KARFE DÜKKA KARFE NE

BABI NA HUDU

by @maidambu41

KARFE DUKKA ƘARFE NE...!!!

 {Zanen ƙaddarar Falilah }


Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai...

      #FREE BOOK


BABI NA HUDU.

Death alarm...

   _Ba laifi ba ne zabawa d'anka abin da ya dace amma tauye hakki ne hana shi abin da yake domin rayuwa bata tafi sai da soyayya da kauna_

     Na sha matukar mamaki da na fahimci cewa duk hakilon da ake ya rabu da ni, amma abin da zai yi buɗe baki sai ya tafi restaurant ya ci. Ina Mariyah me faffutukar a bar mata mijinta? Ina Hajiya me ihun yar bokaye ta mallake mata D'anta? Ko da yake ai ba sabon abu ba ne wai domin naji haka daga gare su, domin kuwa ai ba yau ake ruwa kasa tana shanyewa ba.

    Cikin kunar rai na kira shi, dauka yayi yana faɗin. "Yan mata ina cikin abinci ne fa" wani irin abu naji ya tsaya min a raina kafin na bude baki na ce mishi. "Kaf gidan ku a rasa me maka abin bude baki sai ka tafi wani gidan abinci kaci?" Ko ya fahimci raina ba dadi ne, sai yayi kasa da murya ya ce min. "Calm dawn Lilly ba haka bane a situation din da nake ciki bana son magana da hayaniya ce, nasan da kina nan ina zan tafi na ci abinci, bayan ina da Mrs Chef a gidana.". "Look Lamido!" Na fada cikin takaici, "Mrs Lamido ayi min afuwa yau daya dai nayi imani da Allah idan zaki bani abin da zai fito hannun ki ko guba ce zan ci, amma daga Hajiya har Mariyah da sauran matan gidan tsoron abin da zai fito hannun su nake, bawai don ina gudun mutuwa ba, a'a sai dai rayuwata tana da muhimmanci a wurinki da Yarana idan na rasa ta kece da Yarana zaku yi kewata. Falilah don Allah ki duba min bayana don Allah." Ya furta yana sauke numfashi, kamar yana gaba na. "Hmm, shi kenan" na furta a hankali, domin kuwa jikina ya gama sanyi. Al'amarin danginsa akwai ban tsoro don ban san yadda zan kimata al'amarin ba. Katse kiran nayi na koma can gefe na zubawa sarautar Allah idanu domin al'amarin yafi dacewa da haka. Bayan sallah isha ya kira ni, mun raba dare muna hira wanda baki daya ban da sake min wasu maganganu masu muhimmanci babu abin da yake wasu ma ya tuttura min ta Whatsapp, ya gaya min cewa na duba cikin jakar sarkokina akwai wasu takardun wadanda ya saka min na abin cikina da ni kaina, Lauyan shi Zailani zai ji da sauran. Har kusan karfe biyu na dare ban ma san lokacin da wayar ta fadi ba, domin tun bayan Hanif ban kuma samun ciki me saka barci ba sai wannan makale mata, na kira shi da haka ne domin yawan saka ni barci da yake yi.


AHMAD LAMIDO

Zama yayi cikin motar shi bayan ya dawo gida, yana tattara wasu abubuwan shi, sannan ya fito daga motar ya nufi ɓangaren Hajiya samun yayi gidan a rufe. Kafin ya wuce bangaren shi, sai da ya rufe ko ina sannan ya wuce dakin shi, a zaune ya same ta kallon agogon wayar shi yayi sannan ya wuce ban daki yayi wanka da alola sannan ya fito.

"Ahmad ka hakura da Falilah domin ka tsira da rayuwar mu?" Kugun shi daure da towel, daya hannun shi rike da karamin towel ya cigaba da abin yake yana kallonta ta cikin madubi. 

"Ahmad!!"

"Mariyah barci nake ji" ya fada bayan ya dauki box da jallabiya ya kashe wutar dakin ya kwanta, sannan ya shiga saka kayan shi. Yana gamawa ya kwanta, haurowa gadon ta yi, cikin hauka ta dauki pillown gefen shi ta fara ƙoƙarin danne shi, make ta yayi ta fadi can, sannan ya tashi cikin fushi ya nufi inda take, kawai bai an kara ba, sai ji yayi ta buga mishi abu a goshinsa, rike hannunta yayi tare da murdewa ta fasa ihu.

