Chapter 15
Chapter 15
Ta dade sosai a gidan su don sai da tayi sallar maghrib sannan ta fara shirin tafiya.
Bayan ta gama shiryawa taje yima Momma sallama.
Nasiha ta qara yi mata sosai akan zaman rayuwa da kuma mahimmancin haquri.
Godiya tayi mata sosai sannan ta fito,bayan sun rakata bakin mota zata tafi ta bude back seat na motar ta dakko fruit din da ta siya Momma.
Ta bama auta tace gashi ta kai shi fridge, godiya Momma tayi ta sa mata albarka sannan ta kunna mota ta dauki hanyar komawa gidanta.........................................
Hiii Minnoşum,sadeeq ya fada bayan Jay ta daga kiran da yayi mata.
Hello doctor,I'm sorry ina ta son na kira ki tun dazu naji ya kike da kuma gajiya amma nima wani abu ya taso man dole sai da na fita,I'm really sorry for that.
It’s okay na fahimta, toh yanxu ya kike?
Lafiya na qlau alhamdulillah, are you free now?
I want to have a word with you please,yeah I'm free.
Dama akan maganar da mukayi a baya ne jiya Abbah ya qara yi man magana amma na bashi excuse din dad yayi tafiya amma in shaa Allah da ya dawo zan sanar dashi.
Sai da taji gabanta ya fadi da taji abinda ya fada.
Amma tayi qoqari bai fahimci wani abu daga yanayinta ba tace in shaa Allah gobe su dad zasu dawo.
Idan ya samu nutsuwa bayan ya dawo in shaa Allah mom zata yi masa magana sai yayi masu fixing time din da zasu zo.
Tohm shikenan,idan ya saka time din sai ki fada man.
Tohm ba damuwa,maganar da Munarh take yi mata ne yasa suka yi sallama...................
Irin wannan ba zata haka Meenah zuwa babu sanarwa Layla ta fada tana murmushi.
Murmushi itama tayi tace toh ko na koma ne ba'a buqatar gani na?.
Dan dukan wasa ta kai mata tace ke matsala ta dake kenan yanxu dai ya garin kwana da yawa kin buya ba'a ganin ki.
Wallahi kuwa,nayi abinda nake ganin yafi dacewa nayi ne.
Yanxu ma dalilin da yasa kika ganni a gidan ki Layla na kasa bama zuciyata haquri na cigaba da kallon ki kina kai kanki da kanki cikin jahannama.
Kiji tsoron Allah wallahi Layla wasu lokotan bana iya bacci saboda ina ganin naci amanarki ta hanyar janye jiki na daga gareki ba tare da na fada maki gaskiya ba.
What are friends for idan zan ga kinyi ba dai dai ba kuma nayi shiru ba tare da na gyara maki ba?
Ya kamata ki zauna kiyi tunani da kanki akan rayuwar da kika jefa kanki ciki.
Har yanxu kina da sauran lokaci tunda kina numfashi a doran duniya.
Allah ne shaidata na fada maki iya abinda zan iya sauran kuma ya rage naki ko ki dauka ko kuma ki watsar wannan kuma ya rage naki.
Tana gama fadin haka ta dauki jakarta zata wuce,Layla ta riqe hannunta tace kai Meenah wai tafiya zakiyi ko ruwa ba'a kawo maki ba?
Murmushi tayi me ciwo tace ba ruwa naxo sha gidan ki ba Layla idan ruwa ne nasan inda zan samu.
Abinda ya kawo ni gidan ki na fada maki,ba kya bina bashin rantsuwa amma ina son ki sani Hafsat ba son ki take ba tunda har zata iya kaiki ga halaka.
Sai anjima daga haka ta bude qofa ta fita,bayan ta fita ne Layla tace ki jiman mata haka nan ina cin duniya ta da tsinke zaki wani zo kina cewa naji tsoron Allah da tsoron ki nake ji.
Kiji man yarinya daga zuwanta zata bata man rai dama wasu sunzo sun bata man rai itama taxo ta dora daga inda suka tsaya,haka tayi ta mita ita kadai har ta gaji tayi shiru....................................
