Vllogers Visit
by @zahrabmrs
Tadala ta yi shuru, kalaman Farida sun daki zuciyarta ba karya Ta fara hango ta sanadin Alhaji Kamal, burinta na canza rayuwar iyayenta dake cikin talauci na daf da cika, muddin zata iya jure dumi da zafin soyayyar tasa ta ɓoye...
maitama……
Zaheera ta juyo ta kalli ɗan uwanta bayan sun keba a private lounge dinsa ,Ashe ma wacce kake so a cikin gidanka take Kamal? Gaskiya ka ɗauko mana babban tashin hankali Yanzu ya kake tunanin Sadiya zata ji idan taji labarin cewa cousin ɗinta ta jini kake son aura?
Kamal ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, Haƙuri zata yi Zaheera ,Nima fa ba yin kaina ba ne ,Allah ne ya jarrabe ni da son yarinyar nan, kuma ba ni da yadda zan yi
Zaheera ta zuba masa ido, Ita yarinyar ta yarda da kai ne?
Kamal ya ɗa saki murmushi tuni wayon da yiwa tadala jiya ,Nan take ya labarta wa Zaheera duka irin wayon da ya yi wa Tadala na wannan yarjejeniya ta watan shida (Pinky Promise)
Zaheera ta girgiza kanta tana dariya, Allah ya shirye ka Kamal Nasan Kyawunta ne kawai ya ruɗe ka
Wallahi a'a, Zaheera ,Kamal ya katse ta da sauri Mata nawa na gani masu kyau a rayuwata? No doubt, she is very beautiful, amma wallahi sonta nake yi
Zaheera ta dafe kafaɗarsa, na ji Kamal Na yarda sonta kake yi... wannan shi ne karo na ɗari da kake faɗa mini hakan tun ɗazu,Allah ya tabbatar da alheri. Daga nan suka cigaba da hirar data shafi rayuwarsu da business
Bayan Sun tashi lectures Farida ta matsa wa Tadala lallai sai ta kawo ta gida dan so take taje ta kashe kwarkwatar Idonta a gidan gidadon katsina .Haka kuwa aka yi, suka iso kofar gate din ganin bakuwar mota masu gadin gidan suka ji budewa ,Farida ta bude glass din motar ganin Tadala yasa suka bude inda suka gaisa as usual
Gaba ɗaya jikin Farida rawa yake yau gata a gidan shahararren biloniyaren Gidadon Katsina.
Kai tsaye part din Anty sadiya suka Nufa Tadala ta kira sadiyar a waya ta shaida mata cewa tana falo tare da ƙawarta
Lokacin da Sadiya ta fito daga ɗaki, fuskarta a ɗan yatsine take kamar ba zata saki rai ba Amma tana hada idanu da Farida—ta ganta mace yar gayu mai aji nan take ta saki jiki, fuskarta ta washe .
Bayan Sun gaisa Farida ba ta ɓata lokaci ba, ta kalli Sadiya ta ce, Tadala, gaskiya kaf cikin matan Gidadon Katsina, babu wacce ta kai Anty sadiya kyau Masha Allah wani Farin ciki ne ya ratsa zuciyar sadiya ,twins suka shigo falon da sallama sadiya ta kalli safa ,maza kije kawowa farida snacks kisa bintalo ta shirya mata lunch a dining ,kasake safa tayi Cike da mamakin mamin nasu ,Yaushe Tadala ta samu matsayin da zaa karrrama kawarta haka ?
Farida ta ƙara matsowa cikin hira,Amma Mami ba a fiye ganinki sosai tare da Yallabai a kafafen sada zumunta ba ,Sadiya ta gyara zaman mayafinta cikin takama, "Eh wallahi... da yake ni ba son harkar social media nake ba ,hoton ma ba wani sonsu nake ba
Nan da nan Farida ta zage ta dinga kwarara sadiya yabo with steez ,Wannan ya sanya ta sami shiga har a wajen su 'yan biyu dake zaune a falon, suna jin daɗin yadda ƙawar Tadala ke ta zuba yabo ga mahaifiyarsu ,ruwa da samosa kawai farida tace ta koshi ,Lokacin da ta tashi tafiya Sadiya ta kalle ta cikin faram-faram tace, Bani lambar Opay ɗinki, Farida.
Tana turawa, ba jimawa sai ga alert (credit alert) na Miliyan Ɗaya (₦1,000,000) ya shigo wayar Farida Duk da Farida ta saba riƙe manyan kuɗi saboda harkar daren ta, ganin wannan kyautar ta farat ɗaya ya sanya ta hau yabon Sadiya fiye da dā
Tuni ta zaro wayarta ta kunna kyamara "Jama'a! Yau an mini kyautar ban mamaki a gidan Gidadon Katsina!l Wato wajen Hajiya Sadiya Mami, amaryar gidan kuma shalelen mijinta! Jama'a, Hajiya Sadiya ta wuce duk yadda kuke tunani... takawar ki lafiya, fara fitilar gidan Gidado makiyan ki fadawan ki hajiya sadiya ,Nan take ta danna post a page dinta na TikTok
Marwa tadala kura mata ido ta ce, Kamar ina yawan ganinki a TikTok?
