Chapter fourty one
by @aysharano22
Yana karasa fadan haka ya mike a fusace ya fita daga dakin da wani irin sauri kmr zai tashi sama yayi banging musu kofa, daga Lee har Suhana tsananin mamaki ne ya daskarar dasu a nan inda suke don gaba daya basuga abunda yayi warranting wnn fushin nashi ba, musamman Lee da zai iya rantsuwa rabon da yaga Ayaan yayi mgn cikin fushi haka tun rigimarsu da Juwairiyya lokacinda take yunkurin zubar da cikin pookie, wancan anger din can be justified amma wnn fa?, me Suhana tayi da ya haddasa masa wnn fushi haka?, kodai akwai wani abu a tsakaninsu ne bayan abinda ya sani?, wnn sune tambayoyin da suka cika masa zuciya yayinda bashida amsar ko daya daga cikinsu.
Suhana kuwa idan nace shock ma nayi understating halin data tsinci kanta a ciki, har yanzun kwakwalwarta ya kasa processing mata for the second time yau Ayaan ya sake humiliating dinta, no yayi insulting dinta, har yanzun the word FUCK sai yawo yakeyi cikin zuciyarta, she can’t believe Ayaan said those awful things to her, “i am not your fucking brother, get that into your fucking head”, wayan nan maganganu sunyi mata ciwo sosai fiyeda tureta da yayi ranar birthday dinta, kawai banbancin wancan a gaban mutane yayi mata wnn kuma daga ita sai abokinshi amma dukda haka taji ciwonshi kusan fiyeda yanda taji akan wancan.
Abu mai danshi taji yanabin cheeks dinta tana kai hannu sai taga hawaye ne, ta lumshe ido ta bude tana sake shafo hawayen, kenan kuka takeyi ma ba tareda ta sani ba tsabar kuncin da zuciyarta yake ciki, hadiye wani abu tayi daya tsaya a throat dinta da kyar kafin ta dauki glasses dinta ta maida idonta snn ta mike a nuste zata fita daga dakin Lee da yayi wani irin tsam a gafe tsabar kunya da muzantuwa da yayi sakamakon abinda Ayaan yayi mata sai yanzu yayi saurin mikewa ganin fita zakayi daga dakin yace”i beg you in the holy name of jesus kiyi hakuri..please”, juyawa tayi tana kallonshi baka ganin komai sai glasses daya rufe rabin fuskarta so baiga hawayen dake idonta ba tace”why?, its not your fault?”, da sauri Lee yace mata”i know, and trust me he’s sorry too, nasan duk inda yake yanzu wlh yana nan yana nadamar abinda yayi maki”, rungume hannu Suhana tayi tana kallonshi ganin shi bilhaqqi hakuri yake bata on behalf of Ayaan da tasan bazai taba wani nadama ba, sake matsawa kusada ita Lucas yayi ganin tayi shiru batace komai ba ya hada hannayenshi yace”pls forgive him, he’s very naive”, kallon mamaki kawai take binshi dashi kafin tace”but tell me something, are you sure he’s not mentally unstable?, like bashida any personality disorder?”, wani kallo Lucas yayi mata jin abunda take fada yace”no he’s not”, tace”kenan tsagwaron rashin mutunchi ne yasa yakema mutane abinda yakeyi?”, tana rufe baki Lee yace”bafa kowa yake yiwa haka ba it’s only you, ke dinma kuma don yaga kina kokarin shiga rayuwarmu ne and he’s scared”, tace”scared of me?”, yace”no, scared of women”, da mamaki kawai take kallonshi don ita bata fahimci inda ya dosa ba, lura da haka da yayi sai yace”akwai wani abu daya taba faruwa dashi ne a baya wanda yasa ya tsani mata, yake tsoronsu, yake kuma gudun duk wata mu’amala da zata hadashi dasu sbd bazai iya sake yadda da mace ba”.