Babu wanda yayi ma wani magana har sai da ya aje ta a qofar gate din gidan su.
Sannan tace ya Sadeeq nagode sai da safe.
Tohm yace mata sannan yace ki gaishe da hajiya,zata ji in shaa Allah,sannan ta bude qaramar qofar gate din ta shiga ciki tana zuwa ta wuce dakinta don an fara kiraye kirayen sallar maghriba.
Tayi alwala tayi sallah sannan ta dakko turaren da aunty ta bata da kuma paper bag din da mama ta bata itama ta dakko ta fito ta wuce dakin mamansu.
A daki ta sameta itama ta idar da sallar tana adhkar zama tayi a gefen gado har ta idar sannan tace Hajiyarmu sannun da gida.
Yawwa sa'a, ya kika baro man yayata da aunty hadiza? Duk suna nan lafiya qlau sunce a gaishe ki.
Kinga aunty ta bani turare mama ma kinga ta bani.
Bude jakar tayi wacce keta qamshi itama turare ne a ciki amma oil perfumes ne guda uku.
Karba tayi ta gani tace masha Allah angode sai ki je ki aje su a daki nasan ki kuma da bare bare in kinga dama ki farfasa su duka tunda naga kwalba ce.
Dariya tayi tace kai Hajiyarmu haka ma zaki ce?
Toh ba gaskiya na fada ba?
Gaskiya Hajiyarmu A'a ni na tafi daki nama tunda abin haka ne.........................
A zazzaune suke a parlour washe gari da safe bayan sunyi breakfast.
Jay tace Munarh ki bamu labarin abinda ya faru dake bayan rabuwar mu.
Murmushi tayi me ciwo tace bayan su kawu Hadi sun dauke ni mun tafi na zama baiwa bani da yan cin yin komai a rayuwana sai abinda aka saka ni.
Kowa ya kwaso sharar shi a kaina ze sauke ta ko bata ma mutum rai akayi a waje ni ake sauke ma duk fushin da mutum ya dakko.
Ke Maimuna har yanxu baki gama sharar da na saka ki ba kin san ga wanke wanke can yana jiran ki?
Kuma kin san zaki dora abinci sai rana tayi baki gama ba su Fareedah sun dawo daga makaranta suna jin yinwa?
Kiyi haquri gwaggo na kusa gamawa yanxu zan fara wanke wanken sai na dora girkin.
Munafuka duk abinda mutum ya fada kina da amsar bashi kamar wata mutuniyar arziqi.
Bance mata komai ba na dakko abin kwashe shara na tattara sharar da nayi na kai cikin kwandon shara.
Sannan na zauna na fara uban wanke wanken dake jira na.
Bayan na gama na dakko itace ina hada wuta yaya Sammani ya watso man kayan kwallon shi yace ke Maimuna ga kayan kwallo na nan ki wanke man da la'asar zan fita training kuma wallahi idan na dawo naga baki wanke ba sai na ballaki.
Babu yanda zan iya nace toh yaya,bayan na dora ruwan abinci na dauki kayan da yaya Sammani ya bani ina wankewa.
Lokacin da na gama girki yaran gidan da suka tafi makaranta sun fara dawowa haka na dauki kayan da suka dawo dashi na wanke.
Gwaggo mariya ce ta fito ta dauki abincin da na dafa kasancewar yau girkin tane ta zubawa kowa amma ni sai tace min kinga Maimuna abincin ya qare baki samu ba.
Idan da sabo na saba da irin wannan rayuwar zan dafa abinci amma haka wasu lokutan za'a ce ban samu ba.
Nace babu komai gwaggo ai dama bana jin yinwa tana jin haka ta washe baki muna zaune a tsakar gida sai ga yaro yayi sallama yace gwaggo mariya wai yaya Haladu yace a bawa Maimuna abincin shi ta kawo mai shago.
Kallo na gwaggo Mariya tayi tce toh tashi ki kaiwa Haladu abinci saura kuma kije kiyi zamanki mu rasa dan aike.
Naji dadin kiran da yaya Haladu yayi man saboda duk gidan nan shi kadai yake sona kuma baya son yaga ana takura man.
