JODAH

06

by @sadisakhna


 

_____👑 *JODA* 👑_____ 

 

              

 

Na  

*Sadi-sakhna* 

Ƴar mutan Jama'are 

 

 

 

 

THE TRIO OF TALES  

(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)  

 

 

@sadisakhna on Arewapen 

@SAKHNA03 On Wattpad 

*** on Whatsapp 

 

 

LITTAFI NA 1 

 

 

 

 

*Harƙa ta (6)*👑 

 

 

 

Kaman yanda ya faɗaɗin hakane,duk da na fahimceshi amma kuma kalmomin sunyimin nauyi,bazan iya amfani dasu ba,amma kuma zan ajiyesun wataƙila zasuyimin amfani a gaba. 

 

 

 

Ina cikin tunanin naji muryarsa yacigaba da magana. 

 

 

 

"Shi ilimin taurari bangarene na fikira da lura,wanda bayada kaifin hankali koda yasani bazai iya amfani dashi ba,shiyasa iliminsa ruwan darene amma iya amfani dashi sai wanda Allah yabawa baiwar hakan. Ana amfani da taurari ta hanyar sanin abubuwa da dama,ciki harda abinda ya dace dakuma wanda bai dace ba. Mu a matsayinmu na wanda muke rayuwa a ruwa,mukanyi amfani dasu ne kaɗai domin sanin inda muke,a wanne lokaci muke dakuma ina zamu dosa. 

 

 

 

Kaman yanda kika nuna waccar tauraruwar da take arewa sunan ta Kudusu ita kullum ta kasance tana arewancin duniya ne. Duk sanda matafiyi yaganta to zata bashi damar sanin ƙusurwa huɗu na duniya,wato gabas da yamma kudu da arewa a lokacin da babu rana ballantana mutum ya gane. 

 

 

 

Sannan waɗannan dasuke a haɗe waje guda mukanyi amfani dasune wajen daidaita alƙiblar da jirgi yake bi,sunan su Gungume wani na ƙiransu da Al-awwa. Wannan mai haske sosai kuwa sunanta Dar'i amma zaki iya saninta da Zarah tanada haske sosai da idan tafito takan haske sauran taurari,bata dushewa sai gabannin fitowar alfijir. Anan cikin kogi ko yaushe ana kallanta,sabanin a cikin gari da gini ko duwatsu suka tareta,ba'a kallanta sai idan ta iyo sama lokacin data biyo wata yana kan haskensa" 

 

 

 

Al'jabi abin yabani haɗeda ban mamaki,lokaci guda naji kwaɗayin son sanin wannan ilimi yakamani,sannan naji xuciyata da ƙwaƙwalwata sun natsa waje guda,kenan dama sanin wani abu suke nema,shiyasa suke tayimin kai kawo a cikin gangar jikina? 

 

 

 

Cikin dare muna kwance nida ummah tarin Abah ya tashemu,da sauri tamiƙe tayi inda yake kwance. Ɗagashi tayi a hankali ya jingina da bango,tarin yaɗan tsagaita amma bawai ya daina ba. Jini ne yafara taruwa a bakinsa,yana fesar dashi a duk lokacin da yunƙurin aman ya taso masa,nidai hawayene yafara taruwa a idanuwana domin banason kallon mahaifinnawa a cikin wannan halin,Fasihmman idan na tuna hakan yafaru ne ta dalilin cetona da yayi ƙoƙarin yi. 

 

 

 

Juyowa ummah tayi ta kalleni tareda cewa. 

 

 

 

"Joda maza jeki ƙira baba yakub,kice abanki ya farka amma yanata tari harda aman jini" 

 

 

 

"Toh ummah" 

 

 

 

Na faɗa tareda yin waje da gudu, bamu bata lokaci ba muka shigo taredashi da sauri,lokacin har tsumman data saka masa a gabansa ya jiƙe da jini. Sannu muke ta jera masa,amma babu ɗaya daya amsa mana saboda baya cikin hayyaccinsa.   

 

 

 

Wani magani ya jiƙa a ruwa yabashi yasha,can bayan an ɗauki wani lokaci yatsaya da tarin harma da aman jinin. 

