Page 1.
by @zeeykumurya
BARA A KUFAI
1.
Dare mahutar baya da kowanne ɗan Adam yake yada haƙarƙarinsa a ƙasa domin ya huta, musamman a irin wannan yanayin na tsakiyar damuna.
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, gari ya yi tsit, mutane da dabbobi kowa ya nemi gurin fakewa saboda ruwan saman da ake kamar da bakin ƙwarya.
Duk da karfin ƙarar ruwan da yake sauka hakan bai hana nishin da take yi cika ɗan ƙaramin ɗakin ba.
Idan aka ce mata akwai wani raɗaɗin ciwo a duniya da ba taɓa ɗanɗana shi ba take za ta ƙaryata ba tare da ta bari wanda ya furta ya gama rufe bakinsa ba, saboda tarin raunukan mabanbantan ciwuka da ta rayu da su a cikin zuciyarta, wanda a kullum suke cikin famuwa maimakon waraka. Amma a yau da take durƙushe a kan gwiwoyinta cikin azabar ciwon da ba ta taɓa jin irinsa ba a rayuwarta komai ya goge mata, ta kuma tabbatar mutuwa za ta yi, ranar barin ta duniya ce ta zo shi ya sa har ta nemi waɗancan ciwukan na baya ta rasa sai wannan kawai take ji.
Duk wani ƙarar saukar ruwan saman da yake zuba a rufin kwanon ɗakin da take, ji take tamkar a kanta yake zuba yana ƙara mata azabar da take ji.
"Innalillahi wa'inna ilahiraji'un!" La'ilaha'illallhu Muhammadur Rasulullahi!
Ta furta cikin wata iriyar murya tana jujjuya kanta a matuƙar galabaice.
"Ku taimake ni don Allah! Ku kai ni asibiti!" Ta ƙara faɗa numfashinta na sama kamar zai bar gangar jikinta.
Tsaki matar da ke zaune a gefen gado tana kallon ta a wulaƙance ta ja tare da keɓe fuska ta ɗauke kanta daga gurinta, fuskarta babu alamun tausayi ko kaɗan.
Murɗawar da cikinta ya yi mata ya sa ta buɗa murya ta zabga salati, saboda azabar ciwon da ta ji da ya zarce na baya, wani irin gumi ne yake tsatstsafowa a jikinta, ƙarfen gadon dakin da take riƙe da shi ta ƙara damƙewa tamkar za ta ɓalle shi, cikin fitar hayyaci ta damtse leɓenta na ƙasa tare da sakin nishi da ƙarfi.
Ganin yanayinta ya sa matar da ke bakin gadon saurin sakkowa ta ware ƙafafunta ta fara taimaka mata cikin zafin nama da mugunta har jaririn ya fito duniya, a take kukansa ya cika ɗakin. Ƙaƙƙafar ajiyar zuciya ta sauke ta yi baya ta zauna sharaf tana mayar da numfashi, kamar an zare gashi daga tandar mai haka ta nemi ciwon ta rasa, duk da ba ta ga abin da ta haifa ba bare ta san wanne jinsi ne amma kukansa da ya cika mata kunnuwa ya haifar mata da wani abu mai girma a cikin zuciyarta, ta ji ta yi mata nauyi kamar an ninka mata ita biyu, ta ji ƙaunar shi na bin duk wani lungo da saƙo na jikinta tana samar wa kanta mazauni.
A hankali ta ɗaga kanta ta zuba masa idanunta da suka yi mata nauyi, dishi-dishi take kallon matar da take goge masa jiki da wani farin yadi. Hannunta ta ɗaga da yake yi mata ƙaiƙayi saboda zumuɗin ganin shi a jikinta, ta saita shi tana jira kawai ta ji ta sako mata shi kamar yadda take jin labarin ana yi.