Kodadden mayafi na dake kan igiya na yafa na dauki abincin na tafi.
Ina zuwa na tarar da yaya Haladu a bakin shagon da suke kwana yana gani na yayi man murmushi yace sannunki qanwata.
Yawwa yaya ga abincin da kace a kawo maka ta fada tana miqa mashi kwanon abincin hannunta.
Bai karbi kwanon ba yace kinga qanwa ta shiga shagon nan ki zauna kici abinci nasan ba'a baki abinci a gida ba shiyasa nace ki kawo man abincin da kanki.
Toh kai yaya me zakaci idan naci wannan abincin?
Ke ni bansan iyayi maza je kici abinci naci abinci a kasuwa kafin na taho, dama yunwa takeji hakan yasa cikin mintuna qalilin ta gama cin abincin.
Bayan ta cinye ta fito tace yaya na gama bari na koma kar gwaggo ta nemi ni,bai hanata ba yace toh shikenan qanwata kiyi maza ki koma gida kar ki tsaya ko ina kinji.
Toh yaya baxan tsaya ko ina ba,daga haka ta dauka kwanon abincin data kawo masa ta koma gida.
Haka ya cigaba da faruwa kullum a rayuwata babu hutu har sai ranar da Allah ya kawo su Ummi suka siya gidan dake gefen gidan mu.
A ranar da suka tare ita da danta ta shigo gidan mu suka gaisa da matan kawu Hadi gwaggo Mariya da gwaggo Hasiya.
Tace masu su fulanin jeji ne sun taho tare da yan uwansu a hanya aka kashe yan uwansu su kadai suka tsira.
Mace me faran faran bayan sun gama gaisawa tace toh innar yara a temaka man da ko yarinya daya ce ta taya ni gyara gidan aradu yayi qura da alamun an dade ba'a shiga ciki ba.
Dariya gwaggo Mariya tayi tace gaskiya kam an dade babu mutane a ciki toh shikenan sai ki tafi da Maimuna ta taya ki.
Ina jin ta fadi haka na saka takalmi na da mayafi nabi bayanta,bayan mun gama gyara gidan matar ta dakko take away na abinci ta miqo man.
Kallon ta nayi sannan nace a'a na qoshi, kallo na tayi tace ashe kuwa baza mu shirya dake ba, duk wannan uban aikin da muka yi kice baza ki shi abinci ba?
Maza ki dauki abincin nan kici kinji Maimunatu, bana son yi mata musu hakan yasa na dauki abincin na fara ci,ban san lokacin dana cinye abincin nan ba duka don yayi man dadi sosai rabon da naci irin wannan abincin tun ina gida.
Dariya tayi man tace da kika she kin qoshi gashi nan kin cinye duka,
Dariya nayi na boye fuskata alamun naji kunya,haka nan naji ina qaunar matar,muna ta hira da ita sai ga wani saurayi yayi sallama.
Bayan an amsa masa ya shigo hannun shi riqe da ledoji zama yayi gefen matar yace Ummi sannu da hutawa amsa mashi tayi da yawwa.
Sannan ta dora da har ka dawo Abdul?gyada mata kai yayi alamun eh,Ummi tace Maimunatu wannan dana ne sunan sa Abdul juyawa nayi na kalleshi sannan nace masa yaya Abdul ina yini lafiya qalau ya amsa man.
Ganin kaman magana zasuyi yasa nace toh Ummi na tafi na fadi sunan da naji ya kira ta dashi murmushi tayi tace ba dai zuwan Abdul bane ya koreki?
Murmushin nima nayi a'a Ummi zanje na dora girkin dare ne,kallon rainin wayo Abdul yayi mata ya maida kanshi qasa da dan alamun mamaki ummi tace yar qarama dake kike girki?
Dariya tayi tace kai Ummi babba ce fa ni dariya itama tayi tace toh shikenan maza kije amma a zuciyarta tana mamakin dalilin da zai sa a saka yarinya qarama girki bayan da ta shiga taga yan mata a gidan.
Bata saka komai a ranta ba ta cigaba da harkokin ta,ina komawa gida gwaggo Mariya ta rufe ni da masifa naje nayi zamana bayan nasan zan dora girkin dare.
