KARFE DÜKKA KARFE NE

BABI NA UKU

by @maidambu41


KARFE DUKKA ƘARFE NE...!!!

{Zanen ƙaddarar Falilah}


Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai...

    #FREE BOOK

BABI NA UKU.


       _Ban sani ba, ko akwai wani hujja ko dalilin da zai saka dangin miji da iyayen miji tsanar Surukar su. Kai ban tab'a ji ko ganin gidan Iyayen mace sun tsani namiji ba da har zasu saka mace kaso aurenta ba domin namiji yana gana mata azaba ba. Asalima hakuri shi ne kalmar sirrin da ta sani_

Ubaidah ta cutar da ni, matukar cutarwa Ubaidah har kwanan gobe idan muka hadu kallon juna muke kamar wuta da auduga ba dan kome ba, sai yadda tayi ta zaluntana. "Aunty Lilly ya isa" Hanny ta fada tana kallona. "Duk da bana son tambayar ki, amma don Allah kiyi hakuri kin ji Ubaidah ta cancanci rashin mutunci. Lilly tare muka tashi amma wallahi ban tab'a miki kazamin shaida ba, amma Wancar jakar" saka hannuna nayi a bakinta. 

"Hakan ba laifi  ba ne, amma ki sani Ya Bana kuke son ya rabu da matar shi, kuna dasa mishi kiyayyar ta ne, bayan kun san yadda yake kaunar matar shi. In fact Bana ba zai iya rabuwa da ita ba. Domin ya mata alkawarin zama da ita, idan har kuna sona kuna son Bana dole ku hakura da cutar da matar shi,.haka kawai ne zai rage matsalar da ake fama da shi" shiru tayi tana kallona kafin ta ce min."Aunty Lilly" a hankali na zuba mata idanu domin maganar ce ta fara isata. "Ok ci abincin ko kawai" a hankali na cigaba da shan kunun idan da dangin maza da iyayen maza sun san yadda suke kashe aurarrakin Yaran wasu tabbas da kowa an daina muguwar zalincin nan,  domin wallahi jikina ya bani Mahaifiyar Ahmad raba mu zata yi tunda dama can ba sona take ba, kuma ta gaya min kiri-kiri bata kaunata, kuma ta tabbatar min ba zata tab'a kaunata ba. Domin haka nayi imani da Allah tafiyar Mariyah shi ne sanadin aurena. Kar'ar shigowar sako ne ya katse min tunanina, dubawa nayi ina tare da mamaki.

   *In sha Allah, tunda kika shiga tsakanina da Uban Yarana na rantse da Allah sai dai a rasa kowa ya tashi a tutan babu, naso da ya kwaso ki tsinanniya karuwa me bin maza da auren ta* 

      Murmushi nayi  sannan na tura mata da cewa.

_Maman Basmah har yau ba zaki gane banbancin matar so da cushe a fili yake domin haka zan iya kiranki da matar ƙaddara ko wuka aka sakawa Ahmad Falilah Mustapha Liman itace zab'in shi_ na kashe wayar ma baki daya domin idan ka cika biyewa mutane bakin ciki ya ishe ka duniya da lahira.


AHMAD LAMIDO.


  Gudu yake kamar zai tashi a sama, domin yadda Hajiyar shi take kiran shi, kamar bata san nisan Abuja zuwa Yola ba, amma take mishi barazanar tsine mishi idan bai kwana a Yola ba. Tun daga ranar da ya auri Falilah baki daya ya rasa kan Hajiyar shi, hala so take ya mutu nan ne zata shiga hankalinta. Yana son kiran Falilah amma baki daya tsoron kunna wayar shi yaƙe. Dole yayi kundubalan kunawa. Ai kuwa sai ga sakon Fadime kanwar shi da take bin shi. Haka ya cigaba da tuki yana ganin shigowar sakwannni, har ya shiga garin Jos. Tsayawa yayi a wani babban tashar manyan motocin da suke tafiya garuruwa. Ya fara bude sakon Fadime.

   *Duk inda kake don Allah ka tawo, Hajiyar mu tana cikin damuwa kuma taki kwantar da hankalin ta, domin Mariyah ta gama zugata* kifa kan shi yayi a kan motar shi, kafin yaga sako na gaba.

     *Wallahi tallahi matukar baka sake ƙaruwar nan ba, Allah sai dai mu rasa ka kowa ya huta azzalumi macuci fasiki wanda ya gama yawon bin karuwa* wani irin iska yaja sannan ya fesar. Kiran Jamal ya shigo wayar shi.

