Chapter 2
by @deejasmah
MAƘOFTAKA DA ALJANU
Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah) & Ameenah Abubakar Ƴandoma
CHAPTER 2
…Khaleed bai kara bi ta kanta ba ganin kamar tana yin bacci. Kofar dakin ya kulle masu tare da kwanciya a gefenta. Abin da Khaleed bai sani ba shi ne idon Nana biyu tsoro da fargabar abin da zata gani ne ya hana ta bude ido. "Naaanaaah!" Ta tsinkayo wata iriyar murya tamkar an shake mage ta na Kiran sunanta. Wasu yawu masu ɗaci ta hadiye tare da kara kulle idanuwanta gam.! Tim! Ta ji karar fadowar wani abu a kusa da ita, a firgice ta bude ido tana kallon Khaleed da ke shaƙar bacci ga dukkan alamu bai san me ke faruwa ba. A karo na biyu ta sake jin karar faduwar wani abu, a wannan karon gefenta ta kalla cikin mawuyacin hali. Wayam babu komai, hannunta ta kai da nufin ta kunna fitilar da ke gefen gadonshi. Sai dai kafin hannunta ya kai jikin fitilar haske ta kawo da kanta. Ja da baya ta yi suka hade da Khaleed. Ji tayi numfashinta na kokarin daukewa sakamakon fafarniya da fitilar ta hau yi tamkar wadda ta jima da birkewa. Kokari ta ke ta tayar da Khaleed da ke wani irin bacci mai kama da mutuwa domin girgizashi take ba kadan ba.
Ƙarar sharar da ta ji anci kaga da yi ce ta katse mata kokarin tayar da shi da take. Duka hannuwanta biyu ta saka ta toshe bakinta gudun kada ta yi motsin da zai saka a gama share kara su dawo sama su shareta. Dariya aka kwashe da ita aka ci gaba da hayaniya cikin muryata da dama tamkar ana cin kasuwa.
"Nanaaaaaaaaaaaaaa" aka daka mata uwar tsawa. A yanzu kam mutuwar zaune ta yi idanunta kadai ke motsi a kaf cikin jikinta. "Sauko daga saman gadon nan" rikitacciyar murya ta fada. Kafin Nana ta yi aure da karfin tsiya aka yi jifa da ita ta daki kofar ɗakinta.
Radadi azaba su ne suka yi mata dirar mikiya a lokaci daya. Kasancewar akwai hasken touch light da kyar ta bude kofar dakin ta na dafe da goshi. Sawun tafiyar wani ta ji a bayanta alamun ana take mata baya, tsayawa ta yi can da tafiyar tsit ta ji alamun an daina take mata baya. Ba ta yi aune ba ta ganta a tsakar gida, zubewa ta yi saman guiwowinta a saman siminti ta na mulmula goshinta da take ji tamkar an yage mata wani sashe a cikinsa.
Suuu! Ta ji wani abu ya wuce da gudu ta gabanta. Mikewa ta ke kokarin yi sai dai ji tayi tamkar an saka sarka an daure mata ilahirin jikinta. Sauti ta rika ji a kusa da ita tamkar na rarrafen yaro, a yanzu kam idanunta sun kasa rufuwa sai faman kokarin kulle su take yi.
- Yadda kasan wadda aka tsoma a cikin ruwan ƙanƙara haka ta fara kyarma, haƙoran sama na haduwa da na kasa. Sharar tare da ƙarar wankin wuri ce ta sake yi ma Nana dirar mikiya a cikin kunnuwa. Lemar da ta ji a wurin kafarta ita ta tabbatar mata ruwan da bata gani ne ya karaso inda take. Karar guje-guje hadi da hayaniyar yara ce ta cika mata kunnuwa, lokaci daya kuma ta ji muryar mace ta daka masu tsawa a cikin Yaren da ta kasa banbance wane kalar yare ne. Can kuma sai ta ji sun fara gyalgyacewa da dariya ba kakkautawa. Hannuwanta biyu ta saka ta dafe kunnenta ta na jiran tsammanin masifar da zata cimma ta. Tafiya ta fara ji a bayanta alamun an kusa karasowa inda take. A yanzu kam ta yarda ta amince da wannan masifa da bala'i da take ciki Ubangiji ya dauki rayuwarta ta san can zata fiye mata hutu bisa ga wannan ƙutattacciyar rayuwar. Ba zato ba tsammani ji tayi an dafa kafadarta. 'Nana!" Khaleed ya furta tare da juyo da ita. Nannauyar ajiyar zuciya ta sake jin shi ne "me kike yi a tsakar gida cikin sanyi nan ga kuma dare daya tsala. A iya sani na bakya kaunar sanyi " shuru ta yi ta kasa magana, ji tayi ta kasa fada masa gaskiya maganar ta yi ma harshen ta nauyi. "Kewaye (toilet) na Shiga" ta samu kanta da furtawa. Ta samu kanta da furtawa, duk da dare ne bata kasa gane kallon tuhumar da yake aika mata da shi ba, saboda a cikin dakinsu a kwai dan karamin toilet. A gaba ya sakata har daki sai da ya tabbatar da ta yi bacci kafin shi ma baccin ya daukesa. Ba su suka farka ba sai karfe bakwai na safiya gari har ya fara haske. A gaggauta Khaleed ya yi alwallah ya tayar da Sallah. Nana kuwa ji tayi ilahirin jikinta tamkar anyi mata duka. Kewayen tsakar gida ta shiga domin ta yi tsarki. Tsugune take amma a zahiri gangan jikinta ce cikin kewayen tunaninta da zuciyarta kuwa tuni sun jima da barin gangan jikinta. Ƙushhh! Ita ce karar da ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula. Butar da ke hannunta ce aka yi kwallo da ita ta hadu da bango tuni ruwan da ke cikinta ya watse. A guje ta fito tana mayar da numfashi, bata ɓata lokaci ba ta samu wata butar ta zuba ruwa. Khaleed ya yi mamakin yadda ya ga Nana ta shigo dakin a birkice. Bai tanka Mata ba ganin ta tayar da Sallah bayan ta gama a gaggauce ta shiga kitchen gawayi ta hura, ƙaton bokitin ta dake cike da ruwa ta buɗe. Ido ta fiddo cikin zallar mamaki da tashin hankali. Wayam babu ruwa babu dalilinsa juyawa ta yi ga dayan bokitin ta wanda ta na da tabbacin rabon da ta zuba masa ruwa tun tana cikin tashen amarci. Zuciyarta ce ta buga da karfi ganin ruwan tinjim cikin bokitin sai dai babban abinda ya tayar mata da hankali wa ya juye mata ruwa daga cikin bokitin. Sanin Khaleed ya kusa makara a aiki tukunya ta ɗora bisa gawayin ta saka ƙatuwar moɗa ta ɗebo ruwa. Murza idanunta ta yi ko dai mafarki ta ke ko kuma bacci ne ya fara daukarta a tsaye sakamakon ganin ruwan da ta ɗebo ya koma jini jajur. Ihu ta kwala ta watsar da ruwan ta fita a gigice….