JODAH

09

by @sadisakhna





👑 *JODA* 👑_____

             



Na 

*Sadi-sakhna*

Ƴar mutan Jama'are





THE TRIO OF TALES 
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey) 



@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp


LITTAFI NA 1



*Harƙa ta (9)*👑








“karki shiga damuwa,nasan na yanke miki hukunci batareda na faɗamiki kalubalensa ba,amma ki sani baka samun wani abu saika rasa wani abu,idan kuma kanaso kasamesu dukka to yazama tilas ka dage. Idan kinshirya cika wannan muradi ina dakon kallonki a cikin wanda zasuyi wannan gasa nanda shekara biyar idan da kwana.”

Muna cikin maganarmu har muka isa majalisin da Ummai Asma’u take koyar da yara mata da maza wanda bazasu wuce sa'nnina ba,kowannensu na sanye da kaya na alfarma,kuma fuskarsa ɗauke da takama da nuna amon ƴanci. Maganar Baba Yakub ce tafaɗomin,inaga ƴaƴan sarakuna ne da masu kuɗi. Domin koda ganin shigar ma ya isa ace mutum ya tantance.

Magana ya zagaya yayi mata,sainakalli ta ɗago fuskarta mai cikeda haske da annuri ta kalleni,baƙin saƙin lullubin datayi akanta yayiwa fara fuskarta kyau,duk da ta manyan ta amma hakan bazai hana a hango kyawunta ba.

“To gaskiya a nawa bangaren bana buƙatar baiwa ƙarama,saboda bazata iya yin aikin bangarena ba,bansan ko gaba ba idan ta girma in Allah yakaimu,amma bari zan haɗata da Umma Hajar Kanwata da take kulada bangaren magani, Wato bangaren Guru almahdi, domin naji tana cikiyar samun yarinya ƙarama wacce zata dunga rakata yanko magani a wajen Tsirrai,saboda rike mata wasu abubuwan. Karka damu zaka iya tafiya ta zauna idan muka kammala wannan darasin zan kaita gareta.”

Cikin nutsuwa ta gama yimasa bayanin kuma ya gamsu sosai,hakan yasa yajuya yamin sallama yatafi,sai naji kaman nabishi yakaini gun ummah ta amma hakan bazai yiwuba akwai tarin abubuwa a gabana. Zama nayi a ƙasa gefe da cikin rumfar dasuke yin karatun,wanda ita kanta ma abar kalloce wajen kyau.

Wasa nakeyi da duwatsun da suke gabana,amma dukkan hankalina kacokam yatafi kan karantarwar da sukeyi,wanda akeyinsa ne akan darasin yanayi . Yanda take bayanin sosai nakeji yana shiga cikin kaina saboda yanda bayaninnata yake burgeni.

Bayan an gama darasin wani daga cikin Yaran ta tambaya amma yagagara bata amsa,sauran ma da ɗaɗɗai amma babu wanda ya amsa,akan wai taya ake gane yanayin damuna idan yana zuwa.

Ganin kowa yakasa bada amsa har ranta yafara baci yasa na ɗaga hannu daga waje. Murmushi tayi cikeda mamaki kafin tabani damar yin bayani,da murnata natashi nafara kwararo mata shi,domin fess nake jinsa akaina kaman yanda tayi bayani a daƙiƙu goma da suka wuce.

“Akan gane yanayin daminane farko idan iskar da take ƙadawa daga Yamma zuwa gabas,ta dawo tana kaɗawa daga gabas zuwa yamma,sannan akwai tsuntsaye da basason ruwa ko dabbobi za'a ga suna yin hijira zuwa wani yankin,sannan dabbobi masu son ruwa kuma ko wanda rayuwarsu keda alaƙa da yanayi na damuna sun fara bayyana”

Sakin baki ummi Asma’u tayi tana kallona,harda sauran yaran da ake koyarwa. Ganin kallon da sukemin sai a sannan na kula na karya gargaɗin baba Yakub na farko kenan dun ba'aje ko ina ba. Wai yaga danƙari maƙari………….


