BURIN ZUCIYA Chapter 10
*BURIN ZUCIYA❤* *Arewapen@ayshadansabo*
©️Ayshat Ɗansabo lemu ✍🏻
*Free page 10*
*ABUJA*
Sai ƙarfe kusan ɗaya na rana Rash ta tashi,wanka ta faɗa ta fito ɗaure da alwala domin gabatar da Sallar Azuhur.Bata wasa da sallah ko kaɗan,sai da ta idar da Sallahn ta saka kaya ta fice.Ganin babu Sameera a falon yasa ta nufi kitchen ta sanar da Fauziyyah ta kawo mata abinci falon sama,domin yunwa take ji matuƙa.Sama ta haura daga kitchen ɗin tana ƙwalla kiran.
"Anty Sameera!"
Sameera dake kwance bisa 3 seater da ya ƙawata madaidaicin falonta na up stair's,ta ɗago kai tana duban Rash cike da murnar dawowarta take faɗin,
"Oyoyo Rasheeda,ashe kin tashi.Na sauka ƙasa har sau biyu kina bacci,nace lallai kin kwaso gajiya.Husnah har ta gaji da mitar son ganinki tayi bacci."
Rasheeda ta zauna suna fuskantar juna tana faɗin,"Ayyah! My Angle,wallahi na gaji Anty.Amma fa Dubai tayi,kamar naita zama a can."
Ta ƙare maganar tana dariya sosai,Sameera na taya ta dariyar.Fauziyyah ce ta iso tare da dire plate ɗin da ta zubo ma Rash abinci,ta koma domin ɗakko mata lemu da ruwa.Abincin Rash ta ɗauka ta fara ci cike da kewar abincin gida,domin Fauziyyah ta iya abinci sosai,sabida fannin data karanta kenan.
Idanunta cikin na Sameera take faɗin, "Anty Ya Hisham bai dawo ba kenan.Tunda na tafi duka sau biyu kawai mukai waya,na ɗauka ma ya dawo ne."
Ta ƙare maganar tana aje plate ɗin abincin,ta ɗauki cup ta tsiyayi ruwan da Fauziyyah ta aje.Sameera ta dube ta tana ɓata fuska,cike da kewar mijinta take faɗin,
"Wallahi Rash wai sai gobe zai dawo,ai nace gaskiya idan ya dawo sai ya daɗe bai kuma tafiya ba.Wallahi wannan tafiyar da Yai ji nake a cikin zuciyata kamar ban taɓa kewarsa irin hakan ba,sam zuciyata ta gaza samun nutsuwa Allah dai yasa ba wani abu bane zai faru dashi ba.Ina tsananin son mijina Rasheeda."
Wani murmushi ƙasa-ƙasa Rash tayi kafin tayi saurin faɗin,"Kai Anty Sameera,ka jiki da wani magana.Kamar yau Ya saba tafiye-tafiyensa,lafiya lau zai dawo kawai dai don bai saba tafiya kusa-kusa haka bane.Lafiya lau zai dawo,ai naji daɗin mutanan da Ya haɗani dasu Anty.Komi cikin sauki nayi,My Hussy ma ta tashi in fara fito mata da tsarabarta na baby."
Rash ta ƙare maganar tana sakin smile,ƙasan zuciyarta na jinjina halin mazan yanzu.Tabbas maza yanzu ba kowa bane ya kasance mai amana da tsoran Allah,shaiɗanci kawai suka saka a gaba.Rayuwarsu dashi acan take tunawa yadda suka gurji juna,amma yanzu gasu a mabanbanta waje."
Sameera ce ta furta. "To Allah dawo min dashi lafiya,yanzu bani labarin yadda kika ga Dubai."
Murmushi Rash tayi har haƙoranta suka bayyana,kafin ta furta. "Me kike ci na baka na zuba Anty,ai labari sai kince baki so.Ni dai yanzu wallahi tashin mutuniyar zanyi,domin i really miss her."
Ta ƙare maganar tana nufar hanyar bedroom ɗin n Sameera,domin tado Husnah.Sameera na kiranta amma tayi biris da ita.Bata ɗauki dogon lokaci ba suka fito ita da Husnah,wacce murnan ganin Anty Rash ɗin yasa ta wartsakewa cikin sauri.
