BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 7

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA❤* *Arewapen@ayshadansabo*

©️ _Ayshat D'ansabo_ _lemu_✍️

*Free page 7*

Gabaki ɗaya kayan dake cikin sif ɗinta take fiddosu tana zaran wanda ya yi mata,tana sanya shi cikin kyakykyawar trolley ɗinta dake aje bisa gado.So take ba sai ya tsaya jiranta shirin kaya ba,idan yazo gobe ko jibi kamar yadda yace.Ta kammala shirya kayan ta zuge trolley ɗin tare da aje shi gefe guda,ta shiga maida kayan data fiddo cikin sif ɗin tana shiryasu.Wayarta da ke aje gefen bed side drawer ya fara ringing,daidai da kammala shirya kayan a cikin sif.Hakan yasa ta rufe sif ɗin tana komawa da baya ta zauna bisa bakin gadon ta ɗaga wayar,cikin muryarta mai sanyi da daɗi take gaidashi.Bata ɗauki tsayin mintuna biyar ba ta yanke wayar tana ɗan sakin ƙaramin tsaki,Ya Mubarak ne ke kiran,tunda ta bashi dama shikenan yake fitinarta ko yaushe cikin kira yake.Haka ba dama ta hau online zai nuna sai dai ta talike a kansa,yanzu haka sanar mata yayi gashinan ƙarisowa gidan nasu domin su yi sallama,tunda ta shaida masa cewa gobe ko jibi asabar za ta bi Uncle B Kaduna idan yazo.

Idar da Sallar la'asar ɗinta kenan ta jiyo muryarsa suna gaisawa da Mum,hakan yasa ta miƙewa daga kan sallayar bayan ta ida addu'arta.Hijab ɗin jikinta ta cire tana sake duban kanta a jikin mirror,tana sanye cikin gown ne na wani swiss voil mai ɗankaran kyau.Colour ɗinsa mint green ne da red,sosai colour ɗin ya yi mata kyau ɗinkin ya zauna a jikinta.Gyale ta zara mai ɗan kauri ta yafa a jikinta,domin ta tsani shegen kallon ƙurillan da Ya mubarak ɗin ke binta da shi.Hannunta riƙe da phone ɗ'inta ta fito falon,idanunsa a kanta har ta ƙarisa shigowa cikin falon tana faɗin.

"Har ka gangaro kenan,dama kana kusa da Unguwan tamu kenan? "

Ta ƙare maganar tana zama kusa da Mummy,sai da suka gama gaisawa da Mum kafin ya juyo takan tambayar Surayyah yana bata amsa da faɗin."No! Ko ɗaya,daga gida nake Surryn Mum.Bani ruwa ƙishi nake ji."

Ya ƙare maganar yana jifanta da wani makirin smile,manyan idanunsa na yawo a jikinta.Sosai ya ga tayi masa kyau a cikin shigar,yana yaba iya kwalliyarta da kuma ƙamshinta dake narkar masa da zuciya. Miƙewa tayi tana ɗan murguɗa masa baki,ta nufi hanyar kitchen domin ɗakko masa ruwan.Ba iya ruwan ta ɗakko masa ba,ta haɗo har da chicken bread da lemu.Lokacin da ta fito Mum tayi shigewarta ɗaki domin basu waje,sabida ta riga ta gama ɗago abinda ke yawan kawo Mubarak gidan a yanzu.Domin su ba wani zumunci ne dasu ba,sai a shafe shekara wani bai ziyarci wani ba.Tunda ta ga yana nacin zuwa tasan cewa akwai manufarsa nayin hakan,sanin Surayyah bata son maganar auren zumunci yasa Mum ɗin tai kamar bata san me suke ba tasa musu idanu kawai.Aje tray ɗin tayi bisa table dake kusa dashi,ya bi zara-zaran yatsunta da ta yi ma jan lalli da kallo,kafin hancinsa ya sake shaƙo masa ƙamshinta mai daɗi.Har wani lumshe ido yayi ya sake buɗesu a kanta lokacin da take zama kujerar kusa dashi,ɗauke kai tayi tana faɗin.

"Kallon fa ya Mubarak?Wallahi ka faye yawan kallo na takura bawa."

