BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 9

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA❤*

©️Ayshat Ɗansabo lemu✍️

*Free page 9*

*ABUJA,9:02am*

Rash ce ke sakkowa daga matakalar jirgin da yayi landing a ƙasar,cikin ƙayataccen Airport ɗin Nnamdi Azikiwe dake Abuja.Fuskarta ɗauke da smile take taka stairs case na jirgin,tana shaƙar iskar ƙasarta ta haihuwa.Har ta gama sakkowa ta soma takawa sannu a hankali tana janye da luggage ɗinta,sai ƙatuwar jakarta dake rataye bisa kafaɗunta.Cikin kwanaki bakwai kacal da tayi a Dubai ta sake fresh sosai,da alamu ƙasar ta amsheta sosai.Sanin cewa sunyi waya da Anty Sameera ta sanar mata cewa Shehu driver ta turo ya ɗauketa,yasa Rash ke ta faman baza idanu har ta hangosa daga can nesa yana faman kalla-kalle da alamu ita yake baza ido domin ganin ta inda za ta ɓullo.Shi Ya amsa luggage ɗinta ya sanya a bayan boot,yayin da ta lafe a bayan Range Rover ɗin da Yazo ɗaukarta a ciki.Sai faman zuba mata sannu da zuwa Yake tana amsawa cike da kulawa,domin Rash sam bata da wulaƙanci bare rainin arziƙi.Tana da sauƙin kai da faran-faran da mutane,gata da kyauta sam abin hannunta bai rufe mata ido ba shiyasa take da mutane sosai.

Koda suka iso gida hatta jakar hannunta Shi ta bar wa ta shige ciki,burinta kawai ta jita a gado sabida baccin dake cike a idanunta,wanda bata samu yinsa a daren jiya ba.Sameera dama bata kai ga sakkowa ba hakan yasa kai tsaye Rash ta nufi ɗakinta,kayan jikinta ta cire tabi lafiyar bed daga ita sai bra da pant ta shige cikin blanket bayan ta ƙure sanyin Air-Condition.bata jima da kwanciya ba kuwa bacci yai awon gaba da ita .

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*ZARIA*

Uncle B misalin 12pm na rana ya iso gidan su Surry,yana sanye cikin ƙananun kaya da suka masa kyau tare da fidda ƙuruciyarsa a fili.Surayyah na zaune a cikin seater tana waya da Anty Safiya wacce ke bata labarin yadda suka kwashe da Aliyu,da irin gargaɗin da tayi masa akan Surry ɗin Uncle ya shigo.Surayyah sai dariya take kwasa hankalinta kwance,sallamar da Uncle B Yayi yasa ta ɗaga manyan idanunta ta sauke a kansa tana sakin smile tare da yanke wayarsu da anty Safiya.A lokacin har ya nemi kujerar dake facing ɗinta ya zauna.Sosai Yake ƙare mata kallo,tayi masa kyau cikin riga da skat ɗin dake jikinta na atamfar Batik mai kyau.Colour ɗin atamfar ya amshi fatarta matuƙa sosai,gaidashi tayi cike da shagwaɓa kamar yadda ta saba masa,tana sauke idanunta akan ƙaramin akwatin da Ya shigo dashi.Ya amsa gaisuwar yana faɗin,

"Ina Mum ɗin taki? "

"Yanzu ta shiga wanka."

Cewar Surayyah tana miƙewa tsaye.Dubansa tayi karaf sai idanunta suka kamashi Yana binta da kallo,murmushi tayi tana faɗin.

"Uncle B kar dai Kai ma tsiya za ka mini akan ƴar jikin da ake cewa nayi,naga sai kallona kake tayi tunda ka shigo."

Ɗauke kai Uncle B ɗin Ya yi cike da basarwa yana faɗin,"Eh mana Surryn Mum,kin sake girma sosai fa.Gaskiyar Mum ne,gara mu aurar dake kawai ko? "

Ya ƙare maganar cike da zolaya,hakan yasa Surry sake tunzure baki cike da shagwaɓa take faɗin,"Kai uncle B,ni dai ban san zancen aurennan,yanzu dai me za a kawo maka ko Ka karya a can ne? "

Idanunsa a kanta yake faɗin,"Na karya a can Surry baby,bani ruwa kawai."

Yana gama faɗi tayi gaba zuwa hanyar kitchen,ya bita da kallo har ta ƙulewa ganinsa,Yana mai sauke ajiyar zuciya. Zuwa yanzu abinda yake ji a kanta,sake ƙaruwa ma yake a cikin zuciya da gangar jikinsa.Kafin ta dawo Mum ta fito Ta sha ado cikin riga da zani na lace mara nauyi,tayi kyau sosai babu me cewa takai shekaru 50 a duniya.Za ka fi zaton ƴar shekaru 35 ne sabida bata da jiki sosai,kuma ga hutu da jin daɗi da ya sake ɓoye shekarun nata.Zama tayi Uncle B ɗin na gaidata,ta amsa tana faɗin.

