Chapter 13-14
SANADIN HIJIRA
By
Ummu Fadeela
Chapter 13/14...
Zabura Uwa tayi tana dafe kirji da zaro idanu waje ganin Almuhajir ya nufi inda Yaganah ke kwance bisa gado gadan gadan babu ko dar a fuskarsa sai ma wani tururin hayakin masifa dake cin sa. Sai dai kafin ta iso ya sanya hannu gami da finciko Yaganah da wani irin karfi ya tsaidata bisa kafafunta without second though ya daga hannu ya sauke mata wasu tagwayen maruka da ya sanyata ganin wasu taurari suna gilmawa ta idanunta.
"Me ya kai ki dakina? waya baki izinin shigar min daki? Ya tambaya da wani irin karfi yana kokarin zaro belt na wandonshi. Yaganah data gama rudewa babu abun da jikinta ke yi sai kyarma idanunta na digar hawaye dan ba karamar shiga marin yai ba. "Tambayarki nake who gave you permission to enter my room"? Ya kuma katsa mata wani tsawan da yafi na farko a lokaci daya yana zabga mata belt din, ihu Yaganah ta saki mai karfin gaske amma ta kasa bashi amsar tambayar da yake mata. Zuwa lokacin zuciyar Almuhajir sai zillo take yi kamar zata fado kasa, babban burinsa Fanne ta ji kuma ta yadda cewa hakan ba halinsa bane.!
Cakk Uwa ta rike bulalar da ya dago zai kuma zabgawa Yaganah a karo na uku, rai a bace jikinta yana rawa ta ce, "sha ƙwalle mana__Sha'a ƴazimin? uhye wako sha'a ƴezimin.?...(Sakar ta mana, kasheta za ka yi ne? nace kasheta zakayi). Uwa ta fada a birkice kamar zata yi hauka. Ko dai ka fara shaye shaye da kwankwade kwankwade ne bamu sani ba mun shiga uku??
Bai kulata ba sai kuma daga bulalar yayi zai kaimata" Bazaki bani amsar tambayar da nai miki ba" Cikin ihun kuka Yaganah ta yi tsalle bayan Uwa tana fadin "Wllh Yayaa ba laifi na bane bazan kuma ba Uw...." da hanzari Uwa ta katse ta jin banzar tana gab da tona mata asiri. Bai da bukatar karin bayani kuma.
Koda bata karasa ba yasan inda maganar ta dosa wani irin tsana ce Uwa tayiwa Fanne da Maahh har haka, wace irin tsana ce da zai sanya ta sadaukar da future din yarta dan kawai ta bata ran wadanda takeyiwa kallon makiya ne a gareta a cikin duhun da ita taki bayyana a haske dan fahimtar hakikanin gaskiya?
Kodai dan ba ita ta haifi Yaganah ba yasa batasan zafin ta ba? Innalillahi.
Sassauta murya yayi dan wani irin nauyi yaji kanshi ya dauka ya ce yana kallon Yaganah.
"Ki wuce yanzun nan ki samu Baba Bamai ki sanar musu da bakin ki cewa ban taba aikata miki makamancin wannan ba, yanzu ma saka ki a kayi, sannan abu na gaba ki tabbatar kin sanar musu cewa ke bakya SONA, baza ki kuma aureni ba akwai wadda ki ke so, idan baki aikata haka ba sai na yi sala sala da namar jikinki na tsireshi a tsakar gidan nan".
A wani irin zabure Yaganah da Uwa wacce tayi suman wucin gadi suka dago a tare suna kallonsa gyada mata kai ya yi alamar tabbatarwa.
"Amma ni ina sonka ai Yayaaa, " cewar yaganah cikin zarmiyar baki. Belt din ya kuma dagawa yana zare idanu kin wuce ko sai na karasa ki munafuka mai siffar lagwani, da gudu ta fita ganin ya tunkarota, hada idanu suka yi da Uwa wacce numfashinta ke tseren hawa da sauka, kallon ke kuma zamu hadu ya mata ya sa kai ya fice daga dakin.!
Yaraff Uwa ta zube bakin gadon wani irin zufa yana karyo mata daga kowacce huda na gashin jikinta, me yasaka kowa ke tsoranta a gidan nan amma banda wannan tagadarin yaro mai idanu a tsaitsaiye, me yasa ya zamarwa rayuwar ta annoba me yasa take tsoro da shakkar yaron da aka haifa a hannunta? Da sauri ta tashii tuna cewa Tsaff Yaganah zata iya aikata abun da ya sakata dan ba kai gareta ba tayi waje a guje.