Turo ƙofar ɗakin da aka yi a haukace aka shigo ya sa ta mayar da idonta gurin ƙofar, wata mummunar faɗuwa gabanta ya yi ganin wadda ta shigo, da sauri ta ɗauke kanta tare da fara ambaton sunan Allah a cikin ranta.
"Goge-gogen me kike yi haka ne?" Ta faɗa a tsawace tana kallon mai riƙe da jaririn.
Ba ta jira amsar ta ba ta ƙara faɗin. "Abin da ya fito daga jikin wannan najasar kike ƙoƙarin tsaftacewa kamar kowanne ɗa? Ko kin manta ɗauɗar da take tattare da ita ne? Wadda ko ruwan duniya za a tara a wanke ta da shi ba za ta taɓa fita ba."
Mai riƙe da jaririn ba ta ce komai ba ta kwantar da shi a ƙasa. Hakan ya sa wadda ta shigo jan ƙwafa, a fusace ta ƙaraso ta fizgi hannunta ta miƙar da ita tsaye a wulaƙance, cikin galabaita ta ja zanin jikinta da ƙasansa ke jiƙe da jini ta tallafe shi a ƙirjinta da ɗayan hannun, idonta duka a waje cikin tsananin tsoro. Jan ta ta fara yi kamar farin shigar layya ya siyo rago, ta so turjewa ko don ta ɗauki abin da ta haifa da yake ta tsala kuka, amma kasancewar jikin nata babu kwari ko kaɗan ya sa hakan ya gagara. Ganin sun fice daga ɗakin ya sa ta tsaya duk da jirin da take ji, a raunane ta ce. "Duk da ban san inda za ki kai ni ba amma don Allah ki bari na ɗauki ɗana." Ko tsayawa ba ta yi ba bare ta juyo ta kalle ta, ta ci gaba da jan ta a cikin ruwan kamar mushen dabba, a soro suka tsaya ta zare sakatar gidan ta hankaɗa ta waje, cikin kakkausar murya tana zare idanunta masu ban tsoro ta ce. "Na sha faɗa miki abubuwa da yawa a baya amma kina ɗaukar su wasa, to yau zan tabbatar miki da bana faɗar abin da na san ba zan iya aikatawa ba, a cikin daren nan, a cikin ruwan nan na kore ki daga gidana da rayuwarmu kora ta har abada, don haka ki san inda dare ya yi miki, kar na ƙara buɗe gidan nan na gan ki, wallahi! Wallahi idan ba ki tafi ba kika tsaya ni kaɗai na san abin da zan yi miki!" Daga haka ta tura ƙofar gidan da ƙarfi kamar za ta ɓalla ta, ta mayar ta rufe.
Da sassarfa ta koma ɗakin da suka baro, ganin matar da suka bari da yaron ta kuma ɗaukar shi ya sa ta yi mata wani kallo tare da faɗin. "Na lura kamar tausayi ya fara ratsa zuciyarki akan wannan aikin ko?" Da sauri ta girgiza mata kai ta ce. "Ko ɗaya." Sai da ta zauna a kusa da ita tana kallon jaririn sannan ta ce. "Tunda mun samu jinin haihuwar ita kuma na kore ta je ki cilla abin da aka haifa cikin rijiya." Ba ta amsa ba, ba kuma ta yi musu ba ta miƙe ta fice daga ɗakin.
Wani murmushi ta saki ta ja farin yadin da aka goge jinin jaririn ta nannaɗe ta miƙe ta fice da shi a hannunta, ba tare da ta damu da jiƙewar da jikinta ya yi ba.
***** ***** ******
*MAFARI*
Katon guri ne da ya kasance a rufe ruf wanda aka gina shi da zallar mulmulallen dutse mai ƙyalli da ɗaukar ido. Babu komai a cikinsa sai wasu mutane su bakwai tsirara da ɗaurin jan ƙyalle a ƙugunsu. Suna tsaye riƙe da wani baƙin zare sun zagaye wani rami da yake fitar da hayaƙi yana turniƙe su. A hankali hasken da ke gurin ya fara ɗaukewa, duhu ya mamaye su, tartsatsin wuta ya fara fesowa daga cikin ramin gami da sautin magana cikin wani irin amo mai razanarwa.
