BARRISTER SUHAIL

56&57

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

Masoyana ina maku fatan Alkairi ina godiya da Addu'o'inku a gare ni

🅿️-----56

babu inda yaran ƙwaro basu duba ba ciki hadda madafa da kuma bayan gida amman babu Sama'ila babu dalilin sa 

haka suka futo gwiwa a sake suka duɓi Ubangidan nasu suka ce"mai gida yaron nan fa baya gidan nan"

wani huci mai zafi ƙwaro ya fitar ya dubi gambo dake kwance a gaban sa ya ce"bazaka faɗa mana inda yake ba ko"

Gambo ya ce"na rantse bansani ba, kuma ai kun duba baya nan"

ƙwaro ya kamo hannunsa ya sa wuƙa ya yanke shi a dan yatsa kan wani irin ƙara Gambo ya saki ganin yatsar ta kusa barin hannunsa ga jini ya soma duba daga hannun

ihun da yayi yasa ƙwaro da yaransa suka fita da gudu,dan Asirin na gab da tonuwa

mahaifiyar Sama'ila ta yago zanin dake jinkinta ta saure masa yatsar cikin Sa'a jinin ya rage zuba 

suhail na barin hotel daya kai Sama'ila ya koma gida dakin iman ya fara shiga fitowar daga wanka kenan tana shafa lotions dinta ya shigo sannu da zuwa tayi masa 

fuskar sa ta kalla ganin gajiya kara-kara kan fuskar sa tana lura tunda mijinta ya amshi cases din Amina ya soma ramewa baya samun isasshen lokacin daya kamata duk da ba Wannan bane karin farko daya amshi case mai sarƙaƙƙiya amman tana lura da yadda Wannan case ya tsaya masa a rai Wannan bai da nasaba da tausayin ita Yarinyar da ake zargi ne dan Suhail a cikin halayen sa data sani tasan mutun ne mai matukar tausayi ba kamar ga talakka sun sha fita ya gamu da mabuƙa ta ya tsaya ya taimake su 

hakan yasa take ƙara sansa dan a wannan fanin kusan hali nw yazo ɗaya ita kanta iman tana da tausayi da kuma rauni 

sai ta ƙare masa kallo ta ce"yaya Suhail na gama Abinci yana dining area"

"zanje nayi wanka idan na gama sai ki fito muci tare"

kai ta daga masa

yana fita dai-dai lokacin Zeenah na fitowa daga daki cikin shirin fita unguwa ga hannun ta dake daure da bandage tunda taga fitowar daga ɗakin iman take ciki take batsewa wani kallo mai cike da raini take binsa dashi

shima ya ƙasa dauke idanunsa daga kanta duk da wulaƙantaccen kallon da take binsa dashi 

har ta ƙara so gaban sa ganin tana ƙoƙarin fita ba tare ta kula saba ya ƙasa daure wa ɗan yana da hakkin tambayar ta inda zata ce

"zeenah ina zaki ceje without my permission"

harararsa tayi ta ce"a wajen wa zan nemi iznin ai baka bani fuskar yin hakan ba"

suhail ya ce"zeenah kiji tsoron Allah duk macen dake fita ba tare da izinin mijinta ba Mala'iku na tsine mata kuma matukar kika mutu a wannan halin ba Abinda zai hana ki shiga wuta"

dariya tayi ta nuna sa da hannu ta ce"Malan Suhail wa'azi kuma aka koma to idan wutar a hannun ka take sai ka sakani very stupid" tsaki taja ta daga jakar ta ta fito da robar cingum dinta ta diɓa ta watsa bakin ta tayi ficewar ta

lamarin Zeenah kullum ƙara girmamawa yake a idanunsa ya fara gajiya da karar da yake yi mata wanda yake kallona matsayin hallacin kaunar data yi masa a baya 

wannan halin da take nuna masa shi kesa kullum Zuciyar sa na kara nesanta da ita 

ɗakinsa ya koma yayi wanka ya fito 

bayan ya fito ya shirya cikin wata brown din jallabiya a falo ya tarar da iman tana jiransa. 

suka wuce dinning ta buɗe kular idanunsa yaci karo da dambun shinkafa da aka cika masa veggies wani irin kamshin mai tayar da hankali ya mamaye wajen 

kallon sa tayi tana murmushi tare da kashe masa idanun hagu shima ya mayar mata dashi

"kamar kinsan duk cikin satin nan nake craving din dambun bana so na fada maki kice zaki yi kisan bana saj wahalar da. Ammi's Daugther ɗina kuma love of life din suhail"

murmushi tayi jin sunan da ya kira ta dashi ta ce"ai ya zama dole nayi Abinda zan burge mijina"

yana lura da ita a hankali kunyar sa da take ji tana soma raguwa tunda yanzu har zata iya kallon suna magana ido cikin ido 

a plate daya suka ci abinci har ta koshi ta barsa dan ko bayan ya cinye ma sai da ya nemi kari 

a zuciyar yaji yanaso ya kyautata mata kamar yadda itama kullum take cikin faran ta masa 

