BABI NA BIYAR
by @maidambu41
KARFE DUKKA ƘARFE NE...!!!
{A cikin Karafu akwai Zinari da Azurfa}
Rashin vote da comments firgita ni yake, shi yasa nake tunanin na cire shi ko na bar shi gaskiya idan kuka ga shiru na cire shi ne gara na kudi ko ba kome za a saya
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai...
#FreeBook
Shafin naku ne.
BABI NA BIYAR
_Akwai ciwo da zafi yanayin, akwai damuwa me yawan gaske da zan iya ce idanuna sun yi kokarin ganin abubuwan da har na iya lumshe su ba tare da ce wani abu ba sai dai Ahmadi ya tafi da wani bangare na rayuwata_
Kasancewar zamani ne da aka cigaba, a wayar sadarwa aka fara sake labarin hatsarin su, lokacin ana nufar asibiti da su. Jamal yana office din shi abokin aikin shi ya shigo da sauri yana kallon shi. "Kamar motar gidan ku ne, AB 237 Jimeta ko?" A hankali ya cire kai yana kallon shi kafin ya ce. "Wani abu ya faru ne?" Kafin ya rufe baki wani ya sake shigowa office din shi. "Ahmad yayi hatsari fa, suna babban asibitin yola" cak yaji kome na kan shi ya tsaya. Kafin ya saka dariya yana faɗin. "Kai bana son sakarci yaushe na bar shi a"
"Lallai ka kira shi" wata zuciya ta gaya masa, da sauri ya dauki wayar shi ya fara kokarin kiran shi. Dauka aka yi ana cewa. "Kasan me wayar ne?" "Kanina ne!" "Tow kazo ERC yanzu domin sunyi mugun hatsari da Yaron shi." Jikin shi ne ya dauki wani irin rawa, ya rasa waye zai kira kawai sai ya kira Bana domin sun san juna tare da suka yi bautar ƙasa. "Hello Lamido!" "Bana kai na kira dama? Ahmad yayi hatsari amma kar ka gayawa mutane ka jira zan kira ka, please kar ka gayawa Falilah "
"Innalillahi wa'inna illahi raju'un, Allah ya basu lafiya" domin babu wanda ya kawo Ahmad ya rasu, haka ya wuce asibiti a cikin wannan yanayin ga ruwan sama, yana zuwa ERC ya kira wayar Babangida ya gaya mishi, domin har lokacin Ahmad yana dakin ana duba gawar shi. Dukkan su jikin su yayi sanyi, domin basu san me za a fito musu da shi ba, Babangida ne ya kira Kanin Mahaifin su gaya mishi halin da ake ciki, shi kuma Jamal ya kira Umamata ya gaya mata, kafin kace kwabo asibitin ya cika, itama Umamata ta gayawa Fad'ime. Haka suka taru zaman jiran a fito da shi, bayan an gama binciken gawar suka fito musu da shi da Bassam wanda yake ta surutu. "Dad naga Ummi da wani mutum a kasar motar ka, Dad naga Ummi da wani mutum a ƙasan motar ka." Babu wanda ya fahimci abin da yake fada domin hankalin su ya koma kan Ahmad da aka turo gawan shi, ga agogon shi da hular shi, takalmin shi da zoben shi, sai wayarsa da take gefensa, har lokacin fresh hot blood yake zuba a jikin shi, a hankali Babangida ya ja mayafin da aka rufe shi, fuskar shi fayau me ɗauke da murmushi kamar ka kira shi ya amsa maka. Baffan su ya kalli yadda Umamata take kuka ita da Fad'ime ya kuma kalli Jamal da yayi jigum akan gawar Ahmad. "A wuce da shi gida ko" ya fada yana kasa da kan shi, domin zuciyar sa tayi rauni. "Ashe mutuwa zaka yi? Me yasa ka tafi ka bar mu Ahmad? Allah sarki Falilah" abin da Fad'ime ta fada kenan. "Allah ya raba gardama ne, Hajiya da Mariyah sun rasa shi, kowa ya huta wacce suke yakin ya rabu da ita,zata iya gina rayuwarta, ita kuma Hajiya da Mafiya sun asara."
