Chapter 8
*MIJIN KANWATA..*!
_(k'addarata)_
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty❤️*
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*Page 8*
Kwanakin da suka Biyo duk na Shiryen Shiryen Daurin auran ne Hajiya Zabba"u da tawagansu Hajiya karama da ya"yansu gabadaya gidan Tun Ranar Laraba suka sauka a kargi Sadiq kadai suka Bari agida sai Ranar Jumma"a sai Biyo Abba su Taho tare Hatta da wasu Daga cikin Hadimansu Hajiya ta taho da wasu aminttunta domin ita tafi yarda tayi aiki ko Mu"amala da wanda ta aminta dashi.
Uwar Amarya kuwa Hajiya Salame sai da kowa ya gama zuwa kana ta iso Ranar Alhamis da yammah ita da gayyarta ta Fake da cewa Amarya tayi Lonching ita da kawayenta achan Jos alhalin bayan Taron harda Tsaikon Kawarta Dataje Maradi karbo mata sako sai da ta Jirata ta dawo ta bata sakon kana suka Dunguma suka iso Kargi.
Gabadaya Ahalin Maimartaba na Nesa dana kusa sun Hallara Domin wannan Bikin Hajiya Zabba"u yadda taci Buri akansa in ma wani bai zo ba ai sai ta Kullacesa nan da nan aka Bude Store din Masarauta Ana ta fitowa da kayan abinci Nau"i Nau"i dabam dabam Hadiman Bangaran Madafa suna ta aikinsu.
Amarya ashashen Kilishi aka Sauketa ita da kawayenta Guda Biyu da suka Taho Daga jos sai sauran Dangi yan Biki,sauran suna Shashen Fulani da sauran manyan Sassan Gidan na Sarkin Kargi mai Girma da Fadi.
Sulaiman ya Fadama Saifullahi yadda sukayi da Sunaima sai ya nunamai ya Bata Kudi saboda Hakkinsa ne zai kara aure Tunda ita ba"ayi mata kayan akwatin Dannan Kirji kamar na al"ada ko alokacin Tarewarsu Abba ne yayi mata kayan auran Hajiya karama ita ta Hada kayan shiyasa da Saifullahi yace ya bata wani abu ya Ciro Kudi a banki Sabbin yan Dubu Dubu na 50k ya saka mata ambulan ya rike a wajensa da Niyyar Ranar Jumma"a Da Safe zai bata kafin su wuce.
Rana ai daman bata karya sai dai Uwar Diya ta ji kunya Tun karfe 8am na Safe Saifullahi ya iso Gidan Sulaiman yana Jiransa Tare zasu Tafi Zasu Biya Gidan su Sunaima su Dauki Baba,Tunda zai je sai sulaiman yace ya bari su wuce Tare Sani kuma yana Kamfanin Madaran Sulaiman yake karban packages wanda zasu tafi Dashi Chan Kargi saboda Maimartaba da Sauran iyayan Sulaiman din.
Saifullahi yaci Shadda Riga da wando Harda Babban Riga kalan Sararin Samaniya,ya kafa Hularsa Zanna Bukar da Rufaffan takalminsa baki na Fatar damisa.
Yana ta Kiran Sulaiman yace mai gashinan Fitowa shi kuwa alokacin Ya gama Shirya kansa Cikin Wani Rantsntsiyar wangambari mai maiko da yarari akalah zata bama Dubu hamsin baya Kalanta Sky Blue ce,ya saka yar ciki da Babban Riga sai ya Dora Hularsa Zanna mai Zanen kalar Shaddarsa ya saka bakin Takalminsa rufaffe na Fatar damisa sai agogon Hannu baki shima na kamfanin Rado.
Yayi kyau har yagaji da kyau duk da Fuskarsa ba Fara"a sosai yasan ai bai isa ya Zillema wannan Daurin auran ba Tun Jiya Hajiyarsu ke kiransa wai yana Hanya ne..?ya fadamata sai gobe zai Taho bazai bar ma"aikata ba kowa ba wane shi ya kwanta yace bazashi ba yau da garin Allah ya waye baisan adadin Kiranta dana ya"yanta Daya gani ba Harda Kiran Hajiya karama yayi bakam Domin yasan Duk Hajiyace zatace su Dokamai Kira daga yau ai shikeman anyi an gama Sai Hajiya ta barsa ya Huta.
Yana Saukowa Daga Saman Upstair yana amsa Kiran Saifullahi Daya Gwazabamai da Kira ya Daga wayar Cikin Muryansa akoda yaushe yana Fadin"Kafa isheni da kira..Gani nan Saukowa..!
