SANADIN HIJIRA

17_18

by @ummufadeela01

SANADIN HIJIRA


Ummu Fadeela.




17/18






"Hosni! Alburhan bai mutu ba yana raye, yanzun nan na ganshi, na gansa da idanuna Hosni" Ta shi Hosni ya yi daga kishingidar da yake yana dariya sosai kamar zaikifa ya ce, "Fadlallah da alama tsufa ya fara tafiya da ganinka, taya zakaga Alburhan mutumin da ya mutu shekaru talatin da daya da watanni biyar, sannan yanzu rana a tsaka kace ka ga Alburhan? Kai ina gaskiya ka fara shan maganin kara karfin gani".....

"Hosni let keep joke aside, wallahil-azeem na ga Alburhan Raayal-ayn, na ganshi da idanuna bibbiyu ina fatan Allah ya nuna min Annabi a zahiri kamar yadda na ga Alburhan yanzun nan"... Jin abun da yake fada ya yi serious yasa Hosni gyara zama da daina dariya yace, "Fadlallah me kake shirin cewa ne, tukunna ma a ina ka ganshi, kuma a wane hali ka ganshi anya ba idanun ka ke maka gizo ba ko kuma tsananin tunaninsa da ka sanya a ranka yake dawainiya dakai?"


"Ba daya Hosni, na ganshi yanzun nan a filin jirgi dake luxermberg kasan na kai ziyarar aiki a can na ganshi ya ganni har yamini murmushi ya tashi ya tafi na bishi kuma amma ya bacewa ganina"

Hosni da har maganar Abeey ya fara shigarshi amma jin abun da ya ce daga karshe sai ya kuma kecewa da dariya, "Kawai gizo yake maka Fadlallah, Alburhan ya mutu mamaci kuwa baya dawowa da hannunmu muka binneshi, kawai dai ka sanya shi a ranka ne which is not good, idan ka tinashi kai mishi addu'a kawai shi yafi bukata bawai ka firgice ba, dan Allah ka samawa kanka salama komai ya wuce shekara talatin 3full decades ba wasa ba Fadlallah" Hankici Abeey ya zaro daga aljihunshi yana goge gumin dake tsatstsafo mishi duk da sanyin da ake kwadawa, ya za'ai Hosni ya yadda dashi waye zai fahimci cewa lallai yaga Burhan, "Safeenatu"! Zuciyarshi ta bashi amsa kitt ya yanke wayar ya fara lalubo number Ummie, sai dai tuna halin da take ciki ya sa shi mayar da wayar bisa cinyarshi da kifeta yana ajiyan zuciya, to kodai gaskiyan Hosni ne cewa gizo kawai idanunshi ke mashi? Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un" ya ambata gami da mikewa yana jin kamar kafafunshi sun karye da kyar ya iya mai da kanshi wajen da ya tashi. Babu irin bulayin neman da Thaufeeq bai yiwa Abeey ba amma bai ganshi ba, har ya nufi security zai bada sanarwa kawai ya hangoshi yana tafe yana layi kamar wanda ya shawu ko da ya iso shi kuma Abeey bai bashi fuskar cewa komai ba har aka fara announcing passengers su shiga har kuma jirginsu ya daga Abbey bai fita daga shock ba haka Thaufeeq bai daina mamakin abun da ya same shi ba.

*******
 
Badar tana kwance saman kujera mai zaman mutum uku, cikin kwana biyar dinnan kawai ta zabge ta lalace ko abincin kirki bata iya ci sai tunanin Al-ameen duk ta tuna in da ya tafi da kuma wadanda zai tunkara da sunan yaki sai cikinta ya birkice a rana tana iya shiga toilet tayi zawo a kalla sau biyar, dole Umma ta kira likita yazo yai mata karin ruwa ko zata samu karfi kadan, babban tashin hankalinta kuma ta kira wayarsa ya kai sau miliyan daya amma bata shiga. Saudat ne ta fito tana zama a gefenta,