Almuhajir*
Fitarshi daga dakin Uwa ji yayi kaso goma sha biyar na damuwarshi ta ragu, kai tsaye ya shige dakin Maahh. Tun da ya fara hargowa a dakin muna jinsa daga ni har Maahh, karfin hali na yi na zura rigata cike da rashin karsashi na dawo bakin gadon na zauna ina buga tagumi daduka hannuna biyu, zuciyata sai bugawa take da karfi karfi.
Kamar wanda aka hankado haka ya fado dakin namu. Da hanzari na dago idanuna na Saka cikin nashi, yana tsaye rike da handle na kofar ta ciki idanunsa a kai na ba tare da yaji ko kunyar Maahh dake kallonmu ba. "Fanne I am really sorry about what happened abun da kika gani ba shine exact abun da ya faru ba, ba don ni ba dan darajar soyayyar da nike miki ki bani dama in wanke kaina a gare ki plssss".
Almuhajir ya fada cike da madaukakiyar tashin hankali akan fuskarshi, duk ya zama wani kalar tausayi kamar wadda ya shekara yana jinya......"Fanne pl......" A harzuke na mike nayo kanshi kamar wata zakanya, ina nunashi da yatsa na ce,"___Na adi kwalle wande waltike na'allan ya ruƙiyi. Ka tafi anan banson ganin ka kuma, ka tafi na ceeeee" gyara tsayuwa yayi ya ce, "Fanne....."hannu na daura aka na rusa ihu ka tafi kar in fasa maka kai ka tafi na ce ban son ganinka a nan kumaaa.
Da sauri ya toshe kunnuwanshi maahh kuwa ta rufe idanu da hanzari jin irin ihun da na zabga, da wani irin sauri Muhajir ya bude kofar ya fita, a fusace na tura kofar gami da rufewa harda danna sakata sannan na sulale nabi kofar zuwa kasa,kaina na sanya a tsakanin kafafuna na fara raira kuka mai sauti, babu wata mace da zata fahimceni a lokacin sai wacce ta kama mijinta ko saurayin da ta dauki so, yadda da amanar duniya ta daura akansa a yadda na kama Almuhajir da Yaganah.
Kuka nake mai tsuma zuciyar mai sauraro. Daga waje jikin kofar na jiyo muryarshi a sanyaye, "Fanne dan girman Allah ki daina kukan haka, zuciyata tana min zafi idan na tuna nine silar kukan ki a yanzu, na yadda bazan kuma bayyana miki kaina a nan kusa ba har sai kin huce da kan ki a sannan zan miki bayanin abun da yake faruwa. Plsss Maahh ki mata magana ta daina kukan haka."!
Daga haka ban kuma jin muryarsa ba da alama ya bar wajen, kirjina na hawa da sauka na nufi inda Maahh ke yafitoni da hannu, fadawa na yi jikinta ina kuma sakin sabon kuka, a hankali take patting bayana har na yi shiru ya zama sai ajiyar zuciya nake saukewa.
Ban sani ba ashe wannan shine mafarin mabudin zanen kaddarata, ban sani ba ashe wannan shine SANADIN zubar hawayena na har abada, ashe shi ne Nadamar da bana fata ubangiji ya kara nuna min wata nadamar da zanyi makamancin sa har ranar da numfashina na karshe zai yi bankwana da gangar jikina,ashe........
A hankali nake sauke ajiyar zuciya ina jin yadda Maahh ke lallashina ta hanyar shafar bayana da hannunta, Mahaifiya ke nan duk halin da take a ciki amma damuwar ta ni in samu nutsuwa hakan yasa na rage sautin ajiyar zuciyar da nake ina yin lamo a gefen ta.
◆◆◆
Aminullah*
Washegari kamar yadda aka sanar 6:30am suka bar barikinsu cike da fatan nasara da tarin kayan aiki.
Wasu sun wuce ne a motoci, wasu ko da suka kasance manya irinsu Al'ameen a jirage suka tafi.
Ko da suka iso Babban birnin jihar kuwa jirage masu saukar ungulu ne suka kwashe su zuwa wani jeji inda a nan ne zasu gabatar da aikin su mashahurin daji ne dake tsakanin garinsu Fanne da wani gari da suke makwabtaka, clearing na wajen da za su zauna sojojin suka Fara cikin kiftawar ido har sun kakkafa Tent tent na kwanansu wanda ya kasance kalar kakin sojoji.!
