BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 8

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA❤* *Arewapen@ayshadansabo*

©️ _Ayshat Ɗansabo_ _lemu_ ✍️

*Free page 8*

*ZARIA*

Tun misalin sha biyu na rana Surayyah ta kammala yiwa Uncle B snack's ɗin da tasan yana so,cike take da murna da ɗokin zuwan nasa domin shekara daya da rabi kenan rabon da ta saka shi a idanunta.Ita dai Mum kallonta kawai take yadda ta hana kanta sukuni duk akan zuwan Uncle ɗin nata,wanka ta shiga daga ƙarshe bayan ta fito ne tayi shiri cikin Riga da skat na wani lace mara nauyi.Sosai ɗinkin ya yi mata masifar kyau tare da zama a jikinta,surarta ya fito sosai abin ka ga mai diri Ma Sha Allah. Simple makeup tai wa face ɗinta,domin so take ta dinga rage yawan kwalliyar da Mum kullum sai tayi mata ƙorafin a kansa.Tayi kyau tamkar ka sureta ka gudu,sassanyan ƙamshinta ke tashi a jikinta duk yadda ta motsa.Duk ga zatonta idan Uncle B ɗin ya zo a yau za su wuce Kd,ta je ta ga tsohuwa Hajiya Kaka,wacce itace ta haifi Baban su Mum ɗinta.Allah ya yi mata tsawan rai duk yawancin Yaran nata sun rasu,amma ita tana nan da ranta.

Ta idar da sallah kenan wayarta ta shiga ruri,ganin Mubarak ne mai kiran yasa ta jan tsaki kawai ba tare da tayi ƙoƙarin ɗaga wayar ba.Har kiran ya tsinke wani kiran ya sake shigowa duk tana gani tayi biris dashi,ƙaran shigowar saƙo ta ji hakan yasa ta ɗauki wayar tana dubawa.

_Please Surry ki ɗaga wayata,wallahi abinda ya faru sharrin shaiɗan ne.Nayi miki alqawarin bazan sake neman wani abu daga gareki ba tunda baki so, please My princess ki ɗaga wayata ina buƙatar jin muryarki._

Waɗannan sune kalaman da Mubarak ya rubuto,tana gama karantawa sai tayi deleting tare da saka wayar a silent.Ta fito falo ta zauna tana maida hankalinta akan TV,Mum ce ta fito tana sauke ganinta akan Surayyah take faɗin,

"Auta duk wannan gayun da aka ci na zuwa Kd ɗin ne,amma ina ga ai ba yau za ku wuce ba.Kinsan Basheer da yawo,yana da abokai bazai iya shigowa Zaria a yau ya juya ba."

Surayyah ta ɓata face tana faɗin."Nikam Mum na ƙosa na bar garin nan kona shaƙi iskar wani wajen inji sanyi a cikin raina,ko dan takurar Ya Mubarak."

Riƙe baki Mum tayi cike da nuna son jin ƙarin bayani take faɗin."To fah,mai kuma yayi miki? Ki zuwan da yake domin zumunci shine takuran Surayyah? "

Ta ƙare maganar tana tsare Surryn da ido wacce ta sake shagwaɓe face cike da narke murya take faɗin. "Wallahi Mum ba don wani zumunci yake zuwa ba,shi fa a dole wai sona yake,ni kuma tun farko kinsan ba son auren zumunci nake ba."

Nan dai ta kwashe yanda sukai da Mubarak ɗin tun daga shawarar da Busheera ta bata akan ta bashi dama har kawo kan abinda ya faru kwana biyu da suka wuce,ta sanar da Mum ɗin.Ta ƙare maganar da faɗin, "Mum kin ko ga gara tun wuri in taka masa burki,tunda Shi ma ba don Allah yake sona ba.Duk tafiyarsu ɗaya da Aliyu,gara na bar musu garin na sha iska."Mum sosai ranta ya soso zuciyarta ta ɓaci.Ta shiga tambayar kanta,meyasa duk samarin da suke zuwa ga Surayyah suke zuwa da BURIN lalata ba da soyayya ta tsakani da Allah ba? Ita ba wani shigar banza take ba bare ace hakan ke jawo hankalinsu zuwa gareta.Hasalima duk fita da hijab take fita domin sakaya surarta,ita kuma wannan shine jarabawarta.Sauke numfashi tayi tana faɗin.