Haƙuri na bata na fara qoqarin hada wuta,bayan na hada wuta na dakko garin masara na kwaba shi da ruwa sannan na dora ruwa akan tukunya.
Bayan ruwan ya tafasa na dakko wannan garin masaran da na kwaba na zuba,ina ta juyawa amma yaqi yayi kauri.
Tsoro ya kamani na qwalawa gwaggo Mariya kira daga daki ta fito tana bala'i uban menene kike man kiran mafarauta.
Jikina na karkarwa nace kinga yaqi yin kauri ina ta juyawa amma yaqi yin kauri kallon tukunyar tayi sai kuma tace toh ina garin da zaki zuba ki tuqa tuwun dashi?
Zazzare ido na fara yi saboda ban rage komai ba duka na kwaba shi na zuwa,ganin ban ce komai ba yasa tace zaki dena zazzare man idanu ko sai na tsire su.
Ina tambayar ki ina garin da zaki tuqa tuwun dashi,sai da na sunkuyar da kai sannan nace ban rage ba duka na juye.
Salati ta fara sai kuma ta wawuri iccen dake cikin wutar da nake girki dashi ta fara duka na ina ihu ina bata haquri amma bata saurareni ba.
Gwaggo Hasiya ma ta fito aka fada mata abinda nayi ita ma ta dauki wani icen ta fara duka na.
Ihun da nake yi ne ya janyo hankalin Ummi dake gidanta, da sauri ta janyo hijabinta ta shigo gidan.
A daidai lokacin da ta shigo nayi wani irin qara na fadi a sume abin da ta gani ne yasa ta rufe bakinta tana fadin Subhanallah me nake gani da sauri ta janye ni gefe tana jijjigani.
Dauka ta tayi ta fita dani daga gidan zuwa gidanta,akan tabarma ta aje ni ta dakko ruwa tana shafa man a fuska.
Abdul ne ya fito daga dakin shi yaga abinda ke faruwa mafifici ya dakko yazo ya zauna a gefen da nake kwance ya fara yiman fifita.
Ajiyar zuciya na fara saukewa a jejjere can kuma na fara fadin don Allah gwaggo kiyi haquri wallahi bazan qara ba don Allah kiyi haquri.
Dagoni Ummi tayi ta rungumeni tana shafa baya na alamun rarrashi tace ya isa haka babu abinda zasu yi maki kinji sai da naji muryarta sannan na bude idanu na a hankali ina kallon su.
Duk da ba wani sanin su nayi ba amma na fahimci tausayi daga fuskar Ummi da kuma tsantsar bacin rai daga Fuskar yaya Abdul.
Bayan na gama dawowa hayyaci na ya saka takalmin shi yace Ummi ina son ki bani izini na shiga gidan nan ya kamata a bima yarinyar nan hakkinta.
Hannunshi ta kama ta riqe tace haba Abdul so kake tun yau ka fara nuna halin naka?
Kayi haquri ka kyale su kaji,amma Ummi....
Idan har izini na kake nema to ban baka ba amma kuma idan zaka yi gaban kanka sai na qyaleka jin ta fadi haka yasa yace shikenan kiyi haquri ya fada yana neman wuri akan tabarmar ya zauna.
Ummi ce ta kalle ni tace ina mamanki Maimunatu a dan wayo da hankalin da nake dashi na bata labarin iya abinda na sani da kuma wanda naji mutane na fada.
kallon tausayi suka rinqa bina dashi daga ita har yaya Abdul,lokacin da dare yayi bayan kawu Hadi ya dawo daga kasuwa Ummi dakanta ta sa yaya Abdul yaje yayi sallama da kawu Hadi ya fada masa abinda ke faruwa.
But to his surprise sai kawu Hadi yace ai abinda ya kamata ayi mata kenan da girman ta zata na bata abinci yaya Abdul was shocked da yaji abinda Kawu ya fada yace yanxu Maimuna ce babba?.
Qwarai da gaske yaya Abdul ganin baza su taba fahimtar juna ba yasa yayi masa sallama ya dawo gida yana fadawa Ummi abinda ya faru.
