GADAR TSAUTSAYI 28
by @nusybee143
Page 28
Rai a tsananin ɓace,irin ɓacin ran da ba za su iya tuna yaushe rabon shi da shiga ba ya fara magana
"Abin nan ya ba ni mamaki kuma ya ɗimauta ni, Muyassar dai, yaron da muka sani da biyayya da girmama na gaba, wanda ba ya taɓa yin wani abu ba tare da ya yi shawara da manyansa ba,ya saki matarsa da muka aura masa ya kama gabansa ya tafi, wannan wanne irin abu ne?
Sa'adatu!me yake faruwa ne?"
Kan Hajiya Sa'adatu a ƙasa ta ce "ban sani ba yaya, wallahi ba da yawuna ya yi hakan ba, ban ma san ya yi ba"
Alhaji Yusuf ya dubi Arfa da take ta kuka ya ce"ke Arfa menene ya faru?ko kun samu wani saɓani ne?"
Gyara zama ta yi tana goge hawayenta ta ce"wallahi Abba lafiya ƙalau muke zaune, tunda aka kama Shaheeda sai ya canja,ya yi ta yi min faɗa,ya yi min tsawa,ya gaya min ni ba mace ba ce Shaheeda ce mace,ya ce ya tsane ni dole ce ta sa ya aure ni, Shaheeda yake so
A saboda haka kullum da irin rashin mutuncin da yake yi min, wallahi Abba na gaji da wannan tozarcin"ta ƙarashe tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi
Gaba ɗaya parlourn ya ruɗe da salati da sallallami, Ummeey ji ta yi ta sake muzanta,kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki saboda tashin hankali
Hajiya Sa'adatu ce ta fara magana cikin kuka"ni dai Allah ya jarabce ni, wannan masifar kusan a kanmu ta ƙare kenan,ta tarwatsa gidan ɗana, Allah ka yi min maganinta "
Hajiya Atika cikin sigar rashin mutunci ta ce"Allah ya kyauta dai kam,amma tabbas Muyassar ya faɗa mugun hannu,dama ina zargin yawancin abubuwan da aka ce yana yi ba yin kanshi bane, Allah ya sa dai haka aka bar ku"
Hajiya Sa'adatu ta ce"to Allah ya sa,don yanzu mutum mai shiru -shiru ya fi matsala "
Cikin rashin mutunci Hajiya Ruƙayya ta ce"ba dai wani dabam ba,ke ma ya kamata ki nunawa ɗanki cewa ƙanwata tana da daraja,dama ai tun farko a wulaƙance ya ɗauke ta,kuma babu abin da kika yi akai,idan ma akwai asiri to akwai hali"
Gaba daya parlourn ya yi shiru,ran Hajiya Sa'adatu ta ɓaci sosai,amma kafin ta kai ga yin magana Alhaji Yusuf ya riga ta
"Duk wannan cecekucen ba zai yi ba,mafita za mu nemo kawai,ina buƙatar ganin Muyassar a yau zuwa gobe"ya dubi Hajiya Zainab da ta yi shiru ya ce"Zainab menene shawararki akan hakan?
Kin ga dai abin da yaron nan ya aikata mana,ya saki yarinya ba tare da wani dalili mai girma ba,kuma ya haura ya yi tafiyarsa bai sanar da kowa ba, ya kike gani?"
Kai tsaye Hajiya Zainab ta ce"Alhaji Allah ya kyauta kawai za'a ce,yaran zamani ne ka haife su ba ka haifi halinsu ba,amma duk da haka ya kamata mu ji ɓangarensa tukunna, kafin mu yanke hukunci......"