Shiru Suhana tayi tana kallonshi as tayi sensing so many things cikin wnn mgnr nashi, tabbas dama ta dade tana zargin akwai wani boyayyen abu dangane da rayuwar Ayaan and now gashi ta tabbatar, nan take sai taji tanaso tasan menene wnn abun kilan zaiyi mata amfani cikin plan dinta don haka da sauri kuma cikin zumudi tace”tell me plss, menene ya taba faruwa dashi?”, ganin a yanayin da tayi mgn Lee yace”kiyi hakuri, but i can’t tell you”, daure fuska tayi itama jin abinda ya fada tace”ok then, nima bazan yafe ba”, tana gama fadan haka ta juya zata fita Lucas yayi saurin shan gabanta tareda marairaicewa yace”C’mon now don’t be stubborn, zansa yazo ya baki hakuri da kanshi”, kaucewa daga kusa dashi tayi ba tareda cewa komai ba ta fice daga dakin.
Da sauri Lucas yabi bayanta yana cewa”haba Suhana dan Allah ki tsaya muyi mgn, nasan abinda yayi miki bai kyauta ba amma idan kikaji labarinshi nasan ke da kanki zaki tausaya masa”, juyowa tayi tana kallonshi fuska babu walwala tace”if you really want me to forgive him then ka fadamin dalilinda yasa yake treating dina like trash dukda ni ban tabayin wani abu da zai bata mishi rai koya zubar mashi mutunchi ba, why is he treating me like a lowlife?”, dafe goshi Lucas yayi kafin yace”ok zan fada maki, if really zaki yafe mashi snn ki manta da duk wani abu da yayi miki dama wanda zaiyi miki anan gaba naji zan fada miki, amma dan Allah inaso kimin alkawarin bazaki fadama kowa ba, kiyi alkawarin zaki bar duk abinda zan fada miki a cikinki kuma ba zakiyi judging dinshi ba”, hannunshi ta kamo ta hada da nata hannun ta dunkule kafin tace”shikenan nayi alqawari”, kai ya gyada mata yana dan murmushi yace”thank you”, murmushin itama takeyi tace”to yanzu ta ina zamu fara nemanshi?”, kallonta Lee yayi kafin ya saki wani dariya yace”wa?, ai wnn nasan ya kusa isa gida yanzu haka”, da mamaki tace”wai kana nufin tafiya yayi?, bafa a karasa mashi injection ba?”, wani murmushin Lee ke saki yace”hmm baki san Ayaan bane, idan ranshi ya baci ba abinda bazai iya aikatawa ba”, kai take gyadawa irin ta gamsu din nan tace”gashi nan naga alama”, da sauri Lee ya kalleta yana dan nunata da finger dinshi yace”but mind you, he’s a very sweeeeeeett guy”, dariya ta saki jin yanda yaja sweet din tace”so much emphasis on sweeeeett guy”, yace”eh mana, cause am proud of him”, murmushi takeyi har snn don haka nan takejin itadai Lee din nan ya kwanta mata a rai tace”kuma you love him”, tun bata rufe baki ba yace”alot”, har snn smiling takeyi tace”he’s lucky to have you”, girgiza kai Lucas yayi shima yana murmushin ya amsa mata da”no, i am lucky to have him”, bata sake cewa komai ba kawai sai kallonshi take, ta lura akwai shakuwa da soyayya mai girma a tsakaninsu tareda girmama juna kuma, nan take dai taji tanaso tasan shin are they related by blood ne ko kuma kawai a duniya suka hadu?, batasan meyasa ba haka nan taji tanaso ta sani don genuine kauna taga sukema junansu.
Ganin shirun da tayi Lee yace”yanzu tunda our patient ya sallami kanshi bari inje in dakko mana abinci da sauran kayayyakinmu sai muje gidan muyi breakfast a can”, girgiza kai ta shigayi tana cewa”no kaje kawai, we’ll meet some other day, maybe a school or somewhere else”, girgiza mata kai Lee yayi yace”first of all Madam am not going to take no for an answer cox you’re now my sister remember?, secondly kuma am not in your school, am a graduate”, murmushi ta saki jin abinda ya fada tace”ok Mr graduate lets go”, hannunshi ya fara mika mata yana dage mata girarshi duka biyun yace”high five?”, hannun itama ta mika mashi tana cigaba da dariya tace”high five”, tafawa sukayi kowanne daukeda murmushi fuskanshi.