Shiru tayi tana tunani sallamar da daya daga cikin yaran gidan mu yayi ne ya katse ma Ummi tunanin da take yi.
Babu ko ina yini yace ke Maimunatu wai kizo,babu yanda na iya haka nayi ma su Ummi sallama na tafi gida.
Ina shiga cikin gidan kawu Hadi ya ranqwasheni yace munafuka daga zuwan mutane har kin fara musu shishigi ko?
Gwaggo Mariya da gwaggo Hasiya suma suka fara shegiya jikar arna,mu dai an kawo mana irin bala'i dai a zuri'ar mu.
Ni dai bance musu komai ba har suka gama mitar su suka yi shiru, a haka na cigaba da rayuwa Ummi kullum zata sa a kira ni ta bani abinci tunda ta lura ba'a bani abinci a gidan.
Tun suna surutu akan na fiya zuwa gidan Ummi har suka dena bayan na fada musu aiki nake yi mata don nasan hakan ne kadai zaisa su barni na cigaba da zuwa gidan.
A kullum idan na gama aikin gida zan wuce gidan Ummi muyi ta hira,a kwana a tashi yau su Ummi suka cika wata biyu da zuwa qauyen mu.
Wata rana muna zaune ina tsife ma Ummi gashinta tace Maimunatu nace Na'am Ummi.
Wani satin idan Allah ya nuna mana zamu bar qauyen nan fah, da sauri na daga kaina na kalleta nace amma dai ba dagaske kike ba ko?
Ɗan murmushi tayi wanda iyakarsa lebe tace dagaske nake Maimunatu amma ai zaki bimu ko?
Dariya nayi nace ai kawu Hadi bazai bari ba,gyada man kai tayi tace haka ne amma zanyi masa magana.
A ranar da daddare Ummi ta saka mayafinta ta tafi gidanmu.
Ta zo shiga cikin gidan taji gwaggo Mariya na fadin banda iskanci shi dan gidan me garin ya rasa kaf cikin yaran da aka haifa a gidan nan ya rasa wacce zaice yana so sai dangin arna.
Ga yan mata nan a gidan kala kala amma ya nace sai ita,da Mallam ya zo man da maganar haka na shiga na fita na hana ai da raina bazan taba bari wani abu me kyau ya rabi Maimunatu ba.
Itama gidan da ta nace tana zuwa nasan ba wani abin arziqi garesu ba shiyasa na qyaleta take zuwa.
Bayan Ummi taji wadannan maganganun sai ta fasa shiga ta juyo ta dawo gida a qofar gida suka hadu da yaya Abdul yana kallon fuskarta yasan something is wrong don haka ya riqe hannunta ya shigo da ita ya zaunar da ita akan tabarma.
Sannan yace man na debo mata ruwa tasha,bayan na kawo mata ruwa ta sha yaya Abdul ya tambayeta me yake faruwa?
Sai tace masa babu komai ta kalleni tace Maimunatu keje gida kinga dare yayi kar ayi maki fada tashi nayi nace masu sai da safe.
Bayan na tafi Ummi ta bawa yaya Abdul labarin abinda taji sannan ta riqe hannunshi cikin nata tace ban taba neman wani abu a wurin ka na rasa ba.
Yanxu ma na yanke wani hukunci a cikin raina ina fatan baza ka bani kunya ba,koda hukuncin dana yanke bai yi maka dadi ba ina neman alfarma a wurin ka kar ka watsa man qasa a ido.
Hannunta dake cikin nashi ya qara damqewa yace babu wani hukunci da zaki yanke a rayuwata naga kinyi man ba dai dai ba,ni mai biyayya ne akan duk wani hukuncin da zaki zartar a kaina.
Shafa kanshi tayi ta ce ina roqon Allah ya albarkaci rayuwarka ya sada ka da farin ciki na har abada.
Washe gari da safe kafin kawu Hadi ya fita kasuwa Ummi taxo gidan mu bayan sun gaisa da matan kawu Hadi tace masu wurin kawu Hadi tazo tana son suyi magana da shi.