"Jini da jini sun haɗu sun ƙosar da Ƙanzula! Amma Ƙanzula na buƙatar jinin goɗiya mai jan tauraro! Wadda ke shaƙar numfashi ɗaya da ɗaya daga cikinku! Ku yi gaggawar kawo ta ga Ƙanzula! Za ku yi farinciki da haka! Za ku samu abin da ba ku taɓa samu ba daga Ƙanzula! Ƙanzula na buƙatar godiyar nan da gaggawa!"
Daga haka sautin ya ɗauke ɗif! Hasken gurin ya dawo, zaren hannunsu ya fara komawa cikin ramin da kansa, tartsatsin wuta da hayakin suka ɗauke kamar ba su taɓa wanzuwa ba, ramin ya haɗe kansa ya rufe ruf ba tare da ya bar wata alamar ƙofa ba.
A hankali suka juya suka yi layi, idanunsu a rufe suka nufi wata siririyar hanya, bangon gurin kawai na gaban ya shafa ƙofa ta bayyana ta buɗe kanta, ba tare da sun buɗe idanun ba suka shige.
Ƙaton ɗaki ne mai yalwar haske, na farkon ya zura hannayensa biyu cikin wata jakar fatar zaki da ke maƙale a bango ya ɗauko wata ƙwarya da ke zagaye da harsuna a manne a jikinta ya kafa bakinsa ya fara ɗiɗɗikar baƙin jinin da yake ciki. Sai da suka sha ɗaya bayan ɗaya sannan suka nufi wata ƙofa a cikin ɗakin suka fice suna karanta wasu irin ɗalasumai.
Wani makeken parlour da ya ji komai na kayan alatu suka ɓulla, sai a lokacin suka buɗe idanuwansu, kowa ya nufi inda ya ajiye tufafin jikinsa ya ɗauka ya fara suturta jikinsa. A take su shida suka fito cikin shiga ta kamala, manyan rigunan jikinsu suka ƙara fito da haibarsu, hulunan kansu suka ƙawata fuskokinsu zuwa ta manyan alhazai masu madafan iko, tamkar ba su ba ne naked a mintina ƙalilan ɗin da suka shuɗe.
"An ja shekaru Ƙanzula tana batun wannan goɗiyar amma har yau mun gagara samo ta, abin da bai taɓa faruwa ba tun kafuwar wannan ƙungiyar, anya kuwa babu wanda yake shirya wata manaƙisar a cikinmu a ɓoye? Tunda a kullum sai Ƙanzula ta faɗa mana yarinyar nan tana kusa da ɗayanmu."
Ɗaya daga cikinsu ya faɗa yana saka glasses a fuskarsa.
Kallon shi suka yi a tare kafin wani guntu mai sanƙo ya jijjiga kai ya ce.
"Kuma fa ka zo da magana abar dubawa Janwuya, ban da haka me Ƙanzula ta taɓa buƙata daga gare mu muka gagara ba ta? Wa ne namu ba mu bayar ba? Sai wannan ce kawai za ta gagara?"
Janwuya ya yi taku biyu yana yi musu kallon ƙasan ido ɗaya baya ɗaya, cikin tsanaki ya ce. "Na fara tunanin ko ma wane ne ya gano wace ce goɗiyar, ya ƙi bayyana mana ita ne kawai saboda yana da wani plan nasa a kanta, ko yana so ya kawo wa Ƙanzula ita a sirrance ya samu tagomashin da ta ce shi kaɗai, ko kuma yana yi mata soyayyar da ba zai iya bayar da ita ba."
