Chapter 2
by @barista
BIYU A ƊAYA
***
YOTA 13
Team of FIVE INK legends
Na sadaukar da wannan littafin gare ki, shugaba me capacity ❤️Na'ima Suleiman Sarauta👸🏻
Page 2
Tsimi² taja jiki tana bin Alaja, ƙirjinta na ci gaba da bugawa, tunani ne fal cikin ranta, tsoron ta wanne irin hukunci Alaja za ta yi mata? Tana ta zancen zuci da sake² har suka iso cikin katafaren madafar abinci inda nan ne suke girke-girke kuma anan ne inda sauran yan'uwanta ma'aikata suke, suna shigowa Alaja tayi mata nuni da tulin ganyen Alayyaho sannan tayi mata magana cikin ɗaga murya
"Ke ce yau za ki girka miyar nan kuma ban lamunci asara ba, ki tabbatar tayi daɗi"
Kai ta gyaɗa jin Alaja na kora mata bayani, tare da kashedi, ta kurawa tulin ganyen idanu tana jinjina kanta, tunani take yi yaushe zata kammala yankawa? Kuma har ta kammala miyar kafin lokacin da Alaja take buƙata....
"Bilqees!"
Alaja ta kira sunanta da ƙarfi, da sauri ta wuce inda ganyen yake ta ajiye ɗan ƙaramin bag nata dake maƙale a bayanta ta ɗauki wuƙa ta soma yayyanka wa ba tare da ta kalli inda Alaja take ba, ballantana sauran ma'aikatan da su ma suka maida hankalinsu kan aikinsu saboda ganin shigowar Alaja, tsaki Alaja taja ta fice ta bar musu madafar abincin. Bilqees ta sauke numfashi tana tsinke ganyen tana kuma yayyanka wa ƙanana kasancewar an wanke sa tas da gishiri sai sheƙi yake yi..
"Special cooker, yau kin makara"
Bilqees ta ɗago ta kalleta ta ɗan waro fafaren idanunta waje ta ce
"Same to you yesterday Majada"
Murmushi Majada tayi, ita ma jiya ta maka sosai kamin tazo restaurant, ta sauke numfashi ta sanya hannu tana tsinke ganyen ta ce
"You and Alaja are not on good terms"
Tayi maganar cikin son jin me Bilqees za ta ce,
Sauke numfashi Bilqees tayi, ita ma abin yana matukar damunta, yadda Alaja ke yin treating nata yanzu bata jin daɗinsa kwata-kwata ta rasa dalilin da yasa take yi mata haka, kasancewar a shekarun baya ita ce ƴar gaban goshin Alaja kowa ya san yadda Alaja ke sonta amma yanzu banda hantara ba abin da take yi mata, ta soma yayyanka ganyen a hankali ta ce
"Majada taimaka min mu ƙarashe kada ta sake leƙowa ta tadda ban gama ba"
"Okay Bilqees let us hurry up, mu yi sauri mu kammala yau dai Alaja ta ɗau zafi"
Majada ta taimakawa Bilqees suna hira sama² har suka kammala yankawa, sannan Bilqees ta ɗaura tukunyar miyar, nan da nan ta haɗa miyar ganye wacce taji kifi banda da stoffish da manja, gaba ɗaya wajen ya gauraye da ƙamshim miyar, nan Alaja ta shigo, bata yiwa kowa magana ba ta wuce inda take jin ƙamshin miyar ke tashi, tana buɗewa miyar da Bilqees ta dafa ne, ta sauke numfashi tare da juyowa tana kallon Bilqees ita ma Alajan take kallo, ganin yadda take kallon miyar ga kuma tsananin farin ciki ya bayyana akan fuskar Alaja hakan kuma yayi mata daɗi, Alaja tayi mata alama da ta ƙaraso, ta ƙaraso kusa da ita ta ce
"Ki ɗauraye plate ki zubo min miyar da tuken shinkafa za ki haɗa ba semo ba"
"Ok Maa"
Ta faɗa, Alaja ta fice, ita kuma Bilqees ta ɗauko plate ta ɗauraye ta zuba mata abinci kamar yadda ta buƙata ta kai mata, a inda take zama ta kai mata don ba kasafai Alaja ke zama cikin mutane ba, ta ajiye mata sannan ta fito ganin Alaja na waya.
Madafar abincin ta koma ta zauna tana sauke numfashi, Majada ta iso ta zauna kusa da ita tare da cewa
"Yau kam sai yadda Allah yayi damu"
Bilqees ta kalleta tare da cewa
"Me yasa kika ce haka?