Gwaggo Mariya ce ta shiga dakin shi tayi sallama dashi bayan ya fito suka gaisa tace dama alfarma nazo nema kawu Hadi ne ya katseta ta hanyar cewa Allah yasa ba kudi bane don kuwa jiya nima naje kasuwa babu kudi a hannu na.
Murmushi tayi tace ba maganar kudi bace dama dan waje na ne yaga yar wurinka Maimunatu yake so a bashi ita aure.
Gwaggo Mariya najin haka ta rangada guda tace Alhamdulillah wallahi naji dadin wannan magana ai dama ina ganin yaron idan na fita kana kallonshi kaga nutsattsen yaro.
Wallahi nayi na'am da wannan hadin girgiza kai Ummi tayi saboda tasan da wani abu a cikin ranta shiyasa take ta wannan maganganun.
Gwaggo Mariya ce ta kalli kawu Hadi tace Mallam kasan irin wannan maganar ba'a sanya kamata yayi ace kafin ta bar gidan nan a daura masu auren kaga hankalin kowa sai yafi kwanciya.
Toh shikenan bari naje na sanar da yan uwana sai ayi abinda ya kamata,don kar su zargi wani abu yasa Ummi tace amma maganar aure magana ce ta kudi kuma a yanxu gaskiya bamu da kudi amma da za'a iya daga mana qafa idan muka samu kudin sai ayi.
Ba dai sadaki bane ai ana iya yi akan bashi babu damuwa daga baya sai ku kawo gwaggo Hasiya ta karbe zance.
Jin abinda suka ce yasa Ummi tace toh shikenan bari naje wurin Mallam Liman sai ya zama wakilin Abdulhakeem tunda nace maku mu Fulanin jeji ne bamu da sauran wasu dangi da suka rage mana.
Babu musu suka amince,bayan taje ta samu Liman tayi masa bayanin abinda ke tafe da ita yace mata babu komai kuma in shaa Allah shi da kanshi zai biya wa Abdul sadaki saboda yaron yana da nutsuwa duk sanda suka hadu sai ya gaishe da shi.
Godiya tayi masa sannan ta dawo gida,
bayan ta dawo ta sanar da yaya Abdul abinda ake ciki sannan ita da kanta ta dakko masa sabuwar farar shadda a cikin kayan sa ta bashi tace ya saka sannan yaje ya samu Liman.
Bayan ya gama shiryawa ya wuce gidan Liman yana zuwa suka gaisa sannan yayi masa godiya Mallam Liman yace babu komai ai Mallam Hadi yazo ya sameni yace tunda yanxu za'ayi sallar azahar da an idar da sallah sai a daura auren.
Gyada kai yayi yace toh shikenan Allah ya kaimu,bayan an idar da sallah akayi sanarwa cewa akwai daurin aure da za’a yi, Liman ne ya matso gaban su Mallam Hadi bayan anyi siga ya bada sadakin Maimunatu.
Bayan an kammala duk wasu procedure na aure sanqira yayi sanarwa cewa an daura auren Abdulhakeem Muhammad da kuma amaryar sa Maimunatu Al-qaseem.
Tunda gwaggo Mariya taji an daura aure ta hada kayana baki daya ta taho dani gidan Ummi har lokacin ban san abinda ke faruwa ba.
Sai bayan tazo tsakar gida tace toh Maimunatu yau dai an daura maki aure da wannan yaro Abdul kuma banga amfanin zaman ki a gidan ba shiyasa na kawo ki gidan su mijin ki.
Sai a zauna ayi ta haquri muma duk haqurin muke yi sai da ta juya zata tafi tace toh Allah ya bada zaman lafiya.
Shesheqar kukan da nake yi ce ta fito da Ummi daga bandaki tana gani na tace Subhanallah Maimunatu lafiya?
Ba ina kuka bane saboda aura man yaya Abdul da akayi A'a ina kuka ne akan wulaqantaccen auren da akayi man kamar mara gata duk da shekaru na baza su wuce sha shida amma nasan ba haka ake aurar da kowace yarinya me gata ba.
Nasan da mahaifina nada rai hakan bazai faru ba ko kuma da a wurin mahaifiyata nake bazata bari a wulaqantani ba.