"Fad'ime ki zauna a wurin Yaron, mu bari mu wuce da gawar" "don Allah ku bar ni na raka dan uwana" ta fada cikin matsanancin kuka. "Tow waye zai zauna da Yaron? " Yadda take kuka yasa Umamata daukar duk wani abin da aka saka mishi suka nufi gida, cikin tashin hankali da mutuwar da aka musu, lokacin daya, da suka isa da gawar Mariyah tana kuka. Duk da babu wanda ya gaya mata sakon mutuwar Ahmad ita kawai tasan tabbas zai mutu, amma danta da ya ɗauka shi ne damuwar ta. Ganin sun shigo har da motar gawa dake Allah ba azzalumin sarki ba ne, da gudu ta shiga ihu. "Wayyo Allah na, na kashe kaina na kashe D'ana Bassam shima ya mutu ne?" Ta tambaye Umamata wacce take jin abin da Bassam din yaƙe faɗa. "Dad kar ka tuka motar, Ummi ta saka wani mutum a kasan motar ka.." kura mata idanu Umamata tayi sannan ta mika mata Bassam ɗin.
"Hankalin ki ya kwanta ko? Kin kashe shi kin huta Allah ba Azzalumin sarki ba ne."
"Wai meye haka ne Umamatu?"
"Babangida, baka ji abin da Bassam yake fada ba ne? Dad na ga Ummi da wani a kasar motar ka, amshe shi yana cikin suma ne amma abin da ya gani yana zuciyar shi." Cikin fushi Fad'ime ta fisge Yaron, tana kuka.
"Nayi kuskure wallahi nayi na dama, don Allah kar ku raba ni da d'ana" "kun ga ku ajiye wannan zancen mu shigar da gawar ina?"
"Falon Hajiya" Jamal ya fada a hankali. "A'a ba zata iya daukar wannan al'amarin ba" "wallahi gawar Ahmad falonta za a kai, ai ita ra bukaci da ya zauna da matar shi gara a kawo mata gawar shi, oya dauka yadda Uwa bata iya tausayawa abin da ta haifa ba,duk biyayyar da Yaron nan yake mata" "kana hauka ne" Babangida ya daka mishi tsawa, "Ih na haukace na haukace nace, na ce na haukace, Salele kuzo a wuce da gawar falon Hajiya " yadda suka dauki gawar Babangida zai kuma magana Umamatu ta ce mishi. "Haka ne dai-dai, a kai mata what she wish to see " haka suka wuce da gawar hankalin su a tashe , ita kan Mariyah tsoro da nadama ya kashe ta, tana zaune a kasa sai kuka take risga. "Allah ya gani na fita hakkin ki, na girmama al'amarin ki, ki je na barwa Allah"
Hajiya tana zaune da Basmah aka shigo da gawar Ahmad falonta. Mikewa tayi tana faɗin. "Meye wannan?" "Hajiya cewa kika yi da ya zauna da karuwa gara Allah ya kashe shi a huta, ai addu'ar iyaye da Yaran su, babu hijaba a wurin ubangiji ga gawar Ahmad nan, Ahmad Lamido ya tafi fada da tsinuwa ya kare, Mariyah da kike kaunar ta baki kyautar mutuwarsa da kike bukata." Zubewa tayi akan gwiwar ta, tana jin numfashinta yana sama sama, ji take kamar cutar asthma ce da ita, domin kuwa baki daya taji kofofin numfashin ta sun tsaya cak. Dakyar da buga kirji aka bata ruwa ta sha. Ajiyar zuciya ta sauke tana son magana, amma ta kasa furta furta kalma daya ne, da ja da gindi ta isa wurin gawar shi, ta bude fuskar shi. "Ahmadi na, wai da gaske mutuwar kayi? " Kuka suka fashe da shi, ban da Jamal da ya koma gefe yana tura sakon mutuwar ta wayar shi, sai kuma aka fara kiran wayar Ahmad din. Kafin wani lokaci labarin Mutuwar Ahmad Ayuba Lamido ya karade social media.
---
Falilah Mustapha Liman.
Ina kwance amma ji nake kamar an min duka, a hankali na tsinci kaina da fashewa da kuka, amma kuma na rasa me aka min, shigowar Daddy wato Ya Nafi'u ya zuba min idanu, ganin yadda nake kuka yasa shi takowa har inda nake ya dauki wayata. Ya kashe baki daya. Sannan ya fita domin bai da wani abu da zai iya min, haka na ci kuka na kwanta.
Nafi'u
Wayar shi ce tayi kara, ya dauka yana faɗin.
"Alhamdulillahi, ih wallahi lokaci yayi."
"Tow shi kenan yau zamu wuce tunda naji weather din yana da kyau, ina ga zasu yi jana'izar yau din nan ne, sai dai ban sani ba ko zasu d'aga tunda kasan Yaron a Office din UNICEF yake aiki dole zasu iya d'agawa, Ih Malam in sha Allah da kaina zan kaita, amma ku turo wacce zata zauna da ita kafin bakwai domin laluran da yake tare da ita."
