7
by @gureenjoh
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjoh6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
*SHAFI NA BAKWAI*
Kasuwar cike yake da hayaniya, masu sayar da kaya na yi hada hada ko ta ina haka ta ratso da motarta inda yayi mata tayi parking, sai da ta ɓata lokaci ta sauƙo wearing all Black hannayenta cikin aljihu, fito ma take yi da Bakinta.
Cikin seconds ta ɗauki hankalin mutane dayawa ta inda take duk an yi shiru kawai an zuba mata ido.
Wani matashi ya taɓa na gefenshi da suke sayar da kayan dan kunne da sarka
"Wallahi ita ce! DIVA ce! Wannan da kake gani
Ko manyan maza suna tsoron shiga komarta"
"Ita ce wa? Ni ta burgeni"
"kambala'i na rantse idan kana son kanka da lafiya ka kama bakinka tun kan ta ji ka, ka santa kuwa? To wannan da kake gani idan ta yanke hukunci kanka babu wanda ya isa ya ɗaga mata yatsa kaff zuri'ar ku"
"Meyasa ake kiranta DIVA kaman wata shugaban 'yan dabar indiyawa"
Ya faɗa yana dariya har da sake karkacewa don kallonta da kyau.
Ɗayan ya ce
"Ai duk ɗaya, babu macen da tayi kaurin suna a dabanci irinta, kuma fa har da ma ɗaurin gindi daga wasu 'yan siyasar garin nan saboda ubanta shi ke tafiyar musu da siyasa yadda suke so idan lokaci ya yi. Sunan DIVA kuma na taɓa ji daga wani dan daba wai tun tana shekaru takwas a duniya ta samu sunan, a lokacin farkon riƙe wukarta ta cire yatsar wani da ya nuna babanta da yatsa...DIVA na nufin mai kwarjini, kyau, da kuma confidence na tarar duk wani aradu da ka, irin waennan boss ladies ɗin ake kira DIVA to daga yanayinta ne aka sa mata sunan ga ta da son gayu kuma Ubanta na kashe mata, ta haɗa kyau, iko ga izza irin na duk wani ɗan daba mai ban tsor..."
Wuce su ta zo yi hakan ya sa duk suka yi shiru har ta wuce ta ɗan kallesu kaɗan don ta tsinci maganan da su ke ɗin amma bata yi niyyar kula su ba ne ta shiga shagon turare tana shiga ta zare glasses na idanunta ta tsaya kikam kan ta ce cikin muryarta
"Duk ku fita waje...!"
Ta yiwa costumers da suke wurin umurni, dayawa tsoron ta da suka ji ya sa suka fita amma wasu Matasa na nan tsaye.
"Akan me za ki ce mu fita? Na ga abin da kika zo saya shi mu...."
Wukar da ta zaro shi ya datse maganar ta nufe shi tana juya tsinin wukar a fuskarshi.
"Ban ji da kyau ba maimaita..."
Jikinshi rawa ya kama, yana mamaki.
"Naa fyeɗe fatar fuskarka idan na rufe ido na buɗe na ganka tsaye a gabana....."
Kaman walkiya haka suka yi waje da gudu.
Ta cigaba da riƙe wukar.
****
"Nana"
Zubash ta kira ƙanwartata da ta buɗe ido ta kalleta ta sake lumshewa.
"Yaya Zubaidah ke ce? Kin dawo?"
"Eh Nana ya jikin? Fatan kin ji sauƙi?"
"Da sauƙi yaya Zubaida"
Kallonta ta cigaba da yi har Zubaidar ta tsargu
"Menene kike kallona haka Nana? Na chanza ne?"
Nana ta girgiza kai tamkar za tayi kuka ta ce
"Yaya Zubaidah don Allah ki daina irin wannan rayuwar, bana jin daaɗin ganinki haka... Yaya Zubaida mu gudu mu koma wurin Abbanmu na tabbatar zai riƙe mu...ba na so ki mutu akan wannan tafarkin, yaya Zubaida a makarantarmu har kwatance ake da ke da Diva, idan na shiga mutane a tsarge nake ni karan kaina dayawa kyamata suke, wasu ma cewa suke tare muke yawon iskanc..."