"Sai yanzu ka shigo kenan,ai tun ɗazu mutumiyar taka ke faman mitar baka zo ba,kamar wata baby. "

Ya saki murmushi daidai lokacin da Surry ta fito ɗauke da goran Faro da glass cup ta aje a kusa dashi,tana faɗin,"Uncle B ga ruwan."

Ta ƙare maganar tana zama.Mum ce ta dube ta tana faɗin,

"Surayyah yanzu muka gama waya da Hajiya Halima ta Kaduna ɗinnan,ta shaidamin suna tafe zuwa anjima,wai za su shigo Zaria yau.Don haka maza tashi ki shiga kitchen,Lami ta taimaka miki a shirya abinci mai kyau da ƙayatarwa."

Surayyah ta amsa da, "Tuh Mumy,bari in tashi yanzu don naga gashi har 12pm ta wuce ma. "

Ta ƙare maganar tana sake nufar hanyar kitchen.Uncle B ne Yayi saurin kiranta yana nuna mata akwatin da Ya shigo dashi Yana faɗin,"Zo ki shige da tsarabarku ciki Surry."

Cike da murna Surayyah ta nufi inda akwatin ke aje tana faɗin,"Wow! Uncle B,mun gode,bari dai a buɗe tun yanzu ka cirewa Mum ɗin nata da kanka "

Ta ƙare maganar tana ƙoƙarin buɗe akwatin.Mum ce ta watsa mata harara tana faɗin,"No Surry,maza wuce kitchen,ke fa kika ce lokaci na tafiya."

Surayyah sai ta fasa buɗe akwatin ta juya zuwa kitchen, Uncle B na faɗin,"Kinji baby karki damu,duka ai kayanki ne.Jaka da takalma biyu sune nata."

Bai wani jima ba ya miƙe yace ma Mum zai shiga cikin gari zuwa yamma zai dawo,zuwa gobe sai su wuce Kaduna Shi da Surryn. Mum Tayi masa a dawo lafiya,tana cigaba da zama a cikin falon zuciyarta cike da murnar ziyarar da Hajiya Halima za ta kawo mata.Sosai Allah ya haɗa jininsu da matar,wacce ta girme mata da kusan shekaru sha biyar ma.

A can kitchen ɗin kuwa Surayyah sosai ta zage suka shirya abinci mai kyau.Chinese fraid Rice tayi sai coleslow da pepe chicken,sai ta haɗa lemuka kala 2.Lemun Chapman da kunun Aya,ta sanyasu a fridge domin su ɗauki sanyi.Tana aikin ne tana wassafa yadda za ta ga baƙuwar ta Mum,da ta lura Mum ɗin na girmamata da faɗin irin mutuncinta da karamcin da tayi mata a Umrah.So ɗaya Mum ta taɓa kai mata ziyara lokacin Surayyah na tsaka da fara Service an tura ta Bauchi,don haka Mum ita kaɗai taje shiyasa taji daɗi da yau Hajiyan za ta kawo ziyarar tana nan.Koda suka kammala kuloli masu kyau na alfarma Surayyah ta ɗakko ta zuba abincin a ciki,tare da shiryashi yadda ya dace.Lami ke ta faman gyara ko'ina,Surayyah tana fitowa bayan sun kammala ɗakinta ta nufa domin yin Sallah.Ta idar bada jimawa ba kuwa ta fara jiyo muryar Mum na ma baƙuwarta sannu da zuwa,hakan yasa ta aje hijab ɗin ta gyara face ɗinta kafin ta fito falon domin miƙa gaisuwa.

A Zaune ta samu Hajiya Halima,kusa da ita budurwa ce da za su iya zuwa shekaru guda.Kyakykyawar gaske ce babu inda ta baro kamannin Hajiya Haliman,har ƙasa Surayyah ta rusuna tana gaida Hajiya Halima cike da girmamawa.Hajiya Halimatu ta amsa cike da fara'a tana faɗin,

"Taho nan mana mu gaisa da kyau,da alamu ke ce autar Hajiya Aysha ko?"

Daidai lokacin Mum ta fito daga kitchen bayanta Lami ce ɗauke da tray,wanda aka zubo lemuka da ruwa ta aje a gaban su Hajiya Halima tana mai gaida Hajiyan kafin ta koma ciki.Mum ce ta dubi Surayyah tana faɗin,

"Auta to yau dai ga Hajiya,yanzu nake shirin kiranki ai,ashe ma kin fito."