Sunkuyar da kaina nayi jiki a sabule nakoma na zauna,domin duk sainaji kunya takamani da suka xubomin idon,Fasihmman dana kulada wata a cikinsu mai doguwar riga kalar zinare tana zabgamin harara. Muryar ummi Asma’una tsinkayo tanamin magana.



“Haƙiƙa kinyi ƙoƙari sosai,duk da badake aka fara darasin ba kuma kina can gefe amma har kika samu damar bada amsa yanda ya dace,irin haka akeso mai ɗaukar karatu ya maida hankali da abinda ake koyar dashi. Menene sunanki yake wannan baiwa mai basira?”



Cikin sakin fuska na kalleta tareda bata amsa da “Joda” maimaita sunan tayi a bakinta tana murmushi kafin tace.

“Yayi kyau to Manyan gobe mungama karatun yau,gobe ina Allah yakaimu akwai darasin fiƙihu dan haka kowa ya fito da wuri. Ke kuma taso kibiyoni na kaiki inda zaki kasance”



Da saurina na sake ɗiban kayana nabi bayanta,har lokacin ina waigawa muna haɗa ido da wacce takeyimin kallon tsana da ƙyama,wataƙila gimbiya ce domin shigar kayanta ya bayyana hakan.



Fita mukayi daga Harabar makarantar izuwa wata ƴar hanya dazata kaimu wani gini a can gefe,wanda duk shuke shuke suke neman rufeshi. Shima cikinsa babban ɗakine mai fili,sai wasu ƙofofin na ƙananun ɗakuna kaman goma sun haɗu dashi. Yanayin wajen yasha banban da ɗakin karatun Guru Abdulmumin domin shi nasa litattafaine da rubutu ta ko ina,amma wannan kuma tsirrai ne kala kala a cikin ƙananun tukwane,wasu an rataye su wasu kuma a ƙasa,ga mutum mutumi na sassasan jikin ɗan adam kala kala,anyi zane a jikinsu da tawada. Sannan akwai gadaje na Itace a jere a wajen,wasu da mutane a ciki wasu kuma babu. Banda warin magani dana ganyayyaki Babu abinda yake tashi a wajen. Bayine guda uki suke ta kaikawo a wajen,Kowacce sanye da doguwar riga buba ta saƙi koriya,amma an ɗaure daga kunkumin sai farin ɗankwali akan su. Kenan su nasu Kayan aikin korene sabani wanda suke aiki a wajen karatu su nasu Shuɗine.

Wani Dattijone da ƙaramin gilashi a idonsa yafito daga wani ɗaki hannunsa ɗauke da safar hannu wacce aka ɗinkata da farin ƙyalle. Shima farar fatane suna yanayi da Guru Abdulmumin.

Da sauri ummi Asma’uta karisa gareshi tana murmushi kafin ta rusuna tana yi masa gaisuwa,shima da fara'ah ya amsa har yana tambayar ta wata yarinya da alama ƴar tace.

“Baba ina Ummu hajar kuwa,naji itane mai neman ƴar rakiya na nemo magani,shiyasa da aka kawota wajena itace ta faɗomin a rai”

“ehh hakane kam yanzunma na turata can wajen dubo maganin kuwa,am kawomin wani marar lafiya mai matsalar kumburin zuciya,tun jiya muke ta ƙoƙarin wajen ganin kumburin ya sauƙa amma har yanzu shuru”



Ganin wani zancen daban suke,yasa nayi amfani da wannan damar da nufi wani kwando inda wasu beyare guda biyu suke ciki,an saka musu ciyawa suna ci. Wani kwandonne yasake ɗaukar hankalina shikuma macijine a ciki,ya nannaɗe a jikin wani itace da aka saka masa. Gabaɗaya na shagala da kallonsu har Ummi Asma’u ta tafi ban sani ba.

Shin kina sha'awar Nazartar rayuwarsu ne,gabaɗaya hankalinki ya tafi garesu”

Tun ɗazu ashe kallon abinda nakeyi yake.

“Dukkansu halittune masu rai,amma yanayin halayyarsu da zati na jikinsu ya banbanta,hatta abincin da aka sakamusu dabanne,kaman dai halittun dana gani suna shawagi a saman ruwa,suma halittarsu dabance kuma suna cin halittun da suke cikin ruwane. 

