MAƘOFTAKA DA ALJANU 1
by @deejasmah
Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah) & Ameenah Abubakar Ƴandoma
CHAPTER 1
Bismillahir Rahmanir Rahim
Dare mahutar rana, inda duk wata kujiba-kujibar rana kan ƙare sai hutu da kuma jiran ranar da ke biye. A duniyar mutane ko ba a faɗa maka ba ka san lokacin hutawa ne da bacci, musamman a lokutan da sanyin watan Nuwamba ya kawo kai yana kai harin sumame ga gidaje da gangan jiki kar ma wainda ke cikin fadama su ji labari. Ko'ina ka bi zaka ji tsit sai kururuwar da sanyin kan yi idan tana wucewa a sarari, wanda hakan ke ƙara tausar ka ka shige cikin bargo don neman sukuni.
Nana ma na ɗaya daga cikin mutanen da sanyi kan takura sosai, hakan ya sa tun farkon dare take maƙale cikin bargo tana sake jan shi jikin ta don ji take yi bai ishe ta ba. Ji tayi ana sallama a ƙofar ɗakin ta wanda haka nan ya haifar mata da faɗin ƙirji ba kuma na komai ba sai na tuna bata rufe gidan ba kenan in dai har za'a mata sallama yanzu. Janyo wayar ta dake gefen pillown ta tayi ta duba lokaci, ƙarfe goma saura ya nuna sai zuciyar ta ya bata babu shakka Khalid ne ya dawo gidan yake sallama. Cikin sanyin jiki ta tashi tana kunna tochila ta nufi parlor, har lokacin tana kuma jiyo sallamar.
Hannu ta kai za ta zare sakatar da ke jikin ƙofar ta ji an wuce ta bayan ta suuuuu, dakatawa tayi ta waigo sai dai babu kowa sai tsabar duhun da kamar kuma daɗa shi aka yi. Ajiyar zuciya ta sauke tana cewa '' sanyin nan yayi ta maka gizo'' ta ƙare tana maida hannun jikin ƙofa, wani sabon yanayi ne ya kaiwa hannayen ta ziyara sakamakon jin an ce '' Nana!!!'' cikin wata ƙaramar murya kamar ta mage ga wani sanyi kamar ta riƙe ruwan ƙanƙara yana kwaranya har zuwa ƙafafun ta.
''Innalillahi" ta fara maimaitawa tana buɗe ƙofar gabaɗaya, sai dai kamar an yi ruwa an ɗauke haka sallamar da buga ƙofar ya tsaya cak sai ma iskar da take kaɗawa. Sai kuma ta ji wuf an wuce ta an shige cikin ɗakin amma ba ta ga komai ba, a yanzu kam hatta da ƴaƴan hanjin ta rawa suke yi. Amma ta dake tana haska tsakar gidan babu kowa har ta wurin ƙofar shigowa ma da ke a garƙame, juyawa tayi zata koma ɗakin sai ji tayi garam an rufe ƙofar yayinda wani hannu mai sanyi ya rungume ta ta baya. So take yi ta kira sunan Allah amma kuma ta gaza don ji tayi harshen ya mata nauyi kamar an zarge mata shi, a take ta fice hayyaci n ta ta gaza gane da rai ko akasin haka take tana jin wata murya mai cike da razani tana ƙwalla kiran ''Nana'' yana bada amo cikin iskar sanyin garin.