Surayyah dake murmushi ta zauna a ƙasa kusa da Hajiyan ta sake gaidata,kafin ta dubi Humaida wacce tunda Surayyah ta fito take dubanta,ta gaida Humaidan da murmushi bisa fuskarta.Hakan ya sake saka Humaida jin Surry ta shiga zuciyarta farat ɗaya,Hajiya ce ta dubi Mum ɗin tana faɗin,

"Hajiya wannan ce Autarki da kike faɗi ko? Allah sarki Allah ya jikan Ƴan Uwanta yasa itace za mu rayu da ita rayuwa mai tsayi da albarka.Tubarkallah,Ma Sha Allah,Autar tamu Hajiya."

Hajiya Halima ta ƙare maganar idanunta akan Surayyah dake sakin murmushi,tana jin wani yanayi na ratsa zuciyarta ga me da Yarinyar.Yayin da Mum ta amsa da,"Ameen."

Can ƙasan zuciyarta wani miki na ƙoƙarin taso mata.Surayyah ce ta miƙe tana duban Humaid take faɗin,"Sister ko za ki zo muje ɗakina?"

Humaida ta saki smile tana miƙewa suka wuce ɗakin Surayyah. Iyayensu suka bisu da kallo,Hajiya Halima ɗauki cup ta tsiyayi ruwa ta sha,kafin ta aje cup ɗin suna sake gaisawa da Mum da hirar bayan saduwa.A cikin hirar nasu ne take faɗin.

"Hajiya nace Autar tamu ta samu miji ne,ko har yanzu babu tsayayye? "

Mum ta sauke ajiyar zuciya cike da murmushi take faɗin. "Wallahi Hajiya har yanzu dai,anata addu'a ne Allah ya zaɓa Nagari.Autar taki akwai farin jinin Samarin,sai dai har yau duk masu zuwa da shashanci kawai suke zuwa,hakan yasa har yanzu ta kasa fiddah tsayayye."

A hankali Mum ɗin take labartawa Hajiya Halima yadda Surayyah ke fuskantar matsala da Samari,ta ƙare maganar tana faɗin. "Zamani ne ya lalace,Samari da Ƴan matan duka sai kiga inba wacce Allah ya tsare ba,sam basu ɗauki soyayyar sakarci a bakin komi ba.Musamman su da ake ganin sun kammala jami'a tamkar idanunsu sun buɗe ne,ni kaina na ƙosa tayi auranta ko don surutun mutane,gani suke taƙi fidda mijin ne kawai don son rai."

Hajiya Halimatu ta dubi Mum tana faɗin."Karki damu da Maganan mutane,ke dai kawai mu cigaba da yi musu addu'a kawai.Allah ya cigaba da kare mana su Yai musu zaɓi mafi alkhairi,nima ga Humaida nan babu irin surutun da ba a yi na taƙi auren,amma itama babu tsayayyen.Amma wani hanzari ba gudu ba,a gaskiya Hajiya zan so hasashena ya tabbata.Me zai hana mu sake ƙulla zumunci ta hanyar haɗa Surayyah da Abdallahna,matuƙar ta ganshi Yayi mata.Domin kallo ɗaya nayi mata naga dacewar da za su yi da juna."

Wani daɗi ne ya lulluɓe Mum,tabbas idan hakan ya tabbata za ta yi farin ciki.Domin yadda take jin Hajiya Halimatu na yabon Yaron nata,ta tabbatar idan Surayyah ta sameshi tayi sa a.Ta dubi Hajiyar tana faɗin.

"Hajiya idan hakan ya tabbata zanyi farin ciki sosai,to amma shi bakya ganin za ki shiga haƙƙinsa idan baya ra'ayinta? Kinsan Samarin yanzu sam basu cika son auren haɗi ba."

"Karki damu Hajiya nina haifi Abdallah,kuma duk abinda na nuna ina so Shi ma yana so.Ta tabbatar bazai ƙi zaɓina ba,yaso wata Yarinya amma gani ɗaya Yayi mata basu sake haɗuwa ba.Tabbas Surayyah ta haɗa duk wata nagarta da cikar halittar da za ta ja ra'ayinsa zuwa gareta,muyi addu'a Allah ya shiga lamarin kawai."

Cewar Hajiya Halima.Daga nan suka cigaba da hirarsu cike da nishaɗi,zuwa lokacin Lami ta kawo abinci da komi gaban Hajiya Halima ta aje.

