A Weekend of Unexpected Warmth
by @zahrabmrs
Yau asabar Tun ƙarfe goma na safe, Tadala ta gama shirinta tsaf. Ta sanya abayar da sadiya ta bata kwance .,wani irin ɗoki take ji Tun ranar da Anty Zaheera ta gayyace ta, take ta sa ran zuwa gidanta sai Yau Allah yayi Ba a jima ba, taji ji ƙarar mota a harabar gidan Awaisu ne ya shigo
Mami, hajiya babba(anty zaheera ) ta Kira Wai na taho da tadala ,Sadiya ta washe baki
To maza, je ki ɗauko jakarki ,Tadala ta yi sauri ta shiga ɗaki ta fito da ƙaramin handbag ɗinta,daidai fitowar dr mariya kenan zata raka bakuwa ganin hakan Sadiya ta gyara wa tadala mata mayafi cikin alfahari
Ki gaishe min da Anty Zaheera sosai ,suka hada ido da dr Mariya wacce da gasken ranta ya baci da Jin Tadala zata gidan zaheera sama sama dr ta amsa gaisuwar Tadala da sadiya ,ta nufi main entrance ta barsu a tsaye ,Tadala Yau Kinga halin mariya ko?Bana fada miki Munafuka bace ?yanzu duba yadda take amsa mana gaisuwa sama Jin zaki gidan zaheera,ikon Allah mami Ashe da gaske ne umma ta bani mamaki ,ay shiyasa gara falmata ita bata pretending Kamar Tana sonka ,sak take dan wallahi Ina ga bamu taba shiga dakin juna ba ,ba ruwanta da kowa a gidan nan ,Yauwa idan kinje gidan zaheera Banda kauyenci ,da fadi baa tambayeki ba ,kar ki manta dangin mijina zaki shiga
Gidan Anty Zaheera wuse 1, Abuja
gate ɗin gidan ya buɗe Tadala ta zaro idanu Lawn mai cike da furanni, fountains guda biyu, da manyan bishiyoyi masu kyau suka kawata wurin ,Motar na tsayawa,
Ta nufi kofar falon ,shiru falon ba kowa ta Nema kujera ta zauna ,Chan Anty Zaheera ta fito cikin atamfa mai launin wine, fuskarta cike da fara’a
Ah ah Tadala saukar Yaushe ,saurin zamewa Tadala tayi kasa dan gaishe da Zaheerah ,Ina kwana Anty.
Zaheera ta kamo hannunta.
Haba! Tsugunnawar me zakiyi ? Zaheerah ta dago Tadala ta rungume ta Wani irin daɗi ya ratsa zuciyar Tadala Tun zuwanta Abuja…
Ba a taɓa rungume ta da wannan irin ƙaunar ba
Tadala ce?
Wata yar matashiya ta fito daga kitchen zatayi shekara talatin ko 29 haka ,Tana ɗauke da wani ƙaramin yaro a hannu Zaheera ta yi dariya Ameerah, ga cousin ɗin Sadiya
Ameerah ta yi murmushi.
Ashe ke ce Tadala? Mommy ta dade tana maganar ki.Ina yini Anty Amira ,hannun Tadala ta Mika Tana amsar yaron hannun ta
wata yar budurwa ce ta sauko daga bene
Mom, is she here already?
Budurwar ta ƙaraso Hi, I’m mardiyyah .Tadala ta yi murmushi ,mardiyyah ta zuba mata ido Wallahi kina da kyau,Tadala ta ji kunya suka gaisa da mardiyya Daga baya wani saurayi mai tsayi ya shigo falon Sanye cikin black T-shirt Ya tsaya yana kallonta
Oh wow So this is the famous cousin from Agadez right?dik suka kwashe da Dariya
Kafin dariyar ta lafa, suka ji wata murya daga sama Mom! Is she here?