Kuka ne ya sarƙe ta.
"Dalilin da kika hau hanya kenan ki kashe kanki ki huta?"
Zubash ta faɗa cikin sanyin murya.
"Ko ɗaya, na san duk wanda ya kashe kanshi wuta za shi Yaya Zubaida ba zan fara ba, wasu seniors ne suka yi bullying ɗina akan ki na fito ina tunanin wani irin rayuwa muke ciki ban kula da na zo hanya ba mota ta kaɗe ni. Don Allah ki amince Yaya Zubaida mu gudu Taraba"
Ta ƙarasa da wasu irin hawaye.
Zubash ta ɗaga idanunta sama cikin kokarin hana nata hawayen kwaranya, kan ta yi magana Mamansu da ke daga kofa kusan tun fara maganganun nasu ta banko ta shigo.
"Wato ciwon ƙara tsirarshi kike kina labgwabewa don karya zuciyar yayarki ku gudu ku bar ni ko? Toh Allah ya kamaki...kina tunanin a banza ne Zubaidar ke kula da ni? Bautar da na yi muku kun yi min ne? Wahalar da na sha daga daukar ciki har zuwa haihuwa da raino wallahi idan kuka gudu duk sai na yi muku Allah ya isa a kanshi don ko nawa kuka ba ni baku biyani ba. Kuna komawa wurin ubanku kuma babu ni babu ku har Abada ko mutuwa na yi Allah ya isa wanda ya zo kan gawata. Munafuka Algunguma"
"Mama ta ya zan fara tsirar ciwo? Mama haka Allah ya ce? Ki daina amfani da kalmar tsinuwa kina dulmiyar da mu Mama, babu inda Allah ya ce a miki biyayya a sabonsa ko ita Yaya Zubaida ta sani kin riga dai kin yi brain washing ɗinta ne take biye miki amma wallahi kaso mai girma cikin zunubinta naki ne Mama"
Hannu ta kai za ta kai mata duka Zubaida ta riƙe.
"Kar ki daketa mama"
Yadda tayi magana ya sa maman fusge hannunta.
"Ki cigaba da zama Nana ke faɗa miki abin da za ki yi da wanda ba zaki yi ba, idan kika naɗe hannu kika dawo kika zauna zan ga uban da za mu ci har mu rayu kuma wallahi ina kan bakana Yasin zan ja muku akan nonona da kuka sha muddin kuka waiwayi marar zuciyar ubanku"
Tana kai nan ta fice fuuuu khadijan ta fashe da marayan kuka yayinda da Zubaida ta saki murmushi, ba yau ne ta fara jin hakan daga Mamansu ba tun kan ta gama mallakar hankalinta take ji, a da idan ta faɗi hakan hankalinta kan tashi damuwa ya shigeta har ta ji zata iya koma menene don cikawa Mamansu burinta na dai a kawo mata kuɗi, amma a yanzu ko ɗarr bata ji ba kuma da ta yi niyyar komawa uban nasu tsaff za ta koma amma ta tsane shi, ta mishi mugun tsanar da bata ji ta taɓa yi wa kowa ciki har Iro da basa haɗa Inuwa.
Ko babu komai shi Malam Iro ya bar su sun zauna karkashin inuwarsa, sau dayawa shi ya zama makari kuma jingina a garesu Dukda bai ɗauki ragamar uban gaske a rayuwarsu ba amma ya tare musu wani gibin.
"Khadija ki yi shiru haka kin ga ba lafiya ce da ke ba! Komai zai wuce ne"
"Har yaushe Yaya Zubaida? Har wani lokaci za mu cigaba da irin wannan rayuwar? Me yasa Allah ya ba mu irin waennan iyayen?"