Saifullahi yace"Su Abba fa Tuni sun kusa isa kargi..kai kana Kaduna kana batamana Lokaci..!
Tsaki yaja ya Datse kiran daidai Lokacin yana isowa Falon daya iske Magajiya tana ta gyara Dukawa Tayi ta Gaisheshi ya amsa mata sama sama yana Fadin"Yaran nan sun tashi kuwa Magajiya..?
Kanta na kasa tace"Eh Tun dazu ranka ya Dade..Hajiya ai ta shiryasu itama na ganta ashiryenta ko har dasu zaku Tafi Chan Masauratar Yallabai..?
Kai ya girgiza kafin yace"A"a Gidan su zasu je..Keda da Samira zaku zauna agida in kuma Zata tafi Dake chan Saboda Yara shikenan..!
Bai bata ma Zarafin mgana ba ya Tunkarin Dakin akoda yaushe yana Samun Faduwar gaba indai zai Tun kari Dakin
Ya tura da Niyar shiga yaji Dakin a Garkame,sai ya tsaya yana Knooking Lokacin Tana kokarin sakama Wafiyya Takalminta dan karamin Cover na yara taji Buga Kofar ita Duk azaton to ko Magajiya ce Domin ta Sata Hada musu abinci a lunch Box dinsu da kayan da zata tafi dasu kai Tsaye ta Mike bayan ta gama Sakama Wafiyya Takalmin tana gyara Zaman zanin Leshin Dake Jikinta ta Tunkari kofa kanta Tsaye Wafiyya kuma tabiyo bayanta Digi Digi da Tafiyarta na yara masu jiki.
Bata kawo ma ranta shine ba yasa ta Bude Kofar kanta Tsaye tana Fadin"Sannu magaj....!
Sauran kalamanta sun makale ne sanda Fuskokinsu suka Hadu waje Daya Domin ta bude Kofar ta Tsaya shi kuma bai kawo komai ba ya Tusa kansa zai Shigo goshinsu ya Hade waje Daya sannan Karan Hancinta ya Gogi nashi Dukkansu atare suka Janye Jikinsu Lokaci Daya da wani Bakon Yanayi ya Ziyarce Sunaima Hannunta ya kusa Takore kofar saboda Tayi Saurin janyen jikinta Cikin Zafin Nama Saraki ya Rike hannun nata gam Har sai da yaga ta Tsaya da Kafafunta Idanuwanta Ta lumshe kafun ta Budesa tsab a kansa Shima kallonta yake cikin wani yanayi bai Taba ganin tayi kwalliya irin na yau ba Tunda yake da ita.
Tana Sanye da Daya Daga Cikin Swiss less din Da aka sakamata Cikin akwatin Lefenta,Bata taba saka atamfa ko wani less ba sai dai Takan yi amfani da kayan barci ko Dagayen Riguna sune kayanta bata zuwa Biki bata zuww suna Daga Gida sai wajen aiki Shiyasa amfanin da kayan suka zame mata Wahala bama Haka ba Duk Abunda ya Shafi Sulaiman Kargi Hakuri kawai take tana amfani Dashi Domin babu yadda Zata Gujema Kaddaran data Hadasu zama waje Daya.
Dinkin riga da Zani ne Rigar Fittied ce data amshi Jikinta Matuka Ta Daura Dankwalinta saman Kanta wanda ya Zauna Tsab saman gashin kanta da ta nannadeshi Cikin band,fuskarta ba Kwalliya sai dai ta shafa Hoda da Man Baki mai kalan Ja kalan sai Dankunneye Kunni da wuya sai awarwaro hannunta Tayi kyau matuka kamar ba ita ba ahaka sai ya ganta kamar Sunaira sai dai bambamcin ita Sunaira Tafita jiki da Kiba ayayinda Sunaima take yar Ficika da ita bata da Cikar Jikin Hallita ballatana cikar Dakin Miji.
Ya Shagala da kallonta yasa baisan tana Kokarin zame hannunta ba sai da yaji ta Zame hannun nata kana yadan Basar Cikin Muryansa akoda yaushe yace"Are u ok..?
Kai ta gyadamai Tana kallonsa Ta gefen Ido bata wani Tsaya karemai kallo ba ammh tasan yau kam yasha kyau sosai,Wasim ne da Wafiyya ne suka ga Babansu suka Nufesa suna Kiran Daddy Daddy dukawa yayi ya Tarbesu Dukkansu ya Daukesu Lokaci Daya yana Fadin"Eyye..Kunsha kyau..!