"Sannu small Mom, har yanzu ana nan ana fama da zawon soyayyarce?" a mugun fusace Badar ta mike tana nunata da yatsa "Kin ga Saudat, ban kasa da ke ba, dan haka kada ki kuskura ki kwashi babbar kaso idan ba haka ba kuma"

Kwafa Saudat ta yi tace, "Idan ba haka ba kuma sai me Badariyya? ki daina yaudarar kan kii na fada miki har abada babu aure tsakaninki da Aminu gwara ki nutsu ki maida hankalinki waje daya ki zauna a inda aka san darajarki idan b...."Wani irin tsawa Badar ta katsawa Saudat, "Na bi darajar da gudu babu takalmi, na ce Allah ya tsinewa darajar idan dai irin wannan darajarce da kike ikirari, wallahi ki fita a idanuna in rufe tun wuri kafun in rufe dake a ciki," Yanda ta hayayyako tana bala'i sai hakan ya tunzura saudat itama ta mike, wuyar Badar ta cakumo, "Karya kike wallahi ba ki isa kiyi aure a cikin gidan nan ki barni ba, karya ne wannan bazai taba yiwuwa ba"...Dariya Badar ta yi mai tsayi tana tafa hannu gami da bude tafin hannunta.

"Kinsan dai a nan kike a gareni ko? kin san a tsakiyar tafin hannuna kika ajiye kwai ko, to wallahi idan kika sake sai in yarda shi ya fashe" da sauri Saudat ta tari numfashinta, "Yana fashewa kuwa ke warin zai fara dokarwa hanci har ma kudaje su fara bibiyarki dan nikam na yi gaba kuma bana waige"...

"Haka kikace".

"Eh haka nace, ko kin dauka ni wawiyace da bansan abun da nake ba, ko kin dauka zallar tsanar Aminu ce ta sa bana son aurenki dashi? kawai bazan yadda ina sane kiyi AURE akan AURE ba ne Badariyya,

"Dammmm zuciyar Badar ta bada sauti da karfin gaske kamar zata fado kasa cikin zaro idanu ta ce...

***

Hajiya titi lokacin da kika diba fa ya cika, na miki Alfarma na kara miki wa'adi amma nanma shiru ko dai in saki kayan nan ne su yi ta kansu, "cewar Abu dilalliya cikin dan hargowa tana kallon tsala tsalan yan mata kusan goma sha biyar dake gabanta dan har yau Hajiya titi bata kwashi kayan ba.

"kinga Abu aikin kudi kike yi kuma ko nawa kika bukata za'a baki mun rigada mun gama magana ya kike maida mu bayane, kayan nan an fasa turasu Spain ko Italy kamar yadda aka saba wannan karon yankin larabawa za'a kaisu sai sun fi daraja a can, amma bari in kara kiran Hajiya Babba" Ta yanke wayar tana maida akalar kiran kan Hajiya Babba kamar yadda ta ambata, ringing biyu ta daga,"Yaya ne Titi?"


"Hajiya akwaifa matsala, ya kamata duk yadda zamuyi mu kwashi 'yan matan nan dan Abu ta fara hasala kuma kinsan ta ba mutuncine da ita ba yanzu sai ta janyo mana asara" Dan jimm hajiya babba tayi sannan tace, "Titi zan fita yanzu, mu hadu can gidan ita Abun komai na yaran ya kammala kuma an yi approving daga sama mun gama komai jiya, anytime daga yau zasu iya tafiya, rabin su Kuwait za'a kaisu rabin kuma Saudiyya zamu tura su. ,zan fita yanzu dan haka mu hade can din."