"Wallahi ni ce ajalinka, idan baka rabu da ita ba." Sake murde hannun yayi sai da kashin hannun yayi ƙara, sannan yayi waje da ita ya watsar da ita ya rufe kofar dakin shi.

    _Don Allah duk abin da zata maka kar ka damu, kayi hakuri don Allah kar ka kuma dukkan Uwar Yaran ka_ runtsa idanu shi yayi na wani lokaci kafin ya zauna a bakin gadon shi. Wayar shi ta fara ringing dauka yayi, bai tsaya ya duba waye ya kira shi a lokacin ba. 

"Bobby kana lafiya?" A yadda yaji muryanta yasan tabbas cikin biyu an yi daya, ko tayi mafarkin shi ko kuma ta farka sallah. 

"Ih lilly i'm ok" 

"A'a Bobby muryanka bai gaya min haka ba, nayi mafarkin ka ne. Please tashi kayi sallah, shi ne babban dacewar mu a wannan lokacin."

"Ina kaunarki, ki yafe min na yafe miki duniya da lahira." Daga haka ya katse kiran sake kiran shi tayi yana katse kiran domin yadda yake ji gara mutuwar shi da rayuwar shi. Idan ya cigaba da ɗaukar wayar zai iya fallasa asirin zuciyar shi. Haka tayi ta kira har ta hakura. 

      Har goshin asuba da yaga bata kuma kira, shima bai kira ba. Sai bayan ya dawo masallaci,yasan tana azkar don Allah ya kira ta. "Swampy!"  "Babu ruwanka da ni"  ta fada cikin damuwa. "Kiyi hakuri yanzu zan kwanta ne na huta idan na tashi ki gaya min laifin da na miki zan gyara." Amma kafin nan dauko min hoton ki musamman b**ns." "Allah ya shirya min kai Ahmad wallahi sam baka da kunya. Ga Auntyna a gidan a kusa da kai sai na dauki  hoton b**ns dina na tura maka"

"Allah little bit ina gani zan goge" "ok zan turo " ta fada mishi. 


 Can kuwa kamar minti biyar ya kunna data, Whatsp ya shiga ya ga yadda ta watso mishi hotunar, lumshe idanu shi yayi sannan kifa wayar a kirjin shi ta kira tana yana faɗin. "Me nayi da na cancanci samun mace, irin ki?" "Sai ka godewa Allah shi ya baka ni a matsayin matar auren ka" murmushi ya sake mata, sun jima suna musayan kalamai wanda suke manyan kalamai ne, amma a gare su right ne domin a karkashin inuwar aure suke wannan yanayin, sallama suka yi ya kashe wayar ya shiga ban daki yayi wanka sannan ya fito ya samu Mariyah a dakin, Allah ya so wayar shi tana password. Fisge wayar shi yayi, sannan ya koma ban dakin ya goge kome, domin yasan jahila ce , yanzu sai ta watsa mishi matar shi a social media. "Ahmad ina kara baka last chance ka rabu da ƙaruwar nan da take koya maka Iskanci kala kala"

"Ai haba? Kin manta abin da na miki jiya ne?"

"Ko daya amma ka sani wallahi yau zaka hadu da kaidin mace."  Duk yadda al'amarin yake kokarin fusata shi Falilah ta gama da shi, domin ta gama rokon shi da duk abin da zata mishi kar ya biye mata. Haka kuwa ya kasance, cakumar shi tayi da dambe, tare da kokarin kama gaban shi. Ya rasa yadda zai yi da Mariyah, sosai ta makale mishi, haka ya make ta amma ta fara ihu da kururuwan zai kashe ta. Bayan ita ke niman rayuwar shi. Habawa jin haka yasa Basmah ta fita da gudu ta nufi gidan Hajiya tana kuka.

"Hajiya Ummi na da Abba na zasu mutu" Hajiya me fama da ciwon kafa, haka ta mike ta nufi hanyar gidan, ga hadirin da ya gingimo haka suka nufi gidan.

Suna shiga ta jiyo ihun Mariyah.