A ɗakin Surayyah kuwa ita da kanta ta je ta ɗebo abinci da komi ta kawowa Humaida,suna ɗan taɓa hira wanda rabi duk akan skull ne.Ita Humaida tana sanar da Surayyah jami'an Bayero tayi,ita kuma Surayyah ta shaida mata nan ABU tayi Samaru.Kaɗan Humaida taci abincin,sai kunun Aya da yayi mata daɗi take ta kurba.

"Sister gaskiya Allah ya baki baiwar kyau da diri,ina matuƙar son colour ɗin skin irin naki.Gaskiya kina haɗa go slow na ƴan maza,ina ma ya Abdallah zai ganki ya soki tabbas da Ya gama yin sa a."

Cewar Humaida idanunta akan Surryn wacce ta saki dariya tana faɗin."Kai Sis,kina da abin dariya duk kyawuna ina na kaiki.Kina da Yaya da baiyi aure ba kenan? "

Ta ƙare maganar tana duba wayarta domin jin ƙaran shigowar saƙo,yayin da Humaid ke faɗin,"Ƙwarai kuwa ina da Yaya handsome guy wallahi,wanda za ku dace da juna.Bari ma kiga pic's ɗinsa."

Ta ƙare maganar tana miƙa ma Surayyah wayarta bayan ta nuno mata pic ɗin Abdallah.Idanu Surayyah ta zubawa pic ɗin kyakykyawan matashin saurayin,tana jinjina haɗuwarsa.Bata wani zafafa a kallonsa ba ta miƙa ma Humaida wayar tana faɗin,

"Aiko yaci handsome ɗin Sis,amma ai yafi ƙarfin ajina.Ke nifa yanzu maza sun fice daga raina,kawai dai ina so inyi aure ne don raya sunna da kuma faranta ran Iyayena,da basu da Burin da ya wuce hakan a yanzu."

"Ke ko me yayi zafi haka Sis?"

Humaida ta tambaya cike da mamaki,hakan yasa Surry sakin smile tana tsakura mata kaɗan daga yadda duk mazan da suke zuwar mata suke nuna jikinta suke so ba ita ba.Ta ƙare maganar da faɗin. "Duk wanda zai zo akwai BURIN ZUCIYARSA a kaina Sis."

Humaida ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina kamun kai irin na Surayyah,domin ita kam bata ɗauki soyayyar shan sweet a komi ba.Sosai take sakarwa Junaid jikinta Yayi yadda yake so,kuma bai taɓa neman abinda ya wuce romance daga gareta ba.

"Gaskiya Surry kinji daɗi,kamun kanki har Yayi yawa,tamkar ba ki je jami'a ba.Ƴan mata irinki sunyi karanci gaskiya,na kuma sake jin cewa lallai za ku dace da Yayana,domin irinki yake da burin aure."

Surayyah ta saki dariya tana faɗin,"Haka dai kike cewa Humaida,yanzu dai bari muyi exchanging number a dinga zumunci.Gobe ma zan shigo Kaduna da Uncle ɗina."

Sukai exchanging number Humaida na faɗin,"Amma dai za ki zo wajena ko?"

Surayyah tayi murmushi tana faɗin"In Sha Allah Sis."

Sai da suka tashi tafiya Mum tayi kiransu suka fito,daga Hajiya Halima har Mum mamakin saurin sabon da su Surayyah sukai da juna suke.Domin kowa yasan halin kayansa da rashin saurin sabo,barin ma Surayyah da take jinta miskila-miskila inba sabo tai da mutum can ba.

Har waje suka yo ma su Hajiyar rakiya,Humaida ta dage sai sun ɗauki pics.Hakanan Surayyah ta biye mata domin dama ita ma'abociya son hoto ce,hoton ko ya ɗauku abinka da babbar waya mai ɗan karan tsada.Ita kanta Surry taga kyan hoton hakan yasa tace Humaida ta tura mata ta chat,kuɗi Hajiya Halima ta ba Surry amma sam Mum ta hanata amsa.Snacks da Dambun nama da Mum tayi domin Surayyah ta kaiwa Hajiya Kaka,shi tasa aka ɗakko ta bai wa Hajiya Halima.Sosai taji daɗi tana sake jinjina karamci irin na Mum,sai da Mum ta juya zuwa ciki tabar Humaida na sallama da Surry.Hajiya Halima tai wa Surayyah jan ido akan lallai sai ta amshi kuɗin da tai niyyar bata,hakanan ta amsa tayi godiya tare da juyawa zuwa cikin gida.Su kuma driver ya tashi mota suka bar gidan,za su nufi gidan Alhaji Saleh.Kasancewar nan gidansu Surry suka fara zuwa,daga gidan Alhaji Saleh ne idan suka duba jikin nasa za su wuce KD.......✍🏻