Chapter 15_16
SANADIN HIJIRA
15/16.....
Kallon wristwatch nashi ya yi a karo na barkatai dake tabbatar mishi karfe daya na dare, da hanzari ya mike yana goya jakarshi bisa kafada. "Na tabbata kowa ya yi bacci zuwa yanzu," Almuhajir ya fada yana jin bakin cikin abin da zai aikata,
"Ku yafe mini Baba Ammah ku yafemin, wannan ce kawai mafita a gareni matukar kuka rabani da Fanne rayuwata zata zama useless na san ban kyauta ba amma ku yafemin, "Haka yake ta nanatawa cikin kunan rai shi kansa ya san hakan ba daidai bane, amma why? Me yasa za su rabashi da abun da yakeso, me yasa zasu yanke mishi hukunci akan laifin da bai san yadda akayi ya aikata shi ba? Yan dube dube ya yi sadda ya tabbatar da komai da yake bukata ya dauka sannan ya fito bakin kofa.
Dabarar ajiye jakarsa ya fara leka tsakar gidan ce ta fado mishi, aje jakar ya yi yana sanda da bin bango kamar barawo har ya iso kofar sashen su, dal aka dallaroshi da toci, "Kai waye nan?" Wani irin harbawa zuciyar Almuhajir ta yi jin muryar Baba Bamaina, ya na haske shi da tocin dake hannunshi.
"Waye nan na ce" aka kuma fada, da kyar Almuhajir ya ja sagaggun kafafunsa wani abu na tokare kirjinsa "Ni ne Baba"..Kai ne waye"? Ya kuma tambaya,
"Almuhajir"
Ya fada a takaice, "Aiho me kake nema nan cikin daren nan"? Yana sosa kai ya ce, "Baba ruwa zan deba dama sai na ji sawun mutum ashe ma kaine. Daga haka ya juya zuwa dakinsa cike da bakin ciki, haka Muhajir ya kwashe tsawon dare yana sintiri daga karshe ma babbar tabarma da fitila sai abun sallah ya samu Baba Bamaina ya shimfida nan tsakar gidan yana qiyamullaili wanda ba shi ya tashi ba sai asuba, a lokacin kuwa kowa ya farka, wannan shi ya batawa Almuhajir plan nashi.
A daren washegari ma duk kokarin da yai na son daukar Fanne su gudu a abun yaci tura dan ya lura kamar al'adar Baba Bamai ne sallar dare kuma a tsakar gida. A gefe guda kuwa duk yadda yaso ya ga Fanne abun ya gagara dan nima sosai nake fama da kaina tilas ne kawai ke sauko da ni, shima da zarar na gama aikacena nake komawa daki na kudundune abu daya ke samar min salama shine tilawar Alqur'anin da nake yi a zuciyata dan ina cikin halin rashin tsarki....!
Wasa wasa a lissafina gobe juma'a ranar da aka yanke za'a daura auren Ya Almuhajir idan an sauko jumma'a, babu wani shiri da ake hasalima gidan kamas yake a bushe kamar babu mutane cikinsa, abun mamaki hatta a bangaren Uwa babu wani shirin da take yi as if ba ita ke rawar kai akan auren ba, kowa ka gani ya yi wani kalar tausayi like wani mummunan abu yana shirin faruwa, ko kukan yara bakaji hatta da tsuntsaye basa rera yarensu, "Hasbunallahu wanimal wakeel" na fada a karo na barkatai ina dafe kirjina jin yadda ya yi wani irin bugawa tare da faduwar gaba abun da nake fama dashi ke nan tun wayewar gari, shirun da gidan namu ya dauka ya dameni tun asali sashenmu bai da yawan hayaniya kasancewar babu yara amma sauran sassan babannina uku dake gidan akwai yara kuma ga iyalan Baba Bamai.!
