Chapter 1
by @barista
*BIYU A ƊAYA*
A 2026 Nobel
By SAYYADA barrister Amanar Nimcy SARAUTA 👸🏻
***
The writer of
Wa ya fi so na? 1&2 500
Ƴar gwoggo1&2 1k
Jawaheerah free
Ruɗin zuciya free
MUJARRABI 1&2 1k
AMINAN JUNA 1,2 and 3 1500 and now
BIYU A ƊAYA free book (Don't judge a book by its cover)
Dedicated to the respective leader Na'ima Suleiman Nimcyluv SARAUTA 👸🏻
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION*
YOTA 13
*TEAM OF FIVE INK LEGENDS*
_Bilkisu S Fari ina yi miki addu'ar fatan alkhairi da nasara a rayuwarki, ki ci gaba da halinki na Dattako_
*Godiya ga ahalina na Yota ba ki ɗaya, na ƙara min ƙwarin gwiwar wajen ci gaba da rubutu, da shawarwari. Much love you❤️*
_Wannan labarin ƙirƙirare ne duk wanda ya yi daidai da labarin rayuwarsa arashi ne._
Bismillahir Rahmanir Raheem
Chapter 1
BORNO STATE
Maiduguri Milloniars Quarters 8:00pm
Chaɓal³ shine ƙarar ruwan dake cikin ƙayataccen Baho me ɗauke da ruwan shuɗi, ƙirar zamani wanda ake yiwa yara wanka wannan ƙarar ruwan yake tashi, ruwan dake ƙaran yana zubowa ne har ƙasan ƙayataccen ties fari kal dashi wanda babu ko alamun ɗigon dotti a kansa. Yarinya ce wacce ba zata wuce shekaru biyu ba ko watanni ashirin da ɗaya ba ke zaune cikin wannan Baho me cike da ruwa, ruwan ya kai wa har saman ƙirjinta, sai wasa take yi da ruwan yana wantsulowa ƙasa kuma tana jin daɗin hakan tana ta sakin dariya.
Turo ƙofar toilet ɗin da aka yi ne yasa ta kalli bakin ƙofar, nan da nan ta sake wangale baki tana dariya saboda ganin wacce ta shigo. Ƙarasowa tayi ta tsugunna tana sake karewa yarinyar kallo, ganin yadda yarinyar ke murnar ganin ta yasa ta saki murmushin da ita kaɗai ta san ma'anar sa, hannu ta sanya tana ɗeban ruwa tana zubawa yarinyar a saman gashin kanta, a hankali take yi ita kuma yarinyar gani take wasa take mata tana ta shushure ƙafafunta tana ci gaba da dariya. Shafa jiƙakkun gashin kan yarinyar tayi wanda gashin ya sauƙo har saman gadon bayanta duk da ƙanƙantar shekarunta, amma yawan gashi gareta, baƙi dashi sannan ga laushi, tana jin yarinyar na sake shiga cikin ranta, sosai take jin kaunar ta.
A hankali ta goga Sabulu a hannunta sannan ta soma goga mata a farar fatar ta tana yi mata wanka, sai da ta wanke ta fes sannan ta lulluɓe ta da pink towel ta fito da ita. Akan bed ta kwantar da ita ta soma shafa mata baby lotion ita ko me za ta yi banda dariya gani take kamar chakularta take yi. Murmushi tayi ta ci gaba da shiryata, ta sanya mata pampers sannan ta ɗauko riga mara nawi fari ƙal me hannun vest ta sanya mata, sai ta yi mata kyau akan farar fatarta.
