08
by @sadisakhna
👑 *JODA* 👑_____
Na
*Sadi-sakhna*
Ƴar mutan Jama'are
THE TRIO OF TALES
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey)
@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp
LITTAFI NA 1
*Harƙa ta (8)*👑
Ko sunan ta bata tambaye ta ba,tamkar dai dabbar data ɗauketa a farkon, tunda tanada sunaye da dama irinsu dabba,tunkiya,da baiwa shikenan ya wadatar.
“Ayyah Joda nah ko kina ina? Allah bakya cikin ha'ula'in dana ke ciki,Allah ya tsaremin gabanki da bayanki ƴa ta,kinada zuciya mai kyau Allah ya hana azzalumai cin galaba akanki”
Bayan ta gama addu’ar hawayen idonta ta goge kafin ta nufi hanyar da Jakadiya ta nuna mata,bata sha wahalar zuwa sansanin bayin ba,domin wasu ayarin bayi da samu suna komawa itama tabi bayansu har zuwa wajen.
Yana kama da inda suka baro amma yafi wancan girma da tarin bayi maza da mata,wasu yarane,wasu mata da mijine,wasu iyayene,wasu abokaine dadai sauransu.
Inda wasu mata da bazasu wuce sa'anninta ba ta nufa,suna zaune a ƙasan wata bishiya suna ta shewa duk da yamma ta kusa,da alama wannan ɗin shine ɗan ƙaramin lokacin da suke dashi wanda zasu haɗu su yi raha kuma su tattauna matsalolinsu.
Sallama tayi musu wasu daga cikinsu suka amsa,ganinta da wani kaya daban sun san baƙuwace zuwanta kenan. Kallon banza dayawa daga cikinsu suka bita dashi. Sai kaɗanne suka amsa mata. Wato shi ɗan adam wani yayi maka ne kaima kayiwa wani,banda haka duk kuna bayi menene na ɗagawa.
Bata yi zuciya ba ganin wasu daga cikinsu sun amsa yasa ta ɗora bukatatarta garesu na dalilin yin sallamar.
“Bayin Allah tambaya nakeyi….”
“To saikin saka kalmar bayi tukunna,faɗin kanki tsaye mana,wannan kalma wlh har na tsani jinta a rayuwata”
Wacce ta amsa mata Sallamar ne tabata wannan amsar,bataga laifinta ba,don ko ita kanta ƙiranta tunkiya da dabba a gaban idonta da akayi abun ya mata zafi a zuciya,saidai hakan bazaisa tasakashi a ranta ba,domin idan da sabo ta saba.
“Uhm dama ina tambayar inda zan samu uwar bayine an turoni wajenta”
“Tafita cikin gari taron da akeyi,zasu kulada bayin da aka kai wajen,kije ki jirata saita dawo”
Tana gama faɗin hakan tacigaba da jin hirar da akeyi,Aminatou ganin bazasu sake kulata ba,yasa ta kama wata hanyar tabi, wani lungu tafiyar ta kaita bakin ɗakunan wasu a gefe da gefe,ajiye kullin kayanta tayi ta zauna akai tana kallon ƙasa,gabaɗaya abin duniya ya isheta ga yunwa da kishirwa da suke cin cikinta.
Wani tausayin yarinyar ne taji yakamata,Fasihmman da ita tasan wacce kalar rayuwace take jiranta a gaba,sai taji ta lokaci guda kamar ƴar ta ce.
Ƙaramin hannu taga ya miƙo mata busashshiyar gurasa,wanda baxai wuce hannun Joda nta ba,ɗagowa tayi domin taga mamallakin hannun,yarinya ce tanada haske amma dauɗa da wuya sunsa takoma baƙar dole. Ganin Aminatou ta tsaya tana kallonta batareda ta karbi abin hannunata ba yasa tasake miƙa mata sannan tace.
“Ki karba ummah tace ta gutsiramiki tace na kawo miki,domin da alama ke baƙuwace yanzu kikazo,kuma an daɗe da gama rabon abincin yau”
Karba Aminatou tayi tana haɗiyar yawu,karya takeyi idan tace bataji daɗin samun gurasar ba,inda yarinyar ta nuna data ambaci sunan ummannata ta kalla,matace amma tafita a shekaru sosai tana daga cikin ɗan ɗakinnasu dayaji tsummokara tana hangosu. Ido suka haɗa lokaci ɗaya taji matar da kwanta mata a rai,domin ko a fuska batada yanayin mugaye,sannan kuma ga taimakon da tayi mata tun kafin tasan ko ita wacece.