Abinda yazo cikin kaina shine An halicci wani ne domin wani yaci ya rayu,kuma hakan ba zalunci bane,domin wanda ake ci yawanci zaka samesu suna dayawan gaske,idan wani bayacinsu kuma suna hayayyafa wataƙila zasuyi yawane sucika duniyarnan. Tun tashina na kula kamar komai yana bukatar daidaito,idan babu shi babu abinda zai tafi daidai. Kamar dai yanda ka cire ciyawa ka sakawa waɗannan,shikuma wannan dogon ka ɗauki ɗaya daga cikinsu ka saka masa domin yaci,nasan shima baza'a rasa wanda zai cinyeshi ba koh?”

“ Kafin ki bani amsa inaso ki faɗamin shekarunki da kuma kaɗan na rayuwarki,yanayinki ya nuna kamar kinsan abu fiyeda shekarunki haka kuma bakisan wani abun ba da a shekarunki yaci ace kinsani”

“Sunana Joda shekarata Goma shabiyu inji umma,an haifeni da shanyewar ƙwaƙwalwa,wata ɗaya daya wuce aka tsinceni a jeji a sume,nayi sati biyu da kwanaki a sume kafin na farka,bansan mai ya faru a rayuwata ta bayaba,amma na tsinci kaina da son sanin komai dayake kewaye dani,ciki kuwa harda su kansu mutanen dana kasance jinsunsu sunamin kamar baƙine su a gareni”

Tunda na farayi masa bayanin hankalinsa gabaɗaya ya dawo kan abinda nake faɗa,fuskarsa ɗauke da murmushi. Sallama akayi wata mata tashigo wacce zata kai ummah ta a haife.

Amsa mata yayi kafin ta ajiye kwandon datazo dashi akan wani tebur mai faɗi dayake ɗauke da wasu itatuwan akai,wasu an nannaɗe an busarsu wasu kuma an sakasu a cikin kwalba da ruwa an rufe.

 

“Na dawo Abih kai gaskiya Ganyen daka turani nemowa yafara yin nisa sosai,gabaɗaya nagaji saboda tafiya,Kuma kona tura Bayi basa iya samo wanda akeso,gaskiya yakamata na samu ɗalibi na koya masa wannan aikin saboda na dunga hutawa Abih,ni dama bangaren koyarwa na ɗauka irin nasu Asma’uda yanzu ina zaune a cikin da'irar majalisi abuna”

Taƙarisa maganar tana share gumin fuskarta da wani farin ƙyalle,sannan tafara ɗaukar ganyen tana jugewa akan wani faranti. Gabaɗaya bata kulada Joda ba wacce ke tsaye tana kallonta.



“Har kullum ki daina ƙosawa da baiwar da Allah yayimiki,Hakeem ya turo wasiƙa kan cewar yana dawowa,yana zuwa hankalinki zai kwanta ki daina yanko magani,kiyi maza ki haɗa wannan maganin Marar lafiyan yana buƙatar sa cikin gaggawa.



“barka da rana Ummu hajar”

Na faɗa cikin girmamawa.

Mamaki maganar tawa tabata,domin ko kaɗan bata kula dani a wajen ba. 

“wannan fah daga ina muka samu baƙuncinta?”

“Sabuwar ƙwaƙwalwace data farka daga bacci sati biyu da suka wuce, da alama bata gane mai yake nufi ba,shiyasa ko neman ƙarin bayani batai ba.
 baiwa ce Asma’u ce ta kawota yanxu”

"Kuje ki bata uniform na shara da goge zata fara aikin a nan bangaren magani a gobe, sannan zata tunda halartar Koyarwa idan inayi"

“Abih wacece ita ne haka,tunda naga kana faɗin haka to lallai akwai wani abu a tattare da itah, domin wani lokacin manya ma idan an kawo sai su wuce baka ɗaki ko guda ɗayaba daga cikinsu,sai wannan ƴar karamar da baka ganin zatayi barna kokuma yin aiki ba daidai ba"

"To ai baki bari na gama baki bayanan bama,sannan inaso ki sakata cikin bayi masu koyon ilimi,domin zuwa wani lokaci zata shiga sahun masu taimakawa ta bangaren sani"