Tayi maganar cike da shagwaɓa,wanda Mubarak yaji wani yamm... A cikin jikinsa.Idanunsa akanta yake faɗin "To in banda abinki Baby Surry laifi ne don mutum ya kalli abinda yake so?Bakisan yadda kullum ake sake huramin wutar sonki bane a cikin zuciyata,ke gani nayi a wasa kike ɗaukar komi ko? "

Murmushi ta saki wanda har saida jerarrun haƙoranta farare tas suka bayyana,kafin ta dubeshi cikin ido tana kaɗa ƙwayar idanunta.Cikin wani irin salo tace,"Ya Mubarak kenan,ai dole in dinga ganin komi da wasa.Yanayin yadda ka fara son nawa ne yake bani mamaki,domin na ga dai ada kafin kabar ƙasarnan ko wani kallon kirki ban isheka ba,sai yanzu rana tsaka ka dawo kace wani wai ni kake so."

Ta ƙare maganar tana murgaɗa masa baki,tare da tsuke lips ɗinta da suka sha jambaki raɗau.Hakan ya sanya Mubarak binta da kallo yana ji tamkar ya janyota jikinsa ya haɗe bakin su waje guda,ko zai samu sassaucin yanayin da ta jefashi ciki.Ji yake wani abu na zagaye ilahirin jinin jikinsa.Cup ɗin da ya zuba ruwan da ta kawo yai saurin ɗauka yakai baki yana kurɓar ruwan,a hankali sanyin ruwan ke ratsa maƙoshinsa,har ya shanye tas ya aje cup din ya dubeta yana faɗin,

"Au yanzu tanan kika ɓullo,any way,yaushe za ki dawo daga KD ɗin in kin tafi a goben? "

"One week kawai zanyi Ya Mubarak ko 10 day's,daga can ma Abuja zan wuce gidan Anty Sameera."

Cewar Surayyah tana duban yadda ya wani ɓata face kafin ya furta. "Haba Baby,yanzu don ki azabtar da zuciya da idanuna akan rashin ganinki shine zaki tsiri wucewa Abuja,to wallahi sai dai kina zaune kiji na kiraki nace gani a Abuja na biyoki."

Ya ƙare maganar yana wani shagwaɓe face,abinda yasa Surayyah sakin dariya kenan.Daga nan suka ɗan taɓa hira,duk rabin maganar nasa yana koɗata ne tare da sake jaddada mata irin sonta da ya kama zuciyarsa.

Mum ta kira masa Ya yi mata sallama,suka fito tare don ta taka masa.Sun kawo bakin gate ya ja ya tsaya yana binta da wani shu'umin kallo,kafin ya furta. "Baby da za ki ji tausayina dana nemi wata alfarma a gunki,kafin ki tafi kibar ni da matsananciyar kewarki."

Surayyah ta tsareshi da ido cikin son karantar yanayinsa ta furta."Ina jinka Ya Mubarak,say your mind."

Ga tsananin mamakinta matsowa yayi sosai zuwa gareta,yana ƙoƙarin haɗe gaf ɗin da ke tsakaninsu.Bata ja da baya ba sabida so take ta ga gudun ruwansa,sake ƙasa da murya yayi idanunsa akan lips ɗinta yake faɗin.

"Bakomi nake so ba Baby illah ki ɗan bani bakinki in sha kaɗan ko zan samu nutsuwar zuciya,kinga ni ɗan uwanki ne da ke sonki da aure don kin tausayamin kin bani wani abu daga gareki ai is nothing ko my luv? Nasan ke wayayyace kin gane abinda nake nufi."

Ya ƙare kalamansa yana sake matsawa jikinta sosai.Hannunsa yake ƙoƙarin kaiwa face ɗinta,tasa hannu ta bige hannun nasa tana jifansa da wani irin kallo,kafin taja baya kaɗan tana faɗin.

"Au! Kai ma Ya Mubarak da wannan ka zo?Kai ma jikina kake so,sha'awata ka ke ba sona ba ko? Ni dama nasan za a rina tun daga yadda ka ke tsawaita bin surata da kallo kana kwarzanta cikar halittar da Allah ya yi mini na ɗiga ayar tambaya a kanka.Tir! Da halayyarku na Samarin wannan zamani,bazan iya baka koda yatsuna ka tsotsa ba bare bakina.Kuma daga yau ina so kada ka sake nufoni da kalmar so,mu tsaya a iya mutunci na ƴan Uwantaka kawai."

Daga haka ta juya a guje zuwa cikin gida zuciyarta na matuk'ar suya da tafasa."Me maza suka ɗauketa ne wai? Me yasa duk wanda zai zo gareta BURIN ZUCIYARsa ɗaya ne da sauran?" Ta jefawa kanta tambayar zuciyarta na sake ɗaukar zafi.Cikin sa a bata samu Mum a falo ba,hakan yasa ta wucewa ɗakinta ta faɗa gado tana jin hawaye na bin fuskarta masu tsananin zafi.Duk da abin bai wani bata mamaki can ba,domin abu ne da take hasashe a kansa dama.Amma ba tayi zaton tunda wuri haka zai fara neman cikar BURINsa a kanta ba.