Ganin ina kuka yasa Ummi ta rinqa bani haquri har nayi shiru,bayan auren mu da kwana shida Ummi ta kama hannu na muka shiga gidan kawu Hadi tace masu munxo yi masu sallama ne akan zamu qara gaba.
Tunda dai an san fulanin jeji basu zama wuri daya,babu wanda ya tambayeta ina zamu koma suka ce toh Allah ya tsare gwaggo Hasiya hada yin kukan munafurci tana cewa Allah sarki Maimunatu yarinyar kirki zamuyi kewar ki.
Murmushi nima nayi nace nima zanyi kewar ku gwaggo,washe gari da safe muka hau mota da zata kawo mu cikin gari.
Bayan mun zo cikin gari muka hau motar kaduna,wannan shine farkon zuwa na kaduna don haka nayi ta kalle kalle a hanya bayan mun sauka a tasha muka hau adaidaita sahu.
Yaya Abdul yace masa Malali zai kaimu ya bashi kudin shi sannan muka shiga a qofar wani gate ya ajiye mu sauka mukayi mai gadin gidan tunda yaga Ummi yake ta yaqe haqora yace sannun da dawowa hajiya.
Alhaji sannun da dawowa,amsa mashi suka yi da yawwa sannan Ummi ta kama hannu na muka shiga ciki.
Ba wannan bane karo na farko dana fara ganin manyan gidaje don haka ban wani tsaya kalle kalle ba.
Ɗaki Ummi ta nuna man tace na shiga nayi wanka na huta.
Washe gari da safe bayan mun gama breakfast Ummi take bani labarin su suwaye.
Su dun mutanen kaduna abinda kuma ya kawo su qauyen mu yaya Abdul ma'aikacin DSS ne,labari ya kai musu cewa akwai yan ta'adda dake zaune a cikin jejin dake qauyen mu shiyasa aka aiko shi yayi bincike.
Basa son a gane ko su suwaye shiyasa sukayi disguising kansu a matsayin fulani,bayan ta gama bani labari ta tambaye ni a ina na tsaya a school na fada mata lokacin day nayi JSCE ne su kawu suka zo suka tafi dani.
Lokacin da yaya Abdul zai fita tace masa idan ya fita ya samo man admission a wata makarantar don karatu zan cigaba yaso yace shi matarshi bazata cigaba da karatu ba Ummi naganin take taken sa tace Abdul ni zaka nuna wa iyaka ta akan matarka?
Toh wallahi baka isa ba kuma ina son kaji ni da kyau baza ta tare ba sai bayan ta kammala secondary school dinta.
kallon Ummi yayi da mamaki amma bai ce komai ba tun daga ranar Ummi ta dawo dani dakinta abinda ke hada ni da yaya Abdul kawai sai gaisuwa ko kuma a wurin cin abinci.
Har sai da na gama secondary school tun bayan da na gama secondary school Ummi keta bani wasu abubuwa da ban sansu ba wata rana muna zaune a parlour nida Ummi yaya Abdul ya shigo riqe da wata takadda a hannun shi.
Ummi ya miqa ma yace admission letter dina ce na sami admission a KASU zan karanta mass communication Ummi tayi farin ciki sosai tayi ta shi mana albarka har ya tashi zai tafi tace emmm Abdul yace Na'am idan ka dawo da daddare kazo ka dauki matarka ku koma gidan ku kaji.
Durqusawa yayi yace toh Ummi mungode Allah ya qara girma tace amen tun daga ranar muka koma gidan mu sai dai muxo mu gaida Ummi mu koma.
Ana haka har na gama karatuna na fara aiki yanxu abinda ya kawo mu Abuja bikin yarinyar qawar Ummi akayi muka zo.
An gama bikin zamu koma kaduna ne muka yi accident,tunda Maimunatu ta fara magana Jay take goge hawaye bayan ta gama tayi hugging dinta tace I'm sorry that you have to go through all of this alone.
Munarh dan murmushi tayi tace ai ya wuce Jay kar ki damu,mom kasa ce mata komai tayi sai kallonta take yi can kuma ta juya wurin Ummi tace thank you so much for taking care of my daughter.
Murmushi Ummi tayi tace ai Maimunatu nima yata ce...........................