ƘARFE ƊAYA BA YA AMO

8

by @gureenjoh

ƘARFE ƊAYA BA YA AMO


✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN 

(GUREENJOH)


@Gureenjo on Arewapen

@Gureenjoh6763 on Wattpad 


ADABI WRITERS ASSOCIATION


TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne. 


GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.




*BAABI NA TAKWAS*


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun..."

Ammar da Imam suka faɗa suna balle murfin motar suka fito da hanzari, hill ɗinta ta sa ta take masa kafa sai da ta fasa ya saki karar azaba ta tsinka mishi mari tana furta.


"Kai wani irin dakiki ne kana tafiya baka kallon hanya? Ka san Allah yau sai ka gwamnaci kida da karatu tunda ka taɓo DIVA..." Cikin wani kalar murya take magana da ya ƙarasa kaɗa 'yar hanjin shi, ko kan yayi wani motsi ko ɗaya daga cikinsu ya farga suka ji ƙarar ƙarfe....

WUƘA ta zaro tana ƙoƙarin kai mishi yanka ta ji an riƙe hannun, wani irin riƙo da za ta iya cewa ta ji Ƙashin wurin ya motsa.


Tana Juyowa don ganin mai wannan zarrar ta ji sauƙar wani mahaukacin mari da ya sa tayi taga taga gyalen kanta na suncewa gashinta ya zuba a fuskarta, hannun da ya sake murdewa ya Buge wuƙar ƙasa ya ɗora kafarsa kai, ita kuma hannun ta kai kan fuskarta ta riƙe tana kokarin dawo da kanta duniyar mutane.


Ita wani zai yi wa wannan mari?

Ita aka mara a yau? 

Lallai duk garin Kano babu zaman lafiya, wani irin ɗagowa ta yi Bakinta gefe ya fitar da jini haka idanunta gefen marin ya yi ja.


Idanunsu suka sarƙe yana kallonta cikin wani irin fushi da bai taɓa sani yana da shi ba, sossai ya ji ciwon marin da ta yi wa Malam Bala da zai iya cewa idan bai yi shekaru daidai da su Abba ba kaɗan ne za su fi shi, dattijo mai kirki da kawaici wai wata 'yar kwalta har ta samu zarrar marinshi a karkashinsa? 

A haka ma Allah yake ta ambato don da sai ya ɓallata, wani irin tafasa ranshi ke yi har tsokar jikinshi na rawa don ranshi ya kai makura wurin ɓaci kuma shaidan na ƙoƙarin taking over, bai taɓa duka ba don duk kannenshi presence ɗinshi kawai kan saka su natsuwa bare ya ɗaga idanu ya kalli mutum.


Muryarsa da bai iya ɗagawa har chan ba a yanzu sai yayi ƙasa saboda bacin rai, duk su Ammar sun daskare ya kara matsawa, sai ta zama wata 'yar baby a gabansa, bata taɓa jin abin da ya girgiza zuciyarta ba irin idanunsa masu dauke da fushi da bacin rai.


"Ashe bayan dabancin ke ɗin mahaukaciya ce? Kai ko mahaukaci ba zai kalli furfurar bawan Allahn nan ya tsinka masa mari ba, ko bai yi jika da ke ba ya haifi ire-irenki dayawa..."


Yadda take kallonshi da idanunta waje kaman har lokacin bata fita daga kaɗuwa ba ga shi mutane sun fara taruwa ya ɗauke idanu daga kanta ya ce har lokacin wani kyama, haushi da tsanarta ke sake building a ransa.


"Nasiha ne zan miki ba tare da kin roƙa ba idan kin ɗauka ruwanki, kina yawo da jahilci da rashin wayo a dole ke kin waye. Bari ki ji Allah babu ruwanshi da wannan dole ne kowani matashi ya san addininsa, me addininsa ya koya masa? Menene dalilin halittarsa? Wallahi da addini ne ake gamuwa da Allah ba wannan haukar banzar ta dabancin da kika ɗora wa kanki ba, da a ce za ki fita wannan haukar a kasheki sai kin gayawa Allah dalilin fitarki da kuma dalilin kisanki, kuma sai kin faɗi akan me kika mutu a sannan ne Allah zai kalli abin da zai miki hisabi a kai, idan mutuwarki ta Allah ce ko ta Manzon Allah ko wurin kare hakkin addininki to Allah zai tambayeki kuma zai miki shari'a amma idan kika mutu kan wannan fa? Kina tunanin za ki tsira daga azabarsa?"