Har zuwa yammaci gidan namu shiru Yaganah dama yau kwana uku kenan bata gidan Uwa ta turata can gidan Kakanta a cewarta sai an daura aure za'a daukota daga can, kamar ko yaushe yau ma ni ce nake aikin gidan, misalin karfe biyar na kammala komai wanka na yo gami da dawowa daki tsaftace jikina na yi kamar yadda Maahh ta koyar dani kafun na bude mazubin kayana, da daddaya nake daga kayayyakin ina neman wadda zan sanya tsurawa wasu kaya idanu na yi na tsawon minti biyu,
"Fannetah wannan kayan su zaki sanya ranar aurenki da Almuhajir na san zasu yi bala'in amsarki dan haka ki adana min su can kasan akwatinki"!...Muryar Maahh ta shiga dawowa cikin kunnena tamkar yanzu take furta min maganar. A hankali na zaro su doguwar rigace na wani yadi mai laushi kalar red da touches na green dinkin bubu, sai gyalenshi mai dan girma shima Ja da touchs na green,wani dan karamin jaka na dauko daga gefen kayan, tarkacen su dan kunnene a ciki na juyo ina ganin Maahh dake kwance duk jikinta ya yi weak.
Takowa na yi gabanta, "Maahh kin gaji ko? In daga ki ki huta?" Gyada min kai ta yi a hankali na kamata ta jingina na sanya mata pillow a bayanta da gefe gefenta, "Allah yai miki albarka" ta fada da sanyin murya dake nuna tana cikin wani hali, zama na yi ina matsa mata kafafunta da suka tasa sosai zuwa hannayenta, "Maahh ko in kaiki waje ki sha iska?"
Na kuma tambayarta girgiza min kai tayi tana rufe idanunta. Kusan mintuna takwas ina mata massage kana ina mulmula abun da nake son fada amma na kasa,da kyar na yi gathering courage cikin in ina na ce, "Maahh ina son zan sanya wannan kayan"....Shaaaa sai hawaye kamar an kunna famfo wanda ban san dalilin zubowarsu ba. Bude idanunta da sukayi jaa Maahh ta yi tana kallona, "Fannetu! a duk yanayin da rayuwa zata juya miki kada ki manta da Ubangijinki mahallincin sammai bakwai da kassai bakwai da dukkan komai, ki daga hannu ki rokeshi tabbas zai amsa miki. Idan baki ga sakamakon addu'ar ki ba kada kice Ubangiji ya manta dake ne a'a watakila abun da kika roka ba alkhairi bane a gareki sai ya musanya miki da wanda shine mafi alkhairi, sau tari mu Kan so abu so mai tsanani amma ba alkhairi ba ne a garemu. Mu kan ki abu kuma ki mai tsanani amma wannan abu sai ya zama Shi ne alkhairi a garemu tabbas Allah shi ne mafi sanin abin da ke boye. Fanneh ina ji a jikina cewa Allah ya na amsar addu'ata kuma tuni ya zaba miki miji mafi alkhairi a rayuwarki, na san fitar Almuhajir a ranki abune mai wahala amma kiyi kokari, kuma kisa a ranki Allah baya kuskure duk wani abun da ya zartarwa bawanshi to shi ne daidai. Tashi ki sanya kayanki inga yadda za su yi miki kyau".
Maahh ta gama maganar a galabaice dan ta dade batayi magana mai tsawo haka ba. Salo salo na mike kamar mai ciwon wuya, bra da pant na fara sanyawa kana underwear, kafun na zura rigar, Subhanallah, wani irin lafewa yadin ya yi a jikina, cikakkun breast nawa suka tsaya kyam hakan ya taimaka wajen bayyanar flat tummy dina mai kama da babu yan hanji a cikinsu, daga kasa kadan hips dina wanda suke kamar an dasa su suka baje, ba karamar kwanciya rigar tayi a jikina ba.
Bag na dankunnen na janyo ina tsayawa gaban mirror dan kunnen na saka wanda akayisu da duwatsu ja da kore kana na sanya wani abun hanci cikin bulin hancina wanda yake rawun kamar dan kunnen yara sai murjani da na sanya a wuyata wanda ya sauko har saman kirjina an yi shi da duwatsu manya manya jajaye kana wani sarkar na sanya a can karshen wuyata ta dan matse sosai a gabanshi akwai wani katon kullutu ja, haka kawai na samu kaina da son yin kwalliya wacce ba dabi'ata bace, kwalli na zizara a idanuna na goga jambaki jan gyalen na dauko ina gyara kitsona da aka zubo shi ta gaba gefe daya yafi daya yawa mai yawan ya sauko har saman idona jelar kitson kuwa har yana taba wuyata.
