BURIN ZUCIYA Chapter 12
*BURIN ZUCIYA❤*
*Arewapen@ayshadansabo*
©️ _Ayshat Ɗansabo_ _lemu_ ✍🏻
*Free page 12*
Ƙarfe tara na safe Surayyah ce zaune a gaban Babanta,suna sallama sabida bada jimawa ba Uncle B zai iso daga GRA inda yake kwana wajen friend ɗinsa su wuce KD.Sanye take cikin half buba na lace,da straight skat wanda kayan sukai mata mugun kyau.Face ɗinta ya sha light makeup,tayi kyau sosai abinka ga mace mai son gayu da kwalliya.
"To Autan Baba sai yaushe kenan za a dawo Zarian?"
Cewar Alhaji Mahmud yana dubanta cike da kulawa.Surayyah ta saki murmushi tana faɗin,"Nan da 2 week's Baba,one week a KD sai na wuce Abuja nayi one week."
Ta ƙare maganar tana duban Mum dake kusa da Baban tana haɗa masa tea,yayin da shi kuma ya furta,"To shikenan Auta Allah tsare hanya a kula da kare mutuncin kai,sannan karki manta da maganar fidda Miji Inanan ina lissafi."
"Tuh Baba,bari inje in gama kintsawa kafin Uncle ya iso."
CewarbSurayyah tana tashi ta fito daga side ɗin Baban nata zuwa ɗakin.Zama tayi cikin kujera tare da dafe kanta,"Aure,aure dai shine maganar kowa a kanta? Wato dama don tana skull ne aka ɗaga mata ƙafa kenan?" Tambayar da take wa kanta kenan kafin maganar Abdallah ya kutso kai cikin tunanin nata,sai ta lumshe ido tana ji tabbas gara tabar garin ko ta ɗan sarara.Sam ba za ta taɓa zuwa wajen Humaida ba,tunda wannan maganar ya ɓullo.Ko jiya a chat sai da Humaida ta roƙeta akan in dai ta shigo KD tana tsumayinta.Kamar wacce aka mintsina ta miƙe ta isa bakin bed ɗinta tare da ɗaukar wayartaa,ta zauna a kan gadon tana neman line ɗin Aminiyarta Mardy.Bugu biyu Mardiyya ta ɗaga call ɗin,Surry ta saka wayar a hand's Free domin bata jin rike wayar a kunni.
"Hello ta Mubarak yane?"
Cewar Mardiyya cike da tsokana.Surayyah taja tsaki tana faɗin,
"Matsalata dake kenan wallahi Mardy,ta Mabaruka ce ba Mubarak ba.Banza ni kiranki nayi ince miki zan wuce yau,daga KD Abuja nayi wajen anty Rash."
"Kice za ki tafi chilling abinki,ki barni a zaria.Gaskiya Surry 2 week's baki gari yayi tsawo da yawa."
Cewar Mardiyya cike da narke murya,domin har cikin zuciyarta take ji za ta yi kewar Surryn.Domin in dai suna gari,zai yi wahala suyi 3 days ɗaya bai ziyarci ɗaya ba.Surayyah ce ta saki dariya tana faɗin,
"Kaji Mardiyya dai sai kace Zayyad ne zai yi tafiya ya barki tsawon sati biyun."
"Hmm! Surry kenan da shi ɗin ne wallahi ba zanji komi ba,ke nifa har yanzu bana wani jinsa a zuciyata.Har yanzu ina kan gwadashi ne in gane da me yazo shima,kafin nayi saurin bashi zuciyata."
Cewar Mardiyya tana sakin ƙaramin tsaki.Surayyah ta sake sakin dariya tana faɗin,
"Hakan ma nada kyau ƙawata,don mazan sai da gwaji kam.Duk da cewa sun ƙware wajen iya badda kama,sai dai addu'a kurum.Akwai fa labari amma ki bari mu haɗu anjima a online."
"Allah ta wajena,kice munyi wani babban kamun kenan? To Allah yasa wannan mai kyakykyawan manufa ne ta alkhairi."