Farida ta fari da idanu tana dariya, Eh, nice... Farida Gayu
Suna bincikawa a wayoyinsu, suka ga ashe tana da mabiya (followers) har dubu ɗari takwas (800K Followers) a TikTok,Nan take idanun matan gidan suka ƙara buɗewa a kan Farida...suka danna mata follow suka yi sallama harda cewa ta kara dawowa ta masu yini
daga haka tadala taja farida zuwa dakinta
sabida baki da gata ke dakin naki ma a a kasa yake kenan ?tadala tayi murmushi tace ni kam ko a jikina so suke a dole sai an gane ni ba yar gida bace ,farida tace zan miki transfer din 500k ,kinga yadda kissata tasa cousin dinki tura min 1M ko?
kai farida lamarin ki ay ya bani mamaki yau anty sadiya baza ta iya bacci ba ,amma da kin bar kudin ki ,bana son haka tadala dole kema ki ci arziki ,amma tadala gidan nan ya hadu matuka ,Yau na Kara ganin capacityn Gidadon Katsina a zahiri ,har gate ta raka farida sai taga fitar sannan ta juyo .
kowa ya hallara a falo bayan an gama dinner , Safa kunna bidiyon da Farida ta ɗora page dinta muryar farida ta fito radau Jama'a! Yau an mini kyautar ban mamaki a gidan Gidadon Katsina! Wato wajen Hajiya Sadiya Mami, amaryar gidan kuma shalelen mijinta! Jama'a, Hajiya Sadiya ta wuce duk yadda kuke tunani... takawar ki lafiya, fara fitilar gidan Gidado
Yan biyu suka saki shewa harda tafa hannu. Marwa ta kalli Safa ta ce, maganarta gaskiya ce Mami ita ce ainihin fara fitilar gidan nan farar mace alkayabbar mata
keep your noise down girls cikin bazata suka ji muryar falmata ,kusa airpod kun dame mutane
aa maman kuna kar mu fara haka dake ,Kefa har fa wakoki kala kala ake miki a social media dan yau daya nima an yabe ni zaki ce an dame ki?duk sanda aka miki sabuwar waka ranar yini ake jinta dan su zahra kure volume suke kuma ba wanda ya taba magana sai ke ?wani kallo falmata tayiwa sadiya
I don’t have time for petty talks excuse me ta dauki wayarta ta haye sama
Har daki yan biyun suka bi sadiya tsegumi
Mami yau kin tabo momy dama tana fushi?gaskia dole ki biya ko nawa ne ali jita ya miki waka muga yadda zatayi sadiya tayi murmushi ay yau tadala ta sani cikin farinciki dole ma gobe na bata kwancen abayas dina sanadinta yau naga fushin falmata ku nema min number ali jita
A yau juyon kwanan Falmata ne a tsarin gidan Alhaji Kamal ,Kamar yadda yake a ƙa'ida ta matan gidan, dukan wacce ke da kwana ita ce ke binnsa har c ɗakin baccinsa (master bedroom). Falmata tafe take cikin sanyin jiki, ƙamshin kabbasar nan tata dake tashi a jikinta a kullum yana biye da ita. Hannunta ɗauke da kofin shayin coffee da Alhaji Kamal ya saba sha a kowane dare kafin ya kwanta.
Sai dai duk da ƙamshin da kwalliyar da ta yi, fuskarta babu farin ciki ko kadan
Ta ajiye kofin shayin a kan teburin gefen gado, Alhaji Kamal dake jingine da gadon ya kalle ta, ya fahimci yanayinta nan take. Ya aka yi ne, Madam? Wa ya taɓa mini ke da daddaren nan? ya tambaya cikin muryarsa mai natsuwa.
Falmata ta saki wani uban tsaki, Wacece kuwa idan ba amaryar ka ba Sadiya Imagine fa, wai don ƙawarta ta zo gida take ƙoƙarin faɗa mini baƙar magana da nuna min iko a gidan nan...I hate nonsense
Alhaji Kamal ya ɗan daure fuska, ya katse ta cikin rashin son hayaniya Menene abun baƙar magana a abinda Sadiya ta faɗa don Allah? Kamar yadda kika sani, ba na son tashin hankali a gidan nan Kar ki fara abin da ba halinki ba ne, Falmata I respect you alot kin sani
Ranta ya ƙara ɓaci ,Ba ta ce uffan ba ta juyo da flask din shayin ta tsiya masa a kofi, sannan ta juya masa baya ta haye gadon ta kwanta abinta, ta ja bargo ta rufe jikinta.
Alhaji Kamal ya sha shayin kaɗan, ya nufi toilet ya Kara brush sannan ya matso kusa da ita da niyyar taɓa jikinta domin ya sami abin da yake buƙata,tana jin hannunsa, ta ɗan matsar da hannun nasa da sauri
"I'm not in the mood, please! Tunda dama Sadiya ba ta da laifi a gurin ka ta faɗa cikin tsiwa tare da ƙara gyara kwanciyarta
dare ya yi, rayuwar Farida ta sauya baki ɗaya daga ta ɗalibar jami'ar Base University zuwa striper , ta nufi kulob dinsu dake tsakiyar birnin Abuja, inda da waɗanda suka amsa sunansu a gari ke taruwa.