A saman kaina na yafa gyalen amma rabin kitsona yana waje. Daga saman zanen dake kan goshina wanda ya sauko har saman karshen hancina na fara kallo ni kaina na san nayi kyau murmushine ya kwace min na juyo ina kallon Maahh, sake baki kawai tayi tana kallona daga sama har kasa bakinta ya kasa rufuwa, "Kaga KANURIYAR asali, Fatabarakallahu ahsanul khaliqeen Masha Allah" shi ne abun da ta fada tana yafitoni zuwa gareta dan ba karamin kyau na mata ba.
Cike da kunya na karisa gareta hannuna ta kama zata fara magana kenan wani irin tari ya fara sarketa tari takeyi sosai har idanunta yana fitar da kwallah, a firgice na mike "Sannu Maahh bari in kawo miki ruwa, kin yi magana dayawa ne shi ya sa" na fada ina dauko ruwan dake cikin cup a gefe na kafa mata a baki, tasha mai dan yawa sannan ta mayar da kanta tana jingina da lumshe idanu, wani irin karta mata cikinta ke yi kamar abun da ke cikin yana son balla cikin ne ya fito a take ta fara hada wani irin zufa kamar ta fada a kogi, da kyar ta iya hada kalmomin, "Ki ra min babanku" ban jira ta karisa ba na fita a tamanin ba tare da na cire kayan dake jikina ba, dakin Baba wayam bai nan hakan yasa na garzaya kasa direct hanyar waje na nufa durkushe gaban tsohuwar akuri kurarshi na sameshi yana duba tayar motar na gaba.
"Baba Maahh, maahh maahh" iya abun da bakina yake fada ke nan ina haki da nuna hanyar sashenmu, a birkice Baba ya wuce shima cikin sassarfa nabi bayansa lokacin da muka iso Maahh ta galabaita matuka dan jikinta har wani irin rawa ya dauka kamar an jona mata electric shock idanunta suna kakkafewa.
"Aminatu! Aminatu, Innalillahi Aminatu kiyi magana meke damunki, ina ke maki ciwo? Ganin jikin Maahh na cigaba da rawa yasa shi fita da wani saurin ko hanyar dakin uwa bai duba ba dan yasan idan mutuwa Aminatu za ta yi tana dawowa Uwa bazata taimaka mata ba, "Yakura, yakura ya ambata a daidai dakin da su Bamai suka sauka. Da hanzari Yakura Uwargidan Bamai ta fito zani a hannu
"Na'am baban Fanne Allah dai yasa lafiya ince dai lafiya?" Taho ki duba mini Aminatu" Ah ikon Allah,kada dai ace haihuwarce aiko dazu ma na dubota a sama amma banga alamar haihuwa ba,in ce ko yanzu nakudar ta tashi ne?."
Baba mtodu dai bai ce komai ba sai gaba da yayi ta bishi a baya tana gyaran kallabinta. Kafin su iso Maahh ta gama galabaita Ina tsugunne gabanta sai sannu nake mata amma da alama bata gane me ma nake fadi, "Ya salam" Cewar Yakura tana dafe hannu a kirji Fanne bamu waje, ba dan na so ba na mike jiki ba kwari na fita a kan staircase na zauna hadi da baza tagumi hawaye na rige rigen bin kuncina tausayin halin da Maahh ke cikine yake dawainiya dani, ji nake kamar in mayar da ciwon jikina ita kuma ta huta ko kadan ne, "Astagfirullah" na furta ina share hawayena tuna nasihar Maahh na dazu da ta kara tunatar dani Allah baya kuskure duk abun da yayi shi ne daidai.