A cikin wani Tent manya manyan su ne zagaye da wani calanda mai fadi da girma sosai, zanen taswirar dajin ne gabadaya a kai dukkansu sun rufu akai suna observing yadda wajen yake da yadda zasu iya yakar yan ta'@ddan cikin dabara, wasu zaratan sojoji biyu ne suka shigo daya yaja tunga daga bakin kofar tantin daya kuwa direct wajen Al'ameen ya nufa magana yai mishi na tsawon minti biyu a gefen kunnensa gyada mishi kai Al'ameen ya yi yana wani sign da yatsunsa sojoji biyun suka fita.
Dawo da hankalinsa gaban Map din ya kuma yi kafin ya zaro abun da suke communicating dashi ko da waje babu service ya kara saitin bakinsa. "Hello, hello capt A.F Misry ke layi". Exactly irin abun da yake Hannunsa ya yi magana bisa teburin MG a Abuja. Da hanzari ya dauka dama kiranshi yake jira. "Capt na samu labarin kun isa har kun kafa tent, and na ji labarin ka tura an muku observing yadda dajin yake an kuma kawo maka result, so abun da za'a yi yanzu kuyi zamanku a wajen kar kuyi yunkurin aikata wani abu sai mun samu command daga sama".
"Whatt? taya zamu zauna bayan mun gama gano komai da maboyar su da kuma wajen adana mak*mansu me yasa zamu zauna alhali aiki ne ya kawo mu, shin zama zamuyi har sai sun kawo h@ri muje mu dakile bayan mu ya kamata mu nemosu dan murkushe su"?
Al'ameen ya fada a fusace ya ma manta da wayake magana, abun da MG ya fada daga daya bangaren yasashi dawowa cikin nutsuwarshi gami da kamewa waje daya yana kai hannunsa bisa goshi yayi salute kamar MG din yana gabansa, Cigaba da magana MG ya yi, "Dan haka ka tabbatar kun yi abun da ya dace kada kayi gangancin kai wani farmaki har sai an baka dama, wannan izini ne daga Sama" kitt ya yanke wayar ba tare da ya bawa Al'ameen damar cewa wani abu ba.
Tuni idanunsa sun fara juyewa zuwa na zallar bacin rai da takaici, hannu ya goya a bayansa ya fara zagayen tantin jijiyoyin jikinsa suna harbawa tsabar bacin rai, taya suna sojoji za'ace ba za su kai farmaki wa abokan gaba ba har sai su sun kawo sannan a turasu su dakile harin, ya za'a maida su lusarai kamar wasu mata? Domin me ake samun wannan sa kutsa sa katsin daga sama, kullum daga sama wai ma su wayene a saman nan da MG yake yawan fada? Me yasa baza a farmaki yan ta'@ddan ba har sai sun shigo gari sun barnata rayuwa da dukiyoyin al'umma kafin ake tura jami'an tsaro?
Dafa shi yaji an yi daga baya, a fusace ya juyo sai dai ganin Musty tsaye yasa shi sassauta daurin da yaiwa fuskar tashi, "Whats wrong capt?"
Kwafa Al'ameen ya yi yana komawa gaban taswirar ya zubawa zanen dajin idanu kamar mai son gano wadannan dake sama din cikin zanen ba tare da yacewa Musty komai ba, sanin hali shima sai bai ce komai din ba. "A nad'e" tun bai gama rufe baki ba wani daga cikin sojan ya fara cire pin da aka rike map din dashi sannan ya nade ta mai kyau yana ajiyewa a gefe.
●●●
Cikin kwana daya Kawai maganar hada Ya Muhajir da Yaganah aure ya karad'e lungu da sa'ko na gidanmu. Durkushe nake kamar kullum bakin kwararo ina wanke kwanukan abincin rana da aka gama ci, na tsinkayo muryoyin su Yakura suna maida maganar, wani irin sarawa kaina ya yi jin abun da kunnuwata suke jiyo min kamar wai Ya muhajir da Yaganah zasuyi aure. Ban kai ga gama tantace me suke fada ba na kuma jiyo muryar Uwa a bazata tana surfawa su Yakura masifa" To almunafunfun masu bacci da idanu guda daya, ni dama nasan wannan zuga da kukayo kuka cika min gida babu alkhairi a tattare daku sai masifaffiyar sharri, to gashi tun ba'aje ko ina ba kun fara hada majalisa kuna gulmata kuma ahir dinku Yan gudun hijira, na ce ahir dinku kuma aure babu fashi sai an daura, dama can Yaganah yake so shishshigi ne kawai irin nasu o'o ake shige mishi to gashi ya fallasa sirrin zuciyarsa kuma nan da sati guda zamu baza guda a gidan nan zuciyoyi sai dai su kumbura idan sun so su tarwatse kowa ya huta ku bace min da gani kowa ta yi ta kan ta"
Tun bata gama magana ba suka fara watsewa ban da Iya uwar gidan Baba Bamaina da take jin ta take Uwa a masifa kawai dai ta raga mata ne na yau kawai kafin taga iya gudun ruwanta, dan daga saukarsu jiya ta fahimci akwai haya'ki a kan Uwa, kallon sama da kasa ta mata kafun ta shige daki, rike baki Uwa ta yi tace, "Iyeeee ba shakka, kaga isashshiya ni za ki yi wa kallon wulakanci, to lallai sai kin gwammaci komawa inda kika fito sun karasa ki akan ki shiga bakin Uwa.....