Ta feshe ta da turaren yara me sanyin ƙamshi, ta kura mata idanu tana kallon yadda take dariya, turo ƙofar da aka yi ne yasa ta dakatar da shiryata da take yi, ta kalli ƙofar shigowa, ganin wacce ta shigo ne yasa tayi saurin rutsinawa ƙasa tare da yin magana cikin ƙasa da murya irin ta girmamawa ta ce
"Barka da warhaka Hajjiya"
Wacce ta kira da Hajjiyar ce ta ƙaraso ta zauna a bakin gado tare da sanya hannu ta ɗauki yarinyar dake ta dariya, ta yi magana cikin muryarta mai nuna alamun tana cikin yanayi na jin jikinta babu daɗi, saboda zazzaɓi da take yi
"Shafa'atu yau ko kai min shalele ba kiyi ba, me yasa?"
Shafa'atu dake tsugunne har wannan lokacin kuma kanta na ƙasa cikin rawar murya ta ce
"Wai daman kada ta ganki ne ta ce za tasha nono"
"Uhm ai naga ƙoƙarin shalele ma, ni kam ya jiya ki kayi ne da rigama?"
"Ai da ikon Allah Hajjiya shalele bata yi wata rigima ba, da ta tashi bacci ne ma za tayi rigima na bata ruwa tana sha ta koma bacci"
"Uhm ai duk haihuwar da nayi ban yi mai sauƙi ba irin na Shalele, bata da rigima ko kaɗan"
"Gaskiya ne kam yara da dama da an yi musu yaye suke kwana suna kuka amma banda Shalele. Jiya bacci mu kayi abin mu"
"Yauwa Shafa, Shalele zata zauna a wajen ki har zuwa lokacin da zata manta da batun shan nono, don haka mu je ki ɗauko wasu kayayyakinta da duk wani abin da za ku buƙata ki dawo dasu nan ɗakinki"
Murmushi Shafa'atu tayi wanda yasa Hajjiya sake kallonta na wani lokaci, sannan ta maida kallon ta zuwa ga Shalele da ta soma kukan rigima tana neman a bata nono, ta sauke numfashi ta baiwa Shafa'atu ita sannan ta mik'e tare da ajiye mata kuɗi dake cikin envelope ta ce
"Wannan kuɗin aikin ki ne na wannan watan, Yallaɓai ya ce a ba ki sai kuma na ihsani da ni nayi miki saboda ayyukan da ki ke min yanzu suna yi miki yawa"
Shafa'atu dake tsugunne kan gwaiwowinta har wannan lokacin tana rarrashin shalele dake kuka ta ce
"Na gode Hajjiya, Allah ya biya miki buƙatunki na alkhairi, bani da bakin yi miki godiya Hajjiya sai dai na tayaki da du'a'i"
Hajjiya ta sauke numfashi tare da cewa
"Amin, da tayi shiru sai kije ki haɗo kayan nata"
"To Hajjiya"
Hajjiya ta fice, Shafa'atu ta mik'e da Shalele a hannu tana aikin rarrashi, tayi shiru nan da nan ta soma mata dariya, murmushi Shafa'atu tayi tana jin zuciyarta na raya mata wasu abubuwan, ta kwantar da Shalele sannan ta ɗauki kuɗaɗen tana duban su, shiru tayi tana tunani, daga bisani ta sauke numfashi ta soma kirga kuɗaɗen, ta haɗa lissafin su da waɗan da suke wajenta, waɗan da ta jima take adana su saboda samun dama irin na wannan ranar, a hankali ta juyo ta kalli Shalele dake ta sheƙa bacci. Ta yi murmushi ta gyara mata kwanciyar ta sannan ta ajiye kuɗaɗen ta mik'e, ta fito ta wuce side na Hajjiya.