"Wallahi sai ka sake ni, na gaji na gaji da halinka. Ka tafi na yafewa Jikar bokaye kai Allah ya isa lalata min kome da kayi dan kaga bani da Uwa bani da Uba,.shi ne bari ka kashe ni, Ahmad Allah sai ya saka min abin da kake min"

"Kina da ni a ina kika rasa Uwa, ka sake Falilah ko na maka Allah ya isa nonona da ka sha."

"Hajiya Umma ina son mata ta, kuma ina kaunar ta. Babu dalilin da zai saka na sake ta, idan kuwa zan sake Falilah tow wallahi sai dai dukkan su biyu na sake su." Tashin hankali mara iyaka, ai kuwa Hajiya da ta shiga gaya mishi maganganun masu daci da zafi, ta fita a cikin ruwan ta nufi gidan Babangida tana haki.

"Babangida! Babangida!! Wallahi idan nice Karimah na haifi Ahmadi." 

"Innalillahi wa'inna illahi raju'un, subhanalillahi Hajiya kar ki mishi baki don Allah ayi maganar nan na fahimta amma ban da baki.

    Kuka ta saka musu, dama ga shi ya hadu da girma, haka suka nufi falonta da ita Jamal yana jin hayaniyar yaki zuwa da matar shi ta mishi magana murmushi yayi sannan ya ce mata. "Idan har Ahmad da yake mata biyayya zata rufe idanunta, ta mishi haka waye kike tsammanin Hajiya zata kyale? Ai yaci ace ta gane yadda yake son Yarinyar ba zata iya raba su ba" shiru matar shi tayi, kafin ta ce mishi.

"Baban Ummu yarinyar nan karuwa ce fa? Kuma kasan yadda rayuwa ta b'aci waye zai so ballagazar mace?"

"Leemah kin san gidan da Falilah ta fito kuwa? Koda yake abin da aka gaya muku shi kuke aiki da shi, amma bari na gaya miki matukar akwai irin su Falilah tow wallahi maza irin mu ba zasu iya kallon ku ba, idan zaki zage dantse ki gyara jiki, ki kuma nime wayewar rayuwa ki sani, ita Falilah mijinta ne fa, idan na gaya miki irin matan da suke turo min naked din su ba zaki kuma barci cikin kwanciyar hankali ba. Dan haka Falilah ba karuwa bace."

  Wani abu taji ya tsaya mata a rai, kafin ta sunkuyar da kai tana mamakin shi.


      Zaharadeen dan gidan Babangida ya shigo.

"Assalamu alaikum, Barka da safiya Uncle wai kaje inji Abbi "

"Tow" yana mikewa, suka fita tare. Wato tun da ya shiga bangaren Hajiyar su, ake tuka bala'i da rikici har karfe daya lokacin, suka watse ta ce mishi.

"Idan ka dawo babu takardar shaidar sakin Falilah Allah ya isa ban yafe maka ba, sai ka sake Mariyah da baka sonta" 

"Hajiya ki sassauta mishi "

"Kuma sai na muku Allah ya isa idan baku saka ya sake tsinanniyar yarinyar ba" d'ago kai yayi ya kalle ta hawaye na zuba mishi.

"Ina son mata ta, Hajiya baki tab'a bincikar me Mariyah take min ba, Hajiya baki tab'a tambayar me Mariyah take min ba, Hajiya idan ita marainiya ce ni kuma waye ni, Hajiya zan sake Falilah Allah yana ganin ku, kuma yana ganin abin da kuka min. Hajiya ban kai karar ki wurin Allah ba, amma na san zai bude miki ganinki da jinki lokacin da kome ya wuce." Daga haka ya fita, ba Hajiya ba hatta Babangida da Jamal  jin wani irin yanayi suka yi me kama da tashin hankali. Haka ya nufi bangaren shi ya same ta a falo ta ci Uban kwalliya murmushi tayi tana faɗin.

"Romeo  nasan zuwa yanzu, sakinta ya tsufa mata. Koda yake yadda naga fusatattun idanunka ba zaka iya sake ta ba "

    Wuce ta yayi ya nufi dakin shi, wanka yayi sannan ya dauko farin Material din shi kome na shi fari ne. Ya saka hatta agogon hannun shi fatar fari ne, jin an bude kofar dakin shi lokacin yana saka links ya juya.