Down stair's suka nufa Rash riƙe da hannun Husnah tana faɗin. "Anty to mu dai munyi ƙasa,sai kin sakko."
Sameera ta amsa da. "Tuh sai na sakko,amma sai can zuwa anjima, sabida zan yi gyaran ɗakin Hisham ne."
"Okey, ba don na gaji ba ai dana tayaki."
Cewar Rash suna fara taka stair's ɗin zuwa ƙasa.Direct ɗakinta suka nufa suka baje bisa bed ɗinta,hand bag ɗinta ta janyo ta fara fiddo tsadaddun chocolate da ta siyo ma Husnah.Cause gasu nan birjik a Airport na Dubai,kafin ta buɗe luggage ɗinta ta ciro wata katuwar ƴar bebi ta miƙawa Husnah.Ta saki chocolate ɗin hannunta ta rungume babyn tana tsananin murna,nan Rash ta dinga biyewa Husnah har zuwa lokacin da kiran Hisham ya shigo wayarta.Sai ta koma can ƙarshen bed ɗin tana amsa call ɗin.Sun jima suna magana kafin daga ƙarshe ta bashi wasu zafafan kiss kamar yana kusa da ita,ta aje wayar tana jin kewarsa sosai.Zuciya da gangar jikinta sunyi sabo dashi mai tsanani,za ta yakiceshi tayi aurenta ne domin tasan tarayyarta dashi dole akwai iyaka.Sosai take ji a jikinta cewa asirinsu,daf yake da tonowa.......
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
*ZARIA*
Misalin ƙarfe shida na yamma bayan su Hajiya Halima sun jima da barin gidan,Mum ce da Surayyah zaune a cikin falo suna hira.Rabin hirar duk akan yadda zumuncin yanzu ya lalace ne,sai kaga duk kusancinka da ɗan Uwa in aka ce baka dashi bai maida kai komi ba.Da masu shi ake yi,wanda bai dashi kullum shine koma baya.Duban Surayyah Mum tayi kafin ta kirayi sunanta,hakan yasa Surry maida hankalinta kacokan akan Mum ɗin domin ta gama fahimtar cewa magana mai muhimmanci Mum ɗin zatai mata.Ganin Surryn ta bata nutsuwarta yasa Mum ɗin fara faɗin,
"Surayyah Hajiya Halima ta zo da wata magana mai muhimmanci,tana son mu ƙulla zumunci mai ƙarfi ta hanyar haɗaki aure da Yaronta ɗaya tilo Abdallah,sai dai ba za mu yi muku dole ba,matuƙar baku aminta da juna ba.Ina fatan idan har Shi Ya amince,to Kema ki amsheshi da zuciya ɗaya,kiyi addu'ar Allah yasa alkhairi.Hajiya Halima mace ce da tasan mutunci da ƙimar ɗan Adam,mace ce da nake miki kyakykyawar zaton idan har ta zama suruka a gareki za ki yi alfahari da hakan.Na sha jin tana yabon halayyar Abdallah da irin son da take masa,hakan yasa da ta furta ƙudirinta naji zuciyata ta gamsu da kyakykyawar niyyarta.Don haka kiyi addu'a,idan da alkhairi ne Allah ya haɗa kanku."
Ta ƙare maganar tana tsurawa Surayyah ido,wacce jikinta yayi sanyi tare da jin wani yanayi wanda ba za ta iya fassara mene ne shi ba.Zuciyarta ce ta shiga hasko mata hotonsa da Humaida ta nuna mata,yayin da kunnuwarta ke sake jiyo mata kalaman Humaida tamkar a yanzu take furta matasu.
_Ina ma Ya Abdallah zai ganki ya soki,tabbbas da Ya gama yin sa a._
Waɗannan sune kalaman dake dawo mata, maganar Mum ɗin a karo na biyu ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
"Surayyah baki ce komi ba."
Cewar Mum ɗin tana sake zubawa Surayyah idanu.Sai ta saki ajiyar zuciya tana faɗin,"Mum kawai ina tsoran auren haɗi ne,kada yazo Shi yana da wacce yake so."