Mayar da kallonta tayi kan yarinyar kafin tasaki ɗan karamin murmushi.
“To ki cewa umannaki nagode sosai kinji?”
“To zan faɗamata”
Har ta juya zata tafi Aminatou ta tsayar da ita tareda jefa mata wata maganar.
“Amma baki faɗamin sunanki ba ƴan mata”
Cemata ƴan matan da tayi yasa tayi murmushi tareda rufe fuska,daga bisani tace “Nuratu” cikin ƙaramar muryarta.
Itama Aminatou murmushin tayi haka kurin taji yarinyar da burgeta.
“Sunanki mai daɗi nima inada yarinya kamarki sunanta Jodah,amma an rabani da ita yau kafin akawoni nan wajen”
Lokaci ɗaya taga yarinyar ta firgice alamun ruɗani yashigeta.
“Suwaye suka ɗauketa,nima za'a zo a rabani da ummah ta?”
Ganin ruɗewar da tayi saitaji dama bata faɗamata ba,ganin Joda bayan tashinta yasa take ganin kaman duk wani yaro dayake sa'anta shima zai fahimta,ta manta ashe tata ɗiyar a yanxu dabance data saura.
“Ahah babu wanda zai rabaki da ummanki,tunda kuna cikin gida a kewaye,saidai karki sake ki fita batareda ummanki ba kinji”
“to ai dama umma tacemin kada nabi yara na fita waje,bazan fita ko ina ba. To umman Joda kizo muje gun ummah ta,tunda naga ba'a baki ɗaki ba tukunna”
Bata Fasih ba ta ɗau kayannata tabi yarinyar,a ranta taga wautar hakan tunda ba uwar ce ta ƙirata ba,kar ta zake dayawa,to amma yazatayi batada inda zata zauna,sannan zamanta haka a filin abune mai matuƙar hatsari.
Baba Mairo taga Nuratu suna tahowa da matar amma bata nuna komai a idonta ba,domin itama ji tayi matar ta bata tausayi.
Saida suka ƙariso taji matar tayi mata sallama,amsawa tayi cikin sakin fuska tareda bata waje a gefenta kan tabarmar Kaba ta zauna.
“Naga abinci nagode Allah yasaka,baki sanni ba amma kika raba abinci dani”
“Ahh bakomai yiwa kaine,kaima wataran sai kaga taimako a inda bakayi zato ba,sannan kanaso ayiwa naka wataran idan yanada buƙata”
“hakane kam amma nagode sosai,nace nabiyo yarinya batareda na nemi izininki ba,dan Allah zan samu wajenda zan zauna kafin wai uwar bayi ta dawo”
“Ah maizai hana kiyi zamanki,idan ma bazaki takura ba zama damu da kince mata kin samu ɗaki,domin gaskiya zata iya kaiki bangaren dabbobi domin muhallinnamu yayi ƙaranci idan aka kamantashi da yawanmu”
“Toshikenan babu damuwa idan tazoɗin zan shaida mata indai kinaga baxan takuraku ba kuma bakida miji to ni yayimin sosai,nagode Allah yabar zumunci”
“Uhmm babu miji,Miji yanzu kam ai zayyi wuya kuma. Tun bayan daya rasu bansake kula wani dasunan aure ba,har kuma gashi jika na samu yafi zaman shuru”
“Nima nawan Allah yakarbi abinsa,ƴata kuma sa'ar nuratu Joda an rabamu yau da safe”
“Innalillahi banji miki daɗi ba,idan da rabo Allah yasake gama fuskokinku”
“ameen ameen kema Allah yakareki daga shiga tarkonsu”
Itama ameen ɗin tace,daganan suka shiga taba ƴar hira kowa yana faɗin abubuwan dayaci karo dasu na rayuwar bauta a gidan sarauta. Nuratu kuma tafita wasa wajen yaran bayi a harabar sansanin nasu.
*** ***
*Jodah*
Bugun hannu naji akan cinyata ana tashina, tashina nayi muka hada ido da ita ina kan mutstsike idon. Wani kallo tayimin babu yabo babu fallasa,kana ta miƙomin wani ƙoƙon.
Saka hannuna nayi na karba,kokone a ciki na hatsi fari soll dashi,karba nayi na ajiye kafin nace.
“Dan Allah idan babu damuwa zanyi sallah tukunna kuma kuskure bakina”,dokin ta gefenta nake hango gari ya waye sosai har rana ta fito.