 

 

 

"Da alama gubar tashiga magudanar jininsa,sannan ban kulaba ashe tsinin kibiyar ya huda har huhunsa na gefen hagun. Zuwa gobe zamu iya shiga iyakar Songhay,wannan maganin shine zai zama ruwan shansa har takai ga mun isa cikin gari wajen ɗan uwana. Muyi ta addu'a Allah yasa mukai akan lokaci,indai ba mun makara ba inada tabbacin bazai rasa maganin lalurar tasa ba" 

 

 

 

Bayan yafita sai jikinnasa yayi ɗan sauƙi,domin har bude ido yayi yana kallon ummah,itama kallonsa take tana murmushi. Hannunsa yasaka daƙyar yashafi fuskarta,sai kuma yajuyo da kallonsa gareni. Ɗaya hannun yaɗaga yanason yimin alamar nazo. 

 

 

 

Ummah ce ta kalleni tareda cewa. 

 

 

 

"Joda kizo mahaifinki yana ƙiranki zo da sauri...." 

 

 

 

Matsowa nayi inda yake nasaka hannuna a nasa ina kallonsa,murmushi nima yayimin tareda ɗaga kai alamar yaji daɗin ganina. Shafa kaina yayi tareda ɗaga idonsa da hannunsa sama. Alamar Allah yayimin albarka. Dukkan mu kasancewa mukayi cikin farinciki a lokacin  

 

. A raina ina cewa Allah yasa wanann bashine na ƙarshe ba a kasancewar mu cikin farinciki tare. 

 

 

 

Washagari tun buɗe idona na kalli Baba yakub yana hangen wani tsibiri da muke hangowa,da gudu nanufi inda yake,domin a ɗan zaman da mukayi dashi tun ranar daya sanar dani wani abu na tarihin rayuwarsa da kuma wasu Ilimi da kimiyya daya sani,sai hakan yasa nakeson zama dashi muyi hira ina jinsa tamkar kakana. Kuma hakan yasa na koyi abubuwa da dama daga wajensa. 

 

 

 

"Baba yakub wancan ɗin menene nake hangowa?" 

 

 

 

"Wannan shine garinmu,tabbas masu hikima sunyi gaskiya dasukace wanda yabar gida gida yabarshi,sai naji wata nutsuwa tashigeni dana tuna nadawo gida" 

 

 

 

A hankali tsaunin yake ƙara girma a duk lokacin damuka rage tazara tafiya tsakaninmu dashi, mutane muka fara haɗuwa dasu jefi jefi a cikin jirgin ruwansu ƙana na wanda suka fito domin kamun kifi. 

 

 

 

Sannu bata hana zuwa mun isa bakin gabar teku na babban birnin daular Songhay mai suna Goa,inda babban Sarki yake. Duk da na manta yanda garinmu yake amma hakan bazai hanani ganin girman wannan garin ba tun kafin na shiga cikin,bakin gabar kogin kanta abin kalloce na manyan jiragen ruwa a suke bakin wajen dakuma ayarin mutane. Sai na kalli namu jirgin ruwan ɗan ƙarami kaman an jiye Kaza a gaban giwa. 

 

 

 

Wani gefe baba yakub yayi da jirginnamu ya ɗaureshi inda jirage masu girma kaman nasa suke ɗaure. Yusha'u ne yafara ɗebo kayanmu daga cikin jirgin yana kaisu wata rumfa yana ajiyewa,kaman dama yasaba hakan a duk lokacin dasuka dawo. Nidai kallo kawai na tsaya inayi da hanyar rarraba idanu. Ummah kuma tana cikin ɗakin jirgin tareda Abah. Baba yakub fita yayi yana magana da wani mutum wanda shina dattijonne kamarsa. Wasu matasa guda biyune suka taho da wani gadon katako mai wajen kamawa suka shiga inda su ummah suke. Can saigasu sun fito da Abah na akan gadon ummah kuma tana binsu a baya. 

 

 

 

Hannuna takama muka sauƙa daga cikin jirgin izuwa doron ƙasa. Wani abu naji ya ziyarceni har kaina,ji nake kaman wannane karo na farko dana taba taka doron ƙasa. Wasu mutane ne suka iyo kanmu kaman zasu cinyemu,ganin hakan yasa ummah tayi saurin rungumeni a jikinta. 

 

 

 

"Wannan baiwar nawa kuɗinta yake Masunci Yakub,inaso zan siyeta hadda ɗiyar tata" 

 

 

 

Wani mutum gajere mai ƙaton tumbi yafaɗa yana murza hannun ummah,tana fizgewa amma yana kuma riƙewa kaman yasamu akuya. Abin mamaki yabani wanda hakan yasa nayi saurin kallon baba yakub domin naji mai zaice. 

