a lokacin Zubash bata a tare da su sun samu Innar Aminu na zaune sai ganinsu ta yi kaman an jefo su.
"Diva..."
Aminu ya ƙirata da murmushi.
Ta amsa
"Ya dai? Ya jikin?"
"Ai na ji sauƙi Diva, me kuka kawo min don na gaji da cin abincin nan"
Bata ce komai ba Shaly ce ta fiddo tramadol ta jefe shi
"Shiyasa na riƙe maka wannan don ya rage maka zafi, Jagaban na miƙa saƙon gaisuwa"
"Godiya nake mutuniyata Allah ya bar mini ke, shiyasa nake na fi yinki na kowa anan bayan Uwar ɗakina"
Obafiya ya ce
"Mu da baka yin mu cinna mana wuta mana kawai mu tabbatar"
Suka yi dariya
Mamanshi ta miƙe ta fice tana share hawaye Diva ta bita da ido tana sauƙe wa ta ga wani mutumin ya zura mata ido.
"Na tsiyayar da idon nan na sake ganin kana kallonaa ba ruwana da ciwon ka... Ka wani zura min ido Uwa mujiya me kake kallo a jikin nawa!"
Yadda ta harzuko ya sa dole ya shiga taitayinsa jikinsa na rawa ya natsu.
Su Pabloo suka shiga dariya.
Duk ɗakin a hankali suke zamewa suna ficewa saboda tsoro ita kam ta baje suna ta hira.
Ashe wai ƙararsu aka kai akan suna shaye shaye suna kuma damun patients, securities na asibitin duk sun san wacece kowa tsoron zuwa yake sai Police suka kira su kuma suka kira DPO ya ƙira Jagaban.
"Idan bakwa son ganinta asibitin sai dai a sallami yaron amma nima ban isa in hanata zuwa ba"
Shi ne amsar Jagaban.
Kuma haka aka isar basu bar asibitin ba aka kawo takardar sallama, ita ta biya komai suka tsare napep aka saka shi ciki saboda mamanshi sai da suka tafi kan suka shiga mota suka yi gida.
A waje yau ta yi parking suka bubbude kofofin motar suka zazzauna baki baki suna ta hira tsakaninsu ita dai kujera plastic aka dauko mata ta zauna.
Wannan zama da su kan yi ba karamin rikita 'yan unguwar suke ba don duk wanda ya doso idan ya gansu sai ya koma da baya saboda abu kadan za ka yi su zalunceka.
Cikin rawar jiki ya taho don wallahi bai so zuwa ba amma Malam Iro ya rantse mishi idan suka bari wani abu ya samu khadija to wlh duk sai sun yabawa aya zaƙinta gwara ya zo ya nemi Zubash ɗin.
A rikice yake gabaɗaya haka ya zo ya tsaya kyammm kan su ya rasa me zai fara cewa saboda tsoro.
Idanu ta ɗaga ta kalleshi ta watsar..
"Obo.."
Obafiya ya diro ta kalleshi
"Wannan bai iya gaisuwa ba ne?"
Sarai ta gane shi shima kuma a rikice yake ya sa bai gaishe su ba, kan yayi wani yunkurin Obafiya ya faska mishi mari sai da ya kusa faɗuwa ya gyara tsayuwa yana dafe kunci idanunshi falll hawaye a zuciyarshi kuwa ya tsinewa kafafun da suka biye wa Malam Iro suka kawo shi gaban Diva.
"Babu manya ne a gidanku? Ko gaisuwar ce ba'a koya maka ba"
Hannayenshi biyu kan kumatun ya zube jiki na rawa ya shiga cewa
"Wallahi an koya min...Na rikice ne ya sa na manta..ina yini... Ammm ahh ina kwana? Ina gajiya?"
Babu wanda ya saki fuska a cikinsu Dukda dariyar da ya ba wasu.
"Mu aljanu ne dole mu rikitaka ko?"
Divaa ta faɗa tana zukar tabar hannunta.