"Aniyarsu ta bisu,Allah ya cigaba da kareku Surayyah.Ke kuma ki cigaba da ƙoƙarin kare martabarki,kada ki sake ki bai wa ko wani lalatacce damar da zai cika BURIN ZUCIYARsa a kanki.Allah zai miki zaɓi Na gari mafi alkhairy,amma Mubarak ya zube min,sai dai ina so kibi komi a hankali ku rabu lafiya,ta hanyar fiddo abokin rayuwa kamar yadda Babanku ya baki lokaci.Hakan zai sa ya san bakya ra'ayinsa,domin wanda kike so shi za a baki.Kin san sha'anin zumunci yanzu sai kiji ana magana marasa daɗi,inda za a faɗi manufar da yazo dashi ma ƙaryatawa za a yi ace sharri za ki masa,don haka kibi komi a hankali kinji ko."

Mum ta ƙare maganar cikin sanyin murya.Surayyah ta dubeta tana faɗin, "Hakane Mum,zan yi ƙoƙari na tsaida wanda zuciyata ta aminta da nagartarsa In Sha Allah.Addu'arku shine kawai muke da buƙata Mum,domin mazan zamanin nan sai a slow."

Daga haka suka sauya salon hirar,har zuwa lokacin da Lami ta kammala girki.A plate ɗaya da Mum suka ci abincin,kamar yadda suka saba yi a wasu lokutan.Mum itace ta fara tashi ta nufi ɗaki tana sanar ma Surry cewa za ta ɗan rintsa zuwa la'asar,idan Uncle B ɗin ya ƙariso ne sai ta tadota."

Ƙarfe wajen hudu na yamma ya shigo Zaria,kai tsaye GRA ya fara tsayawa wajen wani abokinsa da sukai skull tare a Turkey.Sai da ya gama dashi ya fito domin zuwa Gaskiya ɗin,a Apple white ya tsaya Ya siya mata ice cream da wasu tarkace kafin ya ƙariso.Duk ya ƙosa Ya ga yadda Surryn tasa ta zama a zahiri,cikin shekara ɗaya da rabi da Yayi bai sakata a cikin idanunsa ba sai dai a hoto.Da sallama ya shiga cikin husky voice ɗinsa,fari ne shi tas,da ka ganshi ka ga kyakykyawan Bafulatani.Babu inda ya baro Mum ɗinta a kamanni,yana da son gayu sosai,kallo ɗaya zakai masa kasan cewa shi ɗin n Butter ne da hutu da jin daɗi suka gama ratsashi.Sanye yake cikin ƙananun kaya,waɗanda sune shigar da ya fiso a rayuwarsa.Idan ka ganshi da shigar manyan kaya sai Friday ko kuma zashi wani ɗaura aure haka,sai ko da Sallah.Amma baya ga haka kullum cikin shigar ƙananun kaya za ka sameshi,ko dan ya fuskanci shigar suna masa kyau ne oho.Duk da cewa a zahiri idan ya saka manyan kaya yafi kyau da kwarjini.Yana sanyo kansa cikin falon da sallama,Surayya dake kwance a cikin kujera tayi saurin sakkowa.A guje ta nufesa yana ware mata hannuwarsa,aiko ta shige ta rungumesa tana faɗin.

"Oyoyo Uncle B."

Daidai lokacin Mum ta fito,tunda ta jiyo ihun Surayyah ta tabbatar Uncle B ɗin ne ya iso.Ganin ta rungume a jikinsa yasa ta daka ma Surayyah tsawa tana faɗin.

"Miye haka Surry? Wani irin sakarcin banza ne wannan? Za ki sakesa ko saina saɓa miki?"

Babu shiri Surry ta saki Uncle B,wanda Ya yi mutuwar tsaye zuciyarsa ya gama shiga wani yanayi,sakamakon jin Surry a kirjinsa.Idanunsa cike da mamakin irin tsawar da Mum tayi mata ya saki murmushi yana zama a cikin kujera yake faɗin.

"Yaya Aysha barka da gida,da fatan na sameku lafiya?"

Mum ma zama tayi tana washe baki cike da murnar ganin Autan nasu take faɗin."Lafiya ƙalau,oyoyo Autan Mami,ya ka baro tsohuwa mai ran ƙarfe Hajiya kaka?"

Ya saki smile yana faɗin. "Tana lafiya,tace a gaisheku.Surry kin ga yadda kika sake zama wata big gal kuwa,shikenan an gama skull sai aure."

Ya ƙare maganar idanunsa na yawo akan Surry wacce fuskarta ke cike da farin cikin ganinsa,sai ta shagwaɓe face tana dubansa da shagwaɓa take faɗin.

"Kai Uncle B,kai ma haka za ka ce? Kowa yace aure,aure dai,duk kun gaji dani kenan ko?"

Yadda tayi maganar cike da shagwaɓa yasa uncle B kasa ɗauke idanunsa a kanta,yana jin wani abu na masa yawo a cikin zuciya da gangar jikinsa.Mum ne ta harareta tana faɗin,

"Bawani an gaji dake,ai kin isa auren ne,me za a jira tunda Allah yasa an kammala karatu lafiya. Oya tashi kije ka kawo masa abin sha ba kizo ki fara zuba taɓarar da kika saba,shi kuma yana biye miki ba."