"Hamma Jamal ya kake?"

"Da fatan baka dauko yar mutane ba?" Ya tambaye shi. Murmushi yayi sannan ya ce mishi. "A cikin wannan crisis din da nake da yakinin rayuwata  Hajiya take farauta ne zan dauko Lilly? Idan na zo dai sa kirata ta ga gawata amma ba zan barta ta ga mutuwata ba. In sha Allah na shigo Jos zuwa karfe goma na safe zan shigo Yola" ya fada a nutse sannan ya kashe wayar, yana dialing number Falilah. Wanda ya mata lakwabi da Swampy.

     Wato fadama, ji yayi wayar a kashe, ya kuma dialing din number a kashe. Haka ya tashi motar rabon shi da abinci tun na karyawan safe kafin ya tafi aiki, koda ya dawo hada kayan shi yana ganin Falilah ya manta da wata shegiya wai yunwar cikin shi. Haka ya cigaba da tsalla gudu, awa daya ya shigar da shi Bauchi, lokacin garin dare yayi sosai, Bauchi club ya nufa. Anan ya sayi tukunyar kaza da drinks ya sake shiga cikin garin Bauchi inda ya fito kofar winti sannan ya mike hanyar Gombe road, har zuwa lokacin kiran Falilah yake domin karfe biyu na dare ne, bata dauka ba. Haka ya ajiye wayar,  har ya bar Bauchi ya cigaba da tafiya, karfe hudu saura ya shiga Gombe, a lokacin ya samu damar tsayawa ya ci abinci da niyyar azumi domin wayewar alhamis ne, tare da rokon Allah ya kawo mishi sauki cikin al'amarin shi. A lokacin ya kira ta, sai yaji wayar ta shiga. 

   "Swampy!"

"Na'am ma sugar cannen, ya hanya?"

"Me yasa kika kashe wayar ki, hankalina ya tashi wallahi"

Murmushi tayi sannan ta ce mishi.

"Ni kuwa barci na sha da takwarar Hajiyar mu" 

"Lilly ina kewar kwanciya a jikinki, ina kewar b**ns dinki da ass din ki, kamar na dawo Abuja nayi Breakfast da su."

Dariya ta saka mishi, tana faɗin.

"Sugar cane, karka manta gobe alhamis akwai azumi idan ka sake wani abu ya fita daga jikinka akwai matsala"

"Na sani yar renin hankali, na sani bari nayi sallah zan shiga Yola don Allah ki saka ni a cikin Addu'ar ki"

"In sha Allah, kuma zan ci-gaba da maka har karshen rayuwata "

"Kin san me?"

"Sai ka faɗa"

"Na yafe miki, kema ki yafe min" murmushi tayi sannan ta ce.

"Dama ai baka tab'a min kome ba, ni ce zan ni me yafiyarka domin ta sanadina kome yake faruwa, kana zaune da iyalinka lafiya lafiya ina shigowa na tarwatsa maka gidan ka, don Allah ka yafe min"

"Ina sonki dayawa, bana jin haka ya faru baki min kome ba, kuma baki tarwatsa min gidana ba. Idan Allah ya ƙaddara saduwar mu, don Allah kiyi hakuri da kome"

      "In sha Allah " kashe wayar yayi domin abin da yake kamar wasiyya yake bar mata, dan haka na kashe wayar ma domin koda ya gwada kiran layin a kashe, haka ya  ciro abin sallah da goran ruwa ya fara gabatar da Alola sannan ya yi sallah, yana jima yana Addu'oin, kafin ya tashi ya ɗauki hanyar yola.

       Karfe goma da rabi ya tsayar da motar shi a compound din gidan su, me wanki da gugan gidan ya iso wurin shi, yana faɗin.

"Barka da zuwa, Alhaji Allah barka da zuwa baya me goya marayu, ina uwar marayu take." Murmushi yake yayi sannan ya ce.

"Salele bata zo ba, ga wannan ka karasa. Na ci a hanya ne" ya mika mishi ragowar kazar da ya ci. Ai kuwa ya shiga kwararo mishi Addu'oin, haka ya kwashi kayan shi ya nufi cikin gidan. 