*****
Cikin zaro idanu Badar ta ce "Me, me, me me kika ce? wani irin devilish smile Saudat ta yi a ranta ta ce shege ka fasa, "Yess abun da kika ji shi na fada, bazan bari kiyi AURE akan AURE ba dan ke din matar aurece kin sani na sani ko in tuna miki ne Badariyyya?" ta karishe tana karkata kanta gefe da langwabar da wuya, karaff sai a kunnen Umma wacce take saukowa da dan sauri sauri tasha sutura ta alfarma sai baza kamshi take yi wuyarta yasha gwala gwlai sai walkiya take, hannunta daya rike da bag da car keys daya kuma rike da gyalenta..

Sororo Umma ta yi tana gani yar tata da kanwarta kafun ta ce, "Wani zance na ke ji na Aure kan aure kuma?" Wayancewa Saudat ta yi," No Umma, ina nunawa small mom wani abun al'ajabi ne da na gani a social media so karshen maganarce ki ka ji" wani wawan ajiyar zuciya Badariyya ta sauke tana dafe saitin zuciyarta dake kokarin bullukowa waje gami da komawa baya ta fada saman kujerar tana dafe goshi.


Bata kara bi ta kansu ba ta ajiye bag da veil nata saman kujera,da sauri sauri ta shige kitchen ba jimawa ta fito dauke da plate sai robar ruwa da cup a hannunta dakin Ummie mahaukaciya ta tura a hankali tana leka kanta,tana kwance sambal saman gadonta kamar marar numfashi, cikin sanda Umma ta karasa shiga sai dai bata kulle kofar ba saboda tsaro.Wasu magani ta ciro kwara biyu a bakin zaninta hadi da jefasu cikin cup din kana ta tsiyaya ruwa a kai,sai da ta tabbatar sun narke sannan ta nufo gaban gadon rike da ruwan da abinci.

Bisa mamakin Umma zaune taga Ummie bisa tsakiyar gadon idanunta sunyi jajawur kamar gautar da yasha rana sai faman kiciniyar cire sarkar da aka daure mata Hannu take amma abun ya ci tura dan haka ta fara wani irin gurnani tana buga kanta da allon gadon da take a kai idanunta suna kuma yin jaaa. Sosai take jijjiga har gadon shima yana rawa,haurowa gadon Umma tayi dama masu iya magana kan ce( ranar biyan bukata rai ba a bakin komai yake ba).Dan haka ta haura duk da wani sashi na zuciyarta na gargadinta, da kyar ta yi nasarar dafe kan Ummie ta bude bakinta ta karfi gami da danna bakin kofin maganin a ciki, ba ita ta cire ba saida ta tabbatar da Ummie ta shanye ruwan tass sannan ta ajiye kofin tana haki.

Kwabe fuska Ummie tayi kamar ta san abun da ta bata tana wani irin gurnani kamar zakanya,Umma bata ankare ba kawai taji saukar kan Ummie a goshinta ji kake Kuuuuummmm,ta buga mata kanta,wani irin katantanwa umma tayi ta fadi a kasa Ummie na cigaba da turo kanta sai dai ba yadda zata iya tashi dan duk jikinta a daure.

Da kyar Hajja Fanta ta mike tana jin duniyar tana juyamata amma haka ta dauko abincin dake cikin plate din ta tura gaban Ummie a fili tace, "Ban da ma ni din zuciyar musulunci gareni ba da ko inda kike zan kalla ne. Yo yanzu wa gareki da zai baki abinci magani da ruwan idan ba niba shi dan naki ya tafi jeji shi kuma mijin naki babu abun da ya sani sai harkar kasuwancinsa, ban da ma burina danake so ya cika ko inda kike zan leko ne...Ta karishe tana yin kwafa, "Daga haka ta sa kai ta fice a dakin tana daure fuska, hannu bibbiyu haka Ummie ke dibar abincin,kasancewar hannun nata a daure rabi ke shiga bakinta rabi kuwa duk ya zube bisa shimfidar gadon.


