Chapter 11-12
*SANADIN HIJIRA*
Chapter 11/12.
Sai da komai ya kammala Al'ameen ya Koma cikin office na shi, tab ya bude ya yi wasu y'an danne danne, zuwa minti biyu Badar ta bayyana gaban tab din tana zaune bisa kujerar dining kan ta babu hula sai guntun gashin ta da ya sha gyara dake bayyane.
"Hiii Sojana" ta fada tana daga mishi hannu daga inda take, "kamar ka san tunanin ka nake yanzu haka, ji nake tamkar in yi tsuntsuwa in ganni a gaban ka, how are you doing?". Lumshe idanu ya yi ya bude, "Ban hana ki zama kai bude ba? "ya fada a can kasan makoshi.
"Awwwn sorry Sojana a cikin gida nake fa shiyasa but kada kaji haushi bari in saka yanzu" ta fada tana janyo hularta dake gefe.
Wayarshi dake burarin neman agaji ya kalla ganin mai kiranshi ya ce, "I will call you later" daga haka ya katse vidcall din yana picking call din Musty.
"Hey Capt. Abun da ka turamin gaskiya ne or you are kidding me?".. Dan murza goshinsa ya yi, yace, "About work issue zan maka wasa? Oya get ready mr man" karfe shida na safiyar gobe ne tafiyar." Cewar Al'ameen yana tattare fatar goshinsa waje daya.
"Gosh. ka san halin da Zeenat take ciki fa, tana bukatar kulawata ta musamman you know shekara d'ai-d'ai har biyar mukayi muna jiran wannan lokaci yazo kuma zan shiga daji in barta cikin taraddadin ta yiwu in dawo ko kuma an rabu kenan har abada!.Cewar Musty yana bata fuska
"Sosai maganar Musty ta doki Al'ameen yaji shima ya kamata yaje yaga Ummie even though ba lallai hakan ya kasance ba amma dan kar ya karyar mishi guiwa yana daure fuska yace, "Ka yi alkawarin kare rayukan al'umma a kowane mataki, so NO GOING BACK. Zeenat kuma da izinin Allah zata haihu lafiya, inyeee wayaga su Musty Daddy amma zaka min kara ka sanya sunana ai ko? "Ya fada da barkwancin da Musty bai saba ji daga gareshi ba sai abun ya mishi wani bambarakwai, yana dariya ya ce,
"Wannan alkawari ne Amin, matukar Namiji ta haifa mai sunanka ne, idan kuma mace ta haifa sunan Ummie za'a sanya Safeenatu, amma idan Namiji ne kai zaka yo mana farautar Giwa a dajin Borno mu yanka mu rakashe a jeji". Cewar Musty dariya dauke saman fuskarshi dan tuni Al'ameen ya kawar mishi tunanin da ya fara na halin da Matar shi ke ciki.
********
Da dare misalin karfe takwas Al'ameen ya dira a gida unexpected kawai suka ganshi, Badar da Saudat ne zaune a palo suna kallon tashar Zeeworld suna kallon wani Drama (Age is just a number). sai Humaira yar Saudat din dake zaune gefe tana assignment na makaranta,
"Sannu da zuwa Uncle A"Cewar Humaira, Hannu ya daga mata yana nufar bangaren dakin Ummie dan sauri yake yi. Badar ta biyo bayanshi da sassarfa.
"Sojana kai dai ka iya mana dirar mikiya, why not ka sanar damu ko dan turare ai zan shafa maka ko?" Ta fada cike da gwalli, sosai ta bashi dariya yadda tayi din, amma sai ya kanne yana fadin zan shiga wajen Ummie". Baya tayi da sauri dan yau kuma jikin na Ummie ya motsa mata sosai Ladi mai aikin gidan taci duka.
Bai yi zaton da mutum a dakin ba dan haka ya shiga kansa tsaye sallamar ma a zuciya yayi ta ba zato ba tsammani Hajja Fanta dake tsaye jikin mirrorn dakin ta juyo a rikice jin sound na bude kofa abun da ke hannunta ta fara kokarin boyewa a bayanta ganin Al'ameen ne ya shigo.