Yake Fada yana kallon Sunaima Data koma Bakin gado ta Dauko bakin Hijabinta ta saka Bata ma juyo ba ballatana ta Fahimci yana kallonta.
Wasim yana Sanye cikin Riga da wando na Shadda,Irin wanda Sulaiman ke Dinkamasa ne,harda Hulansa yayi kyau sosai sai Wafiyya Dake Sanye da Bulawis na yara Iyakarsu gwiwanta mai kalan ja da Fari kanta Sunaima ta saka mata karamar Hula ta Rufe mata kananan Kalaban Datayi mata Jiya da Daddare.
Dukkansu suna sanye da Takalma Rufaffu ne.
Wasim ne mai Surutu fadi yake"Daddy Anty tamana wancha..Ta sakamana sabon kaya zamu je gidan Inna..!
Yake Fada yana Murna Wafiyya ganin Yana Murna sai ita ta fara Washe baki Tana gaurancinsa Shi kuma yana Biye musu Cikin Sha"awa da Burgewa Takawa yafarayi zuwa Cikin Dakin Lokaci Daya ya saka kafa ya maida Kofar ya Rufe har tayidan karan Daya sa Sunaima ta waigo tana kallonsa Bai Taba ganinta da mayafi ba Koda yaushe Cikin irin wadanan Hijaban take masu Daurewa ta saman kai.
Ganin Tana saka wayarta Cikin karamar Jakar Dake hannunta yasa yace"Kuma kun Shirya kenan..!?
Dakai ta amsa mai batace komai ba ganin yaki Sauke yaran yasa ta Dago Tana Fadin"Daka Sauke su..kada su bta maka kaya.!
Mamakinta ya kamasa sai bai ce mata komai ba illah gyara Tsayuwarsa da yayi yana Fadin"Wazai kai ku..?sani na aikesa kuma Dagachan zai wuce Kargi ne..!
Bata Damu ba tace"Daman ai ban saba Shiga Mota ba..Adaidaita Shine Daidai da dan Talaka irina..!
Dakuna Fuska yayi yana kallonta Ita kuma sai ta maida kanta Gefe Cikin Kaushinsa yace"Ko Sau Daya bazaki koyi da Halin yar"uwarki ba..Sunaira ba Haka take ba..Ba haka takemin mgana ba..!
Sai da ya fada sai yaga baikonsa itama sai kalamansa ya bata mamaki ganin ta Tsaya tana Nazarin mganarsa yasa ya Sauke Wasim da wafiyya a kasa ya Saka Hannu a aljihun Wandonsa ya Dauki Farar ambulan din Daya sakamata Kudi ya mika mata Kin karba tayi tana kallonsa Cikin Rashin Sakewarta tace"Name nene..?
Kai Tsaye yace mata"Kudi ne..Ki rike a Hannunki..!
Nokewa Tayi tana Fadin"Bazan karba ba..Nacemaka bana Bukatar komai..!
Bai Tsaya Sauraranta ba jin yadda Wayarsa ke Daukan Agaji yasan Saifullahi ne kan Jakarta Dake gefen gadon ya ijiye mata yana Fadin"Koda baki Bukata ya zama Dole ki karba..Hakkina ne na baki kuma kema Hakki ne ki karba..!
Ku fito mu kaiku daman zamu Biya mu Dauki Baba..!
Yafada yana Kokarin Ficewa Daga Dakin Sunaima Cikin mamaki tace"Baba..?
Juyowa yayi yana Fadin"Eh yayi Laifi Saboda zai je Daurin aurena..!
Baki ta Mele batace komai ba Shi kuma sai ya Duka ya Dauki Wafiyya data Biyosa ya Rike hannun Wasim suka Fice Daga Dakin bata tsayama kallon Kudin ba ta barsa nan saman Madubin Dakin ta Dauki jakarta ta Rataya bayan ta saka wani Takalmi Flat baki ta Fito Daga Dakin haka kurum Taji tana Bukatar Sirri ta Saka Key din Dakin ta kulle aharaban Gidan ta gansu suna jiranta ga Samira ga Magajiya suna Tsaye bayan ya gama Fadamusu su kula da komai.
Magajiya ce tace"Hajiya da Yallabai yace Tare zamu tafi..!?
Sunaima tace"Eh haka yace..Ni nace kiyi Zamanki ai zan iya Kula dasu..Gwara ki Tsaya agida ki kula da komai Domin ba lalle bane wacce aka bari tayi yadda ZAi yi ma su Hajiya Dadi in sun iso ba..!