"Abih wai wacece itane,da har ta ɗauki hankalin ka haka,ko ni baka nuna damuwa akaina haka ba lokacinda nake kamarta,har korata kake idan nashigo nam wajen saboda kada nayi maka barna"

"Daɗina dake ummu hajar saurin yanke hukunci a abu batareda kinga mai yake kushe dashi ba,inaso idan na baki aiki kiyi yanda nace basai kin tsaya tambayoyi ba"


“Shikenan amma zan saka mata ido,har sai ranar danaga ta nuna cancantarta na wannan matsayi da ko ni bansamu ba kafin zan zubda makamaina”

Tashi tayi daga kan kujerar da take tazo inda nake ta tsugunna,murmushi tayimin tana kallon cikin idona,sai da tasaki murmushin kafin zuciyata tayi sanyi,domin nayi zaton dukana zatayi da farko.



“Karki tsorata domin bazan cutar dake ba,saidai zan saka ido akanki domin naga wacce baiwace dake da har taja Guru Almahdi babban Likitan da babu yashi a nahiyar nan ɗaukarki a matsayin mai aiki anan wajen da wannan ƙananun shekaru naki abinda bai tabayiba tsawon shekara talatin da suka wuce. Sannan hakan karyasa kiyi alfahari da nunawa,domin zai iya zama hatsari ga rayuwarki,ki rike hakan a matsayin sirri,ki kwantar da kanki ki tsaya iya matsayinki dakowa yasanki dashi,ta hakanne zaki mori wannan dama da Allah yabaki. Ina yimiki fatan nasara kinji?”



Kallon cikin idonta nayi,haka kawai naji itaɗin macece ta daban,data iya jan ragamar zuciyarta da ƙarfin hankalinta da ilimin ta. Ɗaga mata kai nayi alamar na fahimci duk shawarar data bani”



“nagode da shawararki kuma nayi miki alƙawarin zan tsaya a matsayina na baiwa,yin aikin daya kasance wajibi a gareni,Babu wanda wani abu dazanyi wanda zai zamo matsala a gareku ko wajennan"



A idonta na fahimci tayi mamakin kaifin basirata na mayar mata dukkanin maganar da tayimin a duƙunƙune.

“Allah ya shiga lamarinki,muje na kaiki ga inda zaki zauna”



Daga haka takama hannuna muka Fara tafiya,juyowa nayi na kallin Abih kaman yanda take faɗamasa.

“Na barka lafiya sannan nagode da wannan dama daka bani,bazan taba baka kunya ba da izinin Allah”

“Kije maza ki huta,gobe Ki fara zuwa aiki ko.

Ɗaga masa kai nayi cikin zumuɗi kafin muka bar wajen.



***   



Tun kafin keken dokin ya tsaya ta sauƙa,Allah ya sa yaja burki ta tuni ya ji mata ciwo a kafarta ya biya kuma da bakin ransa. Kaman ana fizgarta haka tashiga bangarennasu na Sunkia Maryama,kai tsaye turakar mahaifiyar tata ta wuce,tana shiga ta cire mayafin dayake kanta taci wurgi dashi. Kallo Sunkia Maryama Tabita dashi tana zaune wata baiwa na nuna mata Wasu sarƙoƙi a ƙaramin akwati na ƙarfe,irin wanda ake kawowa kyauta daga wajen matan manyan gari.

Ɗaga kai tayi ta kalli gimbiya meerah wacce takeyin abu kaman sabuwar ƴar bori,saida tayi ya isheta domin kanta kafin ta zauna tana huci. Da sauri wata baiwa a gefe tabi ta tsine dukkan kayan da ta barbaza a turakar,sanna wata da sauri ta tsiyanyi ruwan inibi mai sanyi ta miƙa mata cikin ladabi,karba tayi batayi musu ba tasha,ta rage sauran kaɗan ta haɗa dukka da kofin ta wurgawa baiwar data bata ruwan inibin a jikinta. Bata nuna ko kaɗan a fuskarta cin fuskan da gimbiya meerah tayi mata ya bata mata rai ba,domin batada ikon yin hakan,saima ɗaukar kofin da tayi tanufi hanyar fita tana tattare kayanta kada ruwan inibin daya bata mata jiki ya zuba a harabar ɗakin wajen ya baci. Wata daga gefe sai sannu take jeramata tareda fatan Allah ya huci zuciyarta.



