BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 11

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA❤* *Arewapen@ayshadansabo*

©️ _Ayshat Ɗansabo_ _lemu_✍🏻

*Free page 11*

Gabaki ɗaya tunda Hajiya ta fara magana Abdallah ya shiga cikin tashin hankali,"Me Hajiya ke faɗi masa haka ne? Ta zaɓo masa mata,bayan tafi kowa sanin yadda soyayyar pretty ya kama zuciyarsa."Maganar da Hajiyan ta sake yi ne yayi saurin dawo dashi hayyacinsa.

"Abdallah ya naga nan da nan ka shiga damuwa? Ko kana zaton zan zaɓa maka abinda bai dace da kai bane? "

Yadda yaji Hajiya tayi maganar a sanyaye hakan sai ya taɓa zuciyarsa,ya kuma tabbatar tana son Yarinyar sosai kenan.Duk duniya bai ga abinda za ta zaɓo ta danganashi dashi Yayi mata musu ko gardama ba,haka yake tun tasowarsa Shi mai tsananin biyayya ne ga duk abinda ta nuna tana so ko Tayi masa umurni.Cikin ƙarfin hali ya sauke manyan idanunsa a kanta yana faɗin,

"Hajiya duk abinda kika zaɓa mini nasan Ya cancanta dani ne,sai dai ban san taya zan fara son wata ɗiya mace ba pretty ba,ita nake ji a cikin zuciyata Hajiya."

Ga tsananin mamakinsa murmushi Hajiya tayi irin nasu na manya,kafin takai hannu ta dafa kafaɗunsa tana faɗin,"Abdallah duk duniya nafi kowa son farin cikinka da cikar burinka matuƙar na alkhairy ne,sai dai tunda kaga na bijiro da wannan maganar to tabbas akwai tarin alkhairin da nake hango maka.Domin samun kamammiyar mace budurwa kamar Surayyah abu ne da Yayi ƙaranci a cikin wannan zamanin da muke ciki,don haka kasa ma zuciyarka cewa soyayyar waccan Yarinyar jarabawa ce.Kuma nayi maka alƙawari duk randa kuka sake haɗuwa ta amshi soyayyarka zan mara maka baya ka aure ta,domin kai mijin mace huɗu ne Abdallah."

Ta ƙare maganar tana bubbuga bayanshi,hakan yasa shi sake narkewa kamanr ƙaramin Yaro.Yayin da wani kaso na ruɗanin da Ya shiga ya fara raguwa,sabida alƙawarin Hajiyan na cewa idan Ya ga pretty za ta goya masa baya ya aureta.Ya ɗaga manyan idanunsa yana dubanta yace,

"Hajiya duk abinda kika zartas ni Abdallah mai biyayya ne a gareki,Allah yasa hakan shine alkhairi.Amma Hajiya ita yarinyar bata da wanda take so ne?"

Yayi tambayar a sanyaye.Hajiya ta murmusa tana faɗin,"Ita ko ke da masoya Abdallah..... "

A hankali Hajiya ta sanar masa labarin da Mum ta bata,na yadda Surayyah ke fama da samarin dake neman ɓata tarbiyyanta.Ta ƙare maganan tana faɗin,

"Ka ko ga Abdallah idan ba Yarinya mai tsananin nagarta da tarbiyya,gami da kamun kai da sanin mutuncin ta na mace ba,da yanzu ta sallama kanta garesu a yadda ƴan matan yanzu suka maida soyayyan shaiɗanci da shashanci ado.Ina maka sha'awar ka mallaki Surayyah,domin sama wa Yaranka kamammiyar Uwa ta gari."

Jikinsa ne yayi sanyi sosai, zuciyarsa ta shiga kai kawo duk da cewa baya ji ko kaɗan zai iya buɗewa wata ƙofa a cikin zuciyarsa inba pretty ɗinsa ba.Sai dai yayi mamaki ace wacce ta kammala jami'a na gudun soyayyar shan minti,wanda ƴan matan yanzu suka mai dashi ado.Ya sha jin yadda abokansa dake harkar soyayya na faɗin yadda ƴan mata ke sallama musu kawunansu,suyi abinda suke so dasu.Hakan ke sake sashi jin tsanar ƴan matan yanzu da tsoran afkawa cikin duniyar luv,amma lokaci guda da idanunsa suka faɗa kan pretty ya ji soyayyarta Tayi masa mugun kamu.Duk da hakan addu'arsa kullum shine Allah ya bashi mata Ta gari,wacce ta tsare mutuncin kanta.A nutse Ya sauke gwauron numfashi yana faɗin,

"Gaskiya ne Hajiya,samun mace kamarta a cikin ƴan matan yanzu sai ɗai-ɗai.Allah yasa ta riƙe miki ni da amana,nima Allah Ya bani ikon yi mata adalci.Tunda kin matsa aure za ki ma Auta,an gaza yi masa haƙuri Ya gano pretty ko Ya ɗanɗani daɗin yadda auren soyayya yake."