 

 

 

"Ahah Bafatake Khuzaif wannan bayin bana siyarwa bane,ka ƙara gaba ko zaka samu wasu" 

 

 

 

"Habadai Yukub bamu saba yin haka dakai ba,a duk lokacin daka kawo bayi daga yankin Adik mukanyi ciniki har na ƙara maka da riba,mai yasa wannan tun kafin kaji farashina zaka yanke ciniki dani" 

 

 

 

"Kayi haƙuri kaman yanda nace maka,wannan nariga da munyi yarjejeniya da Sunkia Madina tun kafin natafi Neman bayi" 

 

 

 

Shin wanne yarene suke faɗi hakane daban gane ba,duk da kuwa yarene danima nake magana dashi. Wai menene yake faruwane,ya nakeji baba yakub yana magana kaman bashiba, anya kuwa kunnuwana suna jiyemin daidai. Ɗaga ido nayi na kalli ummah wacce takeyiwa baba yakub kallon kaman taga dodon daji,sannan duk wani shauƙi da tabbaci sun kau daga cikin ruhin idanuwanta,wani hawayene ya jiraro daga cikin idanunnata. Indai har abinda kunnuwana suka jiyemin gaskiyane cewar baba yakub yaudarar mu yayi to ya ummah zataji wanda dama zuciyar tata a ruguje take. 

 

 

 

Hannu na tariƙe tsam tareda fizgata zata ruga da gudu,da sauri wasu matasa suka tare mu ta hanyar fincikeni daga hannunta ita kuma suka riƙeni. Magana tafarayi kamar na zautacciya wacce bata cikin hayyacinta. 

 

 

 

"Ku sakeni na karbo mijina dasuka tafi dashi, sannan dan Allah ku rabu damu karku cutar damu,baba yakub bai kamata kayimin haka ba,dan Allah kabarmu haka,ko iya abinda na faɗamaka yasamemu inaga ya ishemu a wannan rayuwar. Dan Allah kada kasake salwantar da rayuwarmu bayan ƙokarin da mukayi Allah ya kubutar damu daga farko. 

 

 

 

Shuru baba yakub yayi fuskarsa ɗauke da damuwa yana kallona yana kallon ummah wacce take ta ƙoƙarin zamewa daga riƙon da wani ƙaƙƙarfan bawa yayi mata. Gabaɗaya abin baiyimin daɗi ba,ji nake inama inada ƙarfin ikon dazan umarci bawan da yasakemin mahaifiya, Zahiri ne ya dokeni na farko daga mafarkin daya ɗaukeni a cikin jirgin ruwan. Zatona rayuwar datake jirgin ruwan itace dawwamammiyar rayuwar dazanyi ashe ba haka bane. Wanda yabani shawarar kada na yarda da mutane,sannan nayi taka tsantsan shine wanda yafara yaudarar iyayena akan idona,shin zan yarda dashine na karbi shawararsa kokuma watsi zanyi da ita na nemo tawa a cikin gwagwarmayar dazan fuskanta a gaba. 

 

 

 

Tana turjewa tana komai haka mutumin yajata har zuwa wani tanti,a jikin ƙarfen da akayi tantin ya ɗaureta da igiya,nikuma wani yana iza ƙeyata abayansu,muna shiga ya turani na faɗa akanta rigif sannan yaja ƙofar ya rufe. 

 

 

 

Ɗago idona nayi wanda babu hawaye kokuma farinciki a cikinsu,gabaɗaya ji nake kaman ban fahimci mai ma yake wakana ba. 

 

 

 

Da idanuwan ummah naci karo,wanda suketa zubda hawaye sunyi jajur dasu. Hannuna na ɗaga wanda yayi sanyi ƙalau nafara share mata hawayen,batareda labban bakina sun bani damar furta ko kalma ɗaya ba,duk da kuma ɗaruruwan kalmomine suke yawo a cikin kaina. 

 

 

 

Hakan danayi bai tsagaita sautin kukanta ba saima ƙara masa ƙaimi dayayi,jijjiga kanta ta hauyi tana kallon cikin baƙar ƙwayar idona,wanda nakeji kaman ta Jona nata ruhin danawa. 

