07
by @sadisakhna
_____👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
*Harƙa ta (7)*👑
Muryar Baba Yakub na tsinkayo yana magana.
“Inaso ki saurareni dakyau,Yanzu zamu tafi dake inda wanda zasu tafi dake suke,ki tunada duk abinda ummanki ta faɗamiki sannan ki tuna duk wani waje dazaki taka a duniyar nan akwai ƙakubalen dayake tattare dashi,sannan Allah baya baka wata ni'ima face kaima ya jarrabeka akanta. Sannan wahala ko jarrabawa dazaki fuskanta bazai hana kuma Allah ya yayemiki yamiki sauyi ba. Zan kaiki wannan waje a matsayin baiwa marar sani,amma hakan bashine zaisa ki kasa neman cigaba a wajen ba. Domin kisa a ranki wannan wajen shine mataki na farko na rayuwar dazaki fara,komin wuya karki sake baki ginashi dakyau ba,domin idan yayi kyau zakici ribarsa koda gaba babu kyau,amma idan kika kasa jajircewa baki bari yayi kyau ba ti lallai ko gaba yayimiki dadi dole zakiga gurbinsa. Wannan abu bazan faɗamiki miye ba,amma a yadda na kalli kaifin ƙwaƙwalwarki da sannu zaki gank menene. Ummanki kuma karki damu zata kasance cikin hali mai kyau,sannan idan wani lokaci yayi zanzo inda kike nakaiki gareta ki ganta”
Shin ni baba Yakub wanne irin mutum ne ne,Azzalumi ne kokuma mai son yin taimakone ta wata fuska,yanzunnan yarabani da ummata ya siyar da ita,nima kuma yasayar dani ɗin,amma kuma yanamin nasiha yajuya izuwa yanda nasanshi lokacin da muna cikin jirgin. Dukkan maganganunsa babu wanda banji ba,amma sai nayi biris ina cigaba da kuka na. Saboda bansan wacce irin amsa zan bashi ba.
“Ki taso mu tafi gidana,idan Allah yakaimu gobe zamu kama hanyar inda zaki je ki kama naki aikin”
Bance masa ƙala ba nan ma,ganin ya tashi ya nufi hanyar fita daga tantin yasa nima natashi na bishi,wasu kuma wanda zuwa yanzu na gane suma bayine kamar dai ni. Suka ɗauko gawar abah na suna binmu a baya. To yazanyi bazan bishi ba,da mugun dabaka sani ba ai gwara mugun daka sani…
Bamuyi tafiya mai nisa ba muka iso bakin gidannasa,kokuma munyi tafiya mai nisan shagala danayi da kallon yanayi,tsari da kuma gine gine na garin shiya hna nakalli ƴar doguwar tafiyar damukayi daga bakin gabar babban kogin izuwa cikin garin.
Ba bata lokaci yadanna kansa ciki nima nabi bayansa batareda najira mai zaice ba. Hannuna yana riƙe gam da ƙullin kayana da umma tabani,nata kuma dana abbah ta ɗauka tatafi dashi.
Babban farfajiya ce na fili,sai wata da zata sada ka da cikin gidan inda zaikaika wajenatansa,gefe kuma wasu ɗakuna ne a jere inda bayin suka ajiye gawar saikuma suka shiga ɗaya ɗakin, sannan gefe kuma wasu shanune guda biyu a ɗaure da awaki suna cin yayi. Ba laifi gidan yayi kyau an lailaye da da’ben ƙasa,sannan jikinsa kuma anyi masa shafe na jar ƙasa.
Hanyar dazata kaishi cikin gidan yabi,nima nabishi a baya baice komai ba har muka shiga tsakar gidan. Nan kuma ɗakuna ne a jere guda huɗu,sai gefe wasu ƙanana guda biyu. Yara da bazasu wuce shekara shida ba da biyar sunata wasa. Suna kallonmi suka daina abinda suke suka nufomu da gudu. Nayi zaton wani abune ashe murnar ganinsa sukeyi. Sai yanzu na tuna ashe ya daɗe rabonsa da gida. Wata dattijuwa itama murmushi take najin daɗin ganinsa.
“Sannu da dawowa kaka!”
Ohh haba nidai nace har yanxu yana haihuwar ƙananun yara kaman haka ashe jikokinsa ne. Matar ce ta iso inda muke,haɗa ido mukayi bayan na ɗauke kaina daga kallon yaran,gabaɗaya sainaji sun birgeni,kuma sai nakejin nima ban daɗe da daina wasa irinnasu,kuma a shekaru ma ban wuce hakan sosai ba. Amma a raina nakejin nagirmi yin hakan nesa ba kusa ba,ko hakan yanada nasaba da sauyin danasamu a jikina da kuma hankalina.