Da yatsa ya nuna ta, Muryarsa na sake zama deep don haka yake idan yana ɓacin rai da wuya ka ji ma Muryar na fita.

"Duk sai Allah ya tambayi me kike yi ki ci abinci da nemawa kai tufafi, zalunci ne? Sata ne? Fashi ne? Duk sai kin yi wa Allah bayani, baki isa ki ce za ki zo duniya ki daka tsalle ki zagi uban kowa ki zalunci wanda kika ga dama ki kwana lafiya kuma ki ce za ki shiga lahira lafiya ba wane ke."


"Wallahil azeem ba ki da wani abu mafi munin tarnaki a rayuwa kaman laifukan da kike aikatawa, Allah ya ce in da kun yi imani kun kiyaye dokokin Allah da mun kankare musu laifukansu kuma da mun shigar da su gidajen Al'janna na ni'ima. Imani na tsoron Allah imani na bin dokokin Allah...ko duk don saboda samun duniya ne kike wannan haukar?

Kina ganin in kin bi Allah ba za ki samu duniyar ba ne? ubangiji ya ba wa waenda ma basu bi shi ba bare ke da kika amsa sunan musulma? Kalmar Mutuwa kaɗai Aya ce mai girma!"


Tsaki ya ja, ya juya ya kama Malam Bala da har lokacin jikinshi na rawa ya buɗe bayan mota ya sanyashi, ya kalli Ammar cikin kaushin murya ya ce 

"Drive"

Da sauri Ammar ya shiga mazaunin driver imamu ya zaga da sauri ya buɗe mishi mota ya shiga ya rufe kan shima ya shiga Ammar ya ja suka barta kafe a wurin har lokacin kamar wacce aka dasa.


Hannayenta ta dunkule da ƙarfin gaske, wani zafi ya ziyarce ta a wanda ya murɗe ɗin ta runtse ido da karfin gaske wani irin tafasa da bata taɓa ji ba zuciyarta ke yi, idanunta sun rine kwarai da gaske ga shi bata iya kuka ba, wani irin rawa jikinta ya ɗauka numfashinta na fita da ƙarfi da ƙarfi, cikin wani irin sauri ta je ta shiga motar ta ja da karfin gaske ko kallon gabanta bata yi tayi gida.


Wani irin Horn da take dannawa da karfin gaske shi ya fito da mai gadin su da gudu kan ya buɗe ta sauƙa ta turo karamin kyauren da sauri, daka tsalle yayi amma ganin bata kula shi ba sai wani huci da take kanta babu dankwali iska na kaɗa gashin kanta tamkar sabon shigar kamun hauka tayi hanyar parlor, akwai Matasa masu ɗan dama a tsakar gidan yadda suka kalleta ya sa duk suka mimmike tsaye suna bin bayanta da kallo, babu wanda zai ce ya taɓa ganinta haka kowa ya rasa abin cewa.


Jagaban na zaune kawai ya ga shigarta a haka tamkar wacce aka jefo daga sama, da sauri ya tashi ya tare ta don ta nufi ɗakinta ne.


"Ke! Sohana!! Menene?? Me haka? Wa ya taɓa ki?"

Wani irin jan numfashi tayi tana ƙoƙarin zagaye shi ta wuce ya sake tare ta yana ɗago fuskarta.

"Sohana me ya sameki? Ke da wa?" Idanun da ya sauƙe kan fuskarta ya sa ya zabura yana sake riƙota, Jagaban namijin gaske ne Dukda shekaru sun ja amma tsaye yake kyamm ga tsawo ga ƙira, bashi da imani bai san haƙuri a dukkan lamarinsa ba bare abin da ya shafi ɗiyarshi da duk duniya babu abu da yake ji da shi kamarta...

Muryarshi ta sake kaurara 

"Mari? Uban wa ya mareki haka? Wa ya mareki???"

Da wani irin tsawa ya ƙarasa maganar daidai shigowan yaranta, tambayar kuma ya motsa mata irin kalaman bakinsa da suka fi marin zafi a zuciyarta.


Bata san ta yi wani irin ihu ba tana kokawa da numfashi, rungumeta jagaban yayi ta sake sakin ihu tana kuka irin mai jijjiga haɗe da ihu.

Daga shi har yaran hankalinsu ya ɗaga, basu taɓa ganinta haka ba, janta yayi ɗaki amma suna jin Muryar ihu da kukanta daga inda suke jikinsu na tsuma.