"Koma yaya ne, ko a ina take ni sai na nemo ta na kawo ta! Wannan alƙawari ne na ɗaukar wa kaina!"
Wadda ta kasance mace ɗaya tal a cikinsu ta furta tana wani irin murmushi.
Jinjina Janwuya ya yi mata ya ce. "Duk abin da kika faɗa tabbatacce ne a gurinmu saboda sanin ƙwazonki, na san za ki iya, muna nan muna jiran zuwan wannan ranar da Ƙanzula za ta yi farincikin da ba ta taɓa yi ba, ƙungiya ta samu abin da ba ta taɓa samu ba, Baƙin dage ya yi kalaci da jan tauraro da ya yi shekaru yana tsumayi, dakarun BAƘIN GIDA su yalwata da arziƙin da ba su taɓa samu ba, ke kuma ki samu ƙarin girman da kowa yake ƙulafuci!"
Jinjina suka yi mata a tare fuskokinsu ɗauke da fara'a, ban da mutum ɗaya da ya ƙura mata ido fuska a haɗe yana jifan ta da wani irin kallo.
***** ***** ******
Gida ne ginin ƙasa mai babban tsakar gida da aka jera masa ɗakuna daga farkon gidan har ƙarshe a kowanne bango na kudu da arewa suna fuskantar juna. Daga can ɓarin yamma kuma rijiya ce a hannun dama sai banɗaki daga hannun hagu, ƙofar shigowa da ɗakin soro na maza kuma daga ɓangaren gabas.
Ita kaɗai ce a durƙushe a bakin rariya tana wanki, kamar baƙuwar gidan haka take bin ko'ina da kallo tana hasaso yadda gidan zai kasance a cikin ranta duk ranar da aka ce babu waɗannan rakwacam ɗin shirgin da ko lokacin damuna ba a kwashe su duka. Numfashi ta sauke ta ɗauke idonta daga kan tukwane kusan shida da suke kusa da ita da ragowar kayan wanke-wanke, ta sauke idanun nata a ƙofar ɗakin Inno da shi kaɗai ne a gyare kaf gidan, sabuwar filasta da fentin da aka yi masa suka ƙara ƙawata shi, ga tiles masu ɗaukar ido da aka shafe ɗan tudun da ke ƙofar ɗakin da shi.
Motsin fitowar da ta ji ya sa ta saurin kallon inda take jigo sautin. Zeenat ta ce ta fito sanye da ɗaurin ƙirji tana hamma, ta taho fakam-fakam ta wuce ta shige toilet bayan ta bangaje ta. Ba ta ko ɗaga ido ba ta ci gaba da wankin da take.
"Ahayan! Ahayan!"
Muryar Umma Lantana ta karaɗe kunnuwanta. Da sauri ta tsame hannunta ta ɗauraye tana amsa mata.
"Wanke mini tukunyar da na yi tuwo jiya zan ɗora ɗumame, ban san rana ta yi haka ba ga shi Zeenat za ta je makaranta."
Ahayan ta amsa mata cikin girmamawa sannan ta janyo tukunyar ta fara ƙoƙarin wankewa.
Daidai lokacin Inno ta buɗe ƙofar ɗakinta ta fito cikin tafiyar ƙasaita tana cika da batsewa, fuska babu annuri take duban Ahayan a wulaƙance.
"Ke!"
Ahayan ta ɗaga kai da sauri ta kalle ta, duk da a tsugunne take amma sai da ta ƙara rankwafawa, a ladabce ta ce. "Ina kwana?"
"Janyo mini ruwa ki cika mini bokitin can!"
Cewar Inno cikin gadara tana hure hanci ba tare da ta bi ta kan gaisuwar da take yi mata ba.
Da sauri Ahayan ta ajiye tukunyar hannunta ta nufi gurin rijiya ta kama igiya ta fara janyowa.