 

 

 

"Joda......!!! Kiyi haƙuri ɗiyata kinji,banso kikayi arba da wannan bangaren da baƙar duniyar da muke ciki ba,banso daga farkawarki kikaci karo da wannan baƙin al'amari ba. Amma samm banaso zuciyarki da karye daga samun rayuwa mai kyau a gaba. Keɗin ta dabance ɗaya a cikin dubunnai,tunda naji hirarku da baba yakub a wannan daren naji a raina keɗin da Fasihmmance,da Allah yabaki baiwa da Fasihmman,wannan baiwa kiyi amfani da ita ta hanyar data dace,kada ki taba bari wani yayi amfani da ita ta hanyar son ransa kinji ki taimaki duk wanda kikasan yana buƙatar taimakonki,karki miƙa kanki ga mutum don yanada ƙarfin mulki ko ɗaukaka. Wannan ɗaukakar Allah ne yabashi kuma kema zai iya baki a duk lokacin dayayi niyya,shi bai isa yabaki ba idan Allah bayyi niyyar baki ba. Domin kedashi ɗin duk ɗayane a wajensa,har kin fishi idan kinkasance mai tsoronsa fiyeda shi. Sannan karki taba yaudarar wanda ya yarda dake,kuma karki cutar da duk wani halitta da Allah yasaka a ƙasanki. Kuma kiyi haƙuri da duk wata muzgunawa da wani zaimiki don yafiki matsayi,ki ɗauka Allah ne yake jarrabarki ta hanyar bashi damar yamiki hakan. Idan kikayi haƙuri zakiga amfanin wanann juriyar dakikayi." 

 

 

 

Ɗaga mata kai nayi,zuwa lokacin nima nawa hawayen sun fara zuba. Meyasa takeyimin magana kaman mai wasiyya,ko bazan ƙara ganinta ba. Sannan meyasa kowa yake tunanin inada wani abu da sauran mutane basuda shi.  

 

 

 

Muna a wannan hali aka buɗe ƙofar wani yashigo,baba yakub ne amma maimakon ya shigo sai ya tsaya a bakin ƙofa yanayinsa kamar na marar gaskiya.  

 

 

 

Wani kallon zan kasheka ummah takeyi masa,hakan yasa ya sunkuyar dakai kuma ya sauke ajiyar zuciya. Gyaran murya yayi hakan yasa wasu mutane suka shigo da wanann gadon katakon da aka ɗora Abah na akai,wannan karon ma da mutum akai amma an rufeshi da wani mayafi. 

 

 

 

A gabanmu aka ajiye katakon,sannan baba yakub ya tsugunna ya yaye mayafin dayake kan fuskar mutumin. Abah nane a kwance idanunsa kuma a rufe kamar mai bacci. Amma dasauri zuciyata ta bani ba bacci bane duba da yanda jikin ummah yake ta zuba karkarwa a lokacin dataganshi. Wani abu yana fizgarta kaman tanaso ta fita daga cikin hayyacinta. Alama yayiwa wanda suka kawo Abah dasu kunce ta .  Ba musu sukaje ta bayanmu suka kunceta. 

 

 

 

Kaman jira take maza ta cakumi wuyan rigar Baba yakub tareda cewa. 

 

 

 

"Kafaɗamin mai yasa zaka kashemin miji,meyasa ka kasheshi? Shin yardar danayi dakai laifine da har na cancanci wannan hukuncin?" 

 

 

 

Cire hannunta yayi daga rigarsa daya tambayar takai ayah daga tambayar da takeson yi masa. 

 

 

 

"Domin ranki yabaci kada kiyi saurin zargin mutum harta kaiki ga yanke hukunci,duk da na boye miki abubuwa da dama gamedani,amma hakan bazaisa nayi miki cutarwa har haka ba. Ni ba macuci bane ko mai kisa ba. Ni masucine amma mai safarar Bayi daga gabar kogin Adik izuwa ga Goa. Duk wani bawa daya tsere,ko kuma sanadin yaƙi yasa ya tsinci kansa a bakin gaba mukan tseratar dashi izuwa nan,amma idan mukazo sayar dashi mukeyi ga wani waje da baza'a cutar dashi ba. Saboda mu maida kuɗin jirgin da mukayi masa da kuma guzurin da muka ciyar dashi. 

 

 

 

Har raina danaji labarinki ga marasa lafiya har biyu a tareda ke banyi niyyar sayar daku ga kowa ba. Na kuduri niyyar taimakonku. Ta hanyar sayar daku da ɗan uwana na kuma roƙamiki maganin mijinki,kuma kin yarda da hakan. To amma abun yanzu ba haka bane. 

