9
by @gureenjoh
ƘARFE ƊAYA BA YA AMO
✍️FATIMA MUHAMMAD GURIN
(GUREENJOH)
@Gureenjo on Arewapen
@Gureenjih6763 on Wattpad
ADABI WRITERS ASSOCIATION
TSOKACI: Wannan labari na Ƙarfe ɗaya...kirkirarren labari ne da bai faru a gaske ba, na kirkire shi ne bisa wani babban dalili da kuma saƙo mai muhimmanci da nake da shi, idan yayi daidai da rayuwarki ko ma yanayi labarinki/ka arashi ne.
GARGAƊI: Haƙƙin mallakar wannan littafi nawa ne don haka ban amince da a sarrafamin labari ko juya shi cikin kowace irin siga ba tare da izinina ba.
*SHAFI NA TARA*
Da kyar jabagan ya saka ta bacci bayan hajjo ta kawo mata tea ta sha, da sassafe Shaly ce ta fara shiga wurinta a lokacin ta farka tana ƙoƙarin sauƙa daga gadon ta riƙota.
"Diva! Hannunkin nan akwai matsala"
Hannun ta kalla raɗaɗin na kaiwa har ga zuciyarta ta ce
"Na sani!"
"Shi ne kika bar shi yana tsami Diva? In an zo gyara zai miki ciwo sossai"
Idanunta da suke sakk na mashaya ta ƙara zura wa Shaly, duk cikin click ɗinta Shaly ta fi zama tamkar babbar ya a gareta fiye da 'yar gida, saboda shekarun da ta bata suna da ɗan yawa, tana ƙaunarta kamar yadda itama take ƙaunarta, kuma duk Shaly ta fi su hankali da hange, shawarar da za ta baka za ka yi mamaki in aka ce maka drug addict ce kuma babbar 'yar daba ce, ta san komai daga kan doka har addini.
"Shaly ina son raɗaɗin ya cigaba da fusata zuciyata ne ga ɗaukar fansa don na rantse da Allah ban taɓa kisa ba amma a yanzu da zan ga mutumin nan sai na tabbatar da cewa na kashe shi har lahira"
Shaly ta girgiza kai
"Ba Za ki yi kisa ba Diva, hakkokin da muke ɗauka ma kaɗai sun ishemu...bari na haɗa miki ruwa ki yi wanka in kira Tala ta duba miki hannun nan"
Tala wacce asalin sunan Talatu ne itama tana daga cikin 'yan hayan gidan Jagaban ita dai ba ta kwaya, ta iya ɗauri duk 'yan dabar arear idan sun samu wani matsala na gargajiya wanda ba bukatar zuwa asibiti ita ke yi ana biyan ta taro sisi.
Ruwan ta haɗa mata kaman yadda ta ce Diva ɗin ta shige don yin wanka, ita kuma ta fita anan ta je kitchen ta cewa hajjo ta haɗawa Diva abinci tayi mata doya da eggsauce da tea yanzu, daga nan ta faɗawa Jagaban hannun Diva akwai matsala za ta kira Tala, a sama yake ƙwarai kuma yana jira ne ya ji an sakar masa yaran da aka kama amma har yanzu bai ji kira ba.
Hankalinshi ya sake rabuwa biyu yana so Diva ta gama samun natsuwa ko za ta iya bashi wani hint kan wannan mutumi don ba zai taɓa kyalesa ba alkawari ne, ba'a yi minti ashirin ba sai ga Shaly da Tala suka shige ɗakin Diva sun samu ta fito tana zaune ɗaure da towel don ta kasa komai da hannun wasa wasa, idanunta na zube a hannun amma zuciyarta hasko mata yake sadda hannunshi ya sauƙa a kai ya kuma murɗe.
Ta Yi dauriya don wasu irin gumi ne kawai take tsatsafarwa sai idanunta da suka rine amma bata yi ihu ko kuka ba, tana da wannan kafiyar da taurin ran, Talatu ta mata sannu bayan ta gama ta shafa mata man zafi ta fice, Shaly ce ta duba mata kayan sawa ta saka da kanta ta zaunar da ita ta dinga janta da lalama har ta ɗan ci wani abu kaɗan kan ta sake kwanciya.