Tafada kanta Tsaye ta koma kuma ta Tauke bakin kamar bata taba Dariya ba Samira na jinta tasan da ita take Mirmishi tayi batace komai ba Domin Hajiya Laila na zuwa ai yar Dakinta Zata koma alokacin ne Zata gasa ma wannan Tsohuwar gyada ahannunta.
Abayan Booth aka saka karamar Jakar kayan su Wasin da Tarkacen madaransu harda kayan Wasa Sulaima ya shiga gidan gaba Dauke da Wafiyya ita kuma Saifullahi ya Bude mata Gidan baya yana Fadin"Antynmu barka da Safiya..!
Kadahan kadahan ta amsa mai aranta tace in ma Gatse kake ai sunan kenan Daga haka ta Dinke ranta Sulaiman kuwa Nata Hararan Saifullahi ji yake kamar ya Bugesa in yana Fadin Antynmu din nan to Antynshi shi da Uban wa..!
Har suka Fice Daga Gidan su magajiya da Megadi na Binsu da adawo lafiya da Fatan Allah yasa a Daura aure Lafiya.
Tunda suka Dauki Hanya bata ce komai ba sai Wafiyya Datake ta Gaurancinta Wasim kuma na Jikinta yana Wasansa sai Saifullahi ne ke mganar abokan aikinsu da ma"ikatansu suma duk wasu sun wuce chan Kargi,Sulaiman na Jinsa kala dai bai ce ba sai lura yake da Sunaima ta madubin Mota ita batasan ma yanayi ba shi kallonta yake yana so ya gani Da gaske ne ashe basu kama da Sunaira sai ayanzu yake yarda Sunaira Tana da Dan Fadin Fuska yayinda Sunaima keda Doguwar Fuska ga kananun Idanuwa kamar kuma sai dai kama kawai ta Jini.
Cikin Lokaci sai gasu sun iso anguwar dosa kofar gidan su Sunaima Tun daga nesa suka Hango Ahmad Tsaye Kofar shagon Hamisu yana Tsaye yaci Farar shadda kayan sallansa ne na bara harda Hula Tunda Sunaima ta Hangosa tasam Ahmad yaci Burin shima sai Baba ya tafi Dashi Mirmishi tayi acikin Ranta sanin Halin kanin nata.
Yana ganin Motar ai yasan Motar Sulaiman ya taho da sauri suna gama parking ya Bude ma Sulaiman gaba yana Fadin"Ah yallabai barkan ku da zuwa..Daman mun Shirya ni da Baba kumuke jira..!
Wafiyya na ganinsa ta fara Zillo"anchul..!
Yana Dariya ya mika hannu Sulaiman ya bashi ita yana Fadin"Akwai amana Yar gidan anchul!
Sulaiman yana kallonsa cikin Fara"a yace"Ahmad harda kai za"a je..!?
Yana sosa kansa yace"Ai na Shirya ne kawai..ka tayani Rokon Baba yabari nidai yau naje masarautarku Ranka ya Dade..!
Saifullahi Daya kariso wajen yayi yar Dariya yana Fadin"Mallam Ahmad kada ka damu yau dakai zamu je Kargi da yardan Allah..!
Fadin haka yasa ya washe baki Sunaima Da ke cikin Mota ganin sun manta da ita yasa ta Bude Murfin Mota ta Fito ita da Wasim sai alokacin Ahmad ya ganta yace"Ah..Antynmu...Wai Allah sai da kika ga zan yi tafiya zaki zo..!?
Yafada yana Dariya Wasim ke ta Kiran sunansa yasa ya rike hannunsa Sunaima ta Dungurema Ahmad kai tana Fadin"Ba inda zaka ayaho..Muna Gida Tare dakai da Inna..!
Ahmad ya bata rai yana Fadin"Ah fa nan fa Daya Antynmu..yau kam Fadan Sai dai kijisa ke kadai nida Baba Allah yayi mana Freemode yau..!
Dariya ta kamata har sai da ta Murmusa ta Bugi kafadansa ta Fara Tafiya tana Fadin"Sai na Fadamata..!
Yace"Oh ko kin Fadamata taga bata ganni ba kanki zata Sauke gwarama ki Rufa asiri..!