A falo Saudat kawai ta samu da alama Badar ta tashi, jaka da gyalenta ta sura tana nufar hanyar fita tace, "Zan dan fita yau Abeey dinku yana hanya zan biya store in dubo abun da bamu dashi a gidan".Cikin sauri ta fice bata jira jin abun da Saudat ke fada ba, da kallon mamaki Saudat tabi Uwartata...
Sai da Umma ta kwashe a kalla good 2hours sannan ta dawo driver da mai gadi suna biye da ita da kaya niki niki, gyale da bag nata kawai ta ajiye a sama ta sauko tana kwala kiran sunan mai aikinsu suka fada kitchen, a gaggauce suka hada girki mai kyau kusan kala uku ta fitar da Snacks da akayi wrppng nasu a fridge ta sanyasu a microwave dan tayi warming nasu agogon dake kitchen din ta duba dake nuna mata karfe biyar, idan ba dan su Abeey sun yada zango a Uganda bama da yanzu sun iso,

"Azumi ki hada kwanukan nan ki shirya dining yanzu" Cewar Umma tana fita daga madafar, tana shiga daki ta fada wanka bata dade ba ta fito a daidai lokacin kuma taji bude get da tsayuwar mota, curtains na window ta daga tana hango compound din,da kamilalliyar fuskar mijin nasu mai cike da dattako ta fara arba, sai kuma Thaufeeq da fuskarshi ke washe alamar yaji dadin dawowa, "Ja'iri wato zaka daura da sharholiyarka daga inda ka tsaya ko?" cewar Umma a zahiri murmushi yana kwace mata. Cike da aji ta fara shiryawa shiri irin na manyan mata matan wadanda suka ci suka tada kai sannan ta wuce bangaren Abeey da taji shigowarshi tun dazun. Aje duk wani damuwar da ya dawo dashi yayi a gefe ya karbi matarshi dake shirin mantar dashi komai tana sanar dashi irin yadda tayi kewarshi shima ya nuna mata yayi kewarta, sai da ya samu nutsuwa sannan suka kuma yin wanka suka sauko nan kasa suka samu sauran ahalin gidan aka hadu dan cin abincin da aka shirya mussaman dan dawowar Abeey, "Ya jikin Safeenatu kuwa, hope dai dr shettima yana zuwa yadda ya kamata, and ke kuma kina bin dokokin maganinta" Abeey ya tambaya yana zubawa Umma kaifaffun idanunshi,. Daburcewa tayi. 

"Am ahh ehh kwarai yana zuwa mana ehh sosai yana zuwa yana bata injection nata thou dai Aminu ya ce allurar yai wa problem nata girma kafin ya tafi kuma na sanarwa shi Shettima din but he refused to listen, ya ce aikinsa ne idan bai yi mana ba muna iya canza likita shi sa na barshi kawai, magani kuma ina bata yadda ya kamata, wanda ka kawo na gargajiyar ma ta kare tun kwana biyu back" Da kyau kin kyauta Allah ya miki albarka ita kuma muna mata fatan samun sauki maganar Aminullahi kuma ki barshi a nan babbar damuwarsa a fita da Safeenatu waje, ni kuma ina ganin duk kulawar da zata samu a can asibitocinmu na nan ma akwai kwararru, ko zuwa jibi haka sai in koma wajen na gargajiyar mu karbo wani gwanda a dinga mixing bamu san a ina za'a dace ba".


Kallon kasan ido Umma tai mishi a ranta ta ce,

"Ka kawo sau dubu zan zubar dasu sau dubu dan ban shirya...