"Ahh lale maraba da dan albarka, yanzu ko nake zancen ka a zuciya ta ashe kana tafe" Ta fada tana yaken dole a gefe daya kuma jikinta na dan rawa tana cigaba da boye hannunta a baya.
"Barka da dare " Kawai ya fada kai tsaye yana tunkarar bakin gado inda Ummie ke zaune kanta a kasa, gashin kan nata yayi biji biji da datti kana ya sauko ya rufe har saman fuskarta, hannunta daure da chains hakama kafarta, rigar jikinta ta yayyage har ana iya hango gefen mamanta.
Ganin bai mai da hankali a kanta ba yasa Hajja Fanta saurin fitar da abun da take boyo, maganin Ummie ne da dr ya kawo dazu, ainahin na cikin container din ta juye tana kokarin musanyawa da wanda ta kawo Al'ameen ya shigo, da hanzari ta juye nata ta kwashe na dr din tana zubesu a bakin zaninta...
Rumtse idanu yayi da karfi yana juyowa a fusace ya ce, "What the heck is this, waye ya daure mata hannu da chains bayan na kafarta,? "Ba Ummah kawai ba hatta da su Badar da ke Palo sai da suka tsorata da irin tsawar da ya doka.
"Amm ehh dama Ba jimawa Dr Shettima ya shigo sakamakon kiran da Abeey dinku yai mishi, shi ne ya daure mata hannu, ya kuma yi mata injection ga nan ma sabbin drugs da ya taho mata dashi yanzu na ke shirin bata su, jikin nata ne ya dan motsa mata shi ya sa" Umma ta fada cike da rawar murya tana mikawa Al'ameen maganin da ta musanya. Jikina rawa ta fita cikin kasa da minti biyu ta dawo dauke da bottle water a hannunta.
Yana tsaye yadda ta barshi sai huci yake idanunshi kamar zasuyi aman wuta, tana mikamishi ruwa da drugs din ta fita bakinta alekum dan tasan shi ne kawai mutumin da zai iya bata maganin cikin salama.
Takowa yayi gaban Ummie dake duke har lokacin gabadaya jikinta ya yi weak, "Dr Shettima" yake ta nanatawa a ranshi, wato wannan mugun injection din yau kuma ya yiwa Ummiena? sau nawa zan fada ciwonta bai kai matsayin da zai mata wannan allurar ba? Kwafa yayi yana zama ya dan dago kanta kadan,
"Ummie" Ya fada a hankali kamar ba daga bakinsa kalmat ya fito ba. Lumsassun idanunta da suke nuna halin galabaitar da take ciki ta dago kamar taji kiran da yai mata, suna hada idanu ta fara kyakyacewa da dariyar da zai tabbatar maka cewa lallai ita din sha tarace, "Stop it!" ya fada da dan tsawa dan yasan shi ne kawai mafita idan ta fara irin haka, aiko ta tsorata nan take jikinta ya fara makyarkyata hawaye ya soma gangarowa saman kuncinta. Da wannan damar Al'ameen ya yi amfani wajen bata maganin hadi da ruwa, hannunta ya kama yana kwance chains din, a hankali ya fara magana kamar mai rada.
"Ina bukatar sanyawar albarkar ki kamar ko wanne d'a Ummie, gobe zamu tafi yaki can wani yanki dake gabashin kasar nan ban sani ba ko wannan shine gani na karshe da zan miki tafiyace ta ko a mutu ko a yi rai. Ina fatan Ubangiji ya amshi rokona ya baki lafiya. A daidai lokacin ya gama kwance mata hannu ya dago kai bisa mamakinsa ta yi shiru hatta rawar jikin da ta keyi na tsawan da yayi mata ya tsaya sai kallonshi take kamar mai fahimtar abun da yake fadi, sai dai tunaninshi bai sauka ba ya ji ta fara sambatu tana daukar pillows dake saman gadon ta fara jifanshi da su, ta janyo bedsheet nan ma ta jefa mishi a fuska duk abun da ta rarumo a kanshi take saukewa, Al'ameen yana tsaye kikam as a soldier he is, wani dan murmushi ne ya subuce mishi a ranshi ya ce, ladan kwance hannun ake bani kenan sai dai ko da wasa bai yi niyyar hanata abun da take ba. Kusan minti bakwai tana abu daya kafun a hankali wani irin jiri ya fara kwasarta tayi baya baya zata fadi, yayi azamar tarota yana kwantar da ita saman gadon gyara mata kwanciya ya yi sannan ya sumbaci hannunta ya juya ya nufi palo dan Sallama da su Ummah.