Yamma likis ta farka again sai lokacin ta gwamutsa sallolin ta, Dukda ranta a hautsine yake har lokacin, Shaly na tare da ita tana kwance idanunta lumshe Shaly tace
"Ɗazu Pascal ya shigo kina bacci"
"har ya samu lafiyar da zai dinga yawo?"
"Hankalinshi ne ya tashi kaman yadda na Zubash ya tashi amma na ce komai na under control babu abin da ya faru ta cigaba da kula da ƙanwarta"
"Daidai"
Diva ta faɗa har lokacin idanunta a lumshe amma amsa kuwwar Muryar wannan mutumi take ji, kamshinshi na larabawa na zaune raɗam cikin kanta, alkawari tayi wa kanta da sai ta ɗauki fansa a kanshi ko ba jima ko ba daɗe bare ma ba za'a daden ba, sai ta kawo karshen shi kaman yadda ta yi alkawari.
Bata cika social media ba sai ya kama, ita rayuwarta idan ba'a Buge ba tana zaune cikin su Pabloo tana sauraron hirarrakinsu sai kuma idan rigima ta taso ayi ta, kowa ya san bata da magana wasu ma har son jin muryarta suke wasu na mamakin irin sarautarta da fadancinta kaman wata Gimbiya idan sun faɗi hakan akan ce musu ai Gimbiya ce tunda Gimbiyar titi ce kuma kowa ya amince da basu da Thug Queen kamarta.
"Diva na san zuciyarki bata yi sanyi da abin da ya faru don mun yi kan mai uwa da wabi ba, shi ɗin ne kike so a karan kanshi ban hanaki ɗaukar fansa ta kowacce irin hanya ba amma don Allah kar ki fara tunanin bazarwa, daga sadda kika fara daga nan mun ɗauki hanyar da babu tuba kuma...ba zan iya bari ki faɗa har chan ba"
Diva ta buɗe idanunta da suka sauya ta zurawa Shaly cikin ɓacin rai tace
"Ai sai ki fita daga tafiyar kin ga jini bai shafe ki ba kenan, amma kin san Allah? Na rantse mutuwa ce kawai za ta hanani zubar da jinin mutumin nan, mutuwa ne kawai za ta hanani fara tura sa lahira kan in je! Sai na mishi mafi munin zaluncin da ya ambaceni da shi na janyowa iyayensa zubar hawaye na har abada. Ki daina abu kaman baki sanni ba Shaly"
Jagaban ne ya shigo a kan cushion me kyau dake ɗakin ya zauna
"Shaly ki daina ɓata mata rai bana son hakan, idan ba za ki goyi bayan ra'ayinta ba kawai ki yi shiru"
Shaly ta kalli Jagaban idanunta cike da kwalla, ba zata taɓa bari ba muddin tana tare da Diva ba zata bari tayi kisan kai ba, sun san kan jijiyoyo sossai duk click ɗinsu idan ka ga sun kai sara ko suka basa kaiwa inda mutum zai mutu sai dai su jiggata shi, ko su mishi sanadin wani ɓari na jikinshi ba zata bari Diva tayi kisa ba idan shi Jagaban ya saba ba zata bari ita Diva ta gaji komai har da kisan rai ba.
Miƙewa tayi ta fice, Jagaban ya cigaba da rarrashi Diva da ta narke mishi har dai ta natsu kan ya fice, da kanta ta haɗa ice tun tana sha tana lumshe ido har tayi bacci da haka.
Sai Washegari da ta tashi da safe ta ga shaly ta dawo sun kwana tare saboda yanayinta, bayan sun yi wanka an kawo mata abinci ta ci tace wa Shaly
"Kira su Obo na san suna son ganina"
Shiru Shaly tayi da kyar tace
"Skipo ne kawai waje"
Diva ta zuba mata idanu alamar ban fahimta ba ganin ba zata yi magana ba alamun rashin gaskiya ya sa Diva ta miƙe tsaye
"Kin fara magana ko kuwa?"