A can wajen compound ɗin kuwa,dafe kansa Yayi yana furzar da iska daga bakinsa,tare da jin wani takaicin kansa na kamashi daya kasa danne kwaɗayinsa a kanta.Har gashi ya janyo ta gama gano manufarsa,wani sashi na zuciyarsa na ƙarfafashi da cewa karya damu zai iya shawo kanta,idan ya nuna mata nadamarsa da cewa sharrin shaiɗan ne kawai.Haka ya fice zuwa mota yana jin wani sabon sonta da sha'awarta na sake fisgarsa.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*Burj Al Arab Hotel Dubai*

Rash ce da Hisham kwance a cikin ƙayataccen ɗakin hotel ɗin da sukai masauki.Yau kwanakinsa biyu kenan da biyota,suna holewarsu yadda ya kamata.Sosai garin ke mata daɗi,ta riga ta gama saki cewa Dubai ƙasa ce mai matuƙar daɗi,da ta mallaki manya-manyan wajajen hutawa.Wata fingilwar riga ce a jikinta,tana kwance ne bisa ƙirjinsa yana shafa gadon bayanta.Ƙaunarta mai tsanani ke sake mamaye zuciyarsa,kwanaki biyu kawai da suka yi a ƙasar suna kasancewa da juna ji yake inama itace halalinsa sabida yadda take rikitashi a shimfiɗa.Gashin kanta Ya shafa a hankali yana sake matseta a kirjinsa yace.

"My Baby Rash,i luv u so very much,don Allah Rasheeda mu cigaba da kasancewa da juna kada ki juyamin baya please! Da ace nasan haka kike da baiwa da ke na zaɓo ba Sameera ba.Please Rash kada ki gujeni domin kullum tsoran yadda idanunki ke sake buɗewa nake,ina fata baki ba waɗannan Yaran abin daɗin suna shiga gonata ba,kamar yadda kika sakar min."

Mirginawa Rash tayi ta sauka daga jikinsa,idanunta a kansa take faɗin."Haba Ya Hisham,wallahi bana basu,iyakarsu dani bai wuce ɗan romance da sauran A ya ne,ka gane dai.Kuma maganar juya baya kaima kasan dole zan yi aure Ya Hisham,ba zai yiwu mu cigaba da irin wannan rayuwar ba.Kada ka zama mai son kai,ina so inyi zaman aure tamkar yadda kowace macen kirki ke da buri.Ban taɓa kawo zan yi irin wannan rayuwar ba,da kowani Namiji ma bare kai.Amma kai ka soma ɓata ni tunda ka fara nuna kwaɗayinka a kaina,baka taɓa saurarawa ba saida ka cika BURIN ZUCIYARka a kaina."

Janyota ya kuma yi ta dawo jikinsa,yasa hannu ya rungumeta yana cusa kansa bisa ƙirjinta yana jin yadda zuciyarta ke harbawa.Sonta da tausayinta ke keta ilahirin jinin jikinsa,Ya sani shine silar zamanta koma me ta zama,domin Shi ya fara keta haddinta ba tare da tsoran Allah ko duba dangantakar dake tsakaninsa da ita ba.Ba tare da ya duba maraicinta ba ya biye ma son zuciyarsa.Rarrashinta yake da kalamai masu daɗi har ya sanyaya zuciyarta,cikin ƙwarewa da iya sarrafa mace yake aika mata da salonsa har bata san lokacin da suka sake komawa wata sabuwar duniyar ba.

********

Ƙarfe huɗu a gogon can suka fito domin tafiya wani wurin shakatawar,suna sanye cikin shiga mai kyau daya dace dasu sai zabga ƙamshi suke.Duk wanda ya dubesu zai yi zaton mata da miji ne da suke cin ganiyar lokacinsu,sai dai da mutum zai ji dangantakarsu da juna da tabbas sai yayi tir! Tare da Allah wadai da tarayyar da suke da juna.Wani haɗaɗɗen mall suka yada zango bayan sun gama zaga wuraren hutawa,kayayyaki take ta jida masu asalin tsada.Ta ɗauki nata ta jidarwa Husnah da Anty Sameera abinda tasan za ta yi sha'awa,Ya biya kuɗin suka fice zuwa wani shagon saida gwal.Shida kansa Ya ɗaukar mata wani zobe daya birgesa,hannunta ya kama ya sanya mata zoben.Tamkar don ita aka yi zoben,ya yi mata cas tare da haske lallausar yatsarta.Bakinsa yakai ya sumbaci hannun yatsun yana murzasu cikin salo na takalo fitina,zare hannun tayi tana jefa masa wani kallo da narkakkun idanunta kafin tayi gaba yana binta a baya.Wani siririn sarƙa da ɗan kunni ta ɗauka,Ya biya suka bar shagon domin komawa masauki.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*KADUNA*