A falo ya samu Ummah sai kai da kawowa ta ke yi hannunta goye a bayanta babbar damuwarta kada Al'ameen ya duba maganin nan tunda ai shima likita ne, Badar da Saudat na zaune irin dai zaman da suka saba Saudat a zaune Badar kuwa tana kwance kanta bisa cinyar Saudat din, kallo daya ya musu ya dauke kai.
"Dan Albarka ka fito? ta amshi drugs din ko?" Cewar Ummah.
Daya daga kujerun palon ya samu yana kaiwa zaune ba tare da yace komai ba ba kuma cewa bai ji tambayar tata bane, ganin haka itama Ummah ta zo ta zauna ta san cewa akwai magana a bakinsa dan ba dabi'arshi bace zama a palon kasa. "Zuwa gobe zan jagoranci wata runduna zamu tafi aiki a Maiduguri In sha Allah. Na yi sallama da Abeey ta waya.
Idan dr Shettima ya kuma shigowa lallai a sanar mishi kada ya kuma yiwa Ummie wannan banzar injection din dan ya yi wa lalurar ta girma, idan ya Kuma kuwa I will deal with him". Ya fada fuska babu annuri ba tare da ya lura da yadda maganarshi ta farko ta jefa daukacin occupant na palon a shock ba.
Zabura Humaira ta yi tana mikewa da hannunta a kirji, "What Uncle! Maiduguri fa na ji kace? Dan Allah kada kaje plsss."...Badar kuwa garin saukowa sai da ta kifu da kasa ji ka ke timmm kamar an sake buhun masara amma ta yi azamar tashi tana matsowa inda yake idanunta kamar zasu taba kasa dan yadda ta kwalalosu waje.
"Sojana Maiduguri naji ka fada kasan Maiduguri kuwa? hakan na nufin zakaje yaki da b*k* h*r*m fa ke nan ance suna da karfi da kayan yakin da ko ku baku mallakesu ba ka rufa mini asiri don girman Allah" ta fada Kuka Yana cin karfinta.
Ummah ce ta matso itama with shock on her face ta ce, "Aminullahi anya lokaci bai ba kuwa da zaka aje wannan aikin kamar yadda Abeey din ku ya dade yana bukata, Maiduguri fa ka ke maganar zaka jagoranci runduna ku tafi, anya kuwa Aminullahi!".
"Kada ku damu, naje Liberia, na je Sierra leone, Duk na yi yaki da yanta'adda, so na kasata ba zai gagareni ba, na kare rayukan jama'ar wasu kasashe me kuke tunani a kan kasata da al'ummata?" Wani irin sautin kululululuuu cikin Badar ya bada a lokaci guda kuma ta ruga da gudu zuwa toilet na palo jin kalaman Al'ameen, har cikin palon suke iya jiyo sautin gudawar da ta barkewa Badar tsabar yadda ta tsorata.
Dariya ne ya so kwace mishi amma ya wayance da sosa saman lips nashi. Ummah dai na tsaye fuskarta cike da mixed expression, Saudat kuma kamar bata a palon sai faman latsar waya take a ranta tana fadin Allah ya sa idan kaje kada ka dawo.(Subhanallah,nikam mene ne a tsakanin Saudat da Sojan Badar ne?).
Bata jima a bayin ba ta fito tana share zufan da yai mata sharkaf, tunkararshi ta kuma yi, "Sojana dan Allah kace wasa kake mana bazaka tafi wancan yankin ba" Idanunta tarwai a kanshi tana jiran jin abun da zai fada.
"ka yi shiru faa".Gefen da Ummah ta ke ya dan saci kallo kadan kafin ya mike yana fadin "Biyoni".