Babu yadda ta iya ta sanar mata gaskiya.
Labarin daren su pablo biyu a cell ya ɗaga hankalinta.
"Me Jagaban yake yi basu fita ba?"
Key ta ɗauka zata fita Shaly zata bita tace
"Don't!! Don't you dare Follow me don a yanzu ban yarda da ke ba!"
Tana fita harabar ta ɗauki mota bata kula da gaisuwar da kowa ke miƙa mata ba ma ta fice daidai nan kiran Jagaban ya shigo alamun Shaly ce ta kirashi don ba ya gida, amma tana jin kalaman da ya fara ta katse call din bata ce komai ba.
Police station ɗin da suke tayi parking harabar ta fito ta taka ta shiga cikin police station ɗin sanye da wasu baƙaken hoodie riga da wando bata gama jan zip ɗin ba don ta gaba ana hangar farin vest ɗinta, facing cap ne kanta haka idanunta da baƙar space saboda yanayinsu na kwanakin rashin daaɗin rai da ta yi.
"Ina son ganin IPO na case ɗin su Pabloo"
Ta Yi maganar ba tare da ta kalli kowa ba ma.
"Waye hakan? Ya za ki shigo mana wuri da gadara?"
"Kai!! ba ni da lokacin batawa a kanku ka faɗa min ina zan ga IPO?"
Ta ƙarasa tana matso wa tare da cire glasses ɗin idanunta suka bayyana.
Police ɗin kasa sake magana yayi sai hanya ya nuna mata, ko da ta je da zafin ranta IPO ɗin ya nuna dole za'a yi musu hukunci kai tsaye ta kira Jagaban
"Baaba! Waennan kwalawar suna neman rigima da ni, duk wanda zaka kira ka kira a sakar mini su Pabloo dukkansu tun kan in kunce musu zaren hauka na rantse"
"Ki yi haƙuri! Ban ma so kika je da kanki ba Sohana bari na yi ƙira"
Wayan ya saukar ya shiga kiran Commissioner da kanshi don connections da yake da shi alfarmar dabanci da sayar da kwayoyi baya tunanin wani Chairman ko member ma na da irinshi.
"Jagaban hakan ba zai yiwu ba a yanzu, don Allah ka ba 'yarka shawara ta ɗan dakata tukuna su kwana biyu case ɗin yayi sanyi sai a sake su"
Cewar Commissioner ɗin
"Me kake cewa ne? Jiya haka ka sanar da ni amma ka ƙi faɗa min dalili, Toh saboda mene?"
"Ko na faɗa ba zaka gane ba amma ka ƙira Excellency zai maka bayani.
Kittt ya katse ƙiran.
Excellency ɗin ya ƙira
"Alhaji Bashir Dantani!"
"Jagaban! Ya aka yi kake kirana a irin wannan lokacin? Akwai wani matsala ne?"
Babban ɗan siyasan Alhj Bashir da kowa ke yi wa ganin mutumin kirki saboda tarin kyautatawarsa da taimako na ganin idanu ya faɗa cikin Muryar sanayya mai ƙarfi tsakaninsa da Jagaban ɗin.
"Akwai wasu Yarana da aka kama na kira Commissioner da kaina yake sanar da ni dole sai na tuntubeka don shi ma faɗan ya fi karfinsa"
Jagaban ya faɗa Muryarsa babu wasa don ba zai so a sake baƙantawa diyarsa rai bayan wanda ta sha ba.
"Oh tun shekaranjiyan da aka kama yaran ya sanar da ni yaranka ne amma wannan karon bana tunanin zan iya maka ko wani irin ƙoƙari cikin gaggawa don akwai wanda yayi kane kane ciki da taɓashi daidai yake da lalata siyasata"
"Wanene shi? Meyasa ya fi karfinka?"