****
A hankali take kusa kai ciki tana rarraba idanuwanta, jin tsit babu motsin kowa yasa ta nufi ƙofar ɗakin Hajjiya, sai kuma taji muryar Hajjiya a ɗakin Yallaɓai, a hankali ta iso ta tsaya a bakin ƙofar tana sauraron abin da suke tattaunawa, muryar Yallaɓai taji yana cewa
"Ai da ba don na matsa miki ba, in dai a ra'ayin ki ne da har yanzu baki yaye Shalele ba, yarinya tayi shekaru biyu ace ba za a yayeta ba"
"A'a Abban Shalele watanni ashirin da ɗaya ne fa bata cika shekaru biyun ba"
"To me marabar dambe da faɗa? Ina wata ɗaya ne babu a shekarunta ta cika biyun, yarinya da ƙafafunta tana yawo ko ina ace ba za a mata yaye ba"
"To Yallaɓai ai aikin gama ya gama, tankurunkus in ji masu bada labarin tatsuniya, yanzu dai an yi yaye"
"To saura a sama mata ƙani"
"A'a ita ce dai ƴar Auta ta"
"To ikon Allah, Hajjiya yara uku sun ishe ki"
"Sun isa Allah yayi musu albarka"
"Amin, ina Shalelen?"
"Bai jima ba na duba ta tana wajen Shafa'atu"
"Ina mamakin shaƙuwar da take sakanin Shalele da ƴar aikin nan"
"Ai Shafa'atu akwai ƙoƙari da juriya, bata da ƙiwa ko kaɗan....
A hankali Shafa'atu ta soma dawowa da baya² ta tsaya a sakiyar palour jikinta yayi sanyi sosai, ji taji zuciyarta ta soma karaya, ta juya da sauri zata fice taji muryar Hajjiya ta kira sunanta
"Shafa'atu"
Ta juyo jikinta har wani rawa yake yi ji tayi kamar Hajjiya ta gano shirinta, ta iso ta duka ta ce
"Na'am Hajjiya"
"Tashi tsaye"
Ta tashi duk ta haɗa gumi ta rikice"
"Ba dai komawa za ki yi ba saboda bana cikin ɗakin?"
"Eh Hajjiya daman wai sai na bari da safe nazo na kwashe kayantan"
"Oh! ba komai ai, ki shiga cikin ɗakina ki ɗauki duk abin da zaku buƙata, ni zan wuce kitchen na haɗawa Abban Shalele tea"
"To Hajjiya"
Hajjiya ta wuce kitchen, Shafa'atu ta shigo ɗaki, kai tsaye wardrobe da yake ƙunshe da kayan Shalele ta buɗe nan ta ɗebo kaya lodi guda, sannan ta sanya su cikin wani madaidaicin jaka, tana ƙoƙarin fitowa ta hango photan Shalele akan wani ɗan ƙaramin table ta ɗauka ta sanya shi cikin jakarta sannan ta fito, ta wuce ɗakinta.
Kai wa da komowa take yi a ɗakinta, ta ɗan jima a haka sannan ta iso bakin gado inda Shalele ke bacci ta duka tana kallonta na wani lokaci a hankali kuma ta furta
"Dole ce tasa zan yi haka, kiyi hakuri"
Tana gama faɗin hakan ta mik'e ta haɗo kayanta ta ɗauko kuɗaɗen ta sanya su cikin jakar kayan Shalele sannan ta goya Shalele a bayanta, ta leƙo ta taga taga babu kowa a farfajiyar gidan, ƙafa ya yanke, ta kalli samaniya taga tayi duhu sosai babu ko hasken wata sai na tausari da suka haske sama, ta sauke ajiyar zuciya, ta kinkimo kayayyakin ta fito dasu ta biyo ta ƙofar baya, sai kuma tayi trus ta tsaya saboda ganin gate man dake zaune a main gate suna hira da wasu mutane.
A hankali take sake ƙarewa gidan kallo, tana jinjina kai tana sake mamakin girman da gidan yake dashi, side sun fi 30 a cikin gidan, kuma duk ahali ɗaya ne, abin mamaki yake bata a kullum.
Jarumta tayi ta iso bakin gate babu tsoro ko fargaban komai, kai tsaye ta tunkari ƙofar fita tana yunkurin fita taji gate man ya ce
"Shafa ina zuwa da wannan lokacin?"