“Babu damuwa zaki iya yi,amma kiyi da hanzari domin Mai gidan yashirya yace a baki abin karyawa yanzu shima idan yagama zaku wuce.”
To na amsa mata dashi kafin na fito daga cikin ɗakin, ruwa tabani nayi alwala nayi sallah raka'ah biyu tunda asuba ce ta wuceni banyi ba.
Kokon na ɗauka nakai bakina,babu ɗanɗanon zuma a ciki amma haka na shanyeshi tunda ɗauke yake da kamshin sabon hatsi da garɗi. Abinci rahama ne domin lokaci ɗaya naji jikina yayimin ƙarfi sosai.
Fitowa nayi bayan na ɗauko ƙullin kayana nabiyo bayanta zuwa cikin gidan damuka biyo jiya nida baba Yakub.
A tsakar gida muka sameshi saidai ya sauya kayan da muka dawo jiya yana jikinsa,yayi wanka yasaka kaya mai kyau fess dashi kaman bashine na cikin jirgin ruwan ba.
Rusunawa nayi nagaisheshi shida dukka matan gidan kusan su shida amma biyune manya sauran dukka yarane inaga matan ƴaƴansa.
Bin bayansa nayi kaman jela muka fita daga cikin gidan,tunda muka fara tafiya bai cemin komai ba nima banyi masa magana ba,sai waige waige kawai nake ina nazarin duk abinda naci karo dashi akan hanyar.
Wajen wani mutum ya nufa,komai sukayi dai sai gashi sun taho inda nake shida mutumin yana riƙeda doki wanda aka ɗaura masa kurumbo na ɗaukar mutane.
Bayan sun iso kayan hannuna ya karba ya ɗora a ciki nima na nunamin kan na hau,kasa hawa nayi saboda tsayina baikai ba saida ya taimakamin tukunna. Shima biyo bayana yayi ya hau mai Taragon yafara kaɗa dokin zuwa wanda hanyar daban.
Tafiya muka farayi mai ɗan nisan domin har mun fara barin cikin garin mun doshi jeji. Ƙirjina sai tsananta bugu yakeyi,domin babu abinda ban ayyana a cikin raina ba,ciki harda ko sayar dani zasuyi kai.
Bamu sare ba muna tafiya a cikin keken dokin har idanuwana suka fara hangomin wani ginin katanga mai ɗan tsayi,an kewaye ko ina iya ƙofar shiga ɗayace kawai,wasu masu gadi suna tsaron ƙofar,da mutane a bakin ƙofar suna dakon a basu damar shiga.
Mamaki abin yabani da son sanin inane nan wajen da mukazo,ko wani garinne daban yak saidani a cikinsa.
Ina cikin wannan zullumin har muka iso ƙofar shiga wajen,mun ɗan tsaya kaɗan aka gama dana gabanmu kafin aka zo kanmu,wani mutum ne sanye da riga bubu ta maza Kalar shuɗi mai haske,sai kansa akwai tabani kaji hadisi itakuma fara.
Wata takarda ce a hannunsa na hagun na dama kuma yana riƙeda alƙalami na rubutu,bangaren da baba Yakub yake ya zagayo yana tambayrsa suna daga inda yake da kuma mai yazoyi.
Dukka babu wanda bai amsa ba,saida ƙarshe yayi masa tambayar.
“munaso Fasihn wajen wa kazo sannan da ƙarin bayani a gameda yarinyar dake gefenka”
“Nazo wajen Guru Shehul Azhar ne daga Cikin garin Goa,sannan wannan baiwa ce wacce nakawo masa,inada shaidar ganawa dashi.”
Yaƙarisa bayanin yana cire wani karamin dutse mai faɗi anyi masa hatimin dayake zane a babbar ƙofar shiga wajen.
Mutumin yana kallon wannan Hatimi ya dagawa keken dokinmu hannu akan mushiga. Kenan sunan wanda yasayeni Guru Shehul Azhar wannan wanne irin sunane na faɗa a raina.