Saida numfashin ta yafara sauƙa kafin Sunkia maryama tayi mata alamar taƙarisa gareta,cikin sangartaka ta ƙarisa tana zubewa a jikinta ragwaf 

“Ummahhh”



“menene shalele,meyake damunki keda kika tafi da fara'arki ,kuma kinsani nasha faɗamiki cewar banaso kina irin wannan halin a gaban waɗanda kike mulka,domin hakan bakomai zai haifar ba zai zubar girmanki.”



“Ummah to ya zanyi wai yau muna cikin darasin da ummi Asma’u take ɗaukarmu,wanda nace miki Kaita Hamad dayazo daga Masarautar mali yana halarta,kawai wata baiwa an tambayemu bamu bada amsa ba,ta ɗaga hannu wai zata bayar,Ummi Asma’u ta bata dama ta faɗi amsar daidai. Kaita Hamad hadda kallonta da ido mai alamar ta burgeshi ummah,wayyo ummah ya zanyi shikenan girmana kasaitata da kuma ɗaukakata ta sun faɗi warwass a gaban wata ƙazamiya kuma ƙasaitacciyar baiwa"

Taƙarisa maganar cikin ƙaraji da huci tana mimmiƙewa kaman mai shafen aljanu.

Lokaci guda bacin rai ya mamaye zuciyar Sunkia Maryama domin babu abinda taƙi jini daya wuce taga bacin ran rabin jikinnata.

"Wannan bazai yiwu ba kenan labarin abinda ake faɗa na Jami'ar Al'azhar suna sauƙar da darajar masu mulki ya tabbata kenan,to kuwa dolene a ɗau mataki akan hakan."

Haka tayi ta bawa gimbiya meerah baki da girmama lamarin harta samu tayi kuma tasamu nutsuwar cin abinci.

Washagari da wuri Aminatou ta tashi,kafin su baba mero su farka harta kaɗe shimfiɗarta ta tattare ɗakin da wajen ɗakin yayi tass.

Nuratu ce tafara farkawa wanda ita batayi sallahr asuba ba tashinta kenan,murmushi tayuwa Aminatou kana gani kasan taji daɗin ganinta a ɗakinnasu. Itama murmushin tayi mata kafin tace.

"To maza ki tashi ki wanke idonki naji Baba mero nacewa na zaki tafi wajen aikinki dawuri ko?"

Zabura tayi jin furucin Aminatou da alama ta manta abinda yake gabanta.

"Wayyo wayyo Gimbiya meerah tace naje zan tayata shiryawa tafiya makaranta,shikenan nasan sai tayi farfesuna yau kam,baba mero ki tashi ki tayani wayyo kashina ya bushe"

Tana maganar cikin firgici tana jijjiga baba mero wacce bacci ya ɗan sureta bayab tayi asuba,da sauri kuwa itama ta tashi jin abinda Nuratu take cewa tafara yin abinda ya dace.

Itadai Aminatou tausayi yarinyar tabata ganin ta firgice akan abinda baici ace tasanshi ba a shekarunta,saita tuno da tata ƴar itama,ko ina take Allah masani.

Ƙarfe bakwai daidai da gudu da komai ta isa sashen gimbiya meerah,wani ajiyar zuciya ta sauƙe ganin a lokacinne meerah ta tashi daga bacci kuma ta buƙaci akai mata ruwa mai ɗumi,ba aikin Nuratu bane dan haka cikin kwanciyar hankali tafara nata aikin,na haɗa mata ruwan wanka kafinnan tagama ta taya ta suyi. Sai a lokacin tafara tunanin gurasar da bata tsaya ta karba ba,amma tasan baba mero zata karba mata,ko kuma su raba nata,domin dama sun saba hakan.