"iman" ya ƙira sunanta

"ki shirya anjima zamuje unguwa"

fara'ar kan fuskar ya karu ta ce"okay yaya Suhail"

ta fara kwashe kayan da suka ɓata takai Kitchen 

ƙwaro ne tsaye a gaban salisu suna magana "oga yaron nan fa ya tsere"

shiru ya ratsa tsakanin salisu yaja numfashi da karfi ya dubi ƙwaro "kun tabbatar baku sami yaron nan ba"

ƙwaro ya cije baki ya ce"haba oga ai kasan tsakanin mu akwai amana na rantse da uwata bamu samu yaron nan ba"

"to ku cigaba da nema matukar yaran nan ya kai gaban alkali kashi na ya bushe"

ƙwaro ya tashi ya tafi Salisu ya koma gida 

jaru ya gani a tsakar gida ya zauna gefen ta ya dafe kansa jaru ta ce"yana ganka kai kadai ina Sama'ilan yake"

ajiyar zuciya ya sauke ya ce"basu same sa ba, Gaba ɗaya banda natsuwa ya zama Dole na tattara kayana na gudu tun kan abinda nake hasashe ya faru"

jaru ta ce"ina kuma zaka tafi ka barni"

salisu ya ce"idan kinga dama ki zauna nidai kinga tafiya ta,idan ƙura ta lafa san dawo in tattara kan Dukiya ta"

hanyar fita yayi jaru ta kiransa"ulu,ulu kar ka tafi ka dawo nace ba Abinda zai faru yanzu haka daji ya shiga namun daji cinye sa"

ina ai bai ko bi ta kanta ba yayi tafiyar ba 

Bayan kwana biyu 

salisu na zaune a dajin daya ɓoye wayar tayi Ringing ganin ɓakuwar lamba yaji tsoron daga wa kiran da aka dame da dashi ya shi dagawa ya kara wayar a kunne

"hello ina magana da Salisu Barau"

"Eh nine wake Magana

daga wayar aka ce"ka nutsu kaji abinda zan faɗa maka nasan warhaka kana nan kana neman Sama'ila ko to zan faɗa maka inda yake"

hankali ta she Salisu ya miƙe ya ce"waye kai? kuma ya akayi kasan ina neman sa?"

"sanin koni waye a yanzu bazai amfanar dakai komai ba amman kan nutsu nayi maka bayanin inda yake nan yafada masa nasa Sama'ila na garin Abuja ga kuma inda za'a same sa"

Salisu ya ce"wani tabbaci zaka bani akan haka in kuma yarda da kai"

dariya gayen yayi ya ce"tabbacin da ban baka shine da idona na gansa batun yarda kuma ya rage naka ka yarda ko ka ƙi kayi wasa da damarka yaron nan ya tona maka asiri a zaman kotun za'ayi nan da kwanaki hudu masu zuwa"

katse wayar mutumin yayi salisu yabi wayar da kallo duk da iskan dake ƙadawa bai hana zuba saukowa masa bayan mahaifiyarsa da Sama'ila babu wanda yasan da batun nan cewa su suka kashe barau hakan yasa shi mamaki"

wayar ya ƙara kira dan ya tambayi mutumin ko wanene shi amman wayar a kashe ko ƙwaro basu tambaye sa dalilin da yasa yake neman Sama'ila haka ba
 
tuni ya fara tattare kayan sa ya kama hanyar Abuja har ya kai ga isa address din da aka basa waige-waige yasoma inda zai Sama'ila babu masu wucewa sai ƴan tsirarun mutane ya juya zai tafi ƴan sanda suka cika hannun sa 

duk yadda yayi kokarin kwace kansa ya kasa dan ba riƙon wasa suka masa ba 

sai Yanzu yasan tarko ne aka hada masa kawai dan a kamasa

basu tsaya ko ina dashi ba sai police station direct suka saka shi a cell dpo ya kira mutumin da yasa a kamaso ya ce"sir yaron nan ya shiga hannu"

"weldone officer" kawai ya faɗa ya kashe wayar 

Sama'ila na zaune a hotel din da suhail ya kama masa kullum yana cikin karatun Alkur'ani da addu'a Allah ya bayana mai Gaskiya

A dai-dai wannan lokacin kuma…

A cikin cell kuwa Salisu ne zaune ya dafe kansa 

Sai yanzu ya fahimci cewa duk abin da ya faru masa ba haɗari ba ne…

Tarko ne.