 

 

 

Mijinki ashe ya daɗe da rasuwa,baccin dakike tunanin yayi ba bacci bane face amsa ƙiran mahaliccinsa,sannan kuma su saƙo ya iskeni Ɗan uwana yayi tafiya bazai dawo ba sai nan da wata shida. Sannan nima dukka komai na ya ƙare a kuladaku, ajiyata dana bayar anan Bakin gaba wai Masu karbar Haraji daga gidan sarauta duk sun ƙwace dukka dasuka ga bana nan saboda zalunci irinnasu. Banida wani abu dazan barwa iyalina, idan zan koma bakin aiki. Danayi tuna cewar Sunkia Madina ta bani cikiyar baiwa Mai ɗan shekaru kuma mai hankali,in an samu zata siya da daraja,shine na yanke shawarar kaiki gareta. Kuma ita batada matsala indai ba wanda ke kewaye da ita ba" 

 

 

 

Shuru Ummah tayi tana auna fahimtar maganar tasa,tana cikin tashin hankali ne amma sai yanzu da kula dayake kwance jikinsa yayi sanyi ƙalau,bata kawo mutuwa yayi ba ta ɗauka kawai yanayin ciwonnasane,ashe tafiya yayi ya barta. 

 

 

 

"Sannan zan roƙi wata alfarma a wajenki,na bazaki tafi da Joda cikin masarauta ba" 

 

 

 

Wani kallo ummah ta watsamasa da sauri dataji kumadu wani batu daya furta. Bazai bari nabi ummah taba ina yakeso naje kenan ko mai yake nufi? 

 

 

 

"Baka isa ba,bayan yaudarar dakayimin kuma sannan kanemi rabani da ƴa ta bazan yarda ba" 

 

 

 

Tayi maganar tana ture hannun wani wanda ya yake ƙoƙarin fizgeni daga wajenta. Da dukkan ƙarfinta take ƙoƙarin wajen ganin bata rabu dani ba,amma ƙarfin na miji ba ɗayane da mace ba,macen ma wacce ta gama wujijjiga ƙarfinta duk ya ƙare wajen kare danginnata. 

 

 

 

Tausayinta ne yakamani hakan yasa nima nafara kuka,ganin yadda zuciyarta ta karye tana rusa kuka tareda kama ƙafar baba Yakub tana roƙonsa akan yabarni da ita,amma ya sai ya juya fuskarsa can gefe domin karsu haɗa ido. Wani nazari nayi da yanayinsa,duk yashiga cikin damuwa saboda kallon abinda ummah ta takeyi. Da alamun bayason halinda yasakamu a cikin. Sannan a yanayinsa bayyi kama da maison abun duniya ba,to menene yasakashi yin hakan. Na bawar kaina wannan shakkun. 

 

 

 

Wannan mutanen da suka riƙe ummah ne sukazo zasu fitada ita. Sambatu takeyi duk tafita cikin hayyacinta,wani abun tana ganewa wani kam bama sanin mai take cewa. Soyayyar ta da tausayinta sun cikamin zuciyata,ƙirjina yayimin wani irin nauyi da bansan wanne iri bane. 

 

 

 

"Baba Yakub ka Yaudareni,saidai bansan dalilinka nayin hakan ba,domin a tunanina kafi ƙarfin hakan,bazan sake ja dakai ba domin nasan bazan samu nasara ba,kaman yanda a lokacin baya akayimana muka kasa ɗaukar mataki. Bansan ina zaka kaimin ƴata ba kokuma mai zaka mata,amma ka sani komai zakayi Allah yana kallonka kuma shine ganina da jina akanka,domin ƙarfin addu'a ta da hawayena bazasu taba barinka ba. Sannan alfarma ta ƙarshe da nake nema a wajenka shine ka suturtamin gawar mijina,kayimasa sallah kaman yanda akewa wanda aka ɗaukeshi ɗan adam ba irinmu ba.” 

 

 

 

Tana kawowa wajen da bayaninta maza biyun suka fizgeta zuwa waje,da tayi ƙoƙarin fizgewa wani daga cikinsu ya zabga mata mari ,akan idona hakan yafaru saida na runtse idona,domin ji nayi kaman ya sauƙewa marin akan kuncina. Lokaci ɗaya ƙwaƙwalwata ta farka daga mafarkin data faɗa a cikin jirgin,ashe duk rayuwar nishaɗin danayi mafarki nakeyi,sai yanzu idanuwana suka buɗe nakalli menene zahirin rayuwar danake ciki.  

 

 

 

Ganin cin fuskar da akewa ummah tah yasa baba yakub yimusu magana da su daina dukanta,ina kallonsu ta inda jikin yadin tantin ya tsage har suka bacewa ganina,banida ikon binsu,sannan banida tabbacin shin zan sake ganinta a rayuwata ko akasin haka. Zaffan hawayen daya gangaro daga idanuna nasaka hannu na goge. Yazamin dole a rayuwata na tashi tsaye,nayi yaƙi domin samun damar kare ɗan abinda yake nawa.