Chapter Twenty Seven
Sauyi da yanayin gudun lokaci yana ɗaya daga cikin alamomi masu ban mamaki da Ubangiji ya ɗabi'anci wannan duniyar tamu dashi.
Wasu al'amuran su kan zo su shuɗe kamar ƙiftawar ido. Wasu kuma sai su jima ana kaikawo dasu, musamman lokuta masu nauyi da zafi a zuƙata.
Amma babban abun daɗin shine, su ma zasu wuce kamar ba'a yi ba.
Yau tsawon wata biyar kenan da kwanaki da bayyanar asalin baƙin zaluncin da Uncle Sani ya daɗe yana shiryawa Radiya. Wadda ta sadaukar masa da abu mafi wahalar sadaukarwa a wannan zamanin.
Sai dai duk wannan al'amarin da ya faru, Sultan da Sauban sunyi iya bakin ƙoƙarinsu don ganin bata san komai ba. Har waɗanda suke da alaƙa da shi basu fahimci ainahin abinda yake faruwa dashi ba.
An dai wayi gari an dai na ganinsa.
Sai dai ta ɓangaren su Abbas, sun samu labarin cewar ya tare a Abuja wajen matarsa Radiya. Da yake abun yana matuƙar ƙonawa Abbas rai, ko da wasa bai tambayi Radiya ba.
Yayi shuru ya zuba musu ido, yana jiran lokaci.
Ita kuwa Radiya, ta daɗa samun nutsuwa, hankalinta ya kwanta na wani ɗan lokaci. Saboda yadda Sultan yake saita mata komai cikin hikima. Tun daga gidansu har zuwa tsohon mijinata ba tare da wata matsala ba.
Yayi ƙoƙari matuƙa wajen shawo kan ƴan uwanta cikin dabara. Domin yadda suka shirya shine, ta samu aiki na dindindin a wannan asibitin.
Ya daɗa ƙarfafa zancen ne musamman dab da fara azumin watan Ramadan in da mota guda ta sauke nau'ikan kayan abinci daban-daban wanda suke ɗauke da sunan asibitin da Radiya take aiki da niyyar a rabawa mabuƙata.
Wannan ya saka mutanen unguwa, dangi, da ƴan uwa da abokan arziƙi cikin farinciki sosai tare da san barka. Sannan ya daɗa saka zuciyar Abbas ta sakko sosai akan al'amarin aikin.
Sai dai a kullum ƙorafinsa da ita shine: ko hutu yakamata ace tazo. Amma haka take daɗa tausarsa tana nuna masa cewar zata zo bikin Sadiq. To daga bisani da aka fasa bikin ta sake samun damar miƙe ƙafa.
Ba don komai ba saboda cikinta ya tsufa sosai, ta tabbatar da idan ta sake taje gida, ko wani ya ganta ba zasu barta ta dawo ba. Cewa zasuyi sai ta zauna ta haihu. Ita kuma babban tashin hankalinta a yanzu shine, su fahimci abinda ta aikata.
Hakan ya saka suka taru suka dinga bin dabaru daban-daban domin kaucewa hakan.
Duk da ƴan watannin baya Abbas yazo ya sake ziyartarta, amma a lokacin cikinta bai fito ba sosai ba, lokacin Sultan yana hutun ƙarshen shekara ya daɗa taimaka mata matuka wajen sake binne shirin su kar Abbas ya gane.
Kuma yaji daɗi sosai hakan ya daɗa kwantar masa da hankali. Itama nata hankalinta ya kwanta.
Yanzu babban abinda yake gabanta shine, taga ta sauka lafiya.
Sultan yana matuƙar kula da Radiya. Musamman yanzu da cikinta ya tsufa sosai, dole ya tilastawa kansa ɗaukar hutun sati biyu saboda ya samu ya kula da ita sosai saboda lokacin haihuwarta ya ƙarato sosai.
Haka yake ɗaukarta su je manyan shagunan sayar da kayan jarirai a garin Abuja na alfarma .
Anan fa aka fara rigima da Radiya. Saboda da taga kuɗin kaya ta dinga mita tana rigima, tana cewa: "wallahi a Kano sai an raba kuɗin kayan goma. Wannan ƴan Abujan sun cika tsugawa mutane kuɗi."
Haka Sultan yake lallaɓata su yi siyayyar tana mita, saboda har yanzu rayuwar Kano ta ƙi ta sake ta.
Kwatasam! Wata rana Sauban yazo yi musu sallama shi da Zainab da niyyar zasu tafi UK siyayyar kayan baby.
Aikuwa haka akayi. Siyayya kam ba'a magana. Musamman na kayan baby.
