ALWASHI 2

32

by @rufaidaumar

ALWASHI 

     57


Zakari na zaune a gaban gidansu tare da abokonsa Najeeb suna hira. Haka motar Areef ta zo ta tsaya, ya yi hon, Maigadinsu ya fice don buɗemasa. Ya sauke gilas ya yi wa su Zakari sallama, ciki-ciki Zakari ya amsa yayin da Najeeb fuska a sake yake amsawa. 

"Ashe ka shigo gari? Ya Neja din ya kuma iyali?"

Areef ya furta yana duban Najeeb wanda gaba ɗaya ya yi maka wata uwar ƙiba ga tumbi da ya ajiye. Najeeb ya yi dariya. 

"Neja da iyali duk muna lafiya. Ina taya murna Zaks ya faɗa min ka yi aure har biyu abinka. To Allah ya sanya alheri."

Murmushi Areef ya ɗan yi kawai ya ja motar zuwa farfajiyar gidan wanda tuni Maigadin ya buɗe. 

Bayan shigewarsa Zakari ya ja tsaki. Najeeb ko dayake gulma ke cinsa cikin muryar da ta fi kama da raɗa ya ce. 

"Kalli yanda Guy dinnan gaba ɗaya ya ƙara zama wani babban Don abinsa. Koda ka cemin zai yi aure na sha mamaki, kenan wancan tsohon case din ko maganarsa ba a yi? To meye ribar abin da muka aikata?"

Zakari ya dubi ƙaton ƙyauren da ke ƙara saboda rufewar da Maigadi ke yi sannan da sauri ya dubi Najeeb. 

"Zamu yi zancen, nan babu muhallinta."

Jin haka Najeeb kawai ya jinjina kai. Shi dai zai so jin ya aka yi komai ya wuce. Shi fa tun da ya ɗirkawa wata ƴar ƙanin babansa ciki suka je zubarwa asirinsa ya tonu, babansa ya tursasa shi a dole  sai da ya aure ta bayan ta haihu ɗiyar ba rai, aka tura shi can Neja neman wurin wani aminin Baban, can yake zaune  da iyalinsa yake kuma neman kuɗi, to bai ƙara tayarwa Zakari batun tuggun da suka shiryawa Areef ba sai a yau ganin Areef ɗin. Ko ina yarinyar? Ya ma mance sunanta. Tambayoyi fal a cikinsa haka ya haɗiye yana jiran su bar wurin kamar yanda Zakari ya ce. 

***
"Daren yau idan an idar da sallar isha'i, ina son ganinku kai da matarka." 

Shi ne abin da Abba ya ce ga Areef bayan amsa gaisuwar da ya yi masa. Daga shi sai Abban a falo, Hajja Zayha ce da girki tana daga ɗakin Abban amma kuma tana laɓe duk tana sauraronsu. 

Areef ya numfasa. 

"To in sha Allahu Abba."

Ya amsa, daga nan Abba ya ɗan saki fuska. 

"Ya ya ake ciki game da kayan nan? Yaushe za su taso?"

"Ƙarshen watan nan." 

Abba ya gyaɗa kai. Daga haka suka shiga tattauna batun ginin kamfaninsu na Kano wanda aka cimma kusan rabi da kwatansa. 

Daidai nan Hajja ta koma cikin ɗakin Abban. Kai tsaye whatsapp ta shiga ta aikawa Laila saƙon murya. 

"Ki zama cikin shiri Laila, surukinki zai buƙaci ganinki yau. Na yarda da takunki, ina da tabbacin ba za ki ba ni kunya ba wajen ba shi amsa daidai da dukkanin tambayoyin da zai maki. Jikina na bani bai wuce hakan ba tunda ban ga alamar yana da niyyar ɗaukar wani zafafan mataki a kan aurenku ba. Sai ki kula sosai."

Daga haka ta tura saƙon ya tafi har mark biyu, shaidar Laila na kusa. 

***
Laila ta buɗe saƙon Hajja ta saurara, ita kaɗai ce zaune a falon nata wuraren ƙarfe biyar da mintoci na yammaci. Murmushi ta yi. "Ok" Ita ce amsar da ta aikawa Hajja ɗin kawai. Ta gyara kwanciyarta a saman kujera ta cigaba da kallon status da take. Ita babu wata damuwa don wai Uban mijinta na son ganinta, duk ta inda ya ɓullo to za ta iya wa tijararsa. 