……

Washe gari…

🅿️----57

Tun kafin ƙarfe tara na safe, harabar kotu ta sake cika maƙil fiye da ranar da ta gabata
Rahoton kama Salisu ya bazu a cikin gari tamkar wutar daji 

Yan jarida na ta ɗaukar hotuna Jama’a kuwa kowa na ta hasashe da jimamin cewa Wai da gaske an kama Salisu
da zargi kashe Alhaji Barau

Amina aka fito da ita daga gidan yari cikin rakiyar jami’an tsaro
Da ta shiga harabar kotun, idanunta suka fara neman Suhail
Da idonta ya sauka a kansa sai ta ji wani irin kwanciyar hankali
Suhail ya ɗaga mata kai alamar ta kwantar da hankalinta

a gefe guda kuma jaru na cikin tashin hankali tun nan da kwana biyu take neman lambar salisu amman a kashe gashi yau zamab kotu hakan yasa ta shirya ta tafi ita kaɗai

koda Alƙali ya shigo cikin kotu 

"All rise"

aka fada kowa ya miƙe sai da ya zauna kafin aka  bada umarni kowa ya zauna

Alkali ya bude file tare da cigaba da sauraren Shari'a

Barrister Suhail ya miƙe.
“Ranka ya daɗe, ina da wata sabuwar shaida da kuma babban shaida da zai bayyana wa wannan kotu gaskiyar abin da ya faru"

Nan take kotu ta ɗauki surutu kowa da Abinda yake fada Alƙali ya basa order

dandanan Suhail ya bada umarni a shigo da Sama'ila wanda fuskar ke a rufe sanye cikin farar shadda da hulabba wanda ya gane sa sai da ya iso tsakiyar kotu ya Bayyana fuskar sa

Jaru ta miƙe tsaye cikin firgici

“Sama’ila!”

Ta faɗa ba tare da ta sani ba.
Jama’ar kotu suka sake ɗaukar surutu 

Alƙali ya kalleta "waya baki izinin magana"

komawa tayi ta zauna zuciyar kamar ta fito tsabagen tashin hankali 

gashi babu salisu babu dalilin sa

Barrister Suhail ya dubi Sama’ila

“Ka gaya wa wannan kotu sunanka"

“Sunana Sama’ila Barau"

“Wane ne Alhaji Barau a gare ka?”

"mahaifina ne"

suhail ya ce"ka fadi wa kotu abinda ka sani game da ƙisan mahaifinka"

wani yawu ya haɗiye mai zafi 

ya kalli Amina da itama idanunta ke kansa 

a hankali ya fara magana 

Ranar da aka kashe baba Aunty Amina bata nan hasalima ni na bata kudin motar da taje Asibiti 

Sama’ila ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙu kafin ya ci gaba da Magana

wata rana na shigo gida na samu Baba jaru da salisu suna magana jin Maganar ta shafi ƙisan baba yasa na laɓe bayan taga ba tare da sun san ina nan ba 

Kotu ta yi tsit.

Ko tari babu wanda ya yi.

Sama’ila ya ci gaba.

“Na ji Baba Salisu yana cewa, ‘Yanzu da Barau ya mutu babu wanda zai hana mu cin dukiyarsa.’”

Jaru ta miƙe tsaye.

“Ƙarya yake yi!”

Alƙali ya bugi guduma.

“Order! Idan kika sake katse shari’a zan sa a fitar da ke.”

Jaru ta zauna tana haki

Sama’ila ya ci gaba

Sai Baba Jaru ta ce masa"Yaron nan fa Sama'ila yaji sirrin mu"

Shi kuma ya ce" Ni zan kashe shi kafin ya tona mana asiri"

Nan take hayaniya ta sake tashi a cikin kotun

“Order!”

Alƙali ya sake buga guduma

Barrister Suhail ya dubi Sama’ila

“Wannan magana da ka ji… kana da wata hujja da za ta tabbatar wa kotu?”

Sama’ila ya saka hannu a aljihunsa

Ya fito da wayarsa.

“Eh"

“Na kunna recording tun kafin su gama magana.”

Kamar walƙiya labarin ya bazu cikin kotun.

Lauyoyin gwamnati suka kalli juna.

Jaru kuwa jikinta ya fara rawa.

Barrister Suhail ya karɓi wayar

Ya miƙa wa magatakarda

Magatakardan ya haɗa wayar da speaker ɗin kotu kowa yana saurara

Sai aka kunna recording ɗin

Murya ta farko ita ce ta Salisu

"Amina ce za ta ɗauki laifi Mu kuma mu mallaki komai"

Da recording ɗin ya ƙare…

Kotu ta nutsu tamkar babu kowa a cikinta.

Wasu daga cikin jama’ar kotun har hawaye suke sharewa.