Tayi maganar a sanyaye sosai,tana ji can ƙasar zuciyarta na cika da ruɗani.Tana tsoran auren haɗi musamman idan akai rashin sa a shi ɗin zai amsheta ne domin yin biyayya ga Uwarsa.Ita BURIN ZUCIYARTA a kullum shine tayi auren soyayya,tana so ana sonta.Amma tunda taji Mum ɗin ta tinkareta da maganar ta san tana son abun a ranta ne,kuma tana matuƙar ganin darajar Hajiya Haliman.
"Surayyah inda tasan yana da wacce ya tsayar yana so,da bazata nuna son haɗa zuriya dake ba.Ta shaida mini wata Yarinya ya gani,amma sau ɗaya ya ganta ya kamu da sonta bai kuma sake ganinta ba."
Cewar Mum tana dafa kafaɗun Surayyah tare da cigaba da faɗin. "Abunda nake so dake Surry,kada ki sawa zuciyarki wani abu daban.Kina sane da cewa Babanki ya baki lokaci wanda har kinci fiye da satika uku,a cikin watanni biyu kacal da Ya baki ki fiddo mijin aure.Don haka idan har Abdallah ya amince bana so ki watsamin ƙasa a ido,ki amince dashi ki koyawa kanki sonshi.Idan kuma Mubarak ɗin kike so,ko kina da wani tsayayye ki sanar dani.Domin ni bazan shiga haƙƙinki ba don in faranta ran Hajiya,duk da cewa ina matuƙar ganin kimarta"
Cikin sauri Surry ta kaɗa kai tana faɗin. "Mum bani son Mubarak,ba kuma ni da kowa a yanzu da nake saurara.Allah Yai min zabi mafi alkhairi,ni da sauran musulmai baki ɗaya."
Tana gama faɗin hakan ta wuce ɗaki kai tsaye,ba tare da ta sake jin ta bakin Mum ɗin ba.Saman bed ta kwanta ta saki kukan da bata san dalilin yinsa ba.Soyayyar mutum biyu take ji na mintsinin zuciyarta matuƙa,domin ta so su har cikin zuciyarta.Wato Nas da Aliyu,BURIN ZUCIYARSU a kanta ne kawai ya tarwatsa komi.Domin ta sha alwashin cewa ba za ta taɓa auren duk wani Namijin da Ya nuna jikinta yake so,ba ita karan kanta ba.
Tana nan kwance tana tunane-tunane,gefe guda hoton face ɗin Abdallah na mata kai kawo.Tabbas ya haɗu iya haɗuwa,amma hakanan take ji kamar guy din yafi ƙarfinta.Tana ji sam kamar bazai taɓa sonta ba, muryar Uncle B ta jiyo daga falo amma ta kasa tashi ta fita,har sai da ta jiyosa yana ƙwalla kiran sunanta.Ta yunƙura ta tashi zaune,tana goge fuskarta tare da son saita nutsuwarta,kafin ta zari ɗankwalinta da ya zame tayi waje.
Shi kaɗai ta samu a zaune a cikin falon,idanunsa a kanta har ta ƙariso cikin falon ta nufi kujerar dake kusa dashi ta zauna tana faɗin,
"Uncle har ka dawo,sannu da zuwa. "
"Surryn Mum da Uncle me yafaru naga idanunki kamar kinyi kuka,ko duk shagwaɓar Autancin ne ya tashi?"
Cewar Uncle B ɗin yana kafeta da idanunsa tare da sakin murmushi.Hakan yasa Surry sakin dariya tana faɗin,"Kai Uncle B,ai yanzu an girma an daina kukan shagwaɓa."
Ta ƙare maganar tana kai hannu ta ɗauki wayarsa dake aje.Ya dubeta yana faɗin,"Gobe fa da wuri za mu wuce Autan Mumy,don haka ki shirya da wuri please!"
"In Sha Allah Uncle B,ai duk na ƙosa in ganni a gaban Hajiya Kaka."