"Shi ɗin idon Al'umma ne, ya fi ƙarfina ne saboda ya fi ni kusanci da al'umma magana marar daaɗi ɗaya a kaina zai iya rusa duk wata gwagwarmayana, bari ka ji Irshad ba mutumin da zan yi over looking bane Dukda na tsane sa with passion saboda na sha nuna son sayarsa ta hanyar kudi da sauransu yayi min campaing ta wurin al'umma yana turning ɗina down, ka ga kuwa ya kira Commissioner sau biyu a kan Yarinyarka Diva muddin ya ga ba'a ɗauki mataki ba zai iya bin diddigi kuma zai samu hannuna dumu dumu so ka ga za mun ɓata goma ne biyar bata gyaru ba"
"Irshad!"
Jagaban ya faɗa cikin nazari kan ya sake cewa
"Wannan malamin addinin? Irshad Al-Noor ɗan masu Twins Enterprises?"
"Kwarai da gaske!"
Jagaban ya ce
"To me zai hana a ɓarar maka da shi idan zai hana mu rawan gaban hantsi kowa ma ya huta?"
"Jagaban! Ka bar wanda ya riƙe Allah ka ji, amma dai yanzu ka yi haƙuri a bar yaran nan a rufe zuwa kwana biyu i promise you za su fito kuma za'a kula da su ba za su rasa komai ba, ai na san kalar amfaninsu a wurina bare ma nan da lokaci kankani zan bukace su"
Sallama suka yi, sai sunan Irshad Jagaban ke nanatawa.
Miƙewa yayi ya ɗauki motarsa ya fita, tafiyar mintuna ya kai shi police station ɗin, shiga ciki yayi ya samu Sohana tana zaune ya kama hannunta suka fito waje har jikin motarsa.
"Baaba ya kake fitar da ni ba tare na ga su Pabloo sun zama free ba?"
Ta Yi tambayar hannayenta duka cikin aljihu.
"Akwai babban dalilin hakan, amma ina so ki kwantar da hankalinki mu je gida zan miki bayani"
Ta haɗe gira
"Ban gane ba? Kana nufin an fi karfinka a wannan ɗan karamin case ɗin?"
A ranshi ya ce ba za ki gane ba Sohana a fili ya furta
"A'a ai babu abin da zai fi ƙarfina muddin abin ya shafe yaran nan, mu je gida zan miki bayani"
Ba don ta so ba ta nufi motarta ta ja tayi gaba ya bi ta a baya har gida, a parlor ya sameta tana kai kawo har ya shigo ciki.
"Me kake nufi Baaba?"
Wayanshi ya zaro ya shiga media yayi searching sunan Irshad Al-Noor sai ga hotunanshi iri iri sun fito duk cikin shigar kamala irin ta Larabawa wasu yana kan mimbari wasu yana zaune yana wa'azi wasu yana zaune kawai wuraren taruka da dai sauransu.
Idanunta ta sauƙar kan fuskar wayar daidai wani bugawa da zuciyarta ta yi, hannu ta ɗaga ta nuna shi da yatsa muryarta na rawa ta ce
"Baaba a ina ka...san shi? Wanene shi a garin nan? Kuma a ina ka san zan sameshi?"
"Kin sanshi ne Sohana?"
"Shi ne!"
"Shi ne wa?"
"Wanda ya..."
Sai ta shafa kuncinta tana runtse ido
"shi ya mareki?"
Gira ta ɗaga don kalmar yayi mata mugun nauyi a harshe ba zata iya fitarwa ba idan ta fitar tana jin kaman zuciyarta zai babbake don bacin rai da tafasa.
Hannunta ya kama suka zauna.
"Then wannan malamin shi zai zama makiyinmu na farko a wannan gaɓar, ba zai fito daga No where yayi ta dasa miki baƙin ciki ba Sohana ba zan zuba ido in kalleshi ba! Shi ya sa aka kama su Pabloo a yanzu daga sama kowa na tsoron tsoma baki don kar ya lalata musu siyasa saboda karfin ikonshi cikin al'umma amma idan sun san wata ai basu san wata ba".
Ta riƙe hannunshi.
"Ka bar ni da shi Baba"
Ya girgiza kai
"No! Ki bar ma batun sanya kanki a lamarinshi ni zan ji da komai"
Ta Yi shiru kawai ba don ta ji maganan baban ba, a ranta tana nanata sunan Irshad.
****