Ta daɗe a wannan yanayin na tsakanin rayuwa da mutuwa, sai kuma ta ji an banko ƙofar an buɗe da ƙarfi har yana bige mata fuska. Hira ake yi a bayan ta cikin yaren da bata sani ba balle ta san me ake faɗi, sai shewa ake yi da arerewa har da algaita. Ita dai tana nan kwance ta gaza ɗaki duk da mai rungumar ya sake ta, amma ba ta da ƙarfin miƙewa tsaye balle har ta saita ƙafafun ta ta gudu. To in ma ta fita da gudu ina zata je ne? A tsawon shekaru uku da tayi a unguwar ta Sabuwar Unguwa zata iya cewa ita ɗaya ce cikin shi babu gida sama babu a ƙasa sai can gaban layin su ne ma akwai wani babban gida, bayan nan ko sama da ƙasa babu mahalukin da ke kaiwa da komowa. Ita kam ma zata iya ƙirga adadin mutanen da ke rayuwa a unguwar don duk da ayyukan raya karkara da gwamnati ke yi har yanzu unguwar tasu ba ta cikin wanda mutane ke son rayuwa cikin shi. Duk da suna da wuta amma tsarin wurin da nisan shi zuwa cikin gari ya sanya bai da farin jini, ko mutane sun yi gini ba su dawowa sai dai a bar shi haka nan ba kowa a ciki.........
Ƙarar tsintsiya ne ya katse mata tunanin nata a karo na barkatai a daren nan, shara ake yi bilhaqqi irin na wainda ke yi da ƙarfin nan har kana jin ƙarar kartar siminti. An ɗauki lokaci mai tsayi ana sharar kafin ta ji an fara jan ruwa a rijiyar tsakar gidan, a ka koma wankin gida da ruwan da bata gani sai ƙarar shi take ji sai kuma rabon shi da ta samu a wurin ƙafafun ta da ya kuma daskarar da magudanar jinin jikin ta. Suka gama aka zo aka tsallake ta a wurin aka shige cikin ɗakin tana kuma jiyo wannan hirar da alamu an gama na waje ne an koma ɗaki, bayan mintina hancin ta ya fara jiyo mata ƙamshin turare ya gauraye gidan da wani kalar sauti mai ƙara sosai mai shirin gigita mata kunne. Runtse idanu tayi tana mai jin ina ma ta suma ko zata huta da azabtar luguden tsoro da ƙirjin ta yake yi, amma ta gaza samun cikar burin nata sai ma jin ƙaruwar mutane zuwa cikin ɗakin da take yi an ɗauki lokaci mai tsayi kafin ta ji komai ya tsaya cak buɗe idanun ta tayi a tsorace hasken fitilar ƙwai na haske mata idanu alamun nepa aka dawo. Wanda yayi daidai da tsayuwar mashin a ƙofar gidan da ƙarar makulli jikin ƙofar ana buɗewa.
Khalid ne ya dawo daga shago, shigowa yayi da sallama yana tura mashin ɗin shi sai ya tsaya turus ganin ta yashe tsakar gida ga wayarta a gefe sai ƙofa da ke buɗe wanwar. Da sauri ya tsayar da mashin ɗin yana zuwa gabanta ya ɗago ta yana salati
''Nana, Lafiya?".
Ya tambaya cike da kulawa, ji tayi ta mance duk wani abu da ya faru tsawon awa guda da fitowar ta ɗakin zuwa faɗuwar ta da sautin da aka kunna. Sake maimaita tambayar shi yayi, da sauri ta buɗe idanun ta tana cewa '' Faɗuwa nayi''.
''Na gan ki ai me ya faru?".
''Da na rufe gidan ne zan shiga ɗaki na faɗi a nan wajen'' ta amsa cikin ficewar hayyaci don ita kan ta bata san me take faɗi ba sai ji tayi yace '' Subhanallah, ba ki bige wani wurin ba dai ko?" Ya tambaya yana taɓa jikin ta. Ji tayi hawaye ya toshe mata maƙogwaro amma ta haɗiye ta miƙe zaune, taya ta yayi ta miƙe suka shiga cikin ɗaki. Sai da ya zaunar da ita kan kujerar da take jin kamar akan wuta ta zauna saboda tsabar fargabar ko ta zauna kusa da wani. Tana jin shi ya fita ya rufe gidan ya shigo da mashin ɗin shi ya dawo ɗakin amma har lokacin idanun ta a runtse saboda tsoron kar tayi tozali da abinda bata san ko miye ba..........