Cewar Mardiyya tana mai jin farin ciki, Burinta duka su samu maza na gari suyi auransu,kosa huta da surutun mutane na cewa sunƙi aure.Wasu ma cewa suke suna jiran manyan masu kuɗi ne shiyasa kowa yazo sai su kora shi.
Da "Ameen."Surayyah ta bita tana cutting call ɗin bayan sunyi sallama.Ƙarfe goma Uncle B ya iso,basu ɓata lokaci ba Surayyah ta fitar da kayanta zuwa mota,tare da yin sallama da Mum da Lami mai aiki suka fito tare da Uncle B zuwa mota.
Itace a gaba yana biye da ita idanunsa na yawo a kanta.Sama da ƙasa yake ƙare mata kallo,zuciyarsa na kisima masa abubuwa da yawa a kanta.Tunda ya ɗaura ido a kanta kwalliyarta da shigar da tayi suka taɓa zuciyarsa,tare da sake haifar masa da jin wani yanayi a cikin zuciya da gangar jikinsa.Front seat ta shiga ta zauna,ya ja motar suka fice daga gidan baki ɗaya.
Sai da suka tsaya a gwargwaje ya amshi saƙo,kafin su kama hanya yana tuƙi suna hira cike da nishaɗi.Lokaci bayan lokaci yana kallon kyakykyawar fuskarta ta mirror,ba tare da ita Surayyah tasan ma yana yi ba.
⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡
*KADUNA*
Da yake yau sunday ne babu aiki hakan yasa sai 10am Abdallah ya fito daga side ɗinsa,sanye yake cikin ƙananun kaya da sukai masa mugun kyau.Ƙamshin turarensa na Creed Aventus ke tashi a jikinsa,tafe yake yana amsa call ɗin Lukman abokinsa.Yana sanar dashi cewa ya zo ya sameshi akwai abinda zasu tattauna,akan harkokin businees ɗinsu,domin Abdallah bai tsaya ma aikin gwabnati kawai ba akwai harkokin business da yake sosai. Yana dab da shiga side ɗin Hajiya ya yanke wayar,da sallama ya shiga cikin falon wanda mai aikin shara da mopping ta gama gyareshi tsaf ko'ina sai ƙyalli yake yana fidda ƙamshin turaren wuta dana room freshners. Ɓangaren dining ya nufa kai tsaye ganin Hajiya bata fito ba,buɗe wamas ɗin yake yana ganin abinda ke ciki,daga ƙarshe zama yayi ya zuba soup ɗin cowleg dake tashin ƙamshi.Sai ya zuba potato omelette ya haɗa ruwan tea ya fara cin abincinsa hankali kwance,baiyi nisa da fara cin abincin ba wayarsa ta shiga ringing.Ya ciro yana receiving tare da sanya wayar a hand's Free ya aje bisa dining ɗin.Daga ɓangaren Rayyan ya fara faɗin,
"Turaki don iskanci wai ba kaga missed call ɗina bane?"
Abdallah ya aje spoon ɗin hannunsa yana faɗin."Ban gani ba,ya aka yi ne? May be time din na shiga wanka ka kira.Za ka shigo ɗin anjima ne na sanar da Lukman mu hadu anan gida kawai zuwa anjiman?"
Ya ƙare maganar yana ɗaukar cup ya kurɓi tea ɗinsa,yayin da a ɓangaren Rayyan ya amsa shi da faɗin,
"Alright,sai mu haɗu anan ɗin na pretty,bada kanka mu sare."
Ya ƙare maganar cike da zolaya.Abdallah ya furta,"Za ka sani ne Rayyan,akwai labari sai dai ka shigo.Pretty tana can ta sake baki za a mata snatching ɗina."
Yadda Yayi maganar cikin sanyi yasa Rayyan kwashewa da dariya, Yana faɗin,"How comes Turaki,kace inyi maza inzo a bani labari kenan?"
Abdallah bai ce komi ba ganin Rayyan na son kunnashi ya kashe wayarsa,yana sakin murmushi.Yasan yau Rayyan zai samu abinyi idan yaji aure zai yi kuma wai zaɓo masa matar akai ba pretty ɗinsa ba ce,cigaba da cin abincinsa yayi har zuwa lokacin da Hajiya ta fito sanye cikin riga da zani na atamfar Holland.Tayi kyau sosai babu me cewa ta lamushe shekaru 65 a duniya,side ɗin dining ɗin ta duba ganin Abdallah ne zaune yasa ta murmusawa tana faɗin,"Autan Hajiya ka fito?"