Shiru yayi kafin ya ce. "Yawwa Mama ma tayi domin Falilah tana cikin damuwa, Mama ce zata fi fahimtar halin da take ciki, Allah ya kara girma Ubangiji ya baka Allah ita kuma Allah yasa karshen wahalar kenan"
"Amin Malam Amin Ya Allah, mun gode Malam" kashe wayar yayi hawaye yana zuba mishi, tabbas Ahmad ya mishi kome, Ahmad ya gyara musu kome Ahmad, ya gyara alaƙar su da Mahaifin su, sannan ya tafi ya bar su da kewar shi.
*Yallabai wannan bafa babban al'amari ba ne, kawai ina son naga malam ya saka mata albarkan shi ne, itama ta samu farincikin rayuwa, ina son Falilah tayi ta murmushi da murnar Malam ya sakawa aurenta albarka ne, asalima rabo ya hana ni aurenta tun farko, amma ni ba zan iya niman aurenta a wurin ka ba, tun da Malam yana raye*
"Allah ya maka rahama" ya fada a hankali,
*Yobe State. Damaturu Capital*
*Sabon faggi*
Unguwa ce da ta haɗa manyan mutane da malamai, uwa Uba yan siyasa masu ji da kansu, Gidan Malam Mustapha Liman gida ne da za a kira da babban gida, kasancewar yana kunshe da abubuwa na alfahari. Duk da zamani ta cigaba na yadda yanzu aka daina tare almajirai a kofar gida, sai dai har yau ana karantarwa a kofar gidan, domin kuwa malam bai bar karantarwa ba, gashi duk ranar juma'a, ana abincin sadaka ana rabawa mabukata, sannan yana koyarwa ga manyan mutane da dare da kuma la'asar, kasancewar yau juma'a kuma ana zuwa daukar karatu. Tunda Bana ya kira shi akan labarin hatsarin Ahmad jikin shi yayi sanyi, can kuma ya kuma gaya mishi rasuwar Ahmad ɗin.
Kallon su yayi jiki a sanyayye ya ce.
"Yau karatun nan ayi hakuri da shi, domin mijin Autana ya rasu sai ko wata sati" Allahu Akbar suka yi ta fada, suna mika mishi ta'aziyar rashin da yayi domin sun san Ahmad, har karatu yana zuwa yi lokacin da ya nace sai malam ya amshe shi a matsayin wanda ya zo niman auren Falilah. Mikewa yayi ya shiga cikin gidan bayan ya sallame mu, Salmanu jikar shi ya nad'e kayan karatu, ya nufi babban falon ya gidan zuwan Ahmad da Falilah ya tsaya mishi a rai. *Baba Malam, ni fa ba zan tab'a sake Falilah ba sai dai ta min takaba, kai ko mutuwa tayi wallahi ba zan kuma ajiye mace bayan ita ba, addu'a nayi Allah ya bani ita kuma ya ba ni ita idan ba rashin godiyar Ubangiji ba sai na sako maka ita?*
"Ya Man, ashe mijin Falilah ya rasu?" Hajja Jume take tambayar shi, gyada mata kai yayi yana kallon inda Falilah ta rakube zuwan su da ita.
*Malama sake ki gaishe shi, na rantse da Allah Baba Malam sai ka sanya mata Albarkan da iyaye suke sakawa Yaran su, ban yarda ka saka mata ba, shi yasa na kwasota muka dawo, kuma dai sai ka raka mu da ita har airport zan gamsu ka yafe musu ita da Yayan mu Baban mu. Yawwa zo nan Yan mata ai bamu barin garin nan sai malam ya saka mana albarka domin so nake kafin shekara me zuwa ki cika min gida da Yara dozen*
Dariya matan gidan suka dauka ban da Mahaifiyar Falilah da ta koma daki, tana me kai sujada godiya ga Ubangiji da ya basu wanda xai saka malam yafewa Yarta
_Allah ya albarkaci rayuwar ku, ya kuma baku zuri'a dayyiba, ya saka mutuwa ce zata raba ku ba saki ko yaji ba, zo nan auta tunda kike aure aure baki tab'a kawo mijin da ya mai da ni abokin wasan shi irin Ahmadu ba, Allah ya yafe mana ya kuma yafe mana kura-kuran mu na baya_
Idanun shi ne suka cika da kwalla.
"Yaron nan ya shiga ran kowa Allah ya mishi rahama" "Amin Ya Allah" Hajja Jume ta fada, haka ya wuce kofar da zata sada shi da bangaren Mahaifiyar Falilah, tana zaune akan abin sallah, lazumi take kasancewar yammacin Juma'a ce. Zama yayi a kujeran da yake falon ya kalli yadda take share hawaye lokaci zuwa lokaci, bai cika ganin kukanta ba sai idan Falilah tana cikin damuwa, tow a lokacin har barci bata iyawa tayi ta sallah dare kenan, duk da dama tana yi karawa take akan na da. "Falmata!" Ya kira sunan ta a sanyayye.