"Baƙi za ayi da rana shiyasa Alaja take ta gyare-gyare"
"Yau kam ranta a ɓace tsoro ma nake ji, gani nake bata sauƙo da ɓacin ran ba"
"Ai ba ke ce silar ɓacin ran ba, haka muka taddata tana mita"
"Tashi za mu yi mu ci gaba da aiki, kada mu sake yin laifi"
Miƙewa su kayi zuwa inda sauran ma'aikatan ke aiki suka saka hannu, Bilqees ta kula da Aunty Laraba tun da ta shigo take mata wani irin kallo ta kasa fassara na menene, amma ta kauda kai kamar bata san tana yi ba.......
************************
Nigeria, Maiduguri KIRAWA'S FAMILY
A nutse suka iso inda yake zaune, suka tadda shi da Ya Sa'eed ne don haka suka rage tsawonsu tare da gaidasu lokacin guda
"Barkan ku da safiya"
Ya Sa'eed ne ya amsa da
"Yauwa sannunku, Ashfat how was school?"
Ta amsa cikin siririyar muryarta da
"Alhamdulillah muna ma shirin fara exam"
Ta faɗa idanunta akan Dr Waahab Waseem KIRAWA, wanda ya maida hankalinsa kan wayar sa yana daddannawa, ta sauke numfashi a lokacin da ya ɗago ya kallesu suka sudda kai ƙasa saboda kwarjini da cika ido da yake dashi amma banda Ashfat kur ta kura masa idanu, rabonta da ta sanya shi cikin idanunta yau kusan sati, ta kula cikin kwanaki biyun nan yana fita da safe kuma baya dawowa gida da wuri...
"Har yau baku sauya ba, kuma kamar ma ba za ku sauya ba"
Yayi magana cikin kamewar murya a kuma lokaci guda sannan kuma yana yi yana rarrabe maganar. Sai kuma ya ja numfashi ya sauke a hankali ya ci gaba da cewa
"Ayi ta maimaita muku abu ɗaya amma bakwa ɗaukawa, kusani fa, kun kai munzalin da ku ma za ku yiwa ƙannenku faɗa amma kuma ku kuke yin abin da bai dace ba....
Ya katsewa Ashfat tunanin da take yi game dashi, yayi magana calmly and gently fuskar sa babu wasa ɗauke take da gargadi da kuma faɗa, haɗa baki su kayi wajen cewa
"Kayi hakuri"
Idanunsa na kansu bai ɗauke su ba, yana karantar yanayin su, a hankali ya sauke numfashi ya sake cewa
"A'a ba hakuri za ku bada ba, so nake ku gyara ko don ƙannen ku su yi koyi daku"
Teemah ta ce
"Ya Waahab za mu gyara"
Ya Sa'eed dake kallon su ya ce
"Allah yasa ku gyaran, amma banga alama ba, gashi jiya su Raudat har da zuwa party don Allah dududu shekarunta nawa? 17 ne fa amma har da zuwa party kuma saurayi ya zo ya direta a ƙofar gida"
Suka soma zazzare idanuwa mamaki ƙarara ɗauke kan fuskokinsu Raudat da zuwa party! Ai ko su sun manta when last da suka je party...
"Hakane abin da Sa'eed ya faɗa kuma hakan yana da nasaba ne saboda ganin kuna yi, da bakwa yi su ma ba za su yi ba, amma kuma wannan ya zama gargaɗi na ƙarshe da zan yi muku, ku tabbatar da kun sanya idanu kan ƙannenku ku san duk wani motsin su, duk abin da su kayi ba daidai ba ku sanya su kan hanya"
Jikinsu yayi sanyi, saboda yau cikin ruwan sanyi yayi musu faɗa saɓanin a cen baya da yake musu tsawa da nuna ɓacin rai cikin fushi wani lokacin kamar yayi musu duka. Ashfat ta ce
"Ya Waahab kayi hakuri hakan ba zai sake faruwa ba"
"Uhm"
Kawai ya faɗa Ya Sa'eed ya sake cewa
"Abin da ba ku sani ba shine, we are in large and popularity family an san mu sosai kuma ido yana kan mu, duk motsin mu an sani so ba zayyu mu muna gyarawa ba ku kuma kuna ɓatawa ba, don haka duk wacce tayi ba daidai ba dole a hukunta ta"
A nutse Dr Waahab Waseem KIRAWA ya ɗauki rigar sa ta sama, jallabiya ya zura kan kayan wasan ƙwallon ƙafa, ya ɗauki wayar sa ya mik'e tare da kallon su ya ce
"Za ku iya tafiya"
Sa'eed ma ya mik'e suka bar wajen, Hauwa ta numfasa ta ce
"Gaskiya wannan injustice ne ta yaya wasu da laifi mu da hukunci, wannan bai dace ba, su da su kayi laifi su ya dace a hukunta ba dai mu ba"
"To sis Hauwa ni banga wani laifi a maganar su ba, in kin kula suna nufin sun bamu matsayine a cikin wannan family mu dinga tarbiyyantar da ƙannen mu, kuma haka ne, ko jiya sai da ki kayi ƙorafi akan Muhibbat....