A haka suka koma daki Lee ya tattaro yan kayansu dake dakin ita kuma ta dauka basket din abinci suka fita daga dakin, saida ya fara zuwa yayima nurses bayani snn suka fita zuwa inda sukayi parking, motarsu Lee ya nufa ya zuba kayan dake hannunshi a baya sai gata itama tazo tasa basket din abincin a ciki, Lee ya kalleta don ya zata a motarta zata biyoshi sai tace”tare zamu tafi”, yace”ok but what about your car?”, tace”na kira yanzu zaazo a tafi dashi”, kai kawai ya gyada mata kafin ya bude motar ya shiga itama ta shiga front seat snn ya fada motar suka tafi.
A hanya kowa da tunanin da yakeyi cikin ranshi, shi yana tunanin irin sauqin kai da kirkinta yayinda ita kuma take tunanin shakuwar dake tsakaninshi da Ayaan sai kuma son jin labarin da yace zai bata batasan why ta qagu taji labarin ba, tanaso taji dalilinda yasa Ayaan ke behaving kmr mai ciwon kwakwalwa don ita har yanzu wani bangare na zuciyarta fada mata yake bazai rasa mental disorder ba.
Tafiyar mintuna kusan 30 sukayi wai a hakama babu holdups sosai cikin gari kafin su karaso gidan, daga waje Lee yayi parking bai shiga da motar ciki ba sbd anjima kadan yasan zaije dauko Kiara daga school tunda gashi yanzu har 12 ya wuce, bude motar yayi ya fita bayan yayi parking din itama ta fito tana karema inda suke din kallo taga an rubuta Get Fit With Us a jikin bango ga kuma kalolin kayan gym nan zane jikin bangon wajen, batadai ce komai ba ta hadiye mamakinta snn ta bishi suka nufi gate don tuni ya dau basket din abincin yayi gaba yana ce mata suje, tura gate din yayi nan take ya bude suka shiga nan kuma Suhana ta sake tabbatar da zarginta don kana shiga wurin zaga gane gym ne sbd glass ne gaba daya front view din wanda kana iya hango komai dake ciki clean and clear, wara ido tayi cikeda amusement tace”wow!, is this your gym?”, da sauri Lee ya amsa mata da”yeah, do you wanna take a look?”, tace”of couse i’d love that”, yace”alright yanzu zamu fara zuwa kiyi breakfast ki huta sai muzo in nuna maki”, ba musu ta daga kai tana cewa”ok”, shima yace”ok lets go”, daga haka yacigaba da tafiya tabi bayanshi, wani dogon corridor taga sun shiga duk a tunaninta backyard zasu fita sai kuma ta gansu a wajen staircase, batadai yi mgn ba ta shiga taka stairs din tana haurawa kmr yanda shima yakeyi har suka gama hawa snn Lee ya tura kofar da yake a bude suka shiga cikin gidan.
Another amusement ne ya sake lullubeta ganin wnn cute little parlor da suka shigo nan take taji gidan ya bala’in shiga ranta don tanason taga gida dan cifcif kmr dai haka balle kuma wnn da aka qawatashi da abubuwan qawa masu kyau, juyawa tayi tana kallon Lee with so much excitement tace”i swear to god this is the most cutest place i’ve ever been, its so perfect i can’t even lie”, murmushi shima yake yi yace”thank you, mu karasa ciki”, ba musu ta shiga takawa har cikin parlon sai kalle kalle take tanajin gidan na sake shiga ranta, ajiye basket din abincin dake hannunshi Lee yayi anan kan table snn ya dubi Suhana da har snn tana tsaye tana Karema gidan kallo yace”pls have a seat”, ba musu ta zauna kan kujerar dake kusada ita, shi kuma ya shiga kitchen sai gashi da juice da tumbler ya dorasu kan tray ya kawo ya ajiye a gabanta yana cewa”idan kuma tea kikeso or coffee yanzu zan…”, katseshi tayi da cewa”no this is ok, thank you”, murmushi yayi zaiyi mata mgn saiga Ayaan ya fito daga daki ko riga babu a jikinshi dagashi sai dan gajeren wando da ko guiwarshi bai karasa ba, hakan ya bayyanar da kyakyawan gashin kirjinshi daya kwanta luf a jikin skin dinshi da har yafi fuskanshi ma haske, bai lurada ita ba saida ya shigo har cikin parlorn, idanunshi na sauka kanta ya juya da wani irin gudu ya koma dakinda ya fito har yana neman faduwa garin sauri, idanuwanshi duk a waje yace”what the fuck Lee, what is she doing here?”.