Ba a fi mintuna goma da duba saƙon Hajja ba, sai jin sallamar Areef ta yi. Zaune ta miƙe ta gyara zaman rigarta tana amsawa a ciki. Ya ƙaraso ya zauna daga gefen kujerar da take. Falon ya ɗan ƙarewa kallo, so yake ya ga ta ina ne ƙamshi ke ɓullowa. Sai idanunsa suka sauka kan wata ƙaramar burner mai babba kamar kofi. Hayaƙin kawai ke tashi a hankali yana fidda ƙamshi. Ya maido dubansa gareta. 

"Barka da yamma Mrs Areef."

Ta watsa masa wani banzan kallo, ya kauda kai yana murmushi. 

"Ba fa abinci na zo ci ba balle a min wuta bal bal."

"Idan ka gan shi ai sai ka ci ko?"

Ta faɗa ranta har lokacin a haɗe. Ba ta kuma ƙara kallonsa ba ta ɗaga ƙasan gidan tissue da ke ajiye saman tebur ta ɗauko dubu goman da ya ajiye mata ta dire a gefensa. 

"Kuma ga kuɗinka nan, babu abin da zan yi da su har abada."

Ya ɗan ɗaga gira.

"Ko? To aikuwa amfani da kuɗin nawa na har abada ƙila ya ganki tunda ki ka sanyo ƙafarki gidan nan matsayin matata. Ke ni fa ba irinki ba ne, ba zan bari ki sabar min da wannan ɗabi'un naki na wofi ba kin ji ko? Aljannata nake nema. Ba zai yiwu gobe ƙiyama ki ja min masifa ba."

Don mamaki da takaici kasa magana ma ta yi, dama Areef ya iya magana har haka? Ko kuwa dai wani sabon salo ne zai ɓullo? To ko ma dai da ya zai zo, ita Laila ta fi ƙarfinsa don ba sakara take ba.

"Ki zama cikin shiri idan an yi isha'i, Abba na son ganinmu. Zan zo mu je."

A nan ne ta ɓata rai. 

"Son ganinmu kuma?"

Ya tausasa murya. 

"Eh."

Kamar ta ce wani abu sai kuma dai ta shanye gami da yamutse fuska. 

Ya miƙe ba tare da ya ɗauki kuɗin ba ya fice daga falon. 

***
  Suna tafe a motar Zakari, Najeeb ya hangame baki cike da tsantsar mamaki jin wai Areef  Sameera ya aura. Zakari ya dube shi da murmushi, a ransa fadi yake, don ma ba ka san dalilin auren ba. 

"Kai ni fa na kasa yarda da zancenka, wai dagaske ita ya nemo ya aura? Shegen kaya! Ya ɗanɗanowa kansa zuma dole ya kasa bari dama ta wuce shi."

Haɗe rai Zakari ya yi. 

"Kai ba na son hauka, wane zuma bayan a dole ya aure ta? A yadda na ji zancen Sameera ce ta dage kan lallai sai ya aure ta ko kuma ta mishi tonon silili. Ka fi kowa sanin Abba a fagen nan, duk abin da zai kai ga zubda mutuncinsa a idanun duniya, ba so yake ba. Shi ne fa ya amince ya yaron ya aure ta."

"Oh, abin da ya faru kenan? Ah lallai Sameera ta yi kyan kai. Yarinyar ashe tana da wayo? A taƙaice dai ba sonta yake ba? Ni duka wannan fa sai na ga babu amfanin tarkon da muka yi masa har ya faɗa ciki tunda a ƙarshe ma riba ta zame musu shi da Sameera."

Zakari ya ɗan dubi Najeeb da alamar tambaya. Najeeb ya gyaɗa kai. 

"Ƙwarai kuwa, ga ita Sameera, kai kanka ka san cewa kuɗi ne ya saka ta aurensa, saboda if I can remember kamar ƴar aikin Maminsa ce ko? To shi kuma zai kwashi gara..."