Wani saurayi mai kimanin shekara ashirin ya sauko daga bene Idanunsa suka sauka kan Tadala ,Zaheera ta yi murmushi Tadala ga Kamal man waige waige ta fara ganin idan zata ga daddy ,Ina nufin Kamal Junior auta na ,hey Tadala sunana kamal Everyone calls me Junior.And yes, I was named after my mom’s twin brother.nan fa hira ta barke yaran Anty zaheera very friendly Sam basu da girman kai Kamar sun dade da sanin Tadala
Zaheera ta kalli Tadala ,Yau girls’ day ne
da fatan kin shirya Girls’ day Anty ?ban gane ba ?zaki gane zuwa Anjima
Bayan lunch
Zaheera,Ameerah,mardiyyah da Tadala Suka nufi wani katafaren salon na mata Tadala ta kasa ɓoye mamakinta dan beyi Kama da local shagon hajiya Sidiya ba .
kusan duk weekend tana ganin anty sadiya da twins suna fita salon sau da Dama ma su dawo da lalle a hannun su basu taba zuwa da ita ba ,sai gashi Yau An yi mata facial,An gyara mata gashi,An yi mata pedicure,An yi mata manicure
Ta zauna tana kallon kanta a madubi A hankali ta ceAnty…Ban taɓa yin irin wannan ba Zaheera ta juya Da gaske tadala ?
Tun da na zo Abuja… sai dai na wanke kaina da kaina kisto ma Banyi ba ,har yanzu sadiya bata canza Hali ba kenan ?Kar ki damu Tadala yanzu ay kin same ni
Suna dawowa aka Kira mai lalle Nan da nan mai Lallen nasu tazo ta fara,Aka Cigaba da hira Tadala kuwa tuni manta da duk wata damuwa A karo na farko tun zuwanta Abuja…Ta ji kamar tana cikin danginta na jini.
Life Camp Abuja
Nadira ta tsaya a gaban madubi.
Sanye take da wata doguwar rigar mai launin red wacce ta yi matuƙar karɓar jikinta. Ta yi light makeup, ta shafa ɗa jan baki mai sauƙi, sannan ta sauke gashinta a kafaɗa Ta kalli kanta a madubi.
Ta dade batayi kwaliiyar da taja hankalin hankalin mijinta kamar yau ba A hankali ta sauke numfashi Yau kam, Nawaf dole ya lura da ni…Ta sauko falon Nawaf yana zaune a dining table Sanye da T-shirt baƙa da ash joggers, yana karanta wasu takardu yayin da cup ɗin coffee ke gefensa.
Alya tana zaune kusa da shi tana cin pancakes Amma” Alya ta faɗa cikin farin ciki ganin mahaifiyar ta,Nadira ta yi murmushi Good morning, princess Ta sumbaci goshinta
ta ɗaga kai Idanunta suka sauka kan Nawaf Shi ma ya ɗago kai ,Ya kalleta Daƙiƙa ɗaya
Biyu,Uku, a hankali ya furta good Morning.
Ya mayar da hankalinsa kan takardunsa.
Cak Nadira ta tsaya Shi kenan?Morning?
Babu You look nice ,Babu You dressed up.ta zauna a sanyaye
Alya ta ɗaga kai Amma , kin yi kyau yau.
Nan take Nadira ta yi murmushi ,Nagode, sweetheart Alya ta matso kusa da Nadira
Amma Kina ƙamshi kamar flower Nadira ta sumbaci kanta ta dan sace kallon Nawaf
Har yanzu…gogan duba takardunsa take
Wani irin takaici ya taso mata Bayan ta gama breakfast ta koma falo inda ta kunnawa Ayla cartoon ,Chan Bayan azahar
Bayan Nawaf ya dawo daga massallaci ya duba yar tasa Alya, je ki shirya Za mu je Shan ice cream.
Yayy Yarinyar ta yi tsalle ta nufi dakin ta dan already ta Saba nanny ce ke mata komai
Nadira ta ɗaga kai ta kalli nawaf Kai da ita kawai zaku Shan ice cream din ? Ni fa?
Idan kina son zuwa ki shirya, ta zuba masa ido ,wato Idan Tana so?
Ta ji wani abu ya tsaya mata a maƙoshi.
Okay…” ta furta a hankali ta nufi sama
Ya Allah… me ya faru da mu ne haka?
Abaya tasa saka sai yar handbag dinta data rataya Wannan karon har turaren da Nawaf ya fi so a baya ta fesa ganin basa falon yasa ta nufi garage kai tsaye ,Ta tarar da shi yana saka wa Alya seat belt a’ Ya ɗago ya kalleta a takaice Tana ta tsammanin zai ce wani abu irin Nice perfume ,Amma sai kawai ya ce Kin shirya?