Surayyah ta saki dariya tana tashi ta nufi kitchen,ya bita da ido yana maida dubansa ga Mum yake faɗin.

"Ya Aysha gani nayi Surryn ta sake girma,koda yake she's 22 year's take yanzu ko?"

Mum tayi murmushi tana faɗin."Eh last month tayi birthday ɗin 22 ɗin,ka ga gara ka aurar da ita kai ma ka fiddo mana mata musha biki,tunda dai an kammala master's ga aikinka a hannu kuma.To me za a jira,kai da Rash ya kamata ace zuwa yanzu kun yi aure."

"Hakane Ya Aysha,za mu yi lokaci ne.Jiya mukai chat ashe tana Dubai,Rasheeda ba dai rigima ba,ita a dole sai ta zama big business Woman."

Ya ƙare maganar yana murmushi.Daidai lokacin kuma Surayyah ta fito ɗauke da madaidaicin tray,ta aje a gabansa tana faɗin,

"Bismillah Uncle B,ga snack's nan nayi maka kala-kala sai wanda ka zaɓa."

"Das why I luv u my daughter, godiya nake."

Cewar Uncle B yana kai hannu ya ɗauki chicken envelop ya gutsira,yayin da Surayyah ta saki murmushi tana kallon yadda yake tauna chicken envelope ɗin yana gyaɗa kai alamun Ya yi masa daɗi.Sai ta ɗauki cup ta tsiyaya masa lemun mixed fruit mai sanyi,ta tura gabansa.Yana ci suna labarai,duk rabi yana bai wa Mum labarin rayuwar da yayi a Turkey ne,sai Magriba ya bar gidan domin zuwa Masallaci.

Har Surayyah ta miƙe Mum ta tsaidata ta hanyar kiran sunanta,sai ta koma ta zauna tana kallon yadda Mum ɗin ta haɗa face babu alamun wasa,kafin ta furta.

"Surayyah wannan ya zama karo na farko kuma na ƙarshe,da idanuna za su sake ganinki rungume a jikin Uncle B.Bani so sam,hakan ba daidai bane a cikin wannan zamanin da fitintunu sukai yawa.Kada ki sake kwatanta yin hakan koda wasa,ke ba ƙaramar Yarinya bace kin gane ai,tashi ki bani waje."

Mum ta ƙare maganar cikin daga murya da hargowa,hakan yasa Surayyah jikinta ya yi sanyi tana gano kuskuranta na yin hakan.

*********

Ƙarfe tara na dare dukkaninsu ne a zaune a falon Baba,tare sukai dinner gaba ɗayansu har Uncle B ɗin.A nan ne yake sanar da Baba cewa sai jibi ma zai koma KD,hakan yasa Surayyah tunzure baki cike da nuna ba haka ta so ba.Ita taso a ce gobe kawai ta bar Zaria,gabaki ɗaya garin ya isheta haka nan.Sai goma Uncle B Ya yi musu sai da safe zai wuce GRA,wajen abokinsa Saif zai kwana.

Surayyah ɗakinta ta nufa bayan tafiyar Uncle B din,ta yi shirin kwanciya bacci.Hayewa bed tayi tana ɗaukar wayarta ta hau online,chat suke da Mardy tana sanar mata zancen tafiyarta Kd sai jibi ma.Tambayarta Mubarak tayi,nan Surayyah ta gaya mata yadda suka yi dashi.Ita kanta Mardy sai da abin ya ɓata ranta tana mai jin ciwon yadda Samarin yanzu suka ɗauki soyayya,da yadda suka maida ƴan mata duka sun zama ƴan iska irin su,sabida yadda suka ga ƴan matan yanzu suke zubda darajarsu suna mallaka musu jikinsu.Wasu don tsabar kwaɗayi ne yana kashe mata kuɗi,so duk abinda ya nema ba za ta iya hanashi ba.Wasu kuma tsabar son aure ne,sun ƙosa su san Namiji shi ke sa su karya ƴancinsu su bai wa mazan kawunansu. Sun jima suna maganar,tana shirin kashe data don ta samu tayi karatun buk ɗin Ɗaurin Ɓoye na hugumancy,kiran Nas ya shigo mata.Ta tsurawa wayar ido bata da alamun ɗagawa,tana mamakin naci irin na Nas.Har kiran ya yanke bata ɗaga ba,illah saka wayar da tayi a airplane mode.Ta fara karatun ta hankali kwance,sai da ta kammala ta kwanta bayan tayi addu'ar kwanciya bacci ta shafe jikinta.Kuma bada jimawa ba,bacci ya sureta.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*ABUJA*