"A'aa ki yi haƙuri Diva...kiyi haƙuri"
"Me ya kawo ka?"
Diva ta tambaya.
"Khadija ce tana dawowa makaranta mota ta kaɗeta kuma ta bugu sossai shine...shi ne baba ya ce in zo in duba Zubaidah a kaita asibiti kar wani abu ya sameta"
Idanu Diva ta zuba mishi wato duk gidan babu mai iya kaita asibiti sai Zubaida ta zo? Sun mayar da ita saniyar tatsa shiyasa jikinta baya taɓa hutawa da maza, tsaki mai ƙarfin gaske ta ja cikin wani irin takaici don alamu sun nuna tun jiya Zubash ɗin bata tare da su kuma bata gida.
"Obo...mu tafi mu kai yarinyar nan asibiti"
Ta miƙe da sauri suka shiga mota ta ja zuwa kofar gidan su Zubash ɗin suna parking sai gata tana sauƙa a machine, cikin mamaki take tambayar su me ya faru.
Diva bata ce komai ba sai tsayuwar da ta gyara tana wasa da dankwalinta Bakinta na taunar chewing gum a hankali.
"Shiga ki duba ƙanwarki"
Wani irin tashin hankali ne ya bayyana a fuskarta da gudu ta shiga cikin gidan, yadda ta samu Nana sai da ya sa ta kusa faɗuwa, haka suka daukota sai asibiti.
Da taimakon Allah dai babu abin da ya faru, an kula da ita sossai kan suka baro asibitin yamma ne don haka Diva wanka tayi har ta ma kwanta ta tuna akwai abubuwan da take son saya a kasuwa don turarukanta sun yi ƙasa.
Key ta zara tana gyara trench coat na jikinta, wasu irin takalma hills ta saka ta fito.
"Hajjo!"
Da sauri hajjo ta zo
"Na'am uwar ɗakina"
"Idan su Obo sun shigo ki ce musu su jirani ina zuwa yanzu"
"Toh Sohana amma yau ke kaɗai za ki fita?"
Ta ɗan kalleta sai ta duƙar da kai bata ce komai ba don ba'a yi mata tambayar iskanci ita kanta hajjon ta sani subutar baki ne.
Fitowa tayi ta shiga mota ta kunna tare da juyawa ta isa gate ɗin sai dai bata ga alamun Bilya ba.
Horn ta yi sau ɗaya bai fito ba ta sauƙa a harzuke, daidai yana fitowa daga bayi da gudu, kafa ta sa ta kwashe shi ya zube timmmm a ƙasa.
"Ki yi haƙuri Diva...!"
"A karo na karshe da zaka kira sunana, aikin me aka daukeka da za ka barni ina ta Horn shiru??"
"Cikina ne ya ruɗe shine na je ba..."
"Ka buɗe gate ɗin nan ko sai na ɓurma cikinka in ya so abubuwan su zube nan ƙasa ka huta da zuwa bayin?"
Da gudu ya je ya shiga buɗe gate ɗin ta doka tsaki ta koma motar watarana sai ta cirewa Bilya hannaye in bai kiyayeta da sokanci ba.
Da gudu ta fice daga gidan jiki na rawa ya zube yana sauƙe numfashi.
Allah ya gani ba yadda ya iya ne yake gadin wannan gida, idan ya bar nan ɗin bai san ta inda zai fara neman wata sana'ar da zai ci da kanshi da matarshi ba kuma ya kula da lafiyar yaron su in ba don haka ba da ya bari da jimawa, a haka ɗin sun yi masu gadi sama da goma sha wani abu duk basa iya jure halin Diva don yau za ta iya yi maka kirki gobe ta karta maka rashin mutunci ba damuwarta ba ne, Musamman idan tana Buge kaman yanzu.
Kasuwa ta nufa music na tashi a motar kaman zai ɗaga sama, chewing gum take ci tana gyaɗa kai cikin reckless driving da sai dai a bata hanya ba dai ta bayar ba.
🖤Gureenjoh🖤