55
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️-----55
cikin hanzari ya saka wata farar jallabiya ya fito iman na tsaye bakin dinning tana shirya Abinci rana da mamaki taga Suhail ya fito bayan tabbatar mata da yayi yau babu inda zai je
"yaya Suhail ina kuma zaka"
suhail ya ce"nayi recieving wani urgent call daga office zan dawo yanzu"
kai ta jinjina ta ce"Allah ya tsare hanya"
koda secretary din sa ta ajiye wayar ta kalli mutanen ta ce"Yallabai ya ce ga shinan zuwa"
ko mintuna Ashirin baiyi ba ya karaso secretary na ganin ta miƙe tsaye ya ce"ina suke"
nuni tayi masa dasu Sama'ila dake kan waiting chairs na gaban office din sa Suhail ya ce"ki ce su shigo"
office dinsa ya shiga bayan ya zauna suka shigo yayi masu nuni da kujeru dake gaban da su zauna
bayan sun zauna Sama'ila ya soma cire mayafin dake fuskarsa sa sun gaishe da Suhail ya ce"mike tafe da ku"
gyaran murya mijin mahaifiyar tasa yayi cikin girmamawa ya ce kamar yadda muka ce munzo akan batun yarinyar nan Amina bayan samun labarin cewa kaine lauyen dake kare ta a kotu Ni sunana Gambo ya nuna Sama'ila ya ce"wannan kuma sunansa Sama'ila dan marigayi Alhaji Barau"
suhail ya jingina da kujera ya ce"ina jinku"
Gambo ya ce"munzo mu tabbatar maka cewa ba Amina ta kashe barau ba dan sane Salisu da kuma sa hannun matar sa jaru"
ido Suhail ya zaro mamaki ƙarara ya bayyana kan fuskar sa Sama'ila ya cigaba da magana ya labarta masa duk Abinda yaji da kunnen sa sai da ya kai aya ya dauko wayar sa mai madan nai ya kuna murya salisu da jaru daya jima yana naɗa wanda ko Gambo sai a Lokacin ya san da wannan sautin muryoyin nasu da samaila ya naɗa
Suhail ya daɗe yana kallon Sama’ila ba tare da ya ce komai ba Daga bisani ya lumshe idanunsa ya sauke ajiyar zuciya
“Alhamdulillah…” ya furta a hankali
Na daɗe ina jin akwai wani abu da ake ɓoyewa Amma ban taɓa tunanin hujjar za ta zo ta wannan hanya ba
suhail ya gama sauraren komai ya kalli Sama'ila ya ce"akwai wanda yasan da zuwanka nan"
kai ya girgiza Gambo ya ce"babu wanda ya sani dan tunda suka tabbatar da ya gansu suka fara Neman sa wannan ne Dalilin da yasa ma ya gudu wajen mahaifiyar sa gudun kar shima su kashe sa"
suhail ya ce" i will make sure babu Abinda ya same ka,iya wannan shekara kadai ta isa ta wanke Amina daga zargin da akeyi mata" Suhail ya yaba wa Sama'ila ka ƙoƙarin da yayi
kallon Gambo yayi ya ce"zaka koma kai kaɗai shi zai cigaba da zama karkashin kulawar mu har zuwa lokacin da komai zai daidaita
Gambo ya ce"wannan ba Matsala bace"
tashi yayi zai tafi Suhail ya janyo drower din dake gaban sa kudi ya dauko ya miƙawa Gambo yayi kuɗin mota amsa yayi ya yi masa godiya ya kama hanya
Suhail ya umarci Sama'ila daya maida rufin fuskar sa ya biyo sa wani dan karamin hotel dake kusa da office din ya kama masa na sati guda tare da biyan kudin abincin tun daga safe har dare
koda Zai tafi yace masa "ya rinƙa rufe dakin karya buɗe sai ya tabbatar da shine yazo ko kuma masu kawo masa Abinci"
Sama'ila ya ce"in sha Allah"
har Suhail zai tafi ya kallesa ya ce"ko Akwai abinda kake bukata"
Sama'ila yayi nazari kafin ya ce"Alqur'ani"
suhail ya koma motarsa ya dauko masa Alqur'anin ya basa
ya kama hanyar gida
ƙwaro da mutanen sa sun baza neman Sama'ila idan suka samu Labarin yana garin mahaifiyarsa daya daga cikin mutanensa yaga sanda ya shigar gidan cikin dare
ƙwaro ya kira salisu ya fada masa yana tsakar gida tare da jaru ya ce"ƙwaro aikin ka yayi kyau inaso kuwa garin shigar dare ku kamo min shi duk wanda ya nemi ya bata maku aiki ku sare shi ko wanene ku ƙar shi kar ku bari a kama ku"
ƙwaro ya ce"gamawa oga amman kasan dole lissafi zai chanza ko"
salisu ya ce"Matsala ta dakai baka da haƙuri Matsalar ma a baka kudin kaje ka kashe su a Banza wajen shaye-shaye"
ƙwaro ya ce"oga ai kasan rayuwar ce sai da chagi"
"naji zan kara maka rabin kudin da nayi maka alkawari a baya"
murmushi mugunta ƙwaro yayi ya ce"cau-cau sai dakai Ubangida na Allah dai ya taya maka nawa"
katse wayar Salisu yayi jaru tun daya fara Maganar ta gagara ya katse ya fada mata Abinda ke faruwa ta ce"an same shine"
"Eh, yana chan garin tsohuwar sa"
"ajiyar zuciya ta sauke ta ce inaso ka kawo gaba na da wannan hannun nawa zan kashe dan banza sai yaje chan ya gana da uban nasa"
Da dare ya fara ratsa garin, Ƙwaro tare da mutanensa guda huɗu suka isa ƙofar gidan mahaifiyar Sama'ila
basu boye fuskokinsu suba dan a ganin su babu wanda ya san su a garin
Ƙwaro ya yi musu alama da hannu
kar suyi hayaniya Duk wanda ya yi ihu ku toshe masa baki ko waye
Kai suka ɗaga
A hankali suka tunkari gidan Ƙwaro ya buga ƙofar sau ɗaya
shiru babu alamar motsi hakan yasa ya kara bugun kofar
gambo ya tambaya wanene
"baƙo ne daga tsauni"
Da jin haka, ba tare da ta yi zaton komai ba ya buɗe ƙofar
Kafin ya ankara, suka ture ta suka shiga ciki dashi
yayi ƙoƙarin ihu ɗaya daga cikin ya toshe masa baƙi
jin shiru yasa ta fito daga daki "mai gida su wanene da daren nan"
bata an karaba taji wani ya tureta ya taka mata kirji
ƙwaro yayo kanta cikin tsawa ya ce"ke ina danki yake"
cikin kuka ta ce"ban san wa kake nufi ba"
mari ya kai mata da sauri ta dafe kuncin ta
ya ce"Sama'ila"
Gambo ya kwace bakin sa ya ce"wallahi baya nan tun jiya rabon da nan"
ƙwaro ya dubi yaransa ya ce"ku duba ciki"
like.
share and
comment
Ayi hakuri dai