"Idan kika janyo ruwan nan ba ki gama abin da na saka ki ba wallahi sai na tura ki kin bi gugan cikin rijiyar, idan ya so sai ki zuƙo mata ruwan ta baki da hanci."
Umma Lantana da ta tunkaro inda take ta faɗa a fusace tana gyara ɗaurin zanin jikinta.
A tsawace Inno ta ce. "Ke yi mini abin da na saka ki kafin na saɓar miki, kin kuma san bana son yawa maimaita magana ko?"
Tsayawa kawai Ahayan ta yi tana kallon su cikin tsoro, ta san halin kowaccensu da kalar muguntarta, babu abin da ya faru ma sun gana mata azaba ina ga sun samu dalili. A marairaice ta ce. "Don Allah ku yi haƙuri, duk zan yi muku abin da kuke so yanzu."
"To fara yin nawa tunda ni na fara saka ki!"
Cikin izza Inno ta taka zuwa kusa da Umma Lantana, lokaci ɗaya ta ja baya kamar wadda aka tsikara tana toshe hanci, a wulaƙance ta ce. "Wallahi sai ta zuba mini ruwan nan sannan za ta bar gurin nan, ke har kin isa a gidan nan na saka abu ki ce sai na jira an yi miki naki sannan za a mun? Wace ce ke? Ƙazama da ke kina fama da warin hammata da kwantsar ido ki ce da ni za ki dinga takara? To ki kama kanki kafin na kama miki shi da igiyar da za ta wujijjiga rayuwarki, ki kuma fita a sabgata na faɗa miki!" Ba ta jira cewar Umma Lantana ta kalli Ahayan a fusace ta ce. "Za ki yi abin da na saka ki ko kuma?" Idon Ahayan cike da ƙwalla ta gyaɗa mata kai da sauri cikin tsoro ta fara jan ruwan. Kamar wadda aka cilla haka Umma Lantana ta yi tsalle ta damƙo rigarta ta baya ta janyo ta, ta hankaɗa ta. A ɗimauce Ahayan ta saki gigitacciyar ƙarar da ta cika gidan.
****
Matashiyar budurwa ce zaune a ƙaramin tsakar gidansu tana latsa wayar hannunta, a hankali ta yi zooming status ɗin ƙawarta da ta saka hotunan anniversary na iyayenta, yadda suka jeru a ƙaton parlon gidansu ba ƙaramin burge ta ya yi ba, gabaɗaya matan suna sanye da baƙar abaya da ta ƙara fito da hasken fatarsu, a fili ta furta "Wow." Tare da ƙara faɗaɗa murmushin fuskarta ta ci gaba da kallon status ɗin.
"Hasina! Hasina!"
Ɗago kanta ta yi tare da amsawa, lokaci ɗaya murmushin fuskarta ya ɗauke, ta tsaya kawai tana kallon Amma da take ta fama da hura wutar ice, ta haɗa gumi ta yi sharkaf sai share idonta take saboda hayaƙi.
Fuskar Amma a washe ta ce. "Ki je ki gani idan an gama markaɗen ƙosan ki karɓo mini." Baki Hasina ta zunɓura tare da cunkushe fuska, cikin ƙunƙuni ta ce. "Gaskiya Amma ki nemi almajiri, da girmana da class ɗina kawai a ga ina ɗauko markaɗe a ƙaton bokiti? Salon duk wanda na haɗu da shi ya san ƙosai ake siyarwa a gidanmu?" Baki Amma ta hangame ta ce. "To mene ne a ciki Hasina? Sana'a ce fa ba sata ko wani mugun abun ba." Kamar za ta yi kuka ta miƙe ta zari gyale tana faɗin. "Duk da sana'a ce amma ai a ƙasƙance mutane suke kallon mai yin ta." Amma ta ce. "Sai su yi ta yi, ni dai tunda Allah ya gani neman halak ɗina nake ai shikenan." Za ta kuma magana Amma ta katse ta a tsawace.