Ta dake tare da juyowa ta kalli gate man da ake kira Baba Musa ta ba shi amsa a takaice
"Saƙo Hajjiya ta bani na kai yanzu zan dawo"
"Ah to adawo lafiya, amma da goyo ga kuma kaya, ai abin yayi miki yawa"
Bata bi ta kan sa ba, ta kinkimo kayayyakin ta yi ficewarta, sauri take yi bata ganin gabanta har sai da tayi nesa da unguwar sannan ta tsaya ta tsaida ɗan sahu, ta sanya kayan su a ciki sannan ta shiga yaja suka bar layin unguwar.
********************************
_BAYAN SHEKARU ASHIRIN_
Samari ne kuma matasa ke wasan ƙallon ƙafa cikin madaidaicin wajen wasan buga ƙwallon ƙafa filler, wanda aka keɓance sa daga gefe na wani ɓangare dake cikin gidan. KIRAWA'S FAMILY babban family ne wanda yake ɗauke da ahali ɗaya kuma suna da yawa, maza da mata har da jikokai, kasancewar duk wanda yayi aure a cikin family anan yake zama. Ko da a waje ya auro ko kuma ƴar ahalin ya auro. Shahararren family a garin Maiduguri saboda duk wani ma'aikata akwai KIRAWA'S FAMILY shi yasa ya zama sananne. Duk ƴan gidan suna amfani da KIRAWA a ƙarshen sunansu.
Samarin Sun kai su 10 a cikin wannan wajen wasan, amma 8 ne ke wasan ƙallon ƙafa football kenan, mutum biyu kuma suna buga wasan ƙwallon hannu, hand ball daga gefe.
A nutse yake buga wasan ƙwallon hannu yana yi yana bouncing da ball ɗin, morah nasa yana tashi damtsin hannunsa ya cicciko yayi tudu da shape, kamar zai fashe don cikowa, sakamakon rigar da ya saka mai gajeriyar hannu ce fara tas da dogon wondo maroon color, gume yake zubarwa shar³ har ya iso daidai inda zai jefa ƙallon yana zuwa yayi tsalle ɗaya nan take ya jefa ƙallon ya faɗa cikin kwadon, saboda tsawon da yake dashi bai sha wata wahalar jefawa ba, ya juyo ya kalli ɗan'uwansa wanda tun da ya kwace ball ɗin a hannunsa ya tsare, ya iso wajen sa yayi masa murmushi, yana zuwa ya miƙa masa hannu su kayi shaking hands ya ce
"Dr Waahab Waseem KIRAWA na san tun farko zaka ƙwamushe wasan, ni tayaka wasa ma kawai nayi"
Wanda aka kira da Dr Waahab Waseem KIRAWA ya ɗauki goran ruwa ya kafa a baki yana sha sai da ya kwankwaɗesa tas sannan ya ajiye goran ya ɗauko white hanky ya goge gumin da yake fuskarsa ya zauna kan ɗaya daga cikin kujerun dake wajen ya ce
"Sa'eed Muhammad KIRAWA ka ce dai ka tsorata ka ja da baya"
"A'a bros ai ba a ja dakai a garaje"
Ya ɗan bugi kafaɗar Sa'eed ya ce
"Kada ka damu gobe kai ne da nasara"
Sa'eed ya zauna shima kan kujera tare da tambayar yayansa cike da mamaki
"Ba dai ka ɗaga tafiyar da za kayi ba? Ka ce gobe ma kana nan?"
Ajiye hanky Dr Waahab Waseem KIRAWA yayi ya ce
"A'a ba daga ni bane daga ƙungiyar da ta ɗauki nawin tafiyar mu ne, an mai da tafiyar sai next week"
"Ok Dr Allah ya kai mu kamar yau ne ai"
"Amin"
"Good morning likita"
Ya ɗago ya kallesu, ƙannensa ne da suke wasan ƙwallon ƙafa suka iso dukkanin su suna ta sauke numfashi tare da share gumi suna gaida shi ya amsa,
"Morning guys har kun tashi a wasa Sageer Mustapha KIRAWA?"