"Ni ƙanwata ta samu ingantacciyar tarbiyya,a dai bincika a inda aka samu matsala "a cewar Hajiya Ruƙayya tana katse Hajiya Zainab
Hajiya Zainab ta ja baki ta tsuke ba tare da ta sake magana ba, Alhaji Yusuf ya cigaba da bayani ba tare da ya saurari maganar Hajiya Ruƙayya ba
"Arfa zata zauna a nan,za mu jira Muyassar har sai ya dawo, sannan na yanke hukunci "
Hajiya Ruƙayya ta dube shi fuska a ɗaure ta ce"a'a da dai ta koma gidan ubanta, kamar zata fi ƙima a can"ba tare da Alhaji Yusuf ya kalle ta ba ya ce"na gama magana!
Ta koma sashen Muyassar na nan gidan kafin ya dawo,in sha Allah za'a san abin da za'a yi"ba tare da kowa ya sake tankawa ba suka jinjina kai,kai tsaye ya ce"ku je na sallame ku "Hajiya Zainab ce ta fara miƙewa,ragowar matan ma duka suka fito,suka bar shi da ƙannensa maza waɗanda suka yanke shawarar da ta yi musu
Da sauri Ummeey ta yi gaba don shiga sashenta,amma ina,sai da Hajiya Sa'adatu ta cim mata tana huci
Duk da yadda gabanta yake faɗuwa amma hakan bai hana ta ƙaƙaro murmushi ba
"Sannu Hajiya!
Akwai....."duk inda kika kai min ɗana ki dawo min da shi,na ɗaga ƙafa na tsawon lokaci,na yi kara da kawaici amma na ga abin naki ya zama wulaƙanci,to wallahi idan har ba ki dawo min da ɗana ba abin ba zai yi mana kyau ba
Ƴarki ta shiga duniya ta yi tambaɗewarta, shiyasa nima za ki raba ni da nawa?
Shi tasa ga ki nan kullum shiru -shiru,ai mun daɗe da sanin lumbu-lumbu kike yi, abin da ya samu ƴarki mugun aikinki ne yake koma miki,asirinki ne Allah ya tona,don haka tun wuri ya kamata ki nemo min ɗana"
Kallonta kawai Ummeey take yi ba tare da ta yi magana ba,zuwa yanzu ta fara kai wa ƙarshe,duk da irin abubuwan da suka same ta a dalilin tilon ƴarta,da abubuwan da suka sami ƴar tata,babu wanda ya tausaya musu,shine za'a zo ana yi mata maganar wai ta fito da Muyassar,wai me mutanen nan suke nufi da ita ne?
Hajiya Sa'adatu ta katse mata tunani da faɗin"na yi miki magana kin zuba min idanu, wallahi Allah ɗaya idan har ba ki fito min......"
"Hajiya Sa'adatu!
A maimakon wannan complain da kika zo kina yi me zai hana ki kai ƙara sama?
Na gaji da maimaita magana ɗaya,da masu zargi da masu zagi kar wanda ya fasa,ya rage naki ki je ki nemi ɗanki ko ki zo nan ki yi ta hayaniya,ba ni waje"ta zagaye ta a fusace ta wuce zuwa sashenta
Hajiya Sa'adatu ta bi ta da kallo zuciyarta tana ƙuna,amma kafin ta iya ɗaga ƙafarta sai ga Hajiya Ruƙayya ta ƙaraso wajen tana huci
Hajiya Sa'adatu ta kalle ta fuska a ɗaure ta ce"ai ni Ruƙayya kin ba ni mamaki,ban yi tsammanin ko kowa zai zagi ɗana ya juya masa baya ke za ki......."
"A'a Hajiya dakata!don kina matsayin babba kar ki yi tunanin za ki taka mu ki zauna lafiya!