Murmushin danakeyi saboda ganin yaran nayi saurin bari na tsuke fuskata ina yin bayan baba Yakub kaɗan. Saboda yanda ta tsareni da ido kaman mai hararata.
“Baban yara sannu da dawowa ya hanya ya cikin ruwa? Wannan kuma fah,ince dai ba baiwa ka sake ƙaro mana ba,baiwar ma yarinya kaman wannan”
“Baiwa ce amma ba nan zata zauna ba,In muka kwana gobe zan kaita inda zata kasance”
“Yawwa nace dai,wannan tayi aiki ko ayi raino,saita girma yaran gida su fara kaimata farmaki tana haɗasu faɗa da matansu ƴan tattu,ai nikam baza'a sake wannan karon dani ba”
Bayan tagama maganar da mijinnata juyowa tayi kaina.
“Kike wullah ido ba haka kukeyi ba, sai anci daku kun girma tashan balaga ya bullomuku ku fara yaudarar ƴaƴan gida,in ba ayi sa'a ba ku rabasu da matansu,su daina kallan kowa saiku. Sabeera ina kike zo ga baiwa kikaita ɗakinku ta zauna gobe za'a kaita inda zata yi rayuwa,sannan ki haɗa abinci Baban yara yadawo”
Wata matashiyar budurwa ce ta amsa ƙiran kana ta fito,sanye take da kayan saki ruwan ƙasa sun ɗan mutu wani wajen ma ya yage,sannan zanin guntune baikai har ƙasan gwiwarta ba. Batayimin magana ba sai kama hannu na datayi mukayi wani lungu yamma da tsakar gidan. Wasu bukkoki guda biyu a wajen kaman na baru. Ɗaya daga ciki tajani muka shiga.
Rairayin ƙasa ne a ciki amma an share tass,wani tsohon saƙi ta shimfiɗamin na zauna kafin tafita sai gata da ruwa da kuma wani akushi. Faten tsakin Masarane an zuba ganyen rama a ciki. Ruwan na fara sha kafin na karbi abincin shima na fara ci,babu ɗanɗanon komai a ciki saina tsami da kuma gishiri,yunwar danakeji ce tasakani dole naci. Sannan tabani ruwa nayi alwala nayi sallah yadda ummah ta koyamin da muna cikin jirgi. Allah yasa inada saurin fahimta babu abinda na manta na abubuwan data faɗamin. Shin zan sake ganinta ko bazan sake ganinta ba Allah ne kaɗai masani. A inda nake zaune anan na zame na kwanta domin hutasar da haƙarƙarina daga ƙalubalen dayayi katari dashi a yauɗin. A da nayi zaton Baba Yakub matsayin jika ya ɗaukeni,sai yau danayi arba da jikokinsa na zahiri yanda yake murnar ganinsu,da yanda aka hantare ni amma baiko kulaba,sannan ya rabani da uwata, yasa na sake ɗaukar karatunsa dakyau A yanzu jinake banida kowa sai ubangijina,kuma shi nake roƙo ya fidda ni tsanani a duk wajenda zan tsinci kaina a goben,Allah yasa shine mabuɗin nasara a rayuwata kaman yanda ya ambata ɗin. Da wannan tunane tunanen bacci barawo yayi nasarar rufe ƙwayar idona.
Cikin tozarta da nuna ƙasƙanci na rayuwar bawa suka sakawa Aminatou sarƙa a wuya har izuwa cikin katafariyar fadar ta sarki Sunni Abduljalal Askia Wanda yake mulkin Daular Songhay. Duk da haɗuwa iya haɗuwa da fadar tayi hakan ko kaɗan bai kama hankalin Aminatou ba wacce take cikin alhinin rayuwa da danasanin barowa garinta na Adik. Ko ba komai a can zata zauna da mijinta kuma cikin koshin lafiya,sannan koda Babu ƴar ta wataƙila zasu samu wata. Amma anan ga mijinta ya rasu ga kuma an rabata da ƴar tata itama da take murnar Allah ya sake gama fuskarsu. Sannan bautar ma itace kuma a gidan sarautar da bataso ɗin.
Wani sashe sukayi da ita wanda yakasance gini na biyu a mafi girma da kyau bayan Bangaren inda sarki Yake fadanci da kuma inda turakarsa take. Daga nan sai inda aka nufa da Aminatou wato sashen Sunkia Madina,babbar matar sarkin sai sauran matan Sunkia Maryama da kuma Sunkia Deejah.