Hamisu mai shago ne ya kariso yana Gaisheta ta amsa mai Cikin Dan Sakewa Sun nufi hanyar shiga gida ita da Ahmad da yaran wanda ganin Sunaima yasa ma ya manta da su Sulaiman dake binsu da kallo Saifullahi ya karkato Gefensa yana Fadin"Wlh kadai ji kowa Anty yake Kiranta..Anya Kiran sunanta kai Tsaye ba Rashin ta ido bane..!?
Karamin Tsaki yaja zai yi mgana sai ga Baba ya Fito yana gyara Babban Rigansa sun kusa cin karo dasu Sunaima ganinsa yasa ta Tsaya Cikin Fara"a yake fadin"Maraba da Sunaima..Ah maraba da Aliyu da Zabba"u..!.
Yaran suka fara Kiransa Baba baba..Wafiyya ya Dauka Wasim kuma ya Dafa kansa Sunaima Ramkwafawa tayi tana Gaisheshi ya amsa mata Cikin Sakin Fuska Sulaiman su yake Kallo sai yanzu yagano dawa Sunaima Take kama da Babanta ne Domin Harta Tsarin Dariyarsu irin Tashi ce.
Karisowa sukayi suma suka rankwafa suna gaisheshi ya amsa musu Cikin Fara"a yana Fadin"Ai tun dazu na Shirya kada kuzo kuna jirana..!
Da sauri Ahmad yace"Wlh ai tun Safe muka shirya ko Baba..!?
Hararansa yayi yana Fadin"Na gayamaka bazan je dakai ba ko Amadu..?
Baki ya Tura yana Fadin"Plz Baba..!
Sunaima tayi yar Dariya Tana Fadin"Baba kada kaje dashi..!
Ya marairaice yana kallonta yana Fadin"Kai Antynmu..kar muyi haka Dake..!
Saifullahi ne yace"Baba kayi Hakuri muje dashi ai ba komai Duka Dayane..!
Sulaiman dai bai ce komai ba Baba ya kalli Sunaima yana Fadin"Sunaima Dake za"a tafi chan kargi ne..?
Da sauri Sulaiman yace"nan zata kwana ita da yara Baba..ai ba Taro bane sai zuwa gobe sai ta koma in sun kawo Amaryan..!
Sai da kuma ya fadi Amaryan sai ya Dago yana kallon Sunaima ita kuma ta kauda kanta Baba yace shikenan Daganan sunaima taja ya"yanta suka shige cikin Gida Ahmad na Fadin tace na Inna su sun wuce ta shige Tana Dariya Daman Inna taji Hayaniya Daga Zaure.
Tana ganin Sunaima ko bata Fada ba Taji Dadin ganinta saboda akwai mganar datake so suyi da juna Maraba da sannu da zuwa ta fara musu yaran suka Riketa suna mata Oyoyo Inna na Dariya tace"Ai yau Inna Zatasha Kira..!
Sunaima na Cire Hijabinta tace"Inna Har gobe ma..nan zamu kwana..!
Bata gama Rufe baki ba sai ga Ahmad da Tarkacen kayansu ya ije ya Fita da Gudu yana yi musu Bye Inna ta Bisa da kallo Tana fadin"Wannan yaro dai sai Allah ya shirya..!
Sunaima tayi yar Dariya tana Zama kan Tabarman da Inna ta Shinfidamata ita kuma tana Fadin"Kamar da sanyin safiya wajen nan..Ko zaki shiga ciki ne..!
Tace"Bari dai mu zauna nan Inna..Ina kwana..!
Inna tace"Lafiyalau..su baban naku sun wuce ne..?
Kai ta gyada kafin tace"Eh shi ya kawo mu shi da abokinsa sun Dauki su Baba sun wuce..!
Inna ta kada kai Tana Fadin"Allah ya Kiyaye Hanya..Uhm..Allah yasa a Daura aure lafiya..Sai mukaji Aure Daga sama Daman ko baki zo ba Wlh zan kira ki Sunaima na kuma ji Dadin da zaki kwana anan zamu samu Lokacin mgana Sosai..!
Sunaima tabi Inna da kallo batayi mgana ba to me zatace ai tasan Tsatsuniyar gizo ai bata wuce ta Koki.
*****
Achan Kargi kuwa Fada ta Cika makil Ranar duka Ya"yan maimartaba Mazan dasu akayi sallar jumma"a a masallacin Fada bayan an idar aka Gudar da Daurin auran Sulaiman Aliyu Sulaiman kargi da Amaryansa Laila Isa hamza Kargi akan Sadaki mafi Daraja Tuni maroka da masu algaita da masu Shela suka Fara aikinsu Daga Cikin Gida jakadiya kuwa ita ta Shiga da Labarin Daurin auran Cikin Babban Gidan na Sarkin kargi Tuni Waje ya Kaure da Guda da Kirarin Amaran gidan Sarauta ana Daura auran aka sakama Laila akyabba kamar yadda al"adar Gidan ta gada.