A daki kuwa bayan dube duben da tai mata Yakura ta dago tana sharar zufa, "Anya Baban Fanne baza a kaita asibita ba kuwa, nan da kake ganinta babu nakuda babu alamarta tattare da ita hasalima cikin bai kai haihuwa ba,a dan fahimtata dai kamar rashin wadataccen jini ke wahalar da ita da kuma zazzabin cizon sauro, dan duk wadannan kumbure kumbure da jikinta ke aunewa shike janyo su, kuma suna da matukar hatsari ga mata masu juna biyu da an kaita asibiti domin bata taimakon gaggawa ina ganin zai fi."
Gumi ne kawai ke karyowa Baba Modu ta ko wacce hudar gashi dake jikinsa, yau ya kai kwana biyar bai rike koda sisin kwabo nashi ba, ina zai iya kaita asibiti a halin da yake ciki ko kudin yankar kati bashi da, jiki na rawa ya ce, "Ki kula da ita bara in nemo ko Muhajir ko Baana cikinsu wani ya tukamu zuwa asibitin gashi magariba ta shigo.
FANNE.
Ina zaune na baza tagumi hawayen da suka ki tsayamin sai faman shatata suke saman kumatuna, a jikina na ji kamar ana kallona irin kallon da shi ka dai yake min gangar jiki da zuciya su sanar min, "Baby! is this you? Damn it na yi kewarki kamar zan yi hauka woww you look so beautiful like bri......." maganar tashi ce ta katse yana kaiwa zaune kusa dani ganin hawaye na sauka saman fuskata. "Ya salam me ya faru Fanne, wani abu aka maki ne? Ina Maahh?" jerin gwanon tambayoyin da ya jeromin kenan kamar mai jira kawai na fashe da matsanancin kuka dama a shoulder to cry na ke nema dan abun ya min yawa a dan tsakanin nan. "Zaki haukata ni ne Fanne, fada min mana me ya faru. A dai dai lokacin Baba ya fito daga dakin Maahh fuskarshi dauke da damuwa,
"Yauwa Muhajir taimaka kazo mu kai Aminatu asibit......."maganar tashi ce ta katse shima a lokaci guda muna mikewa ni da Ya Almuhajir sakamakon wani karan ihun da mukajiyo daga makwabtan mu, bamu kai ga fita daga firgicin ba muka jiyo makwabtanmu ta gefen dama nanma an kwallah ihu wanda yafi na daya gefen cikin al'ajabi makwabtanmu ta baya ma aka kuma zabga ihun, cikin kasa da minti biyu ko ina na anguwar ya karade da iface iface, kan kace me gaba daya garin ya rude babu abun da ka ke ji sai kukan jama'a yara da manya da mata musamman.
Hannuna Muhajir ya rike gam kafin ya jani zuwa cikin dakin Maahh. Kada wanda ya fita a dakin nan, "ya fada yana rufo kofar ta waje a tamanin yabi bayan Babana da sauran mazan gidan da wadanda basu tafi kasuwa ko gona ba suka fita waje dan ganin abun da ke faruwa, turuss dukkansu suka ja baya a kofar gidan, "Rike ta nan" Jami'in dan sandan yake fadawa dan uwansa Baba Abbagaana ne malale cikin jini an mishi y@nkan r*ago hatta kai din yana gefe gang@r jiki a gefe.
Yan ta'*adda ne suka aikata musu wannan aika aikar su sittin da daya 61 a hanyarsu ta dawowa daga gonar su ta noman shinkafa wannan ne yasa gari ya rude dan har mutum sittin da daya dole kowa a akwai ta inda kuka hada dangantaka Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wannan shi ne mafarin tagayyarar rayuwarmu, an k@she mana iyaye maza an rabamu da muhallanmu da dukiyoyinmu, wannan shi ne farkon lamarin.
Nan fa gidanmu shima ya rude ya shiga jerin sauran gidaje ihu kawai ake, a sai kuka na gaba, ashe washe garin ranar shine rana mafi muni da yan garin mu na B*ma ba za su taba mantawa dashi ba, wannan kisan gilla ya ruda jama'a kowa ya gigice yayin da wasu suka fara tattara komatsansu dan karawa gaba a matsayin YAN GUDUN HIJIRA,.