A cikin wata rumfa suka yada burki,inda wasu bayi keta ayyukansu na yau da kullum wato hidima ga masu mulki, wasu na wanki wasu kuma suna gyara kayan ado da barguna na ɗakunan Sarakan gidan wasu na shiga na fita yamma kaɗan daga madafarsu ta girki.
Wata baiwa suka kalla wacce take tsugunne tana gyara murjani wanda akayi masa ado da zinare,cikin kulawa takeyin abun kaman idan tayi kuskure zata biya da rayuwar ta,muryar dogarin dasuka rako Aminatou ne da taji yasa ta ɗaga kanta tana kallonsa ganin Kayan aikinsa yasa ta tsaya da abinda take domin saurarensa, sannan ta tashi tsaye tana sunkuyar dakanta kaɗan
“ke yimaza ki mana iso da Jakadiyar Gamji Sunkia,kice mata saƙon data aikemu mu ɗakko yasamu isowa tazo tagani zamu koma wani bakin aiki”
“Bazan ƙi daga cika umarninka ba Shugaba dogari amma Gimbiya Azima ce tabani aikin gyaran murnajinta,sannan ta umarceni dayin sauri domin zata fita kilisa ne sanye dashi idan anjima,idan babu damuwa zanyiwa ƴar uwata habiba Magana ta ida Saƙonka Ranka ya daɗe”
“Shikenan babu matsala amma maza ki hanzarta,domin muma idan muka daɗe bamu koma ba sarkin dogarai Zai hukuntamu”
Ganin Tayi sa'a sun yarda batareda duka ba yasa taje gefe da sauri tafaɗawa Ƴar uwartata aiken itakuma tacigaba da abinda takeyi cikin sauri saboda kada ta bata lokaci.
“Zangina lafiyarka kuwa,kaine baiwa tabaka uzuri kuma ka karba batareda hayaniya ba?”
“Hmmm Gali kenan zatonka wannan Sungumeni muje din danayi mata na banxane,hhhhhhhh zan lallabo da darene na kwashi romo,dan wlh yanayin jikinnata da haskennata yayimin sosai,daga gani jikinnanta zayyi laushi,kuma kana ganinta kaga Luɗiyar budurwa wlh,zatayi romo sosai”
“kai kadaibi a hankali kasan Sunkia Madina ba kaman sauran matan sarkin bace,bataso ana taba mata dukiya sakaka dan haka kayi hankali kota saka a dandaƙeka a bainan nasi wlh,dan haka ina rabaka tammm”
Duk maganganun da dogarawan suke faɗa babu kalma ɗaya data kubce batareda da shiga kunnen Aminatou ba. Ƙirjinta ne ya buga,barka da zuwa gidan sarauta,sai yanzu ta tuno da chakwakiyar dake cikin gidan sarauta,sai wanda Allah ya tseratar ne kaɗai yake tsira. Wani sabon hawayene taji ya zubo daga idanunta,ko wanne hali Joda take ciki,kana kare naka ma a wannan ƙarnin nasu yaka ƙare ballantana baka tareda shi an rabaku.
Suna nan tsaye Jakadiya ta fito,farar matace gajeriya mai ƙiba,tasha baƙin saƙi da bakin kwalli da baƙin jan baki,ga murjani Na jan duwatsu cike tamm a wuyan ta,tana tafe tana bubbuɗawa kaman wata saniya. Tana ƙarisowa wajen suka ɗan rusuna mata alamar girmamawa,bata kula ta kansu ba tayi inda Aminatou take tsaye wuyan ta da sarƙa jikinta duk shatin bulala.
“Kan uba kai gali waye yace ku daketa,daga cewa ku taho da baiwa daga bakin kogi wajen Masinci Yakub sai kuyita dukanta a hanya,babu ruwana zaku gamu da Sunkia Madina”
Saurin tsugunnawa sukayi tareda haɗa hannaye suna roƙonta,
“Kiyi haƙuri Jakadiya wlh bamuyi niyyar dukanta ba,gardama tatsaya yimana kan bazata biyomu ba,sai tutturjewa take wai babu wanda ya isa ya rabata da ƴarta,bakiga yanda take yiwa Baba Yakub masifa ba wai yaci amanar ta daya saida ita ga gidan sarauta,ita batason bauta”……..haka sukayi ta ƙara abinda akayi da wanda ba'ayi ba.
Ko kaɗan abinda sukeyi bai damu Aminatou sosai ba,domin in wannan ne yaci ace tasaba dashi tunda a gidan sarauta ta tashi kuma tayi rayuwa.