Abdallah ya ture plate ɗin gabansa yana hamdala,tare da zaran tissue ya goge bakinsa.Wayarsa ya ɗauka yana takawa zuwa cikin falon yake faɗin,
"Na fito Hajiya,barkanku da fitowa."
Ya ƙarisa maganar Yana zama a kujerar dake kusa da ita,yana gaisheta ta amsa cike da kulawa kafin ta dubesa sosai tana faɗin,
"Abdallah wai ya maganan kuɗin daka ce za a baiwa Karima taja jari, ɗazu da safe kiran ta ya tadani daga bacci."
Dafe kai Abdallah Yayi yana faɗin,"Oh! Allah Na,wallahi Hajiya maganar ya kwantamin ne,amma yanzu zan mata transper don ta turomin account number ɗin Yaronta,tace a tura mata ta nan."
Ya ƙare maganar yana zaro ɗaya wayarsa domin dubo number ɗin,yayin da Hajiya ta furta."To Ma Sha Allah,gara ka tura mata ɗin,domin ta matsu.Zama babu abinyi babu daɗi,bare ita mai marayun Yara a gabanta.Allah dai Yayi albarka Abdallah,kuyi ta haƙuri da mutane.Ku taimaki marasa ƙarfi da marayu kada kuce kun gajiya,duk mai bayarwa bazai taɓa rashi ba."
"In Sha Allah Hajiya za mu yi iyakan ƙoƙarinmu,maganar tafiyarmu Umrah inaga nan da 2 week's Visa ɗin zai fito.Har da Humaid na nemawa Visa ɗin,gara mu tafi tare baki ɗaya."
Cewar Abdallah yana maida dubansa kan wayarsa.Hajiya ta furta, "Gaskiya ne hakan yayi,Allah yayi albarka.Kace Humaida akwai murna yau,dama ta jima bata jeba rannan ta gama mita nace mata lokaci ne,nina fi mata sha'awar yin hajji ne ma."
Abdallah yayi murmushi yana faɗin. "Karki damu Hajiya next year inda rai sai abiya mata."
Kafin Hajiya tayi magana Humaida ta fito,da alamu bata jima da tashi ba tayi wanka ta fito.Gaida Ya Abdallah tayi ta nufi ɓangaren dining domin karyawa.
"Abdallah inaga zuwa wata sati na sama sai ka shirya kai da Rayyan ku je Zaria wajen Surayyah ɗin ko? "
Hajiya tayi maganar tana duban Abdallah cikin ido.Sai ya sadda kansa ƙasa yana faɗin,"Duk yadda kika ce haka za a yi Hajiya."
Ya ƙare maganar yana miƙewa tsaye domin komawa side ɗinsa,domin sam baya so maganan ma tayi tsayi.Tsaf Hajiya ta karancesa,sai kawai tayi murmushi tana faɗin,
"Kuje ɗin zuwa wata satin,ka ganta ta ganka,kafin manya su shiga maganar domin ba za a wani tsaya ɓata lokaci ba."
"Shikenan Hajiya Allah shi kaimu next week ɗin lafiya,ni bari in koma side ɗina kafin su Lukman su shigo."
Cewar Abdallah yana barin sashin,Hajiya ta bishi da kallo tana murmushi.Ta maida dubanta ga Humaida data dawo cikin falon da plate a hannu,tana cigaba da cin abinda ta zubo.
"Hajiya wajen wata Surayyan Ya Abdallah zai je? "
Humaida tayi tambayar cike da ɗokin son jin amsar da Hajiyar za ta bata.Tna mai fatan jin abinda take hasashe ne zai tabbata.
"Surayyah dai da muka je gidan su shekaranjiya,nayi ma Abdallah zaɓinta Humaida.Sabida zuciyata ta natsu da ita,ina kuma hango dacewar da za su yi da juna."