"Gara a ina? Kai fa banza ne! Waya faɗamaki soyayya ce tsakaninsu? Shi a dole ya aure ta, haka ita kanta Sameera ba wai son shi take ba."

"Amma..."

"Ya isa haka Najeeb, kar ka ɓata min rai. Ko me kenan dai, ni dai burina ya cika tunda ko babu komai sunansa ya ɓaci a wurin Abba. Har yau yana kallonsa da abin da ya aikata. Ka ga wannan ma ai riba ta ce."

Suka yi dariya. Har suka rabu Zakari koda wasa bai yi gangancin faɗawa Najeeb komai game da sirrinsu ba. A yanda yake zumuɗin plan ɗinsu ya tafi daidai ba ya ƙaunar ma ya yi wani yunƙurin da zai janyo komai ya lalace har Hajja ta tsine masa. 

***
"Kina tunanin za ki iya saita fushi da ɓacin ranki a gaban Alh Sada?"

Na'eem ya watso mata tambayar ta waya, Laila ta numfasa ta ce, 

"Hauhawar ɓacin raina ya danganta da abin da zai fito daga bakin mutumin. Abu ɗaya na sani, sai bayan aure suka gane wacce  ɗansu ya auro. Zan yi iyakar ƙoƙarina dai na danne fushin. Sai dai muddin zai yi ƙoƙarin cin zarafina, to fa nima ban ga dalilin da zai sa na kasa maida martani ba domin ba na son zama inuwa ɗaya da su sai dole irin wannan."

"Hakane, ki dai yi iyakar yin ki wajen danne komai please. Na kuma goyi bayan ki mayar da mai zafi idan an taɓa mutuncinki ko na gidanmu. Amma ki yi komai da ilimi." Cewar Na'eem. 

Ta ɗan yi murmushi tana kallon madubi lokaci guda tana gyara zaman pin din da ta danne mayafin baƙar abayar da na ta naɗa. 

"I won't let you down. Zan yi handling komai."

"Good. All the best Mrs Areef."

Ya ƙarashe da ƴar dariyar tsokana saboda ta ba shi labarin yanda suka yi da Areef din don ba ƙaramin haushi ya ba ta ba, bai ma jira cewarta ba ya katse kiran ya bar ta da bin wayar da harara gami da jan tsaki. 

 Tsakin ne ya shiga kunnuwan Areef da shigowarsa falo bai ji motsinta ba ya sa shi nufo ɗakinta. 

 "Ke kaɗai ma tsakin kike?"

Ta ɗan dube shi a ɗan razane saboda ya firgita ta tunda ba sallama ya yi ba kuma ba ta ji wani motsin shigowarsa ba. Kauda kai ta yi har da sauke ajiyar zuciya kafin ta daure fuska. Shi ko kallo yake ƙare wa shigarta, baƙar luxury abaya ne jikinta baƙi mai adon wani baƙin kwalliyar lace ja kamar applique haka a daga ƙasa sai ko a gefen hannuwan. Mamaki ta ba sa ganin har da su hoda da jan baki ta saka ja ga kuma kwalli. Tsayawa faɗin ta yi kyau ma ɓata baki ne. Gudun kar ta yaɓa masa baƙa da irin kallon da yake bin ta da shi ya sa shi janye ƙwayoyin idanunsa a kanta gami da juyawa zai fice, dama bai kai ga shigowa cikin ɗakin ba. 

 "Muna iya tafiya."

Daga haka ya saki labulen ya yi gaba. Ta ɗauki red handbag dinta ta zura flat shoe nata shima kalar ja ta bi bayansa a yangance. 

Sai da ya kai wurin mintuna biyar yana jiranta a motar, ita kuwa da gayya ta dinga ɓata lokaci wurin kashe fitilu da leƙawa kicin da komawa ɗaki, daga baya ta rufe ko'ina ta jefa muƙullin a jaka ta fito. 