Tayi blinking Idonta
Good Ya rufe wa Ayla ƙofa ya nufi seat ɗin driver ,Nadira tana tsaya a wajen motar
A karon farko cikin makonni…Ta ji kamar tana gasa ne da wata inuwa da ba ta iya gani ,Saboda komai tana yi…Nawaf yana gani amma kamar ba ya gani Kuma abin da ya fi ba ta tsoro shi ne…Ba ta taɓa ganin mijinta yayi nisa da ita haka ba
Bayan sun yi ɗan yawo a gari, Nawaf ya shigar da motarsa cikin parking lot na wani shahararren ice cream spot a Wuse 2.
ya kashe motar, Alya ta saki ihu cikin farin ciki Ice cream! Ice cream Nawaf ya yi murmushi yana riko hannunta Easy, princess nadira ta zuba masu ido Sai lokacin da yake tare da Alya ne take ganin wannan ɓangaren nasa,mai haƙuri, mai cike da kulawa ,ta rike hannun Ayla na Dama ya rike nata na hagu a haka suka shiga
Wurin cike yake da mutane kasancewar weekend ne ,Ƙamshin waffle da chocolates ya gauraye ko’ina Alya ta kama hannun mahaifinta Abba , pink one Please?”
anything for my princess
Suna tsaye a layi…a gefen su kuma farida ce
Sanye take cikin abaya mai launin olive green da baƙin veil Babu kwalliya ko kadan a fuskarta, Wanda yasa kyawunta ya ƙara fitowa ,Tana tsaye Tana jiran a ba ta ice cream ɗinta ,Ba zato da tan juya ta kalli gefenta dan tun tsayuwar su take ta Jin surutun Ayla a gefen ta Caraf ,Idanunta suka sauka a kansa ji tayi Kamar Numfashinta ya tsaya ta gefen ido Shima ya dan kalleta , kowannensu ya kauda ka,Kamar ba su taɓa ganin juna ba,Kamar ba su taɓa kwana a gida ɗaya ba,Kamar ba su taɓa taɓa juna ba ,Zuciyar Farida ta fara bugawa da sauri Ta sake satar kallonsa sai yanzu ta Lura da wata kyakkyawar mace a gefensa suna rike da hannun yarinyar dake ta surutu Gabanta ya faɗi Kar dai…
Kar dai ace…Crush ɗinta yana da aure?
Ta sake kallon su Yarinyar tana riƙe da hannunsa Farida ta haɗiye yawu Idan yana da aure To ya akayi suka kwana tare a gidansa ranar?chan kuma zuciyarta ta fara ƙoƙarin nemo mata mafita ,Maybe ma kanwarsa ce Wataƙila kanwarsa ce da ’yarta Nawaf beyi kama da wanda zai bar wanna Zankadediyar matar ya nema wata a waje ba
Abba , tell them to hurry yanzu zasu gama princess sabr
Farida ta lumshe idanunta
Ya Allah… Yadda yake wa yarinyar magana da kulawa ,to amma Yarinyar abba tace masa ,ko dayake yara ay suna kiran uncle dinsu da abba ,ta fi son wannan bayanin Zuciyarta ta ɗan lafa a dai-dai lokacin…
Ma’aikacin ya kira ta Your order, ma’am.
Ta karɓi ice cream ɗinta da niyyar tafiya…ta sake waiyowa nawaf Ya ɗaga kai Idanunsu suka sake haɗuwa ,a wannan karo Wani abu kamar murmushi ya kusa bayyana a gefen bakinsa , da sauri ya danne shi ,bata sake waigowa har ta fice daga Wajan baki daya
Har yanzu Nawaf yana kallon ƙofar da ta bi.