Ɗaki guda aka ware a ɓangaren Radiya aka maƙare shi da kayayyakin jarirai kala-kala sai kace za'a buɗe wani shararren shagon kayan jarirai. Abun sai wanda ya gani.
Radiya kam tasha mamaki irin wannan soyayya da shaƙuwa da take tsakanin Sultan da Sauban.
Musamman ma Sauban da a zahiri yafi kowa nuna farin cikinsa akan wannan cikin.
Haka Ammey, Zainab da sauran ƴan uwansa suka yi hidima da ita, basa taɓa gajiyawa.
Wata ranar Alhamis sun je asibiti domin yi scanning na ƙarshe. Sultan yana zaune kusa da allon computer yana kallon yadda ɗansa yake kwance acikin mahaifa, sai murmushi yake yi.
Itama Radiya murmushi tayi sannan tace:
"Gashi nan yayi ƙaton kanka."
Da sauri ya juyo ya kalle ta yace:
"Ƙaton kanki dai."
"Allah wannan ba irin kaina ba ne ka duba sosai."
Murmushi ya sake yi a daidai lokacin da likitan ya kammala aikin ya miƙo musu da takardar.
Ta sake duba hoton tana tsokanarsa. Shi kuma dariya kawai yake yi.
Bayan sun kammala suka fito kai tsaye gidan marayun Sultan suka nufa.
Abun gwanin sha'awa yadda suka dinga wasa da yaran. Sai tsalle suke suna murna da cewar ga Daddy da Mummy.
Wannan yana matuƙar bawa Radiya nishaɗi. Haka kawai taji yaran sun shiga ranta. Musamman yadda suke kai kawo akanta. Masu bata biscuit, chocolate, da sauran kayan kwaɗayi wai tabawa baby da yake cikinta.
Dariya kawai ta dinga yi. Saboda Sultan ne ya koya musu hakan. Bayan sun ɗau lokaci suka fara shirin tafiya.
Kai tsaye gidansu ya kai ta. Acan ta ƙarasa wunin ranar. Ammey tana tarairayarta har zuwa dare sannan suka tafi gida. Suka fara shirin kwanciya cike da nishaɗi da walwala.
Washegari da wani irin yanayi ta tashi, kasala da rashin son cin abinci. Duk da daman cin abinci ta ya ragu amma yau kam wuni tayi ta kasa cin komai.
Musamman da Sultan baya nan yau bai wuni a gida ba daga ita sai Zainab.
Haka itama tayi ta takura mata akan cin abinci amma taƙi.
Sai bayan magariba Sultan ya shigo tare da Sauban. Jikinsa sam bai yi masa daɗi ba yanayin da ya ganta.
Hakan ya ɗaga masa hankali sosai. Bayan su Sauban sun tafi gida ya samu ya zauna kusa da ita yana rarrashinta.
"Me kike so please?"
"I'm OK."
Abinda ta furta kenan tana yamutsa fuska.
Ajiyar zuciya yayi, sannan ya sake kwantar da muryarsa yace:
"More than 24 hours no food in your system. You need to eat something. Please!"
Jim...tayi tana tunani. Sannan ta kalle shi tace:
"Tuwo nake so naci. Kuma yanzu dare yayi."
Da sauri ya miƙe tare da faɗin:
"Bari na saka su dafa miki..."
"Ni ba wannan ba...na kasuwa fa. Irin wanda muka siya rannan."
Ta katse shi tana turo baki.
Ajiyar zuciya yayi ya kalli agogon da ke jikin bango ya ga tara saura na dare. Sannan ya kalle ta yace:
"Let's try ko zamu samu ko?"
Jinjina masa kai tayi, sannan ya taimaka mata ta miƙe ta sauya kaya suka fice.
Haka suka dinga yawo lungu da saƙo na unguwannin gargajiya a Abuja. Da ƙyar suka samu wata mata da take yin tuwo a bakin titi suka siya.
Kamar sallah haka Radiya taji.
Ai kuwa suna komawa gida ta baje ta fara ci kamar bazata bari ba. Shi kuma yana miƙa mata ruwa har ta ƙoshi ta ture.
Take taji wani kuzari ya ziyarce ta, hankalinta ya kwanta sosai. Shima kuma hakan ya saka ya ci nasa abincin.
To da suka zo kwanciya nan ma taji gabaɗaya gidan yayi mata zafi. Hakan ya saka ta miƙe ta nufi can saman gidan da yake sarari ne ta zauna tana shan iska.
Bayan ya fito daga wanka ya iske ba ta nan. Da ya kira ta a waya, ta sanar masa da inda take.
"Nan kuma kika taho?"