Kukan da take taushewa ne ya kwace mata, matsawa yayi inda take ya rike hannunta. "Kiyi hakuri, kiyi hakuri, shine abin da zan gaya miki gobe zaku wuce Yola ki janyo yar ki jikin ki, tana bukatar ki kuka ba zai saka ya gyara kome ba, sai ki kara lalata kome." Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa. "Duk abin da yake faruwa da Falilah ina da hannu a cikin shi, wallahi tallahi Billahi azim, ni na jifeta da rashin albarka, nayi nadama Falmata wallahi na yi nadama, na gane bakina ya lalata min yar da nafi so, saboda ta lalata min suna na kasa hakuri na jife ta Allah ya cire mata albarka da jin dadin kowani da namiji kamar yadda ta saka ni kunci saboda da namiji, nayi mata bakin itama." Kuka Ya Man yake yana matsawa kusa da ita.
"Wallahi soro falmata nadimtikenah, Ki gafarce ni falmata nayi nadama, nayi kuskure akan Falilah amma har yau ban fasa kuka da abin da a aikata ba. Na zata bayan mutuncina da ta zubda na zata abin ba zai wuce ba ne, na ɗauka mutuncina da maluntatta zai bi ruwa ne, Wallahi soro falmata nadimtikenah ki yafe min ke da Yarki na cutar da ku." Kallon shi tayi kafin ta ce. "Mustapha Liman, na aure ka tun kana almajirin ka, fakiri mara arziki sai almajiranci. Mustapha kai ne ka ɗauke ni budurwa ka kuma san wacece ni, Mustapha a cikin palourn nan ka ce Ubangiji ya kunsawa rayuwar ta baƙin cikin haka bai ishe ka ba Mustapha sai da ka shiga tsakani na da ita ka raba tsakanin mu na tsawon shekaru goma. Na ajiye maka maganar ai zaka dawo ka same. Kuskure daya tal yasa ta zama mujiya a cikin unguwar nan, kasa yarinyar karama ta zama wata iri a cikin alumma ka mai da min yarinya karama mara albarka. Yanzu hankalin ka ya kwanta ai, duk abin da ya faru da ita bakin ka ne sanadi domin kai ne ka jefeta da alamomi marasa sauki, Yarinya karama sai da ta ga abin da ni ban isa nace na gan shi a zamana da kai shekaru hamsin ba. Ita ce auren dan fashi? Ita ce auren dan damfara, ita ce zama da muguwar kishiya, ita ce rayuwar kauye MUSTAPHA na hada ka da Allah ka cire mata bakin da yake kanta ko zata huta don Allah" ta fada tana kuka wiwi.
Aunty Zuhrah da tazo gidan, tsayawa tayi a bakin kofar domin taji labarin mutuwar mijin kanwar su, Autar su Yarinya mafi soyuwa a zuciyar su. Amma ganin iyayen su cikin wani irin hali ya sata juyawa babu shiri zuwa dakin Hajja Jume tana kuka. Ita kanta Hajja Jume kuka take.
"Bintu sai muka ji labarin mutuwar Yaro me barkwace kamar me?" "Wallahi kuwa Hajja Falilah ta yi rashin miji, yaron bai dauke mu a surukai ba, sai abokan wasa. Don Allah Hajja ku ce Ya Man ya bar ta ta dawo gida haka wallahi Falilah ta girman da ya dace ta zauna a gaban su Hajja Mama. Don Allah"
"In sha Allah zata dawo gida duk da Yayanku shi ne abin ji, domin ya saba da ita." Lumshe idanun Aunty Zuhrah tayi domin wallahi ba karamin yaki take da zuciyar ta akan Ya Nafi'u ba. Domin ba karamin magana ba ne ya fito a zamanta a gidan shi. Amma kuma gani tayi iyayen su kamar basu damu da haka ba. Sun tsarkake kansa da zuciyar su, kaunar da Nafi'u yakewa Falilah tayi yawa gara kawai ta dawo gaban Iyayen su zargin mutane akan su tayi yawa......
*Ina mika ta'aziya ta ga wadanda irin wannan incident din ya faru da su, zan dauki dan short break kafin ku gama jimamin rashin Ahmad sannan mu waiwayi baya muga me ya faru zuwa yau...*
#Regret#Familyissue#lastborn
#Mai_Dambu