Zaune suke dukkaninsu a ƙasan carfet wanda aka shinfiɗa ƙayataccen ledar cin abinci,kowanne abinda yake ra a yi ya zuba.Farha rabin hankalinta na ga ya Abdallah ne dake cin abincinsa a natse,kominsa burgeta yake shi ko baima san tana yi ba.Shi ya fara tashi yabar wajen tare da komawa cikin falon ya zauna yana latsa wayarsa,Hajiya ce itama ta tashi ta bishi domin akwai maganar da take so tayi dashi.Cin abincin sai ya rage daga Farha sai Humaida suke ci.

"Abdallah baka wani ci abin kirki ba naga ka taso,lafiya yau tun safe nake kula da kai wani sukuku kake komi,ince dai ko lafiya?"

Cewar Hajiyarsa tana tsareshi da ido.Ya ɗago daga danna wayarsa da yake ya dubeta yana sakin smile kaɗan yake faɗin,"Wallahi Hajiya bani jin daɗin bakina ne kawai,ji nake kamar Malaria ce ke son kamani,amma karki damu ga magani can na tsaya na siyo zan sha idan na je ɗaki."

"Ayyah! to Allah ya baka lafiya,har naji na damu,am! Yauwa Abdallah,nace ina so wannan satin inje Zaria domin dubo jikin aminin Mahaifinku,Alhaji Saleh kasan lokacin da ya yi jinya ban sami zuwa na duboshi ba.Kai kuma baka ƙasar lokacin shine na ga ya dace mu je,sam bai kyautu ace mun kasa zuwa duba shi ba,daga can har wajen Hajiya Aysha nake so inyi ziyara,domin ba zan manta kirki da kula dani da ta dinga yi a makka ba,wacce nake baka labarin ita tayi ta taimakamin lokacin da ƙafata ta motsa wancan zuwa Umrar nawa,to ina so in ziyarceta don haka ina so jibi asabar muje ni da Humaida tunda gobe Farha za ta wuce gida."Abdallah ya dubi Hajiya yana faɗin."Shikenan Hajiyata,Allah shi kaimu jibin lafiya,sai Mallam Jamilu Ya kaiku,ni daga baya zansa lokaci inje in duba jikin Baba Saleh ɗin.Domin jibin akwai ɗaura auren da muke dashi,da munyi tafiyar tare."

"To shikenan Abdallah,Allah ya kaimu lafiya."

Cewar Hajiyar yayin da Abdallah ya miƙe bayan ya amsa da "Ameen." Yana mata sai da safe domin zuwa sashinsa Ya sha magani ya kwanta.Sabida yadda yake jin kansa na tsananin ciwo,ƙaramin flask mai ɗauke da ruwan shayinsa na ƙa'ida yasa Humaida ta ɗakko masa ya wuce bayan Hajiya tayi masa addu'ar fatan samun sauƙi.

Koda ya koma sashinsa wanka yayi ya fito ya kintsa kansa cikin shirin kwanciya bacci,sai da ya kammala shan shayin ya sha maganin kafin ya sake wanko bakinsa yazo ya yi light off ya haye bed.Yauma wayarsa ya ɗakko ya cire pin ɗin yana mai tsurawa zanen hotonta ido,wani abu yake ji na sake bin jinin jikinsa.Sonta yake bada wasa ba,Burinsa da addu'arsa ba dare ba rana shine Allah ya sake haɗashi da ita koma a ina take.Yayi yawon zuwa mangal plaza har ya gaji,amma bai kuma ganin wannan kyakykyawar face ɗin nata ba,gashi Hajiya ta fara matsamai akan ya fitar da macen aure tunda ya nuna baya ra'ayin su Farha dake bibiyarsa.Kuma gashi har yanzu bai sake haɗuwa da Yarinyar da yake iƙirarin ita yake so ba,lumshe idanunsa yayi yana kifa wayar a saman ƙirjinsa.Ji yake ina ma ya buɗe ido ya ga pretty ɗinsa rungume a ƙirjinsa,ko me ya tuna ni dai ban sani ba sai gani nayi ya saki lallausan murmushi yana sake matse wayar a kirjinsa.A haka bacci ya suresa cike da mafarkai kala-kala,wanda rabinsu duk na pretty ɗinsa ce.....✍🏻