Ya yaronki zai yiwa ƙanwata sakin wulaƙanci kuma ya yi tafiyarsa kamar ya saki mara galihu amma ki kasa ɗaukar mataki?kar ki manta kwanaki fa dukanta ya yi,ko don kin ga na yi shiru,to wallahi ba zai yiwu ba,ba zan zuba idanu ba,idan ba haka ba wallahi zan fasa ruɓaɓɓen ƙwai warin ya damu kowa wallahi "
Kallonta Hajiya Sa'adatu take yi cikin wani irin yanayi na tsananin baƙin ciki da mamaki, kafin ta iya ɗaga harshenta da ƙyar ta fara magana
"Amma ban tsammaci haka daga gare ki ba Ruƙayya,kin ba ni mamaki,ban taɓa tsammanin wai ke,ke dai,ke da na yiwa abin da ban yiwa yaran cikina ba,wai ke ce kike kallon tsabar idanuna kina yi min barazana ba
Kin manta a yadda na same ki?na aurar da ke ga yayana wanda yake da wadata?ya sakar miki?duk wani taimako da kulawa ba babu wanda ban ba ki ba,amma shine za ki zo kina yi min barazanar za ki tona min asiri?
To ki tona!na yi miki alƙawarin duk lokacin da kika yunƙura tona min asiri wallahi sai na yi miki abin da ba ki taɓa zato ba,babu wanda ya isa ya yi min butulci. ........."
"A'a fa Hajiya!
Kar ki yi min wannan maganar,kar mu fara haka da ke!
Kin san kin amfana min,amma ba ki san na amfana miki ba?ko don an ce ɗan adam butulu shiyasa za ki nuna min halin?
To kar ki sake yi min gori,idan kika sake wallahi gwara kowa ya ɗauki hanyarsa, zan fasa ƙwai kowa ya ji wari
Sai magana ta gaba,ya rage naki ki yiwa ɗanki magana ya mayar da ƙanwata kafin maƙiya su ji su yi mana dariya,akasin haka kuma ran kowa ya ɓaci"tana kai wa nan ta wuce fuuu zuwa sashenta ranta a ɓace
Itama Hajiya Sa'adatu rai a ɓace ta shiga motarta ta fice daga gidan zuwa nasu cikin tashin hankali, abubuwa suna neman ruguje mata a lokacin da ya kamata a ce ta fi kowa farin ciki,wai Ruƙayya, Ruƙayya dai, wadda ta zamarwa gata,ta fito da ita daga rana ta kai ta inuwa ita ce ta tsaya tana kallon idanunta tana gaya mata zata tona mata asiri,a fili cikin wata iriyar murya mai cike da mamaki da ruɗani take faɗin "eh fa!
Ba shakka! Allah ya sawwaƙe!!"
Haka ta yi ta sambatu cikin tsananin mamaki da firgici har ta isa bakin gate ɗin gidansu,a ranta tunani take yi ta hanyar da zata yi maganin wannan masifar da ta danno mata kai,ga ɗanta ya saki matarsa, ba tare da sanin cewa ya ɓallo musu ruwa ba,ga wannan tutsun da Ruƙayya take yi, wanda hakan yana nufin abubuwa da yawa a gare su
Jikinta babu ƙwari har ta shiga sashenta na gidan ba tare da ta nemi kowa ba,tana jin lokacin da Salma ta shigo don yi wa innayyo sallama zata tafi gidanta,amma ta yi musu shiru,don abin da yake damunta ma ya ishe ta
*ROCKY ESTATE*
Da sallama ya shiga sashen Nanny ɗin Amna,ta ɗago da fara'a tana amsa sallamar tashi, kafin ta rissina tana faɗin"sannu da zuwa yallaɓai"
Murmushi ya yi yana faɗin"sannu Nanny,ya yaran?
Sai kika ga na ƙara miki nauyi"Nanny ta yi saurin girgiza kai ta ce"a haba! Allah ya raya mana gaba ɗaya "
Haisam ya zauna yana kallon Amna da ta kwanta tana bacci a parlourn,ya kalli Mubarak da yake kwance a kan one sitter ya takure yana bacci,ya ce"ya baƙon naki?
Ina fatan za'a samu daidaito tsakaninku?"