Wani kallo da Jakadiya ta watso mata bayan sun ida zancenne yasa hantar cikinta ta kaɗa, maganganun nasu sunyi tasiri a kunnenta kenan.
Cikin takun ƙasaita ta taka gaban Aminatou,hannunta na dama ta damƙa kaman tasamu cinyar tunkiya,hatimin bautar da yake hannunta ta ƙarewa kallo,wanda ya warke yazama kaman jikinta,alamun an daɗe dayi mata tun tana shekara sha biyar.
Wani kallo ta jefa mata bayan tagama kallon hatimin.
“Nayi zaton ke sabuwar tunkiyace da har kike gardama,ashe tserarriyar tunkiyace da take tunanin inta gudu daga wajen mai ita zata samu ƴanci, hmmmm a ƙaramar ƙwaƙwalwarku kenan,kin taba ganin tunkiyar da take yawo a cikin gari babu mai itane,ai ko guduwa tayi to zata samu wani ubangidan. Sannan ƙarin bayani a yanda zaki fahimta,idan mai tunkiya zai sayarda ƴar tunkiyarsa,ita tunkiyar batada ikon gardama akan hakan. Kuna haihuwa ne don ƙarawa mai gidanku dukiya,amma badan ku rayu da ƴaƴanku yanda kukeso kamar Wanda suke da ƴanci ba. Ke tsohuwar baiwa ce daga gidan sarauta,kinsan tsari da yanda abubuwan gidan sarauta yake,dan haka bakya buƙatar ƙarin wani bayani. Kuma ina gargaɗarki da kada kiyi gardama domin inda kika fito tamkar akurkine idan aka gamashi da Garin Goa.
Ku kuma zaku iya tafiya,amma nan gaba ku kiyaye taba dabba idan an turaku ɗaukota,bakowane mai ita bane zai ƙyale idan aka taba masa lafiyarta”
Tana gaba faɗin hakan tayi gaba kanta tsaye,tareda yiwa Aminatou alama kan tabiyota a baya.
“Sunkia Madina uwargidan Askia Abduljalal itace ta siyeki,amma ba ita zakiyiwa aiki ba,batanan ta tafi wani taron manyan matan gari a waje,tabada sallahun idan kinxo a kaiki inda zakiyi aiki wato Sashen Gimbiya Asmah,matar Yerima Kabeer wanda ake ƙira da Gamji saboda shine magajin wannan masarauta. Gimbiya tanada cikin cigaban magajin wannan masarauta,dan haka tana buƙatar baiwa mai ɗan girman shekaru kuma ba tsohuwa ba amma mai hankali. Wacce takeyi mata hidima daga bangaren Sunkia Madinah an sameta da cutar ƙazuwa,tsoron kada ta shafa mata yasa aka fita da ita daga masarauta. Baba Yakub yagama tantanceki sannan yabada haƙƙun akan zaki iya shiyasa kai tsaye aka kawoki inda zakiyi aiki batareda gwaji,dan haka munaso ki nuna mana iyawar dayace kinada ita,idan kikayi hakan za'a baki ci mai kyau sha mai kyau,kaya masu tsafta hadda sabulun wanka,domin dolene kiyi tsafta saboda karki yaɗa wata cuta da zata zamo barazana gareta da kuma abin cikinta. Tanada bayi guda uku da tazo dasu daga garinsu,sannan kema bake ɗaya bace akwai Lubna,itama babbace. Sannan ku kiyayi kwalliya dayin duk wani abu dazaija hankalin namiji yin hakan zai jamuku matsala,domin batason wani abu yaja hankalin mijinta bayan ita. Mun iso sashenta wani abun duk zaki gane dakanki idan kikayi kuskuren sa kokuma kikaga wani yayi yaƙarbi hukunci akansa. Domin cikin yasaka mata saurin zuciya da bacin rai”
Itadai Aminatou jinta kawai take har suka ido baƙin ƙofar turakar tata,idan da ranka ai zaka sha kallo.
Wata baiwa ce baƙa gajeriya ta buɗe ƙofar,yanayin adon kayanta dabanne da na matan dasuke yawo a ciki da wajen garin Goa,hakanne ya bawa Aminatou tabbacin wataƙila tana daga cikin bayin da Gimbiya Asmah tazo dasu daga daular Tasu ta Ghana Tana ganin masu buga ƙofar harda Jakadiya yasa ta rusuna mata kafin takoma da sauri tayi musu iso.
Bata jimaba sai gata tadawo kana tasake ɗaga musu asabarin bakin ƙofar suka shigo,wanda yasha ado sai walwali yakeyi.