Da Jagaban ya ga ba zai iya jurewa ba ya haɗa wata allurar bugarwa ya yi mata da kanshi daga haka ta faɗi sai bacci.


Waje ya fito suka yi cirko cirko.


"Mari??"

Ya faɗa yana kai kawo cikin parlorn hannayensa dunkule idanunsa jajazir.


Skipo ya ce 

"Na rantse da Assamadu yau Kano babu zaman lafiya an taɓa DIVA?? Wallahi babu mai bacci cikin daaɗin rai daga yanzu har gobe"


"Faɗa ma ɓata baki ne ai Skipo...aiki da cikawa ya kamata a gani mu jeeee"

Pablo yayi maganan yana zaro addarshi Tuni su Bravo sun fice sun yi kira, Jagaban bai hana su ba, don shi nashi ba a kan jama'ar gari ba ne ya tabbatar duk wanda ya iya ɗaga hannu ya mari Sohana har ta yi irin wannan kukan to ba ƙarami ba ne, faɗar su su biyu ne kuma ko waye yayi alkawari sai ya cire hannun, shi da marin wani halitta kuma har Abada..


Kaman yadda su Pablo suka yi alkawari, ƙira kawai suka dinga yi suna sanar da an taɓa DIVA a take gungun 'yan daba suka haɗu tun daga unguwar suka fara kan mai uwa da wabi suna shara... Har arear kasuwa da abin ya faru sai rufe kasuwa aka yi lokacin tashi bai yi ba.


Tashin hankalin da ya janyo dole polisawa suka kama fiye da rabinsu ciki har da su Pabloo don su ne gaba gaba, gari gabaɗaya ya rikice.

Shaly ce kawai da Skipo ne ba'a kama ba amma an kama Obo, Pabloo da kuma Zee, Zubash tana chan asibiti bata san me ke going ba.


***


A lokacin Shehi na zaune a reception na kyakyawar private hospital da ya sa Ammar kawo Malam Bala don duba kafarsa da ke ta jini, tapping kafarsa ɗaya yake a ƙasa yana ambaton Allah amma har lokacin zuciyarsa ta kasa sanyi.


Bai yi wa kowa magana ba su Ammar ma duk cikin sanyin jiki suke tsaitsaye, kowa ya san Shehi kallo daya za ka mishi ka san an kai shi makura a yau.


Abiey Ammar ya ƙira ya sanar mishi abin da ke faruwa anan Abiey ɗin ke sanar da shi shima yanzu ya fito daga office kenan za shi gida yanzu haka 'yan daba sun tsatsare hanyoyi suna ta barna.

Da sauri Ammar ya kalli Shehi, sai ya ce 

"Abiey yanzu kuna ina? Babu abin da ya same ku?"


"Mun samu dai mun fita babu abin da ya same mu, akwai hukumomi a wurin Dukda su ma abin ya fi karfinsu ashe ku kam har da illata Malam Bala suka yi?"


"Toh Alhamdulillah, da sauƙi shima dressing ne yanzu za mu taho gidan gabaɗaya ba sai kun zo ba"


"Toh Allah ya kiyaye gaba a cigaba da kula Ammar, Allah ya kawo ku lafiya ya tsare mana imaninmu ya shirya mana yaranmu"

Ya amsa da Ameen kan ya katse ƙiran ya kalli Shehi.


"Irshad!"

Idanunsa da suke lumshe ya buɗe har lokacin a rine.


"Ka kuwa san abin da action ɗin ka ya haifar?"

Bakinsa ya ɗan taune bai ce komai ba.


Ammar ya buɗe wayarsa ya shiga Facebook ya miƙa masa videos ne na abin da 'yan daba suka yi yau babu wani shugaba da zai ce yayi maganinsu.


Ransa ya sake ɓaci, wato ma ɓata miyaun bakinsa ya yi ba za ta taɓa chanzawa ba? Meyasa shi da yayi mata bata yi masa ba sai waenda basu ji ba basu gani ba?

Commissioner of police ya ƙira 


"Last time na tura maka hoton yarinyar nan da abin da suke aikawa ban ga ka yi wani hobbasa ba, hasali ma cigaba da yawo ta yi freely yau ta jagoranci mummunar hari irin wannan na zalunci haka za ka bari ta tafi Scott free again?"