Amma , chocolate ko vanilla? Muryar Ayla yajiyo Tana tambayar nadira Nan take ya dawo hayyacinsa,hankalin nadira Sam baya kansu email mai mahimanci take turawa
Wuse
Wayar Zaheera ta yi ƙara Sadiya ce Bayan Sun gaisa Zaheera tace Ya akayi ne Sadiya kin Kira kuma kinyi shiru ?Uhmm dama naga Tadala bata dawo bane gashi dare yayi fara yi,Au Tadala ko ? Ay ku rufe gidan ku dan a nan zata mana weekend ga ta Chan sun hade dasu mardiyya Ana ta sabga ,Sadiya ta yi murmushi har zuciyarta ,ay da gidan ki da nan din dik daya ne Anty zaheerah a gaishe dasu junior ta juya ta dan sace kallon dr mariya dan dik wayar nan take a gabansu take Sun gama dinner Ana falo Kamar kullum ,Alhamduillah yar uwarta daga Agadez ta samu karɓuwa a wajen dangin mijinta fiye da yadda take zato ko yanzu tasan tayiwa su dr mariya rata ,dik wayar da sadiya tayi da zaheera a kunensa ,lalle zaheera shi yana nan yana jiran Tadala Ashe rike masa ita tayi .
Tadala tana zaune a kan wata doguwar kujera a dakin baki, tana kallon jan lallen da aka yi mata a tafukan hannunta, Tun da ta zo gidan nan yau, zuciyarta cike take da farin ciki An kai ta salon,An yi mata lalle
Ta ji kamar tana cikin wani sabuwar duniya da ke cike da kulawa
A daidai lokacin Sukaji karar motar da ta tsaya a compound ,Ibrahim ya leƙa ta taga
Mommy Uncle Kamal ne fa ,Zaheera da ke duba wani abu a wayarta ta ɗaga kai
Kamal?Ta miƙe tsaye A Wannan dare haka to Allah yasa lafiya dai
Shigowa falon yayi Sanye yake cikin baƙar jallabiya Yaran suka gaishe shi cikin girmamawa Ina wuni, Uncle
Lafiya lau,Kiddos kwana biyu baku zo basketball ba ,yace yana kallon Ibrahim da junior Wanda suke yawan zuwa gidan alhaji Kamar buga basketball tare dashi
Bayan ƴan mintuna, suka bar falon… suna fita Zaheera ta zuba masa ido Wajan Tadala ka zo Twin? Alhaji Kamal ya ɗan sosa keya Zaheera ta ƙara kallonsa ,Ka shafa keya mana , ya kara shafa bayan wuyansa kamar yaron da aka kama da laifi ,Zaheera ta kwashe da dariya, Subhanallah! Alhaji Kamal Usman Kibiya lamarin naka har ya kai haka ?
Twin…Ki Bari mana ya katse ta da Sauri
Kwana biyu ne kacal fa zatayi kamal, daddy Ya sauke numfashi Ba zan iya ba yayi yawa ya zaayi yarinya daga zuwa yini ki rike ta ?
Kallonsa kawai zaheera take tama kasa magana
Wai… ina take ne?
Soyayyar har kai wannan matakin?ta fada Tana kunshe baki dan ita wallahi Dariya yake bata ,Ki daina dariya mana.
To me zan yi? Kai ne fa kake ta faman cewa ba zaka sake aure ba daga sadiya Ka rufe kofa ,Ta daɗe ba ta ga ɗan uwanta cikin wannan yanayin ba
Kana son ta sosai ko? Fiye da yadda nake so in yarda
Jeka guest falo zan turo maka ita bana so yaran su fito su ganku Har yanzu you guys are not official
Wani murmushi ya bayyana a fuskarsa Nagode, Twin.
Zaheera ta shiga ɗakin da aka sauke tadala ta samu har ta kwanta ,amma dai ba bacci take ba ,Tadala ta ɗaga kai Anty Kece ?
Zo nan Tadala ,Zaheera buɗe wardrobe Ta fito da wata abaya mai kyau Baƙa ɗa jan ado maza sa wannan , Tadala ta karɓa fuskar ta cike da mamaki ,toilet Tana ta shiga ta sanya abayar Tana ta tunan Ina kuma zasu cikin Daren nan ,gashi abayar ta mata daidai daga gani na mardiyya ne dan tsahon su daya ,Bayan mintuna kaɗan tadala ta fito ,Masha Allah kinyi kyau sosai Tadala ,Tadala ta yi ƙasa da kai cikin kunya ,Zaheera ta ce
Akwai baƙo a guest falo ,Tadala ta ɗaga kai.