Cewar Teemah, cikin sauri Hauwa ta ƙatse ta da cewa
"Kin san rashin kunyarsu kuwa? Ai ni duk wacce tayi min raini sai na kwaɗa mata mari"
"To sai ku tashi mu shige ciki ko breakfast ba mu yi ba"
Cewar Ashfat ta mik'e daman duk ta gaji da tsuguno da ta yi, su ma suka mik'e, Suhaima ta ce
"Hauwa ko manki da faɗa, ni fah hamdala nayi da yau bai daka mana tsawa ba, a nutse yayi mana magana, don haka ina bayan abin da ya faɗa kuma in ƙannenmu sun gyaru ai ci gaban mu ne"
"Dalla gafara cen matsoraciya, don baki da ƙanwa ne shiyasa ki ke faɗin hakan, kin san rashin kunyarsu kuwa uhm keep your mouth kawai"
Suhaima bata son yawan mutsu don haka tayi shiru amma kuma ta taɓo mata abin da yake damunta, ta sauke numfashi ta wuce ciki, suka bi bayan ta....
Dr Waahab Waseem KIRAWA yana barin wajen kai tsaye ya wuce ɗakinsa, a hanyar shigowa suka rabu shi da Sa'eed, kowa yayi side nasa. Yana shiga ya rage kayan jikinsa ya faɗa toilet ya watsa ruwa ya jima yana wanka sannan ya fito ɗaure da towel ya tsaya gaban mirror ya kurawa kansa idanu yana kallon kansa ta cikin madubi, ya ɗan jima a haka sannan ya sauke numfashi a hankali, ya shafa kwantaccen sajensa da ya sha gyara sannan ya shafe jikinsa da Men lotion ya feshe jijinsa da body spray na hug sannan ya shirya cikin shiga ta manyan kaya shadda army green yayi matukar kyau, coloured ɗin ya amshi farin skin nasa sai ƙamshi yake yi, ya ɗaura bakin hand watch kirar Rolex nasa ya sanya white eyes glass ya fito ɗauke da wayarsa a hannu ya wuce side na Mamie, a nutse ya yi sallama ya kusa kai palour ya tadda babu kowa a palour ya wuce ɗakinta yayi nocking ta bada izinin shigowa ya shigo ya zauna cikin girmamawa ya ce
"Barka da safiya Mamie?"
"Likita Alhamdulillah amma dai ba tafiyar bace ta taso da safiyar nan?"
"A'a Mamie sai wani sati"
"Oh! Allah ya nuna mana, nayi tunanin tafiyar ce"
Ta mik'e tana naɗe dardumar sallah da take zaune akai tana lazumi tun bayan sallah asuba, ta zauna bakin bed ta kura masa idanu na wani lokaci, tana karantar yanayin sa, sudda kai ƙasa yayi, a hankali ta ce
"Aiki za ka wuce ko?"
"A'a Mamie yau ba zan je hospital da safe ba, sai zuwa yamma night duty nake dashi, Mommie zan duba sannan na wuce side na Daddy"
"Hake ne, to Ubangiji ya taimaka"
"Amin Mamie"
"Naga jikin nata ma ya soma sauƙi"
"Eh haka ne kam jikin kam sai godiya"
Ya miƙe tare da yiwa Mamie sai an jima, kai tsaye ɗakin da yake kusa da main palour ya shiga ya tura ƙofar tare da sallama, shiru ɗakin babu motsin komai sai ƙarar gudun fanka dake tashi, a hankali ya ƙaraso bakin bed inda ya kura mata idanu yana kallon ta, ganin tana bacci yasa ya sauke numfashi yana jin tausayinta har cikin ransa. Mutum ace a kwance, komai sai an yi mata, bata san me duniya take ciki ba, sai dai kuma jikinta yayi kyau kamar ba wacce take cikin hali jinya ba, turo ƙofar da aka yi ne yasa ya waiga, ganin Suhaima ce yasa ya maida hankalinsa kan Mommie tare da amsa sallamar ta, ta ƙaraso ta ajiye tea flask da plate da 2 cups, a hankali ta ce
"Ya Waahab barka da safiya"
Duk da ɗazu ta gaishe shi, amma tayi saboda wannan lokacin a ɗakinsu yake ba filin Assembly ba. Ya kai hannu yana duba magungunan dake kan bed side yana so yaga wanne ya ƙare don ya sake kawowa ya amsa gaisuwar da Suhaima tayi masa
"Lafiya, ya me jikin?"