Tana shiga ɓangaren bayan fage na musamman (backstage), ta cire doguwar rigar jikinta, ta canza zuwa (sexy lingerie) da suka siyo tare da tadala ,Daga nan ta ɗauko wani takunkumin fuska ta sanya. Takunkumin ya rufe mata fuskarta gaba ɗaya, sassan ramin idanunta kawai da tattausan laɓɓanta dake ɗauke da jan baki mai ɗaukar hankali ake iya gani.
Ta fito zuwa tsakiyar fagen rawar inda fitilu masu kaloli daban-daban ke haskawa. ta nufi daidai ƙarfen dake tsaye a tsakiyar fagen (the pole), ta sarƙafe ƙafafunta da hannayenta ta soma juyawa cikin wani salo mai sanya jikin namiji rawa. Kowa a kulob ɗin ya maida hankalinsa kanta, ana ihu tare da kwararo maƙudan kuɗi.
Sai dai duk da kida da kudin dake yawo, hankalin Farida a tashe yake Tun ranar da ta bi wancan baƙon mutumin (the stranger) zuwa gidansa, inda suka fuskanci juna cikin fage na shauƙi, ba ta sake gani sa ba ko Wannan rashin ganin nasa ya rinka sanya mata fargaba , domin ya tafi da babban sashi na tunaninta.
Tana cikin rawa a kan ƙarfen tana juyawa cikin kasala, ta ɗaga idanunta ta kalli can ɓangaren VIP dake sama. Caraf! Suka haɗa ido da idanunsa masu cike da kwarjini da iko, yana zaune sanye da baƙar riga yana kallonta cikin natsuwa Wani dadi ya ratsa Farida, ba ta san sanda ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta farin ciki a ɓoye ba. Yana nan, bai mance da ita ba ta ayyana a ranta
Ganinsa yasa Ta ƙara nuna kwarewarta a kan ƙarfen har sai da lokacin rawar ya ƙare, aka soma watsewa daga kulob ɗin ya rage daga ita sai ma'aikata kaɗan
Farida ta sauko tana sauke numfashi, tana shirin wucewa ɓangaren canza kaya, ta ji takun takalmansa a bayanta. Ta juyo a hankali Ya matso kusa da ita sosai har tana iya jakar ƙamshin turarensa wanda ke sanya jiki kasala. Cikin muryarsa mai zurfi, kaushi, da daɗin saurare (husky voice), ya duba laɓɓanta na tsawon daƙiƙa guda kafin ya furta Follow me."
Jiki na rawa farida ta tattaro kayanta ta bi bayansa ,suna tafe bace mata Kala ba ,sai satar kallonsa take har suka karaso gidan ,A karo na ƙarshe da suka haɗu, Farida ba ta kwana a gidan ba suna gamawa ya sa direbansa ya mayar da ita gida
let me handle you for today please farida ta fada cikin shagwaba,kallonta yayi tare daga mata kai alamun ya bata go ahead daga nan farida tayi anfani da duk wata kwarewa tata Wajan gamsar dashi Wanda kuma taga alamun gamsuwar a fuskar sa 💯
, bayan sun gama fagen shauƙin nasu , Farida ta miƙe ta soma ƙoƙarin shirya kayanta da niyyar tafiya gida kamar yadda ta saba, bata zato ta ji muryarsa
"Spend the night. Kawai abin da ya ce mata kenan cikin muryar umarni sannan ya juya kai tsaye ya shiga cikin banɗaki domin wanke jikinsa. Farida ta tsaya cike da mamaki da kuma wani irin daɗi a ranta. Ba ta ɓata lokaci ba ta bi bayansa
Bayan sun sake yin wanka suka fito cikin ɗakin baccin, Farida ta kalle shi cikin shagwaba ta ce, Ba ni da kayan bacci a nan.Kallon ta kawai ya yi ba tare da ya ce uffan ba, ya nufi (walk-in closet), ya ɗauko mata sababbin boxers da singlet ya mika mata.
Ya kamata na san sunanka ko?
"Does it matter?" ya tambaye ta cikin sanyin murya ba tare da ya nuna wata damuwa ba.
"Yeah, it does... plssss, ta faɗa tana langwabar da kanta.
A hankali ya kalle ta, ya nisa sannan ya furta Nawaf
Nice name... sunan ya dace da kai sosai,Farida ta faɗa tana murmushi. Ni kuma sunana...
Kafin ta ƙarasa faɗin sunanta, Nawaf ya cafe ta hanyar furta,Farida Abubakar ,na sani
mamaki ne ya kama Farida, jikinta ya ɗan yi sanyi Ta zuba masa ido tana tunani babu fa wanda ya san sunanta na gskia Farida a fadinnkulob ɗin nan, kowa a can ya san ta da sunan Pinky, kuma a kullum tana sanye da takunkumin fuska (mask) idan tana harka
waye nawaf ?ya akayi yasan sunan ta har na babanta