Ya ƙare maganar a shagwaɓe kamar wani ƙaramin Yaro.Hakan yasa Hajiya kai masa dukan wasa cike da tsananin ƙaunar sa,ta sani yana cikin ruɗanin zuciya amma yana yin duk abinda yake yanzu ne cikin ƙarfin hali domin ya nuna ta isa dashi.Ya kuma amshi zaɓinta,ba za ta daina yi masa addu'ar samun zuriya masu albarka da za su bishi tamkar yadda yake binta ba har abada.Shiyasa take masa kwaɗayin samun mace ta gari,wanda take hasashen Surayyah za ta zame masa ta gari da yardar Allah.Buɗe baki tayi tana faɗin,

"Abdallah Allah Ya maka albarka,Allah ya ɗaukaka ka.Ya baka zuriyyar da za su bika fiye da yadda kake min biyayya,kada ka damu da maganar auren so domin Allah ke sanya soyayya a zuciyar bayinsa ba tare da yabi ra'ayinsu ko yayi shawara da su ba.Ina da tabbacin za ka so Surayyah fiye da tunaninka,domin ta haɗa dukkanin nagartar da za ka so.Fatana Allah ya cika min BURIN ZUCIYAta in ga wannan auren Abdallah."

Ta ƙare kalaman tana dubansa sosai,yayin da Shi kuma yake jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarsa.Sabida daɗin albarkar Uwa da yake sha a koda yaushe,duk da cewa a can ƙasan ransa akwai tarin ruɗu da damuwa,wanda ba zai iya bayyanashi a gabanta ba.Domin farin cikinta shine gaba da komi a rayuwarsa,sai ya saki murmushin ƙarfin hali yana faɗin,

"Za ki gani Hajiya In Sha Allah,albarkar da kike saka mini da addu'arki gareni a kullum sune abinda ke haska rayuwata Hajiyata.Bana fata Allah ya nuna mini randa zan bijirema duk wani umurni ko shawara naki."

Sosai kalamansa suka faranta ranta,yayin da kewar Mahaifinsa ke tasowa yana cika zuciyarta."Ina ma ya rayu dasu har kawo yanzu." Ta tabbatar da sai Ya fi kowa farin ciki da samun magajin ɗa kamar Abdallah.Sai ta amsa masa da faɗin,"Ameen Abdallah,Allah Yayi albarka."

Sai da safe Yayi mata a lokacin da agogo ya buga ƙarfe goma da rabi na dare.Ya fito daga ɗakin yana takawa a hankali ya fito falo,tuni Humaida ta shige ɗaki ita ma.Don haka babu kowa cikin falon,ya fice daga part ɗin ya nufi nashi.Wanka ya shiga kai tsaye domin ƙa'idarsa ne komin dare baya iya bacci bai watsa ruwa a jikinsa ba.Ko da Ya fito jallabiya kawai ya zura ya nufi bed bayan ya rage hasken fitilar ɗakin.Kwanciya Yayi zuwa rigingine tare da lumshe idanunsa,maganganun da sukai da Hajiya ke dawo masa ɗaya bayan ɗaya.Rintse idanun nasa Yayi yana jinjina cewa wai shi Abdallah ne maganar aure ya bijiro masa a yanzu,kuma bada pretty ɗinsa ba? Ta ya zai iya fuskantar wata mace bayan zuciyarsa bata taɓa son ko wace mace ba sai pretty ɗinsa wacce bata san ma yana yi ba.Shi kam ko kaɗan soyayya ba tai masa adalci ba.Buɗe idanunsa yayi tare da janyo wayarsa ya ƙurawa hoton ta ido,wani soyayyarta mai sanyi ne ke sake bin jinin jikinsa.A ƙirjinsa ya manna wayar yana mai sake lumshe idanunsa,zuciyarsa na sake shiga ruɗuni na tunanin yadda zai yi ya tunkari zaɓin Hajiya."Ko ya Yarinyar take ma? Ya za ta amsheshi? Ta yayaa za suyi aure babu soyayya a tsakaninsu?" Waɗannan sune tarin tambayoyin da suka addabi zuciyar Abdallah,har zuwa lokacin da bacci ɓarawo yayi awon gaba dashi.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*ZARIA*

Juyi kawai take yi bisa gadonta amma har zuwa lokacin bacci yaƙi ɗaukarta,kallon wayarta take wanda yake a silent amma kiran Mubarak ne keta shigowa ta gagara amsa call ɗin.Domin wani irin haushinsa take ji a yanzu,tunda ya fito da maitansa a fili game da BURIN ZUCIYARsa.Shi ma ya bi sahun da su Aliyu suka bi,tabbas da ace ya danne maitarsa da ta bashi dama ya shigo cikin rayuwarta ta hanyar aure.Duk da cewar bata son auren zumunci,amma a yadda mazan waje ke zuwar mata ta gwammace ta auresa,da ace ta bari wani ya zo yayi auren kashe wutar sha'awa da cika BURIN ZUCIYARsa da ita.Sai dai kash...! Shi ma sai ya zo a cikin jerin mazan da ya kasance BURIN ZUCIYA ɗaya suke da shi a kanta,jikinta da kyawun halittarta kaɗai suke wa.