Muna shiga na saki baki ina kallon wajen, ginin wajen wani iri mai abun mamaki. Babban filine mai matuƙar girma,a tsakiyarsa anyi tsangaya na ɗaukar karatu sunfi goma,kowanne anyi gini rabi ta yanda kana kallon mutum idan yana zaune a rumfar,Cikin an zagaye da Buzun fara damisa masu laushi,sannan rufin kowacce tsangaya anyishi da ganyen bishiyar da kwakwa da giginya. Sannan kowacce tsangaya a wajen an kewayeta da shuke shuke masu kyau,bayi maza da mata sanye da Unifom sunata aiki,wasu suna kai takardu majalisi,wasu naɗaukewa idan an gama ɗaukar karatu,wani nasharewa wasu na kulada Zagayen wajen. Abin gwanin sha'awa da ɗebe kewar ido Fasihmman ga wanda ya tashi ƙishirwar sani na ilimi kamata.
Bansan lokacin dana shagala da kallon wajen ba ina sakin murmushi nikaɗai,har baba Yakub yayimin magana sau uku kan cewar na sauko an iso amma banjishi ba,saida zungureni tukunna na sauƙo ina sunkuyar da ido kaman marar gaskiya.
Da sauri na cigaba dabin bayansa muka shiga wani lungu a cikin ginin dasuke wajen. Wani babban ɗaki muka shiga,kota waje yanada girma,amma da muka shiga sainaga taciki har yafi tawajen girma. Litattafaine da rubutu wanda akayi a jikin fatar dabbobi iya ganinka a wajen,can ƙarshen ɗakin karatun wasu mutanene dattijai sun kewaye wani farin balarabe dattijo har yafisu manyanta, babban littafine a gabansa mai girman gaske domin takardun ma sunada kaurin gaske.
Addu’asukayi suka shafa kafin malamin ya ɗago ya kallemu, kana kallon fuskarsa kasan ya kwankwanɗi madarar ilimi ba kaɗan ba. Iso yayi mana damu ƙariso,Baba Yakub ne ya zauna a kan Buzun amma ni gefe kaɗan nasamu na durƙusa rikeda ƴan kayana.
Murmushi yayi wanda yaƙarawa fuskarsa haiba.
“lale da masinci Yakub,ka daɗe baka kawomana ziyara ba,tun zuwanka kaida ɗan uwanka Ishaq,shin menene yake tafe dakai haka daka aikomin saƙon zuwanka a jiya?”
“Nayi katari ne da wata marainkya a hanyata ta dawowa,mutane sun taya suna sonta,amma naƙi amincewa saboda a ɗan zaman danayi da ita na yarda da hankalin ta da basirarta,dan haka banaso tayi rayuwa ta gidan bauta na sarauta,hakan zai iya lalata rayuwarta. Wannan dalilinne yasa nake roƙarka da koƙon barata a matsayina na tsohon ɗalibinka,kuma maison ganin rayuwar ɗan adam ta inganta da ilimi,daka karbeta a inuwarka ta dunga aiki a wannan majami'a ta Al'azhar,nasan zatayi ƙoƙari sosai kuma zata dace da irin aikin wannan wajen”
“To bazanƙi tayinka ba ya Yakub,tunda ka taso da kanka ka kawota,amma bama bukatar masu aiki a yanzu Fasihmman ma yarinya kamarta,amma zan karbeta tunda naji bayaninka,za'a koya mata aiki idan an yaba da hazaƙarta xan saka a sakata sahun bayi masu shiga aji,domin idan sun iya suna taimakon mu da bangaren aiki wanda mai ilimi kaɗai ake buƙata”
“yawwa da gode sosai Baba guru Allah yakara ilimi mai albarka da nisan kwana”
“ameen ameen haƙiƙa wannan taimako dakayi mata ka kyauta, idan natashi na shiga ciki zan sadata da Ummi Asma'u sannan zance ta kulada ita sosai Allah ya inganta rayuwarta da albarkarsa”
“ameen ameen”
“Kokuma idan zaka fita ka rakata wajenta tana wajen Bada karatu,idan na gama abinda nake zanyi mata magana”
Amsawa yayi da to kafin ya tashi nima na miƙe nabiyoshi,duk abinda suke faɗa a cikin kunnena nakejinsa,nacika matuƙa da mamakin abinda Baba Yakub yayi,kenan yabi duk wannan hanyoyine domin yakawoni wajenda ilimi yake gudana in hakane kuwa………
“Ina fatan kin fahimci inda mukaxo kuma kinsan inane?”
Ɗaga masa kai nayi alamar na fahimta.