Baƙo?Wane ne? Zaheera ta ɗan yi murmushi Daddy ne kamal twin Dina shine bakon
D-Daddy?Yana… yana nan? Nan take kunya ta rufe ta ,to Anty me zan je na masa ?Zaheera ta ɗaga gira Au ni kike tambaya?Je ki tambaye shi
Anty…”Nifa…
yana jiran ki fa ,idan kin sauka kasa kina wuce long corridor Akwai kofa a gefen hagu nan guest parlor din yake ,zaheerah ta fice ta bar Tadala a tsaye
Da sallama ta shiga falon Tana taku Kamar bata son taka kasa ,alhaji miƙe tsaye idonsa sun kasa barin fuskarta
Tadala ta yi ƙasa da kai ta nema Chan edge din L shaped kujerar ta zauna
Daddy Ina yini ? Nan ya dawo hayyacinsa.
Wa… wa alaikumus salam lfy Mi Dahlia… wannan duk ke ce?naga duk cin canja daga zuwa gidan zaheera ,Tadala ta ƙara sunkuyar da kanta Ni ce fa, Daddy…ta faɗa cikin sanyin murya ,ya saki wata ƙaramar dariya ,A’a fa ba wannan yarinyar da nake gani kullum a gidan Sadiya ba ce
Kunya ta ƙara rufe ta tafara wasa da yatsun hannunta masu jan lalle ,Kamal ya kalli yatsun nata ya ɗan matso gaba kaɗan Iyye har Lalle aka yi kenan ? ta jinjina kai Anty Zaheera ce ta sa aka yi min dazu
Ya yi miki kyau sosai
Uhmm Nagode kwata kwata ta kasa kallon idanunsa yana Ankare da ita har yanzu kunya ta kike ?
A’a daddy ,To me yasa duk sanda nake kallon ki, sai ki sauke idanunki? Ta sake sunkuyar da kanta itafa ba ta da amsar da zata bashi Mi Dahlia dago ki kalle ni
Ta ɗaga idanunta karon farko kenan tun da ta shigo suka haɗa ido na tsawon wasu daƙiƙu ,Kamal ya ji kamar zuciyarsa ta yi skipping ,ya Allah…Idanun nan nata
Yauwa Much better ko Kefa ,tayi saurin kauda kai bazata iya jure wanan kallon ba
Zaheera ta leƙo ta bakin ƙofa ,ta kalli Kamal ta kalli Tadala ,ta sake kallon Kamal ta nuna shi da yatsa,mintuna goma kacal ya rage maka,bacci Tadala zatayi ka tattara ka tafi Wajan Matanka yanmatan gidan nan basa kaiwa war haka suna zance
Lalle zaheera ni kike jerowa warning haka ?kawai dan nazo gidan ki ?
Ba gidana kazo ba twin, Wajan tadala kazo Kai ne fa ka ce ba za ka iya kwana biyu Baka ganta so cut the pretense ,Zan dawo nanda minti goma I mean it kamal
Bayan fitar zaheera shiru ya mamaye falon tadala ta ɗaga kai Daddy da gaske… saboda ni ka zo?waje na kazo mussaman ?Tamkar tana tambayar abin da amsarsa a fili take ,Eh wajanki nazo ,naji sadiya suna waya Akan bazaki dawo ba shiyasa nazo ganin ki ,Wani irin dumi ya ratsa zuciyarta Ashe haka take da mahimanci a wajansa ,itafa duk a zaton Wajan anty zaheera yazo kawai ya aika a kirata ne su dan gaisa ,to Meyasa mansoor baya mata irin soyyyar nan ne ?
A hankali ya miƙa hannunsa zan iya gani?
Ta ɗaga kai cikin rashin fahimta ,Lallen nake son gani , ta miƙa masa hannunta
ya riƙe hannun nata dik suka yi shiru
Hannunta ƙarami ,mai taushi Kamal ya zuba wa lallen ido ya shafa ɗan yatsanta da babban yatsansa this is Beautiful ,bata san ko lallen yake nufi ba ko ita ba
Uhmm Daddy…anty na iya shigowa fa
Zaheeran kike tsoro ? Come on mi dahlia dan ta shigo taga Ina kallon Lallen hannun ki me zata ce ? Kin San Allah mi dahlia ban taɓa tunanin zan sake jin haka ba a rayuwata.