Da kyar na iya tattara gabadaya bayanan da su ka fada cikin kwanyata kafin in fara sarrafa su.
Wani irin bugawa gabana ya yi a lokaci daya zuciyata ta bada sautin Damm ban yi aune ba na fara jin wani abu mai d'umi yana biyo kafafuna, da kyar na kai duqe a wajen wani sanyi nake ji yana shiga tun daga kan dan yatsa ta har zuwa tsakiyar kai na. Bana raba daya biyu bakona na wata wata ne yazomin a bazata dan saura kwana biyu zuwanshi a lissafina.
Hakan na nufin tsinkewar zuciyace ta janyo shi. Cikin rashin karsashi na kammala wanke wanken na koma sama, ina shiga daki kukan dana ke ta faman rikewa ya tahomin da masifar karfi na toshe bakina ina zaman gefen Maahh dake ta hada zufa alamun akwai abun da ke damunta.
Maahh kuwa maganganun Uwa ne ke dukan ranta dan tsaff taji duk abun da take fada a waje....
Wasa wasa sai ga zazzabi ya rufeni rufff ba shakka ba karamar so zuciyata ke yiwa Almuhajir ba, sai yanzu nake ganin wautata na barin soyayya ta min mugun cafka haka bayan ni kaina na san ni din mummunace maza kuma kyawawan mata suke muradi, ashe dama can fooling dina yake yi, so yake ya shagaltar dani sai daga karshe ya buga min guduma a kirji me yasa ya mini haka Maahh? Rarrashina kawai take yi hade da ban baki da nusar dani komawa ga Allah da kuma yadda da kaddara a duk halin da nake ciki,
"Fannetah kin taba ganin mutum mai Imani wanda Allah bai jarrabceshi ba? Bawai dan ba ya sonshi ko ya manta dashi bane,a'a Ubangijinmu yana jarrabtar mune dan ya gwada karfin Imaninmu. Duk da halin rashin lafiyar da na tsinci kaina a ciki amma Uwa bata raga min ba na daga aikace aikacen gidan, ina yi kuwa tana yada min habaici da yimin gori duk gidan kuwa babu mai karbata dama Ya Muhajir ne, shikuwa tun ranar da yace bazan kara ganinshi ba har sai na nemeshi hakan ce ta kasance dan yau kwana uku kenan ban sanyashi a idanuna ba.
Almuhajir*
Tun da ya koma dakinsa sai ciwon kanshi ya dawo sabo, amma duk da haka bai gaza ba wajen komawa gun mahaifinshi domin tabbatar mishi lallai bayason Yaganah Amma baba Aisami yayi kememe yace wannan shine daidai hukuncin abun da ya aikata dan ya zama izina ga sauran kannensa.
Koda Amma ta nemi sanya baki a maganar ganin yadda danta ya zama cikin kwana daya kacal sai Baba Aisami ya dawo kanta da kafa mata sharadin bai amince ta shiga cikin maganar ba.!
Wadannan kwanaki ukun gabadaya Almuhajir ya kwashe sune a dakinsa yana jinya da tunanin mafita, yau da maganar ke cika kwana uku kuma kwana uku din kenan cur bai sanya Fanne a idanunsa ba, a irin so da kaunar da yake hangowa nashi a idanunta bai taba zaton zata kai warhaka bata nemeshi ba, don haka ya yanke shawara kuma wannan shi ne yake ganin mafita a gareshi.
Yana idar da sallar isha ya dauko travelling bag nashi kaya seti uku ya zuba a ciki sai sauran tarkacensa da kudin da yake ta tarawa dan aurensu duk ya zuba a jakar ya zuge gami da adanata a gefe, "Ina zuwa gareki Fanne, zan daukeki mu gudu muyi nisa da garin nan, mu tafi wata duniyar a daura mana aure bazamu dawo ba har sai mun hayayyafa a lokacin na san kowa ya hakura" Cewar Almuhajir a bayyane yana duba agogon dake fuskar wayarsa jjira kawai yake lokacin da ya tsara ya cika......