Sameera ce kwance bisa bed ɗin ɗakin Hisham,gama vedio call ɗinsu kenan ta haɗashi da husnah ta gama zayyano masa tsarabar da take so.Suna cikin yin Vedio call ɗin Husnah tayi bacci,aje wayar tayi tana jin kewarsa na ratsata sosai.Duk da cewa yayi mata albishir jibi war haka suna manne da juna,hakan baisa taji kewarsa ya ragu ba.Hannu ta miƙa ta ɗauki pillow ɗinsa tana sanya kanta a ciki,ƙamshinsa da ya kama komai take shaƙa tana sake jin kewarsa na sake rarike zuciyarta.Aje pillow ɗin tayi tana sake ɗaukar phone ɗinta ta domin kiran Rash,sai dai har wayar ya yi ringing ya katse bata ɗauki wayar ba.Hakan yasa Sameera aje wayar,ta ɗauki ɗaya phone ɗinta dake gefenta da kira ke shigowa.Ganin number ɗin Jamcy ce,ƙawarta da tare suke harkokin business ɗin saida jakuna da takalmar da suke order daga China.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*Dubai*

Gama wayanlrsu da Sameera da mintoci kenan yaga kiran Sameeran ya shigo cikin wayar Rash,a lokacin tana bathroom ta shiga wanka,hakan yasa ya tsurawa wayar ido kawai yana sakin murmushi.

Ɗaure da ƙaramin towel ta fito wanda ko cinyoyinta bai rufe ba,da murmushi ta dubeshi tana kashe masa ido ɗayaa.Cikin narke murya take faɗin,

"Kallon fa Ya Hisham?"

Tana maganar ne tana takowa zuwa wajensa cike da juya jiki,nuni Yai mata ga wayarta idanunsa fes akan cinyoyinta yake faɗin,

"Sameera ta kiraki."

Rash tayi wani farr...! Da ido tana faɗin,"To Ya baka ɗaga ba?"

Dariya Yayi sosai yana faɗin."Rash kina so yau Sameera ta biyo jirgin dare ta iskemu a nan kenan ko?"

Rash ta zauna a bakin bed ɗin tana watsa hannuwa alamun oho! Saura kaɗan towel ɗinta ya kwance ta riƙeshi da hannu,tana ɗaukar wayar ta shiga kiran line ɗin Sameeran.Yayin da Shi kuma Hisham ya mirgino zuwa gareta yana janta jikinsa,tare da sauke towel ɗin zuwa ƙas.Hannuwansa duka biyu ya ɗaura bisa ƙirjinta yana matsasu har saida ta saki ƙara,a lokacin Sameera ta ɗaga call ɗin.Hakan yasa Rash ta fara ƙoƙarin saita muryarta, suna magana da Sameeran.Basu wani jima akan line ɗin ba ta yanke wayar sabida yadda Hisham ke neman dagula lissafinta, ƙwace jikinta tayi tana zabga masa harara take faɗin.

"Ka cika son kanka da yawa, lina wanka ina jiyo yadda kuke waya kana tsarata,amma ni yanzu ka hana mu gaisa bare in tambayi ya Hussyna take."

Murmushi Hisham yayi yana tsareta da mayen kallonsa yake faɗin. "Sorry Baby,bani iya controlling kaina ne muddin zanga nan da nan a waje haka muraran."

Ya ƙare maganar hannuwansa na yawo a jikinta.Man da ya hanata shafawa kenan suka ɓige da wasanni da juna,kamar basu jima da gama gurzar juna ba tayo wankan.Tare suka sake shiga domin yin wani sabon wankan yana sanar mata yadda zai yi missing ɗinta tun yau,domin nan da 2 hours jirgin da za ta bi zai tashi,shi kuma Hisham sai jibi.

A gurguje Rash ta shirya cikin wasu riga da wando,sun kama jikinta sosai tare da yi mata kyau.Sai ta ɗaura baƙar Abaya a sama,tayi mugun kyau fatarta ya sake haske da fresh kamar wacce tayi watanni a cikin kasar.Azababban ƙamshinta ke tashi a jikinta kamar tayi ɓarin turare ne a jikin ta,kominta is ready,hatta kayanta da ta auno tana jin a daren yauma za su rigata isa 9ja ɗin.Luggage ɗinta kawai Hisham ya tayata ɗauka suka fito tana rataye da hand bag ɗinta.

Koda suka isa Airport ɗin saida Hisham ya ga an kirasu sannan suka rabu suna ɗagawa juna hannu,rayuwar da suka yi da Hisham na sake zama a cikin kanta.Can ƙasan zuciyarta tausayin Sameera take ji,ko ya za ta ji duk randa ta gano tarayyar da take da Hisham ɗin?Har jirginsu ya daidaita kansa a saman gajimare,Rash tana faman saka da warwara ne.....✍🏻