Hajiya ta ƙare maganar tana kallon yadda Humaida ke murna,kafin ta furta. "Kai amma Hajiya kin birgeni da kikai wannan tunanin,nima ina ɗaura ido a kanta nace ina ma Ya Abdallah ne zai sameta.Gaskiya sun dace da juna sosai,Allah ya haɗa zukatansu tuh Hajiya.Amma da kike maganar ya je next week to ai yau za ta zo Kaduna fa,kuma tace min daga nan Abuja za ta wuce ma,sai dai ya sameta anan KD ɗin kafin ta wuce Abuja next week ɗin."
"To ai ban sani ba,shikenan ma abu yazo cikin sauƙi sai ya je inda tazo ɗin suga juna.Anjima zan sanar dashi hakan bayan nayi magana da Hajiya Ayshatu a waya na sanar mata."
Cewar Hajiya suna cigaba da magana tana sanar da Humaida maganar tafiyar da za su yi tare,sosai ta shiga murna tana ma Yayan nata addu'ar Allah ya kara masa buɗi na alkhairai masu yawa.
********
A can side ɗin Ya Abdallah kuwa Rayyan Shi ya fara isowa,zaune ya samu Abdallah ya tasa system a gaba yana shigar da wasu bayanai da suka shafi office.Amsa sallamar Rayyan yayi yana ture system ɗin daga gabansa bayan ya kashe,idanunsa fes akan Rayyan dake wani sakin dariya ƙasa-ƙasa.Hakan yasa Abdallah ya haɗe face yana faɗin,
"Ɗan iska yau kuma wani sabon salo ne za ka shigomin kana wani dariya ƙasa-ƙasa?"
Rayyan ya zauna yana duban Abdallah cikin ido yake faɗin,"Turaki ai kai ɗin ne ka bani dariya tun a waya,ni dai yanzu mutumina bani labari me ke going ne?"
Taɓe baki Abdallah yayi bayan ya watsawa Rayyan ɗin harara yana faɗin,"Ai kuma tunda ka shigo da wannan dariyan shaƙiyancin na fasa sanar dakai komi."
"Haba Turaki ai kasan bazai yiwu ba wallahi,sai ka faɗi,haba Angon Pretty."
Duka Abdallah ya kai masa,amma sai Rayyan ɗin ya goce yana sakin dariya.Abdallah ya ja tsaki yana faɗin,
"Ba-ba wallahi soyayya bata min adalci ba sam,ya za ai ace tsawon watanni huɗu zuciyata na azabtuwa da sonta,ba tare da na sake cin karo da koda mai kama da ita bane.Wallahi da ku ne kuka cemin akwai lokacin da soyayyar wata ɗiya mace zai min mugun kamu kamar haka dana Karyataku,sai gashi na tsinci kaina dumu-dumu akan son wacce bata ma san inayi ba,Rayyan kuma wai ina cikin wannan situation ɗin ne zanyi aure?Hajiya aure za ta min wai ta zabo min mata ƴar Zaria."
Ya ƙare maganar yana gyara zamansa sosai,yayin da Rayyan ya kwashe da dariya yana faɗin,"Aure fa kace Turaki,kuma bada Pretty ɗin ba garin ya hakan? "
Cikin murya can ƙasa cike da haushin dariyan da Rayyan ke masa ya furta "Getout! R.A tunda Abdallah ya zama mahaukac........ "
Maganar Rayyan ne ya katse Abdallah da Ya hasala,yana ƙoƙarin zama serious sosai yake faɗin,"Sorry Turaki,abin ne daban dariya.Wace mai sa'ar ce take ƙoƙarin samunka a sama haka?Gaskiya Hajiya tayi abinda ya dace."
Kafin Abdallah ya tanka Lukman Yai sallama ya shigo,hakan yasa suka basar da maganar bayan sun gaggaisa da juna suka shiga abinda ya tara su ɗin.
Sai a zuhur suka fito daga side ɗin Abdallah suka nufi masallaci,koda suka dawo sai kowa ya shiga motarsa ya wuce.Yayin da Abdallah shi ya koma side ɗinsa,domin ya huta kafin anjima ya fita..... ✍🏻