"Yap bros za mu koma ciki mu huta ne, wasa bayyi daɗi ba"
"To yau kuma ba dai an kada team naka ba?"
"Kunnen doki muka zo shine muka tarwatsa wasan"
Murmushi yayi ya kalli Abdullahi Umar KIRAWA wanda yake jagorantar ɗayan team ɗin ya ce
"Little bro kana jin Sageer ko?"
"Ina jin sa ai ba a gama ba akwai gobe sai ya kwashe takalmi a hannu"
Suka yi dariya suna tafa wa, haka sometimes suke kiran junansu da full name nasu, musamman waɗan da suke age mate Doctor ya ce
"Sageer ka je ka kira min ƴan matan nan ka ce ina neman su yanzu su zo dukkanin su"
Sageer ya fahimci me yayan nasu yake nufi ya riƙe hannun ɗayan mate nasa Sani Waseem KIRAWA suka wuce ɗayan bangaren, a palour su kayi sallama aka amsa ita kaɗai ke kwance kan 2 seater tana chatting tana ganin shigowar su ta tashi ta zauna tare da gyara mayafinta ta ce
"Ya Sageer ina kwana"
"Lafiya Teemah, ina su Ashfat"
"Suna cikin ɗaki"
"Doctor yana nemanku"
Ƙirjinta ya bada ras, ta ce
"To bari na faɗa musu"
"Ok ku same sa a side"
Cewar Ya Sageer suka fice ta mik'e cikin sauri ta shigo cikin ɗakin ta tadda kowacce na chatting babu me magana a cikin su, suna kwance babu mai niyyar tashi ta ce
"To ladies akwai Assembly yanzun nan"
Kamar haɗin baki suka dakatar da yin chat ɗin lokaci guda suka zuba mata ido ba tare da kowacce tayi magana ba, ganin haka yasa Teemah sake cewa
"Da gaske yanzu Ya Sageer ya shigo ya ce Doctor yana neman mu yana side"
"Oh my God, wacce tasan tayi laifi jiya, don Allah ta faɗi don ni nasan through out jiya ban fita ba"
"To ke Suhaima ce miki aka yi laifi mu kayi tun da ya ce mu je yana neman mu, mu je mana"
Cewar Hauwa, tana kallon Suhaima wacce ta tsure tsoro ya kamata, Ashfat ta ce
"Ku tashi muje nasan dai ba zai wuce ni ɗin nan bace"
"Ah to Ya Ashfat tun da kin san ke ce da laifi sai ki yi masa magana don kada ya haɗa damu"
"Hauwa ni sa'ar ki ce, da kike faɗa min haka? To ki sani babba nake a gare ki, mind your tongue"
"To Ya Ashfat ba batun girma bane wannan, gani nayi ban aikata laifi ba banga dalilin da zai sa na amsa laifin da ba nawa ba"
Cewar Hauwa tana ciccin magani, rai a ɓace ta ajiye wayar hannunta
"Come on ladies duk wannan bai taso ba, big bros yayi kira kuma dole mu amsa ko jiki yayi tsami"
Cewar Teemah tana ƙoƙarin kashe rigima don tasan muddin Ashfat ta hassala to za ayi ba daɗi don haka da ƙyar ta samu ta shawo kan su ko wacce ta naɗe duvet nata ta tashi ta sanya hijabinta suka fito, kai tsaye suka nufi inda yake.