"Ki je ki karɓo mini ba jan magana na nema ba, ke da idan ba ki yi musu ba ba kya jin daɗi a rayuwarki."
Baki ta tura gaba ta fice tana ƙunƙuni, tsabar jin haushin aiken ko kuɗin markaɗen ba ta tsaya ta karɓa ba. Bayan ta je ta ɗauko a hanyar dawowa ta ji ana kiran sunanta, da sauri ta ajiye bokitin da ya fara sagar mata da hannu ta juya, wata ƙawarta da suke Islamiyya ta gani tana bin ta da wani irin kallo mai kama da ƙyama, hakan ya sa ta ji duk ta muzanta, da rawar murya ta ce. "Tas..tas...tasneem me ya kawo ki unguwar nan da sassafe haka?" Kallon sama da ƙasa Tasneem ta yi mata ta ce. "Shekaran jiya muka dawo nan baya, ga gidanmu can da muka tare kina shan kwanar can." Ta nuna mata direction ɗin da hannunta sannan ta ci gaba da faɗin. "Ke kuma fa? Daga ina haka na ga kamar markaɗe ma kika ɗauko?" Ta ƙarashe maganar tana leƙa bokitin da Hasina take ta karewa a bayanta.
Yaƙe Hasina ta yi ta ce. "Na zo gidan masu aikin gidanmu ne da muke ba su aikin yi mana ƙosain sadaka, saboda kwana biyu ba sa yi da wuri almajirai suna zuwa su cika a ƙofar gidanmu, shi ne Dad ɗina ya ce na zo na yi musu magana akan haka, da na zo sai suke sanar mini yaron da yake kai markaɗen ne ba shi da lafiya, shi ne na kai musu da kaina saboda' kar Dad ya kuma magana." Wani murmushi Tasneem ta yi ta ce. "Gaskiya ne, amma kin yi ƙoƙari fa, kai markaɗe da kanki, da farko har na fara tunanin ko gidanku ne a nan har zan ce zan bi ki mu je na gani." Da sauri Hasina ta ce. "A'a, ba gidanmu ba ne, mu muna can G.R.A ne na bayan unguwar nan."
Daga haka suka yi sallama Tasneem ta juya ta tafi, ƙaƙƙafar ajiyar zuciya Hasina ta sauke, ranta a ɓace ta ɗauki markaɗen ta ci gaba da tafiya, tana shiga gida ko sallama babu ta fara mita.
"Wallahi daga yau ba zan ƙara kai markaɗen nan ba, da ba don Allah ya taimake ni ba da tuni asirina gama ya tonuwa."
Amma ba ta tanka mata ba ta girgiza kai kawai ta ci gaba da aikinta, a zuciye Hasina ta koma inda ta tashi ta zauna tana ƙunƙuni, hangowa kawai take Tasneem ta biyo ta ta zo ta ga Amma a wannan cukurkuɗen da take, da ba ta san adadin kunyar da za ta kwasa ba a ce ga mahaifiyarta, mai ƙosai da kokon siyarwa da safe, da rana kuma shinkafa da wake da daddare kuma awara, hamdala ta yi ta janyo wayarta ta ci gaba da kallon status ɗin da take, a ranta tana taya su Ameera murna da Mamansu ta kasance kyakkyawa ƴar gayu ƴar boko da ba za su ji kunyar nuna ta a ko'ina ba ko kuma a zo gidansu a gan ta ba, saɓanin ita da Amma kwata-kwata ba ta san wani abu gayu da wayewa ba, kodayaushe tana bakin murhu ko kuma tana kai kawo a aikace-aikacen gida. Kamar wadda aka yi wa mutuwa haka ta rafka tagumi tana fatan da ma a ce bawa shi yake da ikon tsara rayuwarsa, da tabbas ko a kusa da unguwar masu siyar da ƙosai ba za ta zo ba bare kuma a ce mahaifiyarta ce take yi!