Sauran abubuwan da suka biyo baya an shi ancha anyi Soyaye nama da kilishi da gasassun kaji shanaye akayi ta yankawa aka Gashesu abun sai wanda ya gani Ahmad ai bakinsa har kunne yau gashi acikin Fada yana ganin yadda Suke gudanar da Bikinsu bama wannan ba ba"a ware su ba suna Cikin Fadar Sarki Domin sunji Dadin wannan karan matuka da Baba yayi musu.
Daga Cikin Gida kuma Hajiya Zabba"u Burinta ya Cika suka Rumgume juna da Hajiya Salame suna ma juna Barka Haka ta Rike Laila tana dariya haka su Safiya dasu Raliya kowa kagani baki har Kunne yau Ya Saraki ya Cika Burin Hajiya sauran Shagulgulane suka Biyo baya na al'adun Gidan Sarauta sunyi Kilasa wanda Saraki yaso yaki ki Ashe Hajiyarsu ta Shirya komai Ranar an sha Kilasa Saifullahi ya Hau Doki Amaryama ta Fito ta Sauke Angonta saman Doki ta Fesamai Turare,Sulaiman bai ga Fuskarta ba Domin Hulan alkyabban ta Rufe mata Fuska sai hannunta kadai ake iya gani abunda kowa bai sani ba ba Laila bace saboda Sharadin Mganin da Salame ta kashe makudin kudi akansa bazasu hadu da Sulaiman ba sai agobe an kaita Gidansa kuma gashi An matsa sai anyi Kilasa shiyasa taso ta daujema abun ammh ba Hali ita da kawarta Hajiya Zaliha da suka Shirya komai aka saka Laila ta Cire kayan Jikinta Tabama kawarta da aka Duba yanayinsu kusan Daya ta kuma bata akkayyaba da Takalminta Daman Itana tasha kushi sai ba wanda ya gane ba Laila bace wacce suka Boyeta Chan Cikin wani Daki Dake Shashen Fulami dasu kadai ya"yan Sarki sukasan da Boyayyan Wajen.
Ahmad yasha kallo cijen yatsa yake da yana waya babba dasu inna sun sha Kallo yana Tare da sani Direba Daya zama kamar dan masarauta Har shi sai da Sulaiman yayimai Izini yahau Doki su sani an iya Shishhigi.
Mahaifiyar Saifullahi tazo Kargi Taya Hajiya Zabba"u Murna kuma Hakika Taji Dadi a bangaran na Musamman aka Sauketa ana mata Hidima.
Har Dare masarautar tana Cike da jama"a su Abba dasu baba Sa"idu suna ta shan Furan kamfanin Sulaiman suna sakamai albarka Domin kebaanttacen waje suka samu suka zauna gabadayansu suna Hira ta yan"uwa Baba yaso su koma aranar Sulaiman ya hana shima yana cikin su ko Daya basu ware shi ba Shiyasa yake ganin Kimar wannan babban Masarautar data maida Takala nasu kamar Duka Dayane.
Washegari kuma aka tashi da Shirin Tahowa Kaduna kawo Amarya karfe 10am na safe zasu tafi Tunda aranar kowa zai watse,Hajiya Zabba"u wannan karon bata ita ba,ita da Hajiya Salame Daga Kargi sai gidajensu Dukkansu Wakilai suka Tura ita Hajiya Zabba"u hajiya Falmatace kan gaba sai ya"yansu bangaran Amarya kuma akwai su Hajiya Uwani Hajiya Jamila da Hajiya Bilkisu Ta lagos Dayake tazo su da sauran ya"yan su da Hajiya Zaliha kawar Hajiya Salame da kawayen Laila zasu rakata Gidanta Dagachan Wasu bazasu dawo kargi ba irin su Hajiya karama da Tawagan ya"yansu Abuja zasu wuce hajiya zabba"u kuma sai gobe zasu dawo ita da Abba.
An kai Laila Shashen Fulani ta mata sallama bayan Kilishi tayi mata Daganan aka kaita manya Sassan Gidan tayi sallama dasu Daganan sai Fadar Maimartaba Sarki Sulaiman Kargi.