Ganin yana duba basket dake ɗauke da magungunan yasa ta ce
"Da sauƙi, magungunan ma sun kusa ƙarewa"
"Eh na gani ai, kamata yayi ki sanar dani tun tuni sai yanzu za ki faɗa min"
"Kayi hakuri Ya Wahaab naje side naka jiya a rufe kusan sau biyu ma naje"
Ya dubi abin da ta shigo dasu ya ce
"Jiya ban zauna ba, amma in hakan ya taso ki kirani a waya"
"To Yaya"
Mamakin sa take yi bayyi musu faɗa ba ɗazu yanzu ma cikin sanyin murya yake magana...
"Tana iya cin abinci ne?"
Ya katse mata tunanin da take yi, tayi saurin cewa
"Eh Yaya amma sai abu mara nawi, ko me ruwa² haka"
Bai ce komai ba, ya juya ya fito, ya bi ta main palour.....
****************************
Zaune suke a main palour sun yi ɗaiɗai sun kishingiɗe jikin manya manyan kujerun dake palourn suna danne dannen wayarsu, tun da suka dawo anan suka yada zango kowacce ta hau online, unexpected suka ji murya kamar daga sama
"Ikon Allah! ni kam ban yi farin ciki da Bature ya ƙirƙiro waya ba, ace yaran yanzu baku da abin yi sai danne dannen waya!"
Tashi kowacce tayi tare da cewa
"Barka da safiya Ammie"
"To ba wannan ba ma ku riƙe gaisuwar ku, kuna nufin ba za ku ɗaura breakfast bane?
"Za mu ɗaura Ammie yanzun nan ma"
Cewar Ashfat, Hauwa ta ce
"Ammie me zamu girka?"
"Ga ku ga store ga kuma kitchen ku yi duk abin da ya dace"
Suka amsa da
"To"
Suna ƙoƙarin barin wajen ƙamshin turaren jikinsa ya ɓade palour suka juyo suna kallon sa, ya iso tare da gaida Ammie cikin girmamawa
"Ina kwana Ammie"
"Lafiya Abdulwaahab, ya aiki"
"Alhamdulillah"
Ta zauna tana sake cewa
"Kayi breakfast ne?"
"A'a Ammie ba fita zan yi ba, side na Daddy zan je"
"To bari su kammala su kai maka ɗakinka"
"Na gode Ammie"
Ya faɗa ya shige ƙofar da zata sada shi da side na Daddynsa, Ashfat ta sauke numfashi suka dawo kitchen tana mamakin yadda ƙamshin turaren sa ya zama na musamman...
"White Yam with eggs sauce za mu yi"
Cewar Teemah, Hauwa ta ce
"Kin manta garin Jalingo za mu girka"
Suka sanya dariya, Ashfat ta ce
"Ku dafa abinci na kowa da kowa ni na Ya Wahaab zanyi"
Suka juyo suna kallon ta tare da taɓe baki, Hauwa ta ce
"To ni fah kamar na fara fahimtar wani abu"
"Kan ki ake ji ni bani waje na fara aikina"
Cewar Ashfat tana ƙoƙarin zaɓo abubuwan da za tayi amfani dasu
"In tayi wari ma ji"
Cewar Teemah, Hauwa ta ce
"Aiko bata yi wari bama za mu ji"
"To ya ishe ku, ku yi aikin ku nayi nawa"
Nan suka sanya dariya, ta harare su tare da cewa
"Ok ina ga kun manta ni yayar ku ce"
Nan ma su kayi mata dariya. A nutsu ta haɗa masa breakfast me sauƙi a lokacin su ma suka kammala, suna ta ta tsokanarta bata ce komai ba sai ma manna musu da tayi, ta fito ta wuce ɗakin Dr Waahab..
A lokacin da ya wuce side na Daddynsa, ya tadda Daddynsa da Abbie suna zaune da alama tattaunawa suke yi akan abu me muhimmanci, baya so ya katse su har zai juya kuma, Abbie ya ce
"