“Dukkan abubuwan danayi na aikatane domin sadaki da wannan wajen,bance miki babu ƙalubale ba,amma idan kinason cimma burinki to yazama wajibine ki jure. So nake duk wani ilimi dayake wajennan idan zaki iya yazamto kin haɗiyeshi,indai wanda kikasan zaymiki amfanine,baizama dole a koya miki ba a matsayinki na baiwa,amma kinemi dabaru kala kala wajen ganin kin kai kanki wajen. Hakanne kaɗai zaisa kici moriyar zaman wajen. Ki kasance mai biyayya dakuma ƙanƙan dakai,kada ki nuna baiwar da Allah yayimiki nam take,sai kinga buƙatar hakan ya taso. Zan kaiki wajen Ummi Asma’u, itace babbar ƴar Baba guru kuma itama babbar malamace data samu ilimi tun tana ƙarama,kibi rayuwarta sauda ƙafa wajen ganin kin amfana sosai. Tana son mutum mai biyayya,ilimi da kuma cikar burin dayasa a gaba,ki jajirce wajen nuna cancantarki,batabin matsayi ko asali idan kin cika sharadin datake buƙata to lalle zata taimakeki”
Muna tafiya yana yimin bayani na malaman dasuke a wajen, wanda yawancin Ƴanƴan gurune dakuma ɗaliban daya karantar sai kuma manyan malamai masu kawo ziyara, a na nanne nakejin ashe babbar cibiya ce ta ilimin addini,kimiyya,magunguna da kuma fasahohi. Manyan malamai da dama sukanzo daga wasu ƙashashen domin neman ilimi, ko kuma su koyar danasu ilimin,ashe banga komai bama daga bangarorin dasuke dashi. Sannan ana karantar da ƴaƴan sarakuna manyan sirruka na ilimi da dabarun mulki wanda Baba Guru ne dakansa yake koyar dasu idan an kawosu,wanda sune zasu gaji karagar mahaifansu. Dama sauran ƴaƴan masu mulki harda mata abin tunƙaho ne na nunawa ace sun karbi karatu a wannan wajen.
Jami'ar Al'azhar Babbar cibiyar ɗaukar ilimine mafi girma a dukkan africa bayan wacce take a daular Masar ,samun damar yin aikin bauta a cikinta yasa naji kaman babu wanda yafini,inaga ace na samu damar cafkar ilimin dayake cikinta.
Hawayen farin cikine ya gangaro kan fuskata,tsugunnawa nayi a gaban Baba Yakub,domin bansan dame zan saka masa ba daya wuce hakan.
“nagode baba Yakub nayi alƙawarin komai wahala zan jure wajen ganin na kankari alkhairin dayake wajennan,indai har shine makulli na tafiyar rayuwata, Insha’allahu kaman yanda ka kawoni nikuma bazan baka kunya ba,saikayi alfahari dani a wannan duniyar. Sannan ka dunga dubamin ummah ta. Sannan kayimin alƙawarin zaka kaini gareta”
“Bazayyiwu na kaiki gareta ba kokuma ita na kawota,saidai nayi alƙawarin zan dunga duba halinda take ciki,wannan dalilin ne yasa ban faɗamata inda zan kaiki ba saboda kada tayi tason zuwa. Kada na sakamiki damuwa amma bazasu taba bari ki tafiba ko su saidaki a wani wajen ba indai har suka sakaki a cikin bayi masu Aiki a bangaren ilimi,saboda kada wannan bayi suna amfani da wannan dama suna cutar da mamallakansu,hakanne yasa duk wani bawa dayasan ilimi anan waje to fita ta haramta gareshi har abada,Saidai hanya ɗayace zata sa su barki ki fita shine saikin gama littafin Qur'an da hadith,sannan kin gama matakin karatun rukunina na Ajin ƙarshe anyi gasa kinci,to shine zasu iya barinki ki fita idan kin roƙi fita daga wajen a matsayin kyautarki,wannan mataki kuwa ko wasu sarakunan ma basu taka matsayarsa ba, Saboda ana tunanin duk wanda yakai wannan mataki a ilimi to bazayyi abinda za'a yi Allah wadai dashi ba,saidai shigarsa duniya ma zaisa a amfana da ilimin dayayi. Bawa ɗayane yataba siyan tikitin barin wajannan da wannan matsayi a kundin ttarihi shine malam bilal,aka bashi ƴan cinsa yaje yakafa tasa malantar da har yau ana amfana daga gareta.”
Shuru nayi ina nazari a raina nace ansamu bawa ɗaya Insha’allahu baiwa ta biyu mace ce kuma itace Joda.. Indai har zan samu yan cina to zan jure duk wuya wajen ganin nakai ga matakin nasara.