Ɗaga masa kai kawai tayi ba tare da tace komai ba. Murmushi yayi sannan ya ƙaraso dab da ita yace:
"Dare yayi ki daure mu shiga ciki ki kwanta ko?"
"Ni bana son ciki gabaɗaya. Gabaɗaya wani irin ƙamshi yake min."
Ta faɗa tana yamutsa fuska.
Da ƙyar ya iya lallaɓa ta suka shiga. Sai dai suna shiga ƙaramin parlour da yake dab da bedroom ɗinsa ta cake.
"Ni bana son ciki fa. Anan zan kwanta."
Ta faɗa tare da zama akan ɗaya daga cikin kujerun da suke parlour.
Ajiyar zuciya yayi. Sannan ya shiga ya ɗakko barguna da pillow yazo ya shimfiɗa musu a wajen sannan ya lallaɓata suka kwanta.
Sam bacci kasa ɗaukarta yayi sai juyi take yi. Hakan ya saka ta miƙe zaune ta ɗakko wayarta ta ci gaba da dannnawa.
"Kiyi haƙuri ki kwanta dare yayi sosai fa."
A nutse ta ƙare masa kallo. Sannan tace:
"Waye yace maka idan ciki ya tsufa ana iya yin bacci? Kai dai kawai kayi kwanciyar ka."
Murmushin yaƙe yayi, sannan ya miƙe zaune yace:
"In dai bazaki kwanta ba nima na fasa baccin."
Sake kallonsa tayi taga alamar da gaske yake. Take taji wani tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Saboda tunda ta samu cikin nan yake kai kawo akanta. Musamman a yanzu da cikin ya tsufa. Yadda bata iya yin bacci shima baya iya yi.
Gabaɗaya ya faɗa baya samun isasshen bacci. Ko yaya ta motsa zai farka, sai ya tabbatar da ta koma sannan zai kwanta. Duk da ya samu hutu amma sam bai huta ba.
Yanzu ma alamar bacci nr ƙarara a fuskarsa. Hakan ya saka ta kwanta da niyyar baccin ƙarya, saboda wani lokacin haka take yi masa idan tana so ya samu bacci.
Ai kuwa y tana kwanciya shima ya kwanta. Da ya lura da tayi bacci shima bai san lokacin da nasa baccin ya ɗauke shi ba bayan yayi mata addu'a.
Ita kuma a hankali ta zaro carbinta ta fara jan "Hasbunallahu Wani'imal Wakeel" kamar yadda ta saba.
Can taji wata yunwa ta kama ta, hakan ya saka a hankali ta zare jikinta daga nasa ta miƙe. Kasancewar bacci ne sosai a kansa bai ji motsinta ba.
A hankali ta fara sauka daga hawan farko.
Amma kafin ta ƙarasa sauka can ƙasa bayanta ya riƙe sosai. Hakan ya saka ta zauna don ta huta. Bayan ta ɗan huta ta sake miƙewa.
Tana sauka baya ya rike kam, mararta da kwankawasonta suka amsa, bata san lokacin data durƙushe a ƙasa ba.
Kafin kace me...ruwan naƙuda ya wanke in da take zaune.
Cikin tsananin ciwo ta ɗago idonta taga zurfin benen da ta sakko. Gashi babu waya a hannunta, babu kowa, ga Sultan yana can sama, masu aikinta suna ɓangarensu. Gashi ta kasa motsi ballantana ta ƙarasa in da landline ɗin parlour take.
Haka ta durƙushe, da kyar da rarrafe da jan gwiwa ta fara motsawa. Amma ina ta kasa kaiwa inda take.
Cikin ƙarfin hali ta jawo flower vase ɗin da yake kusa da ita, ta da doka shi da ƙasa ko da wani zaiji motsi ya kawo mata ɗauki, amma shuru dole ta haƙura ta durƙushe tana neman agaji daga Ubangiji.
Firgit! Ya farka daga baccinsa, kamar wanda aka tasa. Ya shafa gefensa yaji bai ji ta ba. Hakan ya saka ya buɗe idonsa.
Da sauri ya miƙe, kai tsaye ya fara duba bedroom ɗinsa amma bai ganta ba. Hakan ya saka ya nufi ɓangarenta, amma shuru babu alamarta.
Cikin hanzari ya sake komawa can saman gidan, da tunanin ko ta koma ta sake shan iska. Nan ma wayam. Hakan ya saka da saurinsa ya nufi matattakalar da zata sada shi da ƙasa.
Daga nesa ya hangota a durƙushe ta riƙe ƙugu tana murƙususu sai haɗa gumi take yi duk da sanyin AC da yake parlour. Sannan gata male/male cikin ruwa.
Da gudu ya ƙaraso.
Tana hango shi ta fara miƙa masa hannu...alamar neman taimako.