**************************************
GHANA
_Alaja's special restaurant_
Shine a rubuce a sign board dake bakin gate na wajen, katafaren wajen cin abinci ne wanda yaji tsari da ƙayatuwa, yadda mutane ke shiga suna fita kawai zai tabbatar da cewa restaurant ne na musamman, wanɗan da suka ƙware wajen tarɓan baki da daɗaɗan girke_girkensu, tsabar ƙwarewar su ma har sun haɗa collaboration da wasu hotels da suke kusa dasu. A sakiyar gari restaurant ɗin yake manya manyan hotels sun kai uku kewaye dashi, kasancewar a wealthy area ne ba dare ba rana cike yake da jama'a, ga kuma hotels da suke aikowa ana ɗaukar musu abinci kala daban daban daga Alaja restaurant musamman ma abincin gargajiya na Nigeria saboda yawancin manyan mutane dake sauƙa a hotels ɗin ƴan Nigeria ne, sun fi buƙatar ire-iren abincin da Alaja's restaurant ke dafawa, yawancin waɗan da ke sauƙa a hotels ɗin da zaran sun sauƙa fitowa suke yi su ci abinci a restaurant ɗin hakan kuma ba ya yiwa Managers na hotels ɗin daɗi har suka nema da Alaja ta basu wasu daga cikin ma'aikatanta su dinga girka musu acen amma taƙi har suka ce za su bata makuɗan kuɗaɗe kuma a kowanne ƙarshen wata da nata kason amma taƙi, shine suka haɗa kai da ita suke sara a wajenta.
8:30 am siririn hand watch dake ɗaure a hannunta ya nuna mata, hankalin ta ya matukar tashi ta san yau ta matukar makara sai ta sha faɗa a wajen Alaja.
Sauri take yi sosai har tana haɗawa da ɗan gudu ta shigo cikin restaurant ɗin, ganin kowa na harkar sa yasa kai tsaye ta wuce ciki, tana rarraba idanu saboda gujewa Alaja kada ta ganta, amma ina babu ta ganta kan ta ankare ta iso inda take tare da daka mata tsawa tana tambayar ta wannan shene lokacin da ya dace tazo aiki? amma tayi zuruzuru da idanu tana kallonta ta kasa amsa mata, nan Alaja ta sake tambayar ta cikin ɗaga murya cikin yaren French
"D'ou' viens_tu?
Alaja ke tambayar ta where are you from? Daga ina take? Jikinta ya soma rawa ba abin da ta ƙi a rayuwarta irin tsawa yana rikitata, a hankali tayi magana kamar za tayi kuka
Bonjour Maa.
Good morning ta faɗa, barka da safiya kenan. Maimakon ta amsawa Alaja ta faɗa mata daga inda take amma kawai ta gaisheta saboda Alaja tafi kowa sanin daga inda take, Alaja ta tsaya tana kare mata kallo, sanye take da uniform na aiki red skirt and black polo sai kuma face cap da ta ɗaura akan hular dake maƙale a kanta don rufe gashin kanta, kallon ta take har zuwa ƙasanta ganin skirt nata tayi har ƙasa ta ɗinka maimakon ta saka half skirt, alternatively mini skirt amma ta sanya dogo har ƙasa, sanye take da takalmi baƙi sneakers sai kuma farin safa, sabar takaici ma Alaja ta ja guntun tsaki ta ce
"Viens avec moi"
Tana zare mata manyan idanunta tana ce mata come with me, ta biyota zuwa ciki, tsoro ya kamata cikin rawar murya ta ce
Je suis de'sole'.
Tana cewa I'm sorry tana baiwa Alaja hakuri don kada ta hukunta ta, Alaja ta dakata daga tafiyar da take yi tare da juyowa cikin ɓacin rai da takaici ta ce
"Ferme ta bouche with your crocodile tears"
Ta faɗa cikin ɗaga murya shut you mouth, ta rufe mata baki da wannan shegen hawayen ƙaryan da take yi.
________________________
Kamar yadda na fara lafiya Allah ya bani ikon ƙarashe sa lafiya, to fah ga wata tafiyar kuma ya kuke ganin abin zai kasance? Da fatan za a ƙarfafa min gwiwa wajen yin comments
Comments and share fisabilillah