"Dad" ya kira sunan shi a tsorace. Juyawa yayi yana me kiran shi, baki daya yaron a tsorace yaƙe. Dan haka bai yi noticing yaron ba ya gama shiri suka fita abin su, da farin lema, ya budewa Yaron gaba ya zauna shima ya shigo ya zauna suka fita, kallon gidan su yayi na while time. Kafin ya karya motar ya fita. Kiran Falilah yayi ya koma gefen hanya, suka sha hiran su. Har ta tura mishi hotunarta, ta Whatsapp abin ya matukar birge shi, shi yasa farin yadi ita kuma ta saka kaya shima yadin ne amma ruwan goro, gashi ta karya dan kwalli. samun mace irinta duniya ce.

"Dad naga Ummi"

 Kallon shi tayi tana faɗin.

"Ya naji muryan Bassam?"

"Dad naga Ummi da" ya fada kamar zai yi kuka, shi a tunanin shi abin da ya faru ne, dan haka ya ce.

"Ya isa Yaron Dad, Lilly bari na nufi cikin gari naga an sauko sallah juma'a a cikin unguwar mu, ki yafe min ki yafe min, ki min addu'a ina cikin wani irin yanayi, Hajiya tana jirana da takardar rabuwar mu"

    "Kar ka damu ina sonka domin wannan biyayyar taka, Ubangiji ya baka nisan kwana da Yaranka zasu maka biyayya"

Ya kashe kiran sannan ya goge duk wani hiran da suka yi,


Mariyah

Sai da ta kira Nancy, ta tambaye ta.

"Nana ina fatan mutumin yasan kan aikin shi, bana son a samu matsala."

"Shegiya babu abinda zai faru, sai alkhairi ban ji dadin kafewa da yayi ba, Uwar shi itama jaka ta kasa saka danta yayi abin da ya da ce ai shi kenan" 

   Tashi tayi ta nufi ɓangaren Hajiya, tana shiga ta zauna a gaban Hajiya. 

"Hajiya Bassam bai shigo bane?"

"A'a bai shigo ba, Mariyah kiyi hakuri da mijinki, ina ga a hakura raba shi da jikar bokayen nan domin wallahi akwai damuwa"

"Hajiya me zance kuma? Kin san abin ta kira da shi? Ni matar cushe, matar da ba so, Jahila jaka mara ilimi ai Ahmad ya gaya mata ban iya karatu ba,  hatta kwanciyar aure ban iya ba shi yasa ya nime ta domin ya share hawayen shi."


 Jim Hajiya tayi kafin ta ce mata.

"Tow kuwa ai dole ya rabu da ita, tsinanniya ta tafi can ta kare barbadar ta." Dake munafunci ne mantawa tayi da danta ta shiga zuga Hajiya.


  ----

Bai fita ta babban titi ba, domin yadda ake ruwa sosai, yasa shi dole ya bi ta cikin kananun tititunan da zasu kai shi cikin gari. Sai dai wani abin da kana naka Allah yana na sa ya faru. Shine yadda ya taka birki amma taki takuwa, haka motar ta ki bashi haɗin kai har ya fada babban titi, wata babban daf da ta ciko shanu, tayi arangama da shi, tare da cilla motar sabin lambatun da ake da aikin su, yadda motar tayi tana wani irin tsalle ta kifa, hango wani karfe yayi zai sake ɗansa, yayi ta maza ya dauke Yaron, amma al'amarin Allah daban yaƙe, haka motar ta fada kan karfen, ta huda kujeran wanda yake haɗe da bayansa  ta fito ta kirjinsa, jini ne ya wanke su tare da Yaron suka jike jagwab. Dakyar ya kai kalmar shahada tare da wani siririn hawaye da ya zubo daga idanusa.

      Ai motar shanun tsayawa tayi drive ya fito da gudu ,yan uwansa aka fara kokarin ciro motar, kafin kace kwabo titin ya cika da mutane makil kasancewar sai da aka kira motar fire service, dakyar aka cire motar daga lambatun, aka sauke. Kafin aka fara kiciniyar cire su a motar.......

 *KULLU NAFSIN ZA'IKATUL MAUT*

#Deathalerm#Loveybirds#Murden

Shares and comment.

#Mai_Dambu