"Kin yi shiru bakice komai ba, da sauri ta dago, "Ehh ba shakka hakane ranka shi dade, Allah ya datar damu..Tare suka shiga dakin Ummie dake fama dan kwannan nan duka da wani irin ciwo take kwana take yini, ji take kamar ana yankar naman jikinta ne ana zubarwa kusan ko yaushe cikin satin nan bata a hayyacinta, sosai Abeey ya nuna tausayawarshi gareta ya tottofa mata addu'oi sannan suka fita........Lokacin da dare ya yi dare, ko wani dan Adam ya sanya hakarkarinshi bisa gado dan hutawa kamar yadda akan ce dare mahutar bawa, dare mai rufe sirri. A cikin wani daki gidansu Al'ameen, tsaye cikin dakin mai dauke da duhu dulum ko tafin hannunka baka iya gani anyi backing kofa da waya kare a kunne, cikin yanayi na fusata ake magana, "Lallai banason Al'ameen ya dawo a raye, duk yadda za'ayi ka tabbatar ka sanya bakin bindigar ka ka aika dashi inda ba'a dawowa ko burbushin gawarshi bana bukatan gani a gidan nan kasan yadda zakayi ya bakunci lahira a ce yan ta'@ddane suka kashe shi Daniel kada ka manta idan aikin ka ya tafi yadda nake so zan kara maka miliyan goma akan deal namu," daga daya bangaren aka yi magana kafun aka kashe wayar, wani kira aka kuma yi ana karawa a kunne bugu biyu aka daga "Dr Shettima aiki yana kyau, sai dai wannan allurar gubar kamar bata aiki yadda ya kamata banison a samu wata kofarr da zargi zai shigo, ina son ayi mai gaba daya kawai a dannawa mahaukaciyar allurar mutuwa nan take inaga lokacin da muke jira ya yi, mutuwar Uwa da danta zai zone a lokaci guda hhhhhhhhh daga nan kuma komai zai zama a karkashin ikona daga nan damuwa da fargaba me kaje ka dawo zai fita daga raina zamu rayu cikin nutsuwa dagani sai yayana (wa'iyazubillah). Lallai a gaggauta wannan aikin Shettima ladanka kuma basai na fada ba kaima ka sani. Kofa aka nufa aka fice daga dakin

******
Aminullahi*

Suna zaune kusan su bakwai a gaban wani babban tent bisa wani abu mai kama da tabarma amma kalar kayan sojoji wutan itace ne a kunne a gefe haka ma sauran tent tent din duka dauke da sojoji a mafi yawan su sun kunna wutar itace a gefe wasu suna shan shayi. 

Al'ameen kallo daya zaka mishi ka fahimci ranshi a mugun bace yake dan har wani dagowa kirjinsa yake yana komawa, maganar shi ta dazu da MG ne ke dawo mishi cikin kwanya daki daki, "Lallai kada kayi gigin aikata komai har sai mun samu command daga sama Capt." How dare him yana sanar mishi cewa yan bindiga sun fito har sun yiwa wasu manoma sittin da daya kisan gilla amma yace kada a bisu har sai an samu izini daga sama"? me aka mayar dasu ne, kuma haka yana ji yana gani bazai iya yin komai din ba har sai an bashi izini

"What the heck" ya fada da karfi yana dunkule hannunsa daya gami da kaiwa daya hannun naushi, a hankali Daniel dake zaune kusa dashi ya mike tafiya ya yi kadan zuwa bayan wata bishiya ya tsaya kamar mai yin fitsari wani abu ya manna a kunnenshi ya fara magana a hankali, tun tashin sa Al'ameen yaji bai yadda dashi ba haka kawai mussaman yadda yake kif kifta idanu kamar tsohon dan jari hujja, amma sai bai ce komai ba, ganin ya dan dade a wajen ne Al' ameen ya janyo abun gani daga nesa, idanunshi ya sanya akai yana kallon setin inda yake tsaye, 

"Heyy dude, me zaka gani cikin daren nan? kasan idan ka gano yayan Inna dai bamuda masu ruqya a wajen nan." cewar musty yana matsowa kusa dashi, bai ce komai ba sai wata karamar bindiga da ya janyo ya saita daidai inda Daniel ke tsaye ya saki kunamar bindigar, sound na gun din shi ya janyo hankalin sauran soldiers din suka mike kowa na saita tashi bindigar a zaton su wadanda suke harine suka kawo musu farmaki.....