Babu musu ta bi bayanshi da sassarfa bata bi ta gefen da Saudat take ba dan bata shiryawa jidalinta ba a yanzu, zabura Ummah ta yi ta haura sama da sauri kamar zata kifa itama, tana shiga bedroom dinta wayarta dake saman gado ya katse daga kiran da ake mata, tana yunkurin kira wani call din ya kuma shigowa. Da hanzarinta ta kama, "Hajiya Titi yanzu nake kokarin kiranki ko da kuwa baki kirani ba" Ummah ta katsewa H titi maganar da ta fara. "Kinji abun da Aminu ya ke sanar mana yanzu kuwa?" nan ta kwashe duk abun da Al'ameen ya fada yanzu ta sanar mata.
Wani irin dariya hajiya Titi ta kece dashi sannan ta ce, "Sai me Hajja Fanta",magana ta yi na tsawon minti biyu Fanta dai tana jinta bata ce komai ba, sai da ta kai aya kafun ta samu kwarin guiwar fadin, "Bazaki gane ba Titi, tsorona Allah tsorona wannan yarinyar Badariyya da ta dauki son duniya ta daura akan Aminu, kina ji fa yanzu daga cewa zai tafi cikinta ya birkice ta dinga zawo babu control" Dogon tsaki titi taja kafun tace, "Ki samu lokaci ki taho gidana dan ni bazan zo inda kike insha matsa a banza ba ni ba gyada ba".
A parking lot ya tsaya yana kare mata kallo ganin yadda ta zage tana kuka kamar ranta zai fita. "Why all this Badar?" ya tambaya still wondering me ke sata kuka haka. "Sojana dan Allah kace wasa kake min bazaka je wanccan wajen ba, kana gani yadda ake nunawa a news fa hatta sojojin gudu suke yi tsabar karfin mutanen nan i don't want to loose you Capt" Ta fada tana fashewa da wani kukan. Sosai ta bashi tausayi wannan ya kara tabbatar mishi Badar tana sonshi. Front seat ya bude ya kamo hannunta cikin nashi bai ce komai ba itama batace ba sai da ya tabbatar ta shiga ta zauna kana ya zaga driver seat ya zauna shima yana kallonta har cikin ido, tsawon lokaci suna a haka kafun ya dan ja fasali ya fara magana.... Sai da ya tabbatar da ya cire mata duka kokwanton ta har ta fara dariya sannan ya ce, "Muje in sai miki Ice cream tana dariya ta ce da pizza ohh har da burger" juyowa ya yi yana kallonta ya ce, "No wonder kike ta zama bukekiya mana ashe fatness food kike ci, anyways muje, but ki tabbata idan mun dawo daga wannan service din barrack zan kai ki ki fara exercise.
Dariya ta kuma sanyawa cike da nishadi, "Da ko na Fi kowacce mace sa'a da murna a wannan duniya Sojana, dan matukar Zaka kaini Barrack da kan ka, then hakan na nufin an shafa mana fatiha ne". Ko uffan bai ce ba sai horn da ya danna da karfin gaske mai gadi ya wangale musu kofa ya fice a guje, sakin labulen Saudat ta yi tana fadawa saman kujera yaraff kamar kayan wanki, tun fitar Badar take lekensu har sai da ta ga sun fita.
*BAMA*
Fanne, washegari da asuba ma ruwan sanyi ne ya tashemu ni da Maahh, a firgice na bude idanuna na sauke bisa fuskar Uwa da ta sha murr, "Don uw**ki ni ce zan yi aikace aikacen gidan da kike kwance har yanzu kamar ruwa?" Ban ce komai ba sai mikewa da nai ina tsane ruwan da yai wa fuskata wanka da hannuna, ganin Maahh itama ta tashi ta zauna da kan ta hakan ya sani farin ciki har ma ina kokarin mancewa da Uwa dake a tsaye a kanmu har lokacin, "Mahh kin tashi? Jikin ki ya yi sauki, me ki ke so in miki yanzu, zaki iya tashi ke kadai?"