Sai a lokacin zuciyar Zubaida ya karye ta miƙe kawai ta fice don hawa sama ne kawai zai hanata kuka a lokacin kuma tabbas ta shawu ɗin don codein uku ta kwankwaɗe wani nurse ne ya hange ta ya taho
"Me kike yi haka a asibiti?"
Ta kalleshi ta watsar tare da juyawa ta koma ɗakin
Khadija sai ganinta tayi ta dawo ɗakin ta zauna sai bacci.
Idanu khadija ta zuba mata tana ta kallonta cikin wani irin tausayi da karayar zuciya.
*****
"Kai!"
Mai sayar da kayan ya matso da sauri yana zubewa
"Ranki ya dade"
"Haɗomin abin da na saba saye"
Tun ranar da ta zo ta zaɓi turarukan da take so ta tafi bayan kwana biyu ta dawo ya tambayeta waennene ta kikkifa mishi maruka bai sake tambaya ba idan ta zo tana faɗa zai tattaro su ya zube mata a leda ya kai mata har mota.
Wannan karo ma haka aka yi ya gama ta bashi Atm ya zara ta juya ya bi ta har mota ya kai mata.
Ta jima zaune ciki tana shan ice wanda ita fa shi ne kabb ya zama addiction ɗinta idan bata sha ba har ciwon kai take, ba ma ta fara tunanin yadda za ta yi rayuwa babu shi, idanunta ne ya kai kan wani ya shakure wuyan karamin yaro mai sayar da pure water yana kokarin dukan shi ta buɗe motar ta fita.
Ya ɗaga hannu kenan ya ji an riƙe ta murɗe tare da ture shi yayi tangal tangal yana kallonta.
"Ƙaton banza Ƙaton wofi idan kwanji kake son nunawa ka samu kato mana daidai kai sai ka samu yaro ƙarami ka zalunce shi?"
Miƙewa yayi zai tunkareta wasu kananun ɓarayin kasuwa suka riƙe shi
"Kai malam Wuta gabanka wallahi.... Kiyaye kar ta soye ka gwara ka shafawa kanka lafiya ka bata haƙuri idan ba haka ba...."
"Idan ba haka ba m...."
Ƙulii suka kaiwa bakinshi bai zaci za su dakeshi ba ya riƙe da wuri yana jin gishiri gishiri na jini da ya tarar mishi
"Ka ware ko kuwa?"
Da sauri ya wuce suka fara mata kirari, Ta juya wurin yaron ta bashi dubu biyu tace ya kara jari yayi sana'a.
Yayi mata godiya bata kula shi ba tayi mota waennan Matasa na bayanta su ma sallanarsu tayi suna ta mata kirari har kan ta ja ta fice da wani irin gudu, music na tashi cikin motar, daidai ta zo shan wata kwana motar Malam Bala ma ta sanyo kai Dukda ya yi Horn sossai bai ji alamar wata mota ba ita kuma ba Horn tayi ba kuma gudu take, ta yi wani irin buga musu gefen mota, ƙiiiiiiiii ta jaa wani uban birki a fili ta furta
"Kan uba!!"
Cikin fushi, motar take kallo da ido ta mirror amma don rainin wayo na cikin bai sauƙo ya bata hakuri ba, ranta ne ya ƙarasa ɓaci da wani irin zafin nama ta ɓalle murfin ta fitoo...
Tana kallon yadda gaban motarta ya gurje har danger light ɗinta na gaban ya fashe tayi saurin isa farar motar ta ɓalle murfin, malam Bala da tun da ya ga ita ce yake salati jikinshi na wani irin rawa, Ammar na ƙoƙarin mishi magana sai gani suka yi an janye shi waje, shima malam bala bai gama firgita ba sai da ya ji ta mishi riƙon ɓarayu hannun mata, ta chakumo kwalarsa ta janyosa waje tamkar wani ƙaya ta haɗashi da jikin motar idanunta gabaɗaya a waje suka kara firgita dattijon...
🖤Gureenjoh🖤