 Ya zuba mata idanu tana takowa zuwa inda motar take, kallo na tun daga sama har ƙasa, Laila Adam Kibiya fa ta kai a kira ta mace, matsalarta ɗaya halayenta. A nan ne kaɗai take da mishkila a tunaninsa, sai dai hakan ma yana uzuri saboda ya sani ko mene ne da ace bai gifta cikin rayuwarsu ba, to ba lallai a risƙeta a haka ba. Tunani yake, anya akwai ranar da wata aba wai soyayya zai gifta tsakaninsu? Ya kawar da kai daga dubanta bayan ya ji ta buɗe murfin motar. 

 'Babu, it will never happen.' Ya ba kansa amsa. Jin ƙarar rufe ƙofa da ma ƙamshin turarenta da ya cakuɗe da nasa, ya sa shi jan motar. Maigadin ya buɗe gate suka fice. Shiru motar ta yi kamar ta kurame, ita tana latse- latse a waya, yayin da shi ko tunanin Sameera ya sauya masa lissafi. Ina ta ke? Ina ta shiga? Ya gama haƙikancewa kansa cewa ya ƙaunaci Sameera, ya kuma kalli Laila matsayin Sameera a baya har ya kasance yakan ji wani abu idan ta yi mishi waya ko ya taka ya je Kano wurinta a baya. Bai ƙara tantance cewa har ransa yake son Sameera ba, sai da ya fahimci ya rasa ta, ba ita ya aura ba. Ya tuna sadda Fareed ke ce mishi ba iya tausayi da nadama kawai ya ke ji a kan Sameera ba, ya jima da gane hakan don kansa. Sai dai bai ƙara gasƙatawa ba sai a daren da ya gama gano lallai ba ita ya aura ba. 

 Har suka iso gidan Abba dayake ba tazara tsakaninsu sosai, Areef tunanin lamarin Sameera da Laila yake yi, Laila kuwa ko inda yake ma ba ta kallo, ba ta san me ya kawo shirun nasa ba. Ta san dai ƙila ma fargabar haɗuwa yake da Abban nasa saboda ita. Sai ta ji ranta ya ƙara fari sol, don a duniya tana farin ciki da damuwar zuri'ar nan. 

 Kai tsaye ɓangaren Abba suka nufa. Yana zaune a falon yana amsa waya, da hannu ya yi wa Areef nuni alamar su zauna. Laila ta dube shi tsakar ido kafin ta sadda kai ta nemi gefe ta zauna. Kanta na ƙasa, hasko abin da ya yi wa Mama da Sameera kawai take, cillo kuɗi da kuma barazana. Duk a kan abin da ya kasance laifi na ɗan sa. An dake su kuma an hana su kuka. 

  Sai da ta ji Areef na gaida shi kafin ta ankara cewa ya kammala wayar. Ta gyara murya daƙyar ta ce. 

 "Ina wuni."

"Lafiya lau Sameera, ko Laila zan ce?"

Areef ya ji ɗan dam, sai fa ya tuna da duka sunan suka santa yanzu. 

 "Eh duk biyun sunan ne." Ta furta a ɗan gadarance saboda zuciyarta ta soma zafi. Areef ya ɗan dube ta, sai ya juya kai bai ce uffan ba. 

 "Masha Allahu. Babban dalilin da ya sa ni kiranki Sameera, na farko shi ne na baki haƙuri na dukkan abin da ya faru a baya. Har a raina nake jin nadamar abin da muka aikata maki. A lokacin tabbas mun yi amfani da son zuciya da son kanmu. Mun kare mutuncin kanmu, alhalin ke mun tona asirinku. Ina roƙonki gafara Sameera, ki rufamana asiri kamar yanda a yanzun kika zama ɗaya a cikin ahalin gidan nan, ki ka kasance zuri'armu, toh maganar da ta wuce a bar ta, a yafi juna kowannenmu ya rungumi ƙaddararsa."

 "Wace ƙaddarar Abba?"

Laila ta furta tana kallon Abban cikin idanu yayin da hawayen da take riƙewa suka sauko a saman kuncinta, Areef wannan karon bai kalle ta ba sai ɗan rintse idanu da ya yi zuciyarsa na zafi kaɗan. Duk lalacewar uba, uba ne. Yana fatan kar Laila ta ce za ta ci zarafin Mahaifinsa, ya sani ba zai iya controlling fushinsa ba. 


©Rufaida Umar