Ƴar dariya Nanny ta yi ta ce "to Allah ya sa ko nan gaba,don yau dai ba'a wanye lafiya ba, ƴar'uwar tana ta rawar ƙafar ta samu ɗan'uwa amma shi sai kuka yake yi yana kiran mamansa, juyin duniya ya ƙi ya yi shiru,sai da bacci ya ɗauke shi a kan kujerar da yake kwance sannan na samu nutsuwa,da na motsa shi zan gyara kwanciyar na ga zai tashi ya cigaba da kuka na ce sha zamanka ka yi baccinka "
Dariya sosai Haisam ya yi yana kallon Mubarak da ya kasance photocopy na mahaifiyarsa, soyayyar yaron yake ji har cikin jinin jikinsa,ya matsa inda yake kwance ya shafa fuskarsa yana faɗin"bai ci abinci ba ya zama dole ya tashi, gudun kar ya tashi ce cikin dare
Tunda bai saba ba bari na tafi da shi,idan ya saba sai na rinƙa barinsa a nan ɗin,kar a haɗa miki aiki"Nanny tana murmushi ta ce "to ranka ya daɗe,ina matuƙar godiya, Allah ya sa ka fi haka"
Haisam ya ce "Ameen!
Zan yi miki ƙari, saboda yaron yanzu zamansa ya dawo hannuna, sannan kuma bashi da ishashshiyar lafiya,sai kin ba shi kulawa sosai"Nanny ta sake rissinawa tana godiya, Haisam ya saɓa Mubarak a kafaɗa a hankali, ya yi mata sallama ya fice zuwa sashensa
Yana zuwa daf da ƙofar sashen nashi ya hango Nimra a tsaye a wajen, murmushi ya yi,ɗazu ya sa aka zo aka canja makullin sashen,don haka yanzu dole ta jira idan ba ya nan,ya gaji da yadda take shigar masa sashe kamar wasu dabbobi ko marasa addini
Ita kuwa yaron hannunsa ta bi da kallo da wani irin yanayi a fuskarta,bai kalli sashen da take ba ya zo zai shige sashensa, ranta a ɓace ta ce"excuse me!
Ina Amna ɗin?"tambayar tata sai ta ba shi dariya,amma bai yi ba,kuma bai kalle ta ba ya shige part ɗin sa,ya biyo shi a baya tana faɗin "bacci yake yi kuma za ka ɗago shi?
Ba zai tashi ba?"banza ya yi mata,yana shigewa sashensa ya mayar da ƙofa ya rufe
Yana kwantar da Haisam akan gadonsa ya fara jin bugun ƙofa na hauka kamar za'a karya ƙofar,har sai da Mubarak ya firgita,ya tashi yana ƙoƙarin fara kuka, Haisam ya lallaɓa shi ya samu ya koma sannan ya tashi ya nufi bakin ƙofar inda ake ta bugun
Bai yi mamakin ganin Nimra ba a tsaye tana ta huci, abin ma sai ya ba shi dariya,ta dube shi ta ce "yau kuma?abin da wulaƙanci ya zo?ka san ina biye da kai shine za ka mayar da ƙofa ka rufe?
Meyasa kake yi min irin wannan wulaƙancin ne?don kawai ina sonka?"hawaye Masu zafi suka zubo mata,take kuma ta fashe da kuka sosai
Ɗan ƙaramin tsaki ya ja,ya ce"Nimra,kin san yadda aikina yake,kin san ina buƙatar hutu da kwanciyar hankali da dogon nazari akan aikina, menene dalilin da ya sa kike so ki ƙara ba ni ciwon kai ne?
A tunanina ke ma mai taimaka min ce na samu nasara akan aikina, menene dalilin da ya sa ke ce kike saka ni wasa da aiki?
Look Nimra,akwai gobe,akwai jibi,akwai sauran kwanaki,za mu iya zama mu yi maganar da kike so,amma yanzu bacci ya kamata na yi please "
Nimra da take jefa masa wani kallo ta ce"to kai da kake buƙatar ka kwanta ka huta me ya haɗa ka da yaro karami? meyasa ba ka bar shi a wajen mai rainonsu ba?tun farko na menene alaƙarka da yaron da kake ƙoƙarin fifita shi akan kowa?"
#Nusy_bee