Rudewa muka yi dagani har Yakura jin ihun da ake tayi ga Maahh a take bakinta ya kuma rufuwa, ashe Allah ya bata daman yi min magana ne dan ta min nasiha wanda zan iya kiranshi nasiha ta karshe jijjiga kofar Yakura take tana a kawo mana agaji, me yake faruwa ne, a agajemu mana,"
"Uwa da fitowarta kenan itama har zata wuce ta jiyo ihun kamar da muryar Yakura hakan yasa ta bude kofar ta waje bata bi ta kan mu ba ta sauka a wani irin firgice dan gida fa ya gama rudewa, wasu daga cikin yayan Abbagana da matarshi sun suma.
Ina son fita amma bazan iya barin Maahh a halin da take ciki ba fan haka na sanyata a gaba kawai ina kuka na nima.!
Tabbas zuciyoyi sun raunata bisa wannan mummunar aika aika da yan ta'@dda suka aikata mana bango masu yawa sun rushe, aka tattara su dukkansu akayi musu suttura wanda masu karfin haline kawai suka iya yi aka sallace su kana aka mikasu gidajensu na gaskiya.
Haka garin ya kwashe wannan dare cike da alhini wanda ya shiga cikin tarihin yakin arewa maso gabas da baza'a taba mantawa dashi ba.
Ni dai ina jikin Maahh da har lokacin bata a hayyacinta mutuwar da aka kawo sai ta mantar da kowa halin da Maahh ke ciki.....
LUXEMBERG...
A yau Abeey da thaufeeq suka gama duk abun da ya kaisu, sun zauna meetings kala kala da kamfanonin da suke son yin collaboration da su kuma komai ya tafi successfully sai shirin dawowa....
Washe gari kuwa suka wuce airport dan dawowa gida Thaufeeq kamar ya zuba ruwa a kasa yasha dan murna dan dama a takure yake "zama kusa da Abeey matsala ne wllh dan adam bai isa ya sha iska ba ko kadan" ya fada lokacin da yake jan akwatunansu zuwa cikin filin jirgin...A kan abun zama da aka tanada a cikin airport din Abeey ya zauna, "Thaufeeq shiga ka karisa mana duk abun da ya dace bari in dan huta a nan" Abeey ya fada yana sanya hular sweater dinshi gami da zaro bottle water ya kafa a baki, duk da sanyin da ake kwadawa mai daskarar da jinin mutum amma wani irin kishirwa yake ji.
Turo baki gaba yayi yana kunkuni ya shiga ciki, sai da Abeey yasha kusan rabin gorar sannan ya sauke yana hamdala ya aje a gefen bencin, a daidai lokacin wanda ke zaune bisa irin kujerar da Abeey ke zaune a gefensa ya dago kai suka hada idanu, wani kayataccen murmushi ya sakarwa Abeey ya na mikewa, hular rigar sanyinshi mai dauke da gashi a gaban ya janyo ya rufe fuskarshi da shi ya fara tafiya.
Ruwan da Abeey ya gumtsa bai kai ga hadiyewa ba ne ya dawo mishi wani ta baki wani ko ya biyo ta hancinshi, yana kwalalo idanu waje a wani irin birkice ya zabura sai dai can ya hango mutumin ya yi nisa dashi sosai. Sauri sauri gudu gudu Abeey ya fara binsa yana ambaton wani suna, wani kwana ya shiga da hanzari Abeey ya fada kwanar shima, sai dai wayam babu wannan mutumin babu alamarsa kuma filine fetal babu inda wani mahaluki zai iya buya bare Abeey ya ce ko buya ya yi, kamar mahaukaci haka Abeey ke juyawa wajen gabas da yamma kudu da arewa amma babu alamar wannan mutumin. Zaune ya kai bisa wani kujera yana lalubar wayarsa gami da fara neman wani lamba, sau uku wayar tana faduwa tsabar yadda jikinsa ke mazari, rike wayar ya yi da karfi yana karawa a kunnensa bugu biyu aka daga, da muryar fitar hayyaci ya ce,
"Hosni kana ina?" Wanda aka kira Hosni ya gyara zama a hamshakin palonsa ya ce, "Ina gida, lafiya dai Fadlallah na ji muryarka a birkice,.
"Hosni, ALBURHAN yana RAYE bai MUTU ba!........