Mahaifiyar Amina ta dafe ƙirji tana kuka

“Alhamdulillah… Ya Allah na gode maka daka wanke Amina daga zargi"

Barrister Suhail ya miƙe

“Ranka ya daɗe, wannan recording tare da shaidar Sama’ila sun tabbatar da cewa Amina ba ta da hannu a wannan kisan Muna roƙon wannan kotu ta wanke ta tare da bayar da umarnin ci gaba da bincike kan Salisu da Jaru"

Alƙali ya gyara zamansa

Ya kalli lauyan gwamnati

“Kana da wata tambaya ga wannan shaidar?”

Lauyan gwamnati ya yi shiru na wasu daƙiƙu

Daga bisani ya ce

“…A’a, ranka ya daɗe"

Wata sabuwar hayaniya ta sake tashi a cikin kotun

Jaru kuwa ta fara ja da baya a hankali

Asiri ya tonu 

Cikin rawar murya ta miƙe tsaye

“Ranka ya daɗe… ƙarya ce! An haɗa wannan recording ne domin a cutar da mu"

Barrister Suhail ya kalleta cikin nutsuwa

Ya ce“Ranka ya daɗe, idan wannan recording ƙarya ce, muna roƙon kotu ta bai wa ƙwararrun masana damar tantance sahihancinta"

Alƙali ya gyada kai

“Hakan zai kasance"

Nan take wani jami’in binciken fasahar sadarwa (Forensic Expert) da kotu ta tanada ya miƙe
Ya karɓi wayar

Bayan ya duba recording ɗin da na’urorinsa na wasu mintuna, ya ɗago kai ya ce
“Ranka ya daɗe"

“Na binciki recording ɗin Ba a yi mata gyara ba, ba a haɗa ta daga wurare daban-daban ba,Asalin recording ce da aka dauka"

Kotu gaba ɗaya ta kaure da surutu.
Jaru ta dafe baki
Hawaye suka fara zubo mata
Alƙali ya buga guduma sau uku

“Order! Order!! Order!!!”
kafin kowa yayi shiru

Barrister Suhail ya sake miƙewa
“Ranka ya daɗe, mun gabatar da
Shaidar asibiti, Bidiyon CCTV,Shaidar gani da ido ta Sama’ila, Recording da ƙwararre ya tabbatar da ingancinta
Saboda haka muna roƙon wannan kotu ta wanke Amina daga dukkan zarge-zargen da ake mata"

Alƙali ya sunkuyar da kansa
Ya daɗe yana duba file ɗin shari’ar
Kowa ya yi shiru
Har ana jin bugun zuciyar mutane
Amina kuwa ta haɗe hannayenta tana ta karanta addu’a a zuciyarta
Mahaifiyarta kuwa hawaye kawai take sharewa

Bayan wasu daƙiƙu…
Alƙali ya ɗaga kansa
Ya ce “Bayan nazarin hujjojin da aka gabatar a wannan kotu"


da kuma rashin wata hujja da ke tabbatar da cewa Amina ce ta aikata wannan laifi…”

“Wannan kotu mai girma ta tabbatar da cewa"

Ya ɗan yi shiru

Numfashin kowa ya tsaya.


“Amina ba ta da laifi"

“Wannan kotu ta wanke ta daga dukkan zarge-zargen da ake mata"

“Ina kuma bayar da umarnin a sake ta nan take"

Kafin Alƙali ya gama magana…
Mahaifiyar Amina ta fashe da kuka mai taɓa zuciya

“Alhamdulillah!”

Ta durƙusa tana sujada cikin kotu
Amina ma ta kasa riƙe hawayenta

Ta fashe da kuka tare da duƙewa ƙasa wannan kukan take ta so tayi amman bata samu damar yinsa ba sai a yau

Jama’ar kotu da dama suka fara taya su murna ciki harda Sama'ila inda shima ya godewa Allah daya silar dawowa da farin cikin Amina

Barrister Suhail ya lumshe idanunsa
A hankali ya furta

“Alhamdulillahi Rabbil Alamin"

ya ƙagara ya koma gida ya sanarwa da iman yayi nasara a case din Amina

Sai dai Alƙali bai gama ba

Ya ɗaga murya ya ce,
“Haka kuma"

“Wannan kotu tana bayar da umarnin a tsare Jaru nan take"

“Kuma a ci gaba da bincike kan Salisu Barau, wanda tuni aka tabbatar yana hannun jami’an tsaro"
Da jin haka…
Jaru ta yi ƙoƙarin guduwa.
Amma kafin ta kai ƙofa…
Jami’an ’yan sanda biyu suka tare ta
Suka saka mata ankwa
Ta fashe da ihu.
“Na shiga uku!”
“Ka taimake ni Salisu!”

Amma…
Salisu yana can cikin cell
Shi ma yana jiran ranar da zai fuskanci hukuncin da ya cancanta

share 
like 
and comment