Cewar Surayyah tana dariya.Kiran Sallar Magriba da aka yi ne yasa su tashi a tare, Shi ya fita domin zuwa masallacin dake kusa dasu,ita kuma ta nufi room ɗinta domin ɗaura alwala.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
*KADUNA*
Shigowarsa gidan kenan misalin tara da rabi na dare,yunwa yake ji sosai domin rabonsa da abinci tun rana a wajen reception ɗin ɗaura auren da suka je da Rayyan.Gashi sam bai iya cin abinci mai nauyi da dare ba,yana faka motar ya fito bayan ya kulle kai tsaye sashin Hajiya ya nufa.Humaida ya tadda a kwance cikin seater tana Sana'ar danna waya,gefe guda TV ke aiki ba tare da hankalinta na kai ba.Sallamarshi ta amsa tare da tashi zaune tana gaidashi,Ya amsa fuskarsa babu wani fara'a kafin ya furta,
"Ke ina Hajiyata take? And ki tashi yanzu ki dafamin shayi,sai haɗa min spicy bread omellete ƙwara biyu kacal."
Ya ƙare maganar yana yin gaba.Muryar Humaid ɗin ya jiyo tana faɗin,"Tuh Ya Abdallah,Hajiya na ɗaki."
Aje wayar hannunta tayi ta nufi kitchen domin yi masa abinda ya sata,yayin da shi kuma ya nufi ɗakin Hajiya bakinsa ɗauke da sallama.Murɗa handle ɗin ƙofar Yayi,Yana jiyo muryar Hajiya tana bashi izinin shiga bayan ta amsa sallamar tasa.A zaune ya sameta ƙasan carfet tana duba wasu kaya,da ta dawo ta iske an aiko mata dasu.Gaidata Yayi yana faɗin,
"Hajiya Ya gajiyan hanya,ya jikin Baba Saleh ɗin kuma? "
Hajiya ta aje kayan tana dubansa da murmushi take faɗin,"Jikinsa kam Alhamdulillah! Ya warware sosai,gajiyan hanya kam yabi lafiya Auta."
Abdallah Yayi murmushi sosai yana jin daɗi idan ta kirashi da Auta ɗinnan,duk da a yanzu ga Humaida nan itace Autar tunda Billy ta rasu.Hira suka fara taɓawa har zuwa lokacin da Humaida tayi sallama ta aje mai ƙaramin tire a gabansa,tana faɗin.
"Gashi Ya Abdallah. "
"Ok thank's."
Cewar Ya Abdallah yana kai hannu ya buɗe plate ɗin spicy bread ɗin,tare da ɗaukar ɗaya ya gutsira ya aje.Tuni Humaida ta fice abinta,hakan yasa Hajiya ta gyara zama tana dubansa,bakin ta cike da magana amma so take ta barshi yaci abincin sa kafin ta sanar dashi abinda ke zuciyarta.Tunda ya ga yadda take dubansa tana sakin masa smile jikinsa ya bashi akwai magana,sai ya kurɓi ruwan shayin tare da aje cup ɗin yana dubanta da murmushi yace,
"Hajiya duk yadda akai ta samu ne,akwai magana a bakinki."
Wani ƙayataccen murmushin ta sake saki,kafin ta kirayi sunansa."Abdullahi."
Ya amsa da "Na'am Hajiya." Yana mai tattare nutsuwarsa da hankalinsa baki ɗaya Ya miƙa zuwa gareta.
Ganin Ya tattara hankalinsa zuwa gareta baki ɗaya yasa ta fara da faɗin,"Abdallah kamar yadda kasani bani da wani BURI a yanzu da Ya wuce ace naga aurenku kai da Humaida,kai musamman ma kai Abdallah,amma sam ka kasa tsaida hankalinka ka zaɓi abokiyar rayuwa.Masu kawo kansu gareka duka ka nuna ba suyi maka ba,baka da sha'awar auren zumunci,ita wacce kake iƙirarin kana so har yau Allah bai sake haɗa fuskokinku ba.To Alhamdulillah ni a yau na gano maka matar aure Abdallah,wacce za ku dace da juna.Yarinya mai tarbiyya da nutsuwa.Uwa Uba kyau da diri,Abdallah a matsayina na Uwa wacce tayi silar kawoka duniya na zaɓa maka Yarinyar da nake ganin za ku dace da juna sosai.Ina maka sha'awar auren Surayyah ɗiyar Hajiya Ayshatu.....✍🏻