Rintse idanunta tayi sosai,tana jin zafi a can cikin zuciyarta.Hoton fuskar Abdallah da maganarsu da Mum akan haɗin auren da ake so ai musu ke dawowa cikin kwanyarta,sai ta buɗe idanunta tare da kai dubanta ga agogon wayarta.Ganin har sha ɗaya da rabi ta gota ya sanya ta mirginawa zuwa ɗaya gefen damarta,tare da lumshe idanunta tana mai addu'ar Allah kawo bacci a idanunta cikin sauri.Amma sam hakan bai samu ba,domin duk yadda ta so yakice abin a cikin zuciyarta ta kasa,tunanin yadda za su fuskanci juna ita da shi kawai take.Wani irin duba zai mata? Ya zai amshi tayinta da Mahaifiyarsa za ta kai masa? Ko miye shi kuma zai zama nashi BURIN ZUCIYAR a kanta?" Waɗannan sune tarin tambayoyin dake hautsina kwanyarta,banda bacci ɓarawo ne bata san sanda ya sure taba.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*ABUJA*

"Anty Sameera bari in fita zuwa sitting room,Shushu ne yazo min sannu da dawowa."

Cewar Rash kenan wacce taci ado cikin English wear's riga da wando ƴan gaske, waɗanda sukai mata kyau matuƙa tare da fidda surarta sosai.Wani shara-sharan kimono ta saka wanda ake hango a salin surarta a cikin shigar da tai,azababban ƙamshinta dake narka zuciyar ƴan mazan kawai ke tashi a jikinta.

"Tuh Rasheeda,Am! Nace ba.Ya kamata shi wannan Shureim ɗin inda gaske yake ya turo Rash,lokaci yayi da ya kamata ace kinyi aure don Allah.Wannan kule-kulen samarin yayi yawa,ki duba yanzu 11pm shine yazo miki sannu da zuwa Rash?"

Sameera ta ƙare maganar idanunta akan Rash,wacce tuni ta kusa ƙofa.Muryarta kawai ta jiyo tana faɗin,

"Tuh Anty Sameera,karki damu in dai aure ne soon maganar zai taso."

Tana maganar ne tana murda handle ɗin ƙofar ta fice abinta,ta bar Sameera da bin bayanta da kallo tana jinjina cewa anya ba tayi sakacin da Rash idanunta suka buɗe ba kuwa? Gabaki ɗaya Rash ɗin sake sauyawa take a halayya da gangar jikinta ma baki ɗaya,ya zama dole ta fara sanya ma duk wani motsinta idanu.Da wannan tunanin ta miƙe ta haura zuwa sama,tuni dama Husnah ta jima da yin bacci.Rash ɗin ce ta kaita ɗakinta wai tare za su kwana,domin lokuta da yawa dama tafi kwana wajen Rash ɗin saboda shaƙuwar da sukai da juna.

Sai 12am Rash ta shigo ciki daga wajen Shureim,sai da suka gama shafe-shafensu da abinda suka saba kafin ta rakashi har wajen mota ya bar estate ɗin.Ita kuma ta juyo zuwa cikin gidan tana jin ƙaunarsa sosai,domin Shureim kyakykyawan matashi ne mai shekaru 35 da Ya mallaki duk wani abu da ɗiya mace za ta so.Sai dai shaiɗani ne na gaske,don ma duk abinsa har yau ya kasa samun abinda yake so a jikin Rash ɗin,domin Ya Hisham shi kaɗai take yadda ya shigeta.Su dai gangar jikin kawai take basu suyi yadda suke so,amma bata basu can asalin wajen kayan daɗin.Kayan jikinta ta cire ta shiga wanka,koda ta fito sha biyu da rabi ta wuce. Wayarta data barshi a ɗakin ta ɗauka tana dubawa,missed call ɗin Fahad dana Ya Hisham ta gani.Hakan yasa ta zauna a bakin bed daga ita sai bathrobe a jikinta ta danna ma Ya Hisham ɗin kira vedio call,kamar jira yake,ya kashe ya kuma kiranta suka fara magana kafin hirar ya canza salo zuwa na shaiɗanci.Bai barta ba sai wajen ƙarfe ɗaya,shibma ganin yadda bacci ya fara rinjayarta ne.Tana ko aje wayar,rigar wankan kawai ta cire ta zura na bacci tabi lafiyar gado....... ✍