Jin me daddy ?Bari kawai mi dahlia
Daddy…please ta fada a shagwabe ,Gara ya fara haramar tafiya Kafin yarinyar nan ta Hauka tashi ,dan ji yake Kamar yayi hugging dinta
knocking sukaji daga bakin kofa ,May I come in? Kamal yayi saurin sakin hannun tadala
Mintuna goma sun zama kusan talatin ,Kamal ya gyara murya ,bamu lura da lokaci ba ne ,Ohhh… ba ku lura da lokaci ba kamal ?wow love birds
Ta juyo kan tadala ,Ke kuma, Mi Dahlia Ashe kina iya sa twin brother ɗina manta lokaci?
Anty…Nidai ba ruwana Tadala ta faɗa cikin kunya , ta miƙe a hankali Sai da safe, Anty…sai da safe tadala ,Tana kokarin fita taji zaheera na cewa kamal zo ka tafi gida dan mijina baya nan bashi zai Baka damar kwanar min a gida ba ,Ni fa ban gama ba ko sallama kina gani bata yinmin ba
Ban tambaye ka ba kamal ,Tadala ta kasa riƙe dariyarta Ta yi saurin rufe baki Kamal ya juya ya kalleta Au Kema dariya kike min ?Ta girgiza kai da sauri A’a Daddy…
Ki je ki kwanta, Tadala. Zan kawo miki mutumin nan gobe idan ya yi halin kirki
Tadala ta yi musu sallama sannan ta nufi hanyar ɗakin baƙi Kafin ta fita falon gabadaya ta waiwayo Idanunta suka sauka kan Daddy Shi ma kallonta yake, ya ɗaga mata hannu,ta ɗan yi murmushi kaɗan, sannan ta ɗaga nata hannun
Zaheera ta juya ta kalli ɗan uwanta Har yanzu idanunsa suna kan ƙofar da Tadala ta fita ,Twin Ka shiga uku ,kamal ya juya ya kalleta Me kike nufi? Ta karaso ta zauna a kan kujera irin kallon da ka ke wa yarinyar nan…ta girgiza kai you’re gone Kamal ya sauke ajiyar zuciya ,bazaki gane bane twin ,Ka san me nake tunani?Me?
Ko na faɗa wa Hajiya?nan take Kamal ya ɗaga kai aa ba yanzu ba gaskiya ,Saboda me kamal ?Har yanzu ba mu shirya ba
Mu? Ta ɗaga gira ban gane bane ba?
Kamal ya yi murmushi ,Ni da ita nake nufi
Zaheera ta zuba masa ido ,Har ka kai ga cewa ‘mu’ kenan? Ah lalle lamarin babba ne
Ya sauke numfashi ,Twin… yarinyar nan tana bani wani irin salama ne da ban taɓa ji ba,Zaheera ta yi shiru tana sauraronsa
Komai ya yi min yawa a rayuwa,Kasuwanci , Iyali, mutanan gari, Amma idan ina tare da ita…Ya ɗan yi murmushi ,Like everything slows down
Ka tabbata ba kawai kyawunta ke burge kaba ?Ban sani ba,Amma abu ɗaya na sani…Bana son ta fita daga rayuwata ,to Allah ya tabbatar da alkairi duk dai Wannan soyoyyar taku ba karamin tashin hankali zata janyo nan gaba ba ,most especially sadiya amma haka dole Zan rufe ido nayi supporting Dinka Farin cikin ka ya fiye min komai twin ,Nagode sosai zaheera you’ve always been my number supporter Allah ya barki da engineer ,Allah ya rufe idonsa daga hango wata dan duk ranar da aka mana kishiya abuja bazata dauke ni da shi ba,zaheera ta kwashe da Dariya ,suka nufi hanyar fita falo Chan kamal ya juyo ya kalli zaheera
Ta yi kyau ko? Zaheera ta haɗe hannu a ƙirji.
Na shiga uku kamal?me kuma kake nufi ?Ja da baƙin ƙunshin mana , Twin… ka gama faɗuwa Allah ya fito da kai lafiya Kamal ya yi murmushi kamar saurayi ɗan shekara ashirin Bai ma musanta ba ya yarda da gasken ya gama Faduwa
Har Wajan parking lot ta kara shi ta tsaya tana kallon bayansa ta girgiza kai tana murmushi ,oh Alhaji Kamal Usman Kibiya da soyayya? Lallen wannan yarinya ta zo da wani sabon chapter a rayuwar ɗan uwana