"Assalamu alaikum"

  "Wa'alaikumunsalam, Dad" dawo da yaron tayi ya koma ya zauna a kusa da ita. Ta cigaba da chatt dinta, bai kalli inda take ya wuce corridon gidan, ta bude wani daki ya shiga, sai da ya shiga ban daki ya watsa ruwa, ya gaji barci yake son yi amma yasan bai isa ba, dan haka ya saka wata Material na maza, cheese colour sai wando dark maroon ko nace berry colour. Sai da ya fesa turare sannan ya gyara dakin shi tsaf, kafin ya fito fita yayi a sashin ya nufi cikin gidan su, da sallama ya isa falon. D'ago kai tayi ta zuba mishi ido gabanta ne ya fadi, jikinta yayi wani irin sanyi.

"Ahmadi!" Zubewa yayi akan gwiwar shi yana ce mata.

"Barka da safiya Hajiya!"  "Barka dai Ahmadi, ya aikin ka?"

"Alhamdulillahi" daga nan bai ce mata kome ba, domin yasan ba zata tab'a tambayar Falilah ba. Yana zaune a gabanta ta dauki wayar ta, tayi kira.

"Sai ku iso ai"

  Haka tayi ta kiran Yaranta, shi dai kanshi a sunkuye. Har yayun shi maza biyu suka shigo, kan shi a sunkuye tunda ya gaishe su babu wanda ya kuma tari.

"Kaje ka kira min Mariyah"

",Tow ya fada" yana me mikewa jikin shi babu kwari. Koda ya fita kallon Hajiyar su Babban Yayan su yayi yana faɗin.

"Gaskiya Hajiya ba a kyautawa Ahmadi ba, matukar aka matsa ya rabu da matar shi tow babu adalci a cikin wannan.."

"Tow ubana ko zaka rufe ni da duka ne?" Shiru yayi kwafa Jamal yayi yana jin kamar ya rufe Hajiyar su da duka. Amma babu yadda ya iya da ita.

     Lokacin da Ahmad ya nufi ɓangaren su, ya samu Yaran a falo uwar tana ciki, dakin ta ya nufa ta corridon din su, kofar shi ya gani a bude, ya shiga ita ce dai, sai watsi take tana bincike, murmushi yayi mata sannan ya ce mata.

"Idan kin dauki abin da kika ajiye min, ki je tana kiranki" ya juya abin shi, yana daga cikin abinda ya tura shi ga auro Falilah, Mariyah bata rena abin sata, sannan kullum cikin zargin shi take, a zaman su na shekara takwas bai tab'a kawo karar ta ba, bai tab'a gayawa wani abin da take mishi ba, asalima bai tab'a d'aga kai da abin da take mishi ba. Iskar bakin shi ya fesar, yana me nufar cikin gidan su. Tasan ba yau ya fara kamata tana mishi bincike ba, amma kuma na yau yafi na koda yaushe bata kunya, haka ta mai da mishi kayan shi ta fito, tana share zufa. Ta riko hannun Yaranta suka nufi wurin Hajiya. Lokacin da ta shiga zama tayi kamar na Allah. 

"Barka da hutawa Hajiya"

"Barka dai Mariyah."

Ganin yadda Mariyah ta koma kalar tausayi yasa Hajiya kallon Yayun shi, Yunus da Jamal.

"Babangida na tara ku ne anan domin kawo karshen rikicin, Ahmadi da Matar shi. Gata nan tunda  Ahmadu ya auri Fadilah ko Falilah take, Yarinyar nan take ganin tasku, da farko ya ajiye su anan duk karshen wata yana zuwa, karshe wancar jinin yan tsubun ta tadda masifa da son zuciya ya mai da ita can, ya bar Uwar Yaransa da ta aure shi da farin sawun shi, ai kusan kome"

Ajiyar zuciya Ahmad yake saukewa a kai a kai,. Domin zuciyar shi ruruwa take. Ji yake kamar ya hàdiye zuciyar shi ya huta da damuwar Hajiya da Mariyah.

"Kuna ji na, tow haka sai da na saka shi ya mai da Mariyah can, amma dake jinin yan tsubu ce, ta mallake shi ta hana shi sakat hatta yar tafiyar nan da ake yarinyar nan sai dai Ahmadi ya dauke ta, ya manta da Mariyah, wato dan bata yi boko ba. Haka Mariyah ta gaya min ya bawa tsinaniyar yarinyar nan kudi tana jari, kai wasu abubuwan da ni Uwar shi ban samu ba, yayiwa fasikar yarinyar nan me zubin kilaki. Yarinyar da sai da ta gama zagaye kan mazaje, da bin mazan banza da auren ta. Kai karkarewa na samu labarin Yayanta da take wurin shi, shi ne kwartonta "

"Hajiya!" Ya kira sunanta da ƙarfi.