Kafin akaita Fada sai da Hajiya Zaliha tace abar Uwa da ya suyi sallama sai aka basu Daki guda suka Kule aciki.
Hajiya Salame ta Fito da Wani kullin mgani abakar Leda ta warware agaban Laila wacce take kallonta Cike da mamaki sai da ta gama Kwancewa kana ta Dago abunda ke Ciki wani Kwalli ne a karamin kalba da maciyinsa kadan acikin wata karamar kwalba Bakin abu ne aciki Dis baki sosai yana Daukan iso sai kuma wata karamar Kwalba mai Dauke da Turare Fari kar dashi kamar almiski shima Kadan acikin kwalban ta Zauna Gefen Laila Lokaci Daya tana Fadin"Laila Yaye wannan alkyabbab ki Dago ki kalleni Dakyau da duka Hankalin da Allah ya baki..!
Ba gaddama tayi yadda Uwar tace mata Kyakyawan Farar Fuskarta ta Bayyana Laila ba Doguwar mace bace Gajerace sannan tana da Jiki har asaman Fuskatra Kibaanta ta bayyana irin Jikin Yara yan Hutu da fatarsu ta samu jin Dadi sosai.
Hajiya Salame ta Rike hannunta Guda na Dama ta Damkamata mganin nan Guda Daya mai kama da kwalli Tana kallonta Cikin mamaki Laila tace"Mommah nameye wannan..?
Hajiya Salame tace"Kinga wannan abun da na baki..Kwalli ne kuma Sau Daya Tak zaki amfani dashi..!
Laila ta Cigaba da kallonta da karin Bayani yasa ta gyara Zama Tana Fadin"Eh sau daya ina Nufin in kika Sakashi Sau daya bazaki kara amfani Dashi ba Har Abada amfaninsa ya gama..Zaki Sakashi nebayan an kaiki Gidan Sulaiman an shigar Dake Shashenki..Zaki sakashi ne bayan Kin Tabbarar bazaki hadu da kowa ba sai shi wannan kwallin an yi shine Domin Sulaiman kadai in kika Sanyanshi kika Hada ido da wanda ba"ayi mganin Dominsa ba kin bata komai Laila.!
Laila ta kara kallon yar kwalbar Dake hannunta kafin tace"Duk saboda menene haka Mommah..!?
Kai ta Girgiza tana Fadin"Dadina Dake baki cin Riban zence ki bari zan miki bayanin komai mana..Yanzu rike wannan Turaran shima.!
Hada mata tayi awaje daya ta Karba tana kallo kafin tacigaba da Fadin"Wannan Turaran shima Sau Daya zai miki amfani Laila amfaninsa ki Gogosa a hannunki na Hagu ki kisan yadda zaki yau ba sai gobe ba kin Shafi Tafin Hannun Sulaiman na Hagu da wannan Turaran ina Fatan kin jini kuma kin gane sannan zaki aiwatar da abunda na Umarceki.!
Laila tace"Mommah naji zan yi komai kuma na gane Buh ammh baki gayamin Why zan yi wadanan abubuwan ba Ni da Burina ya gama Cika na Samu Saraki..!
Hajiya salame ta mata wani kallo kafin tace"Ke yarinyan ce baki san komai ba..Waya Fadamiki da kin Auri Sulaiman shikenan ai da Sauran aiki agabanmu..Sulaiman ya aureki ne Domin ba yadda zai yi ammh ke kanki kinsan ba sonkiyake yi ba har yau har gobe..Duk da Uban Wahalan da kikasha akansa!
Laaila tace"and so..ai na zama matarsa komai ya kare Mommah..!
Hajiya salame taja Tsaki kafin tace"Dubeni Dakyau komai bai kare ba..Shiyasa ban zauna ba Laila na Shiga na Fita na Kashe kudade saboda ki Samu yadda kike so agidan Sulaiman bana soWahalan da kika sha Kafin ki auresa kuma bayan kin auresa ki kara Ninka wannan Wahalan..Wannan mganin da na baki Har maradi naje nida Hajiya Zaliha makarin Mganin Mallakan Sulaiman ne da naba kudade masu kauri akayi Miki in kika yi yadda na Fadamiki Wlh Tallahi ko Zabba"u sai kin basa Unarnin ya Daga ido ya Dubeta zai Dubeta Laila zaki Juya Sulaiman Dashi da Duk wanda ke karkarshinsa Indai kikayi wannan yadda na Gayamiki..!
Laila ta Dan Washe baki Tana Fadin"Mommah da gaske..?hajiyarsa ta san da wannan..?
