FreeArewaPen original
BIYU A ƊAYA
- 1views
- 31chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · Chapter 1
*BIYU A ƊAYA* A 2026 Nobel By SAYYADA barrister Amanar Nimcy SARAUTA 👸🏻***The writer ofWa ya fi so na? 1&2 500Ƴar gwoggo1&2 1kJawaheerah free Ruɗin zuciya freeMUJARRABI 1&2 1k AMINAN JUNA 1,2 and 3 1500 and now BIYU A ƊAYA free book (Don't judge a book by its cover)Dedicated to the respective leader Na'ima Suleiman Nimcyluv SARAUTA 👸🏻 *YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION* YOTA 13 *TEAM OF FIVE INK LEGENDS* _Bilkisu S Fari ina yi miki addu'ar fatan alkhairi da nasara a rayuwarki, ki ci gaba da halinki na Dattako_ *Godiya ga ahalina na Yota ba ki ɗaya, na ƙara min ƙwarin gwiwar wajen ci gaba da rubutu, da shawarwari. Much love you❤️* _Wannan labarin ƙirƙirare ne duk wanda ya yi daidai da labarin rayuwarsa arashi ne._ Bismillahir Rahmanir RaheemChapter 1BORNO STATE Maiduguri Milloniars Quarters 8:00pm Chaɓal³ shine ƙarar ruwan dake cikin ƙayataccen Baho me ɗauke da ruwan shuɗi, ƙirar zamani wanda ake yiwa yara wanka wannan ƙarar ruwan yake tashi, ruwan dake ƙaran yana zubowa ne har ƙasan ƙayataccen ties fari kal dashi wanda babu ko alamun ɗigon dotti a kansa. Yarinya ce wacce ba zata wuce shekaru biyu ba ko watanni ashirin da ɗaya ba ke zaune cikin wannan Baho me cike da ruwa, ruwan ya kai wa har saman ƙirjinta, sai wasa take yi da ruwan yana wantsulowa ƙasa kuma tana jin daɗin hakan tana ta sakin dariya.Turo ƙofar toilet ɗin da aka yi ne yasa ta kalli bakin ƙofar, nan da nan ta sake wangale baki tana dariya saboda ganin wacce ta shigo. Ƙarasowa tayi ta tsugunna tana sake karewa yarinyar kallo, ganin yadda yarinyar ke murnar ganin ta yasa ta saki murmushin da ita kaɗai ta san ma'anar sa, hannu ta sanya tana ɗeban ruwa tana zubawa yarinyar a saman gashin kanta, a hankali take yi ita kuma yarinyar gani take wasa take mata tana ta shushure ƙafafunta tana ci gaba da dariya. Shafa jiƙakkun gashin kan yarinyar tayi wanda gashin ya sauƙo har saman gadon bayanta duk da ƙanƙantar shekarunta, amma yawan gashi gareta, baƙi dashi sannan ga laushi, tana jin yarinyar na sake shiga cikin ranta, sosai take jin kaunar ta.A hankali ta goga Sabulu a hannunta sannan ta soma goga mata a farar fatar ta tana yi mata wanka, sai da ta wanke ta fes sannan ta lulluɓe ta da pink towel ta fito da ita. Akan bed ta kwantar da ita ta soma shafa mata baby lotion ita ko me za ta yi banda dariya gani take kamar chakularta take yi. Murmushi tayi ta ci gaba da shiryata, ta sanya mata pampers sannan ta ɗauko riga mara nawi fari ƙal me hannun vest ta sanya mata, sai ta yi mata kyau akan farar fatarta.Ta feshe ta da turaren yara me sanyin ƙamshi, ta kura mata idanu tana kallon yadda take dariya, turo ƙofar da aka yi ne yasa ta dak...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.