Tambayoyin da nake ta jeho mata baki na a washe tamkar gonar auduga...Murmushi ta min itama ta ce, "Fannetu na maza wuce ki yi aiyukkan da aka sakaki sai kizo ko, "kwafa Uwa ta yi a fili ta ce "kwainane da iyayi" kafin ta tusa keyata zuwa waje. Kamar yadda na saba sai da na gyara bangarenmu tas sannan na daura abun karin kumallo, dumamen tuwon jiya ne sai bakin shayi da na dafa mai yawan gaske saboda bakin da muke dashi a gidan, kamar ko yaushe uwa ce ke raba abinci idan na gama girkawa sai dai yau fuskar nan a hade tamau tamkar hadari haka ta sauko alamar dake nuna babu wasa ko wargi a tattare da ita.
Bakin shayin ta miko min a kofi da yankan dumamen tuwo guda uku ta ce, "Kuna gama ci keda uwartaki ki kimtsa ki wuce min tallar kuli da mangyada ta dan bazan dauki asara ba, kar ki ga jiya an barki a gida an wani fake da gari babu lafiya. Yau babu dagin kafa sannan kika zubar min da shi yau kuma sai na lahira yafi ki jin dadi.
Zuciyata tana lugude haka na wuce sama da abincin, Maahh bata iya taci sosai ba a cewarta bakinta babu dadi dan haka nima cakalar abincin kawai na yi na bar saura,ba jimawa Baba ya shigo yana duba jikinta yadda ta tashi, jikinshi yana rawa ya fitar da soyayyar kwai da biredi irin na wajen masu shayi a aljihunshi duk a tsorace yake ya ba Maahh.
"Aminatu kici wannan na san bakya jin dadi amma ki kara hakuri watarana sai labari" Ya fada cike da tausayawa sannan ya fice a ranshi yana tsoran kar Uwa ta shigo ta taraddashi a wajen.
Wanka na yi a gaggauce na shigo dakin ina cire jibgegen hijabin da na rufo jikina dashi,Alum na dauko na fara gogawa a hammata na, wannan koyarwar Maahh ce a gare ni, tana yawan fadamin cewa.
"Fannetu na tsabta shi ne mace, duk rintsi kada ki yadda wani ya shaki wari daga wani bangare na jikinki, kin ga Hammata da baki da kuma gashin kan mace, sune abubuwa mafi bukatar kulawa da tsafta, Fanne koda baki da kudin sayan turare ki dinga amfani da alum a hammatar ki bazai taba yin wari ba, kamshi daraja ce, kamshi na masu daraja ne, ki dinga girmama kan ki ta hanyar amfani da kayan kamshi sai na kusa dake ma su girmama ki,".
Wannan dalili yasa bana rabuwa da aluum da kuma turare na yar diba dan duwala. Kayan da zan sanya na fitar na daura zani ina kiciniyar sanya riga na jiyo Muryarshi sama sama a dakin Uwa yana magana da karfi karfi.
*Almuhajir*
A daddafe ya kai kanshi daki bayan su Baba Bamai sun tabbatar mishi za'a daura mishi aure da Yaganah, a lokacin ba komai yake ganewa ba, Wani irin zazzabi ne ya rufeshi mai zafi, ba abun da yake imagining a ranshi sai cewa an daura mishi aure da wata can ba Fanne ba. Duk ya tuna hakan sai gabanshi ya fadi hakan ya kara rura zafin zazzabin da yake ciki. washegari sai wajan bakwai na safe ya farka saboda dai around 4:40 bacci ya daukeshi. Da hanzari ya gabatar da sallah yana auziya na korar shaidanin da ya rinjayeshi har haka da kuma addu'ar Allah yasa mafarki yayi akan duk abubuwan da suka faru jiya amma yana zuwa gaida iyayenashi ya fahimci addu'arshi dai bata karbuba dan tiryan tiryan suka kuma maimatamishi wadannan kalmomi masu kama da harbin kibiya a zuciyarsa wanda hakan ya kuma rura wutar kiyayyar Yaganah sabuwa a ransa, direct samansu ya wuce ba tare da shayin komai ba ya bude dakin Uwa yana zare idanunsa da suka sauya kala fuskar nan babu alamar rahama zabura Uwa ta yi tana mikewa gami da dafe kirjinta ta ce.
"Na shiga uku ni Uwani me..."maganar tata ce ta katse da hanzari tana zaro ido a lokaci guda ganin abun da Almuhajir ke aikatawa.........