Hajiya Salame tace"Ina mai tabbarar miki..Yau ba sai gobe ba zaki Zama Taurarura a wajen Sulaiman bazai ji ba sai ke kuma bazai ga kowa ba sai ke..kuma kada ki sake ki Fadama wani wannan Labarin Hajiya Zabba"u batsan komai ba ke yata ce..Akwai Sirri Tsakanina Dake kamar yadda ita ma akwai sirri Tsakaninta da Danta bakomai take Fadamin ba.kada ki yadda ki Fadamawa kowa in kika Kuskura wani yaji mganar nan bayan nida ke da Hajiya Zaliha zaki Kara Lalata komai Laila..!
Laila ta Jimke mganin A hannunta Tana Fadin"Wlh bazan Fadama kowa Ba..Mommah kuma i promise u zan Yi yadda kikace ko domin na samu yadda nake so agidan ya Saraki na Rama kwatankwancin yadda Soyayyarsa ta bani Wahala..!
Hajiya Salame dataji Dadi ta rumgume yarta tana Fadin"Yauwa My Dota...!
Laila tayi Mirmishi kafin tace"Mommh matar sa fa..?harda ita zan mallaketa..!
Hajiya salame tace"Ita din banza..ita da banza Daya suke agidan..Kikama Mulki wanda ya ijeta ballatana ita..Ke fa kina da yarintarki har yanzu Laila dashi zaki nuna mata Banbamci Karamin kashi da wanda kashinsa ya Nuna Tun agida..!
Sannan sharadin Mganin na karshe shine awannan lokacin dakika gama amfani da duka sharadin na karshen shine kiyi yadda zakiyi Sulaiman ya kusanceki..Saboda Haduwar Maniyinki da maniyinsa shine makarin mgani na karshe da hakan ta Faru komai ya kamallah sulaiman da gidansa sai yadda kikayi dasu..!
Laila tayi wani Dariya kafin tace"Tanque Mommah..U are d good Mother ever in this World..!
Rumgumr juna suka sake yi kafin Hajiya zaliha ta Leko tace su fito su ake jira Mganin Hajiya Salame ta mayar mata aleda tabata a hannunta ta Jimke kana ta mikata wajen Hajiya Zaliha bayan ta maida Hular alkyabbanta ta fito ita wajen su Hajiya Uwani suka shiga da ita wajen Maimartaba.
Ya Dafa kanta yayi mata addu"a da Saka albarka tare da Nasiha kana aka Fito da ita saman Doki zuwa wajen Mota Saifullahi shi ya Dauki Amarya Saraki yabi sani tun dazu sun koma Kaduna shi da Baba da Ahmd basu da mtsalan Motoci bayan na gidam kowacce ai ta mallaki Mota yawanci da Direbobinsu suke tafe.
Kwambon Motoci ne sun fi ashirin aka Hada ajere zuwa kaduna Karfe 2pm da wani abu na Rana suna Kaduna Saifullahi Mahaifiyarsa tun Safe ta koma kargi bata samu raka Amarya Kaduna ba..
Koda suka iso sun samu Tarban Magajiya da Samira da suka gama komai na Taryansu Dama Maimartaba ya bama Laila kyautar Hadimai guda Biyu da su aka Taho.
Kai Tsaye ba"a sauke Laila ako"ina ba sai kayattacen gadonta Daya ji Shimfidun alfarma Dake Shashenta Bayan an Bude Barayin Ba wanda ya Damu da rashin ganin Sunaima sai Hajiya karama da Magajiya ta shaida mata btanan tana gidansu tun jiya.
Ita ta kira Saraki dake Kamfani tacemai bai kamata azo gida Sunaima batanan ba yace tana Hanya tun dazu ya Tura sani ya Daukota ita da yaran.
To bayan sun gama mganar ne ba Dadewa sai ga Suniman ta Dawo ita da yaran Wlh acikin wajen nan banda Iyayen irin su Hajiya Uwani ba wanda ya amsa mata sallama ballatana gaisuwanta sai Sadiya da Sadiqa da suka Nufi yaran suka Dauke su Raliya kamar sun ga kashi Sauran suna Sama Shashen Amarya sauran kuma suna kasa suna cin abinci yaran kuma sun kannen Ubansu suka Nane musu Sunaima Tana gama gaisawa dasu Hajiya karama ta Shige Dakinta Tana Boye kwallarta Lokaci Daya Tarin Nasihun inna suna Dawo mata Daki Daki.
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*Janafty*