Bangaren Aminatou kai tsaye sashen da suke je jiyan ta nufa,gabanta sai tsinkewa yakeyi domin batasan mai zata tarar a wajen ba. Da wata baiwa sukaci karo a bakin ƙofa tanacin wani abinci dayayi tsami wai watinsane take tashi,jikinta sai tsuma yake ta haɗa uban gumi,amma hakan bai hanata kaiwa lomar abinci ba,wasu dogarai guda biyu na tsaye akanta. A bayin dasuke gefe taji labarin wai abinci ta sata ta boye to bata samu damar ci ba har ya rube yafara wari a cikin kayanta tukunna aka gani,shine Gimbiya Asmah tasaka ta dole saita cinye abincin, kuma ɗayace daga cikin bayin data taho dasu,hmmm nata ma kenan inaga wani can barene yayi laifi. Jiki babu laka ta wuce masu hukuncin da wanda akewa hukuncin ta shiga sashen.

A zaune take kaman jiya,sai kayan jikin ta kawai data sauya zuwa Silki kalar rawaya(yellow). Wani yatsinewa takeyi kan bazata ci ayabar ba,yayinda baiwar wacce take da ɗan yawan shekaru take ta nan nan da ita. A gefe Aminatou ta tsugunna bayan ta miƙa gaisuwa,tana jira taji wanne umarni za'a bata ta karba ta cika.

Wata baiwa ce tashigo tareda tsugunnawa a gefe sannan tace

"Ranki ya daɗe Yerima Kabeer na Jiran iso daga gareki zai shigo ku gana"

Tana jin waye yake zuwa tayi saurin tashi zaune kaman ba itaba tace.

"Kice masa maza ya shigo ina jiran dakon isowarsa gareni"

Tana gama faɗin hakan mai bata ayabar ta ajiye tareda kinkkintsa mata jikinta cikin sauri,domin duk ta yamutse kaman wata mai shirin haihuwa ta biyar.

Da sallama a bakinsa yashigo,dukkan bayin kowa ya kalli ƙasa kaman baya wajen. Dogone baƙi mai kyawun fuska,yashe buba kalar ruwan Jibi anyi mata ado na Fasihmman. Bashida yawan shekaru saidai jarumtaka da izza ta mulki. Kai tsaye idon mai kallo zai nuna yanda gimbiya Asmah ke zumuɗin ya ƙariso shi sam babu hakan a tattare dashi,domin yana zama bayan sun gaisa hannun sa kawai yakai kan cikinta yana tambayar lafiyarsa,ita kanta jikinta ya ɗanyi sanyi ganin cewa bata ita ya damu ba sai abinda yake cikinta,hakan bai isheshi ba yaƙara dacewa.

"Dafatan kina kulamin da cikinnan sosai ko,domin wannan idan namiji ne ba ƙaramin zarrah zan bawa maƙiya ba"

Hararar sa tayi cikeda takaici kafin tace.

"Ranka ya daɗe shin ni kazo ganine kodai cikin jikina,kai ko zumuɗina bakayi tunda na baro sashenmu na dawo nan,ni inata begenka kullum,Allah Allah nake na haihu na koma sashena amma kai ko a jikinka"

Wata fuska yayi irin ta ƴan duniya kafin yace.

"Meyasa zaki faɗi haka masoyiya ina ƙaunarki mana,kuma banda abinki keda cikin dayake jikinki ai dukka ɗayane ina ce? Ina nan ina jira mana ki haihu lafiya ki dawo mu zauna,na damu sosai da Ummi (Sunkia Madina) ta ɗaukemin ke"

Da daɗin baki da komai ya ɗaureta ta manta komai,amma sau ɗaya zakaji bayanin nasa indai kasan halin maza ƴan duniya ka tabbatar yaudarar ta kawai yakeyi,amma babu soyayyarta a ƙwayar idonsa.

Bayan ya fita wani dogarine ya kawo masa wata wasiƙa,waigawa yayi ganin babu kowa yasa wasiƙar a aljihu,kunnensa yakai wajen bakin dogarin ya faɗamasa mai ake ciki.

"Ranka ya daɗe an kamota yanda kace,tana can an ɗaureta a wajen da yake rubuce cikin wasiƙar,ashe daɗi lafiya taƙawa"

Yaƙarisa maganar yana sheƙe dariya irin ta yaran masu kuɗi ƴan duniya.