Commissioner da ba zai so shiga bad list na Shehi ba don ya san ja da shi ba daaɗi ya ce 

"Wannan karo ba ita ba ce! Amma ina maka albishir da cewa mun samu nasarar kama yaran kuma za mu gurfanar da su gaban court cikin gaggawa don a yanke musu hukunci daidai da abin da suka aikata"


Ɗan shiru Shehi yayi kan ya ce

"Zan cigaba da bibiyar wannan case har sai na ga ka yi abin da ka ce ɗin, ka kula da gaskiya a kan aikinka ka sani duk abin da ka yi Allah na nan yana kallo mala'iku suna rubutawa sai an tambayeka ranar gobe"

Yana kai nan ya katse wayan tare da damketa a hannunsa da ƙarfi kaman ita ce ta masa laifi.


Daidai nan Malam Bala ya fito yana ɗingisa ƙafa, Imam ya riƙe shi suka yi mota yana yi wa Shehi godiya.


Sai da suka zauna Ammar na driving Irshad ya ce

"Malam Bala ina roƙon ka da ka yi haƙuri da abin da ya faru, ka yafemin"


"Baka yi min komai ba Shehi, ita ma da tayi ina mata Fatan shiriya da samun rabauta don tabbas ina mata tsoron mutuwa a haka"

Shehi bai sake cewa komai ba suna isa gida kuma suka samu duk ahalin gidan a waje ana jiran isowarsu shi kam sannu da gida kawai ya musu ya wuce sashenshi don ko a ƙalau ma bashi da wani abin mayar da magana bare har lokacin yana jin zuciyarshi na zafi, idanunshi na hasko mishi marin da ta sauƙe wa malam bala haƙiƙa ya ji zafin marin nan wane Abbiey ɗinshi aka mara, ya san darajar mutum ya san darajar duk wani dake zagaye da shi.


Ammar ne da Imam suka basu labarin abin da ke faruwa lamarin ya girgiza su har wasu na cewa a nuna musu wannan mai tsaurin idon su ganta, saboda riƙe waya a gidan sai ka yi aure ya sa duk ba media suke ba basu wani san Diva ba, tuni Ammar ya nemo ta a media ya shiga nuna musu don su Abba sun wuce sashukansu bayan gama tattaunawa don shirin alwala tunda Magrib ya gabato.


"Wannan za ta aikata abin da ya fi haka ma na sha jin labarinta, ashe ita ce DIVA?"

Sumayya ɗiyar Goggo hindatu ta faɗa.


Kanwar Ammar da suke uwa daya uba daya hawwa ta ce

"Allah kar ya kawo abin da zai hada mu da wannan don kam abin neman tsari ce kaman yadda za mu nemi tsari da shaidan haka za mu nemi tsari da ita"


Ƙanwar Shehi da suke uwa daya Mufeeda ta ce 

"Ki ga fa irin wukar da ke hannunta, ga gardawan da suke take mata baya?"


"Amma tana da kyau"

Cewar mai bi ma Sumayya Aisha.


"Kyaun banza babu kyaun hali?"

Cewar sumayya.


"Kai ya isa haka ku ba ni wayata"

Ammar ya faɗa yana kwace wayarsa duk suka watse shima yayi sashen da yake.


****


Ta ɓangaren Diva sai ɗaya na dare ta farka, ko da ta farka bata ji zafin zuciyarta ya ragu ba, kalamanshi ke dawo mata. Haka kuma ta kasa motsa hannun da ya murɗen don babu tantama ta samu gocewar kashi ko ma kariya kuma yayi tsami daga jin alamu tunda ba yau ne karon farko ba ta kan goce a ƙashi garin faɗa.


Ita ce ɓarauniya? 

Ita ce 'yar fashi?

Ita ce Mahaukaciya?

Ita ce azzaluma?

Ita ce dabba marar hankali...

Ita ce...!


Janyo bedside lamb tayi ta buga da gini da ƙarfin gaske tana ihu, Jagaban da yake gadin farkawarta ya shiga da sauri ya riƙeta.


"Baaba an ci mutuncina irin wanda ba'a taɓa ba a garin nan"

Ta faɗa tana taune hakorinta, idanunta jajazir amma babu digon hawaye don ta gama mishi kuka kuma.


"Waye ne? Faɗa min sunansa kawai...!"


"Ban sanshi ba! Ban taɓa ganinsa ba amma na rantse da Allah sai na ɗauki fansa mai muni a kansa, sai na bincikosa duk inda ya shiga a birnin Kano na nuna masa haukar da yake ambata a kaina, zan nuna masa jahilcin da ya dangantani da shi, zan nuna masa zaluncin da yake ambata da bakinsa...."