Babban ɗakine daya cika da kayan alatu na zinare da kuma sauran kayan ƙyaleƙyale,ga tuntuna manya manya na zama an bazasu akan shimfiɗin dayake tsakiyar ɗakin mai laushi kaman bayan kuliya.
A gefe kuma wani shimfidin gadone mai tudun gaske tana kwance a ciki saida ta lotsa. Tashi tayi zaune sai shagwabe fuska take tana wani narkewa. Bayi guda biyu gefe da gefe suna tarota tareda jera sannu sunfi cikin carbi.
Saƙƙowa tayi bayan wani lokaci data ɗauka kaman bazata sauƙo ɗin ba,akan ɗaya daga cikin tuntunan ta zauna tareda miƙe ƙafa,kaman jira suke suka hau matsa mata su cikin kulawa sannu a hankali dakuma ƙwarewa.
Ɗaga kai tayi ta kalli Jakadiya kafin tayi magana,Aminatou dake ta aikin gaisheda ita ko kallonta batayi ba ballantana ta amsa mata.
“Shin zan iya sanin mai yakawo Jakadiyar gamjiyar Askia wajena da har ta tasheni ina tsaka da hutawa?”
Jin furucin da gimbiya Asmah tayi yasaka Jakadiya saurin ɗan durƙusawa tana neman tuba,domin daga jin maganar tata tasan sotake tayi mata ɗaurin huhun goro da harshennata.
“Tuba nake Gamjiyar gobe,tuba nake uwar magajin Daular Songhay tuba nake wacce ta gaji mulki kuma take gadar dashi,tuba nake Hasken Ghana sannan ginshiƙin Songhay tuba nake a huce huce ranki ya daɗe.
Sake baki Aminatou tayi tana ƙallon Jakadiya wacce tagama ƙasaita a waje yanzu ta zube warwass a gaban yarinya jikinta har rawa yake domin taga ta warware ƙullin da tayi mata da kalamanta.
Wani murmushin ƙasaita Gimbiya Asmah tayi bayan ta ɗauki inibi guda ɗaya ta tauna kana ta haɗiye ruwan.
“ Jakadiya kenan,wannan halayyar taki tana burgeni,kina iya ƙoƙarinki wajen yin amfani da bakinki ki ƙwaci kanki. Uhmmm a dabbobi da wanne zan misaltaki…….yawwa Aku!” ko ba shine ba, Baiwata faɗamin”
“Tabbas shine ranki ya daɗe,ai kinada basira sosai”
“To duk ba wannan ba naga kin shigomin da wani abu cikin turaka ta,bayan wanda kuka kawo yakusa sakamin jinya har ila yau wata cutar kuka sake kawomin. Ni ki faɗamin Jakadiya anya kuna babban shiri da tarbar wannan magajin kuwa,bazan yi wani tunanin daban ba?”
“karki yi wani tunani bayan mai kyau shugabata,kaff ɗauka cin Songhay babu wani da baya murnar fitowar ɗan yeriman farko kuma jika na farko a ƙarnin sa ba. Wannan murna da kulawa ce tasa sunkia Madina ɗaukar matakin gaggawa wajen kawar da waccar baiwa kuma babu bata lokaci takawo miki sabuwa wacce aka yarda da iya aikinta,zata maye miki wancan gurbataccen gurbi da mai kyau ya shugabata…….”
Haka ta cigaba da shiga tana fita wajen amfani da baiwar da Allah yayi mata na surutu harta samu damar ɗaure Gimbiya Asmah tamau da nata ɗaurin magansr itama,sannan saida ta tabbatar yayi tasiri yanda ya dace kafin suka fito daga sashen itada Aminatou. Itadai Aminatou tayi shuru tana tuna ikon Allah da tagani,wani abin gaba da gaban ta ne wai aljani ya taka wuta.
Bayan sun fito ko kallon arziƙi Jakadiya batayi mata,sai nuna mata wani waje da tayi da hannunta tace.
“kibi waccar hanyar zakiga bayi mata suna tafiya wajen,kibisu zaikaiki sansanin bayi inkinje kice ina uwar bayi,idan kinganta kice kece mai gurbin Hansai,idan kika faɗin haka zata gane,daga nan idan kowa yataho aiki saiki taho nan,kaman yanda na faɗa bakya buƙatar wasu ƙarin bayani,kiyi amfani da ƙwaƙwalwarki har ki tsira kikai baɗi. Ni na gama nawa aikin da Uwar ɗakina tasakani sauran naki aikin zai fara gobe.”
Tana gama faɗin hakan takama hanta ɗungul ɗungul ita adole ga Jakadiya ƙasaita takeyi harta bar wajen.
.