"Kina da Yara mata, uku a gidan mazajen su. Ki fadi alkhairin ko kiyi shiru amma Falilah ba fasika ba ce. Na yarda nayi laifi na fifita Falilah akan Mariyah kuskure ne ba zan kuma ba, amma don Allah kina bincike kafin hukunci..."

"Innalillahi wa'inna illahi raju'un! Ahmadi Ni kake gayawa maganar da ta maka? Akan wancar ƙaruwar?"

"Tow ni dai ban ga wani abin tashin hankali anan ba, yana son matar shi akan me zai saka ya ana aibanta mishi ita, duk macen da ta iya mallakar miji ta sihiri ko tsafi, yawa ce Hajiya ita Mariyah da take da goyan bayan ki me yasa bata iya mallakar shi ba?"

"Jamal kai ma bayan shi kabi? Wallahi sai na tsine maka na tsine mishi " mikewa yayi yana faɗin.

"Allah ya rufa min asiri, ki tsine min na lalace ina dab da haduwa da commissioner lafiya za a bani cantract? Na rasa nayi asara, ku kare lafiya."


        Haka ya fita daga falon, kallon Babangida tayi tana faɗin.

"Kai ma kana da ta cewa ne?" 

"A'a da dai an bi a sannu, shi rayuwar duniya babu yawa, idan yau kai ne gobe ba kai bane, amma ya rabu da Falilah akwai son kai..."

"Ikon Allah, Mariyah mareniya ce bata da kowa sai ni, ku idan aka muku haka zaku ji dad'i?" Yadda take shiga ba nan take fita ba, shima barazanar tsinuwar ta mishi, ya ce yana bukatar promotion a wurin aiki, ba zai yi sanadin da zata kashe shi ba. Haka ya fita ya bar su.

    Shi kuma Ahmad ya rantse a ranshi matukar ya rabu da Falilah tow wallahi sai ya sake Mariyah ma. Tun karfe sha daya suke zaune ana abu daya har karfe biyu na rana, tun maganar da yayi yaki magana balle har ta fusata, lokacin sallah nayi ya fita bai dawo ba, ya zauna a motar shi ya sha soyayyar shi da Falilah, sai la'asar ya koma cikin gidan bayan yayi sallah la'asar, bai nufi wurin Hajiya ba bangaren shi ya koma, ya kwanta. Ko minti biyar ba ayi ba sai gata ta shigo tana kallon shi.

"Ba zaka rabu da Falilah ba?"

"Idan da kudinki a cikin auren sai ki sake ta ai "

"Tow wallahi billahi azim ni ce, ajalin ka domin kuwa sai dai murasa ka" murmushi yayi sannan ya ce mata.

"Duk abin da kika yi daya ne." Ya fada yana me juya mata baya, haka ta fita zuciyar ta yana kuna. Wayarta ta ɗauka ta kira Kawarta.

"Nancy ki turo min shi kawai"

"Ok matar Ahmad, kin samu takardun kuwa?"

"Zamu yi magana idan kome yayi kyau"

-----

FALILAH MUSTAPHA

Ina matukar kewar shi, sosai domin cikin jikina ya saka min bukatar shi ainun, shi yasa na shiga ban daki sakarwa kaina ruwa. Haka na fito bayan nayi tsarki da ruwan zafi, na sauya kaya na zauna ina sauke ajiyar zuciya, nasan yana azumi da na kira shi na d'aga mishi hankali, haka na kwanta lumo kamar me nazarin wani abu, Allah da ikon shi barci yayi gaba da ni, dake na kwanta da abin a raina mafarki nayi muna having sex da shi,  a cikin wannan yanayin shi kuka ni kuka, ina ganin wasu mutane suna saka mishi igiya a wuyar shi, suka fara jan shi. 

"Ahmad!!!" Na farka. Jina da nayi a jike jagwab, yasa kunya ta kama ni. A hankali na sauka a gadon na nufi hanyar ban daki nayi wanka sosai, sannan na fito na dauki wayata na kira shi. 

"Bobby!"

"Na'am Lilly, kin ga zan fita shan ruwa ne idan na dawo zan kira ki" gyada kai nayi kamar yana gabana.

"Tow" na fada ina jin kamar na bishi ta wayar, domin da mamaki a ce magidanci kamar shi sai ya fita niman abin da zai ci ai ba dad'i......

_Wani lokacin kana naka faffutukar Allah yana na shi, wanda masu iya magana suna ce na Allah shi ne gaskiya Allah ka  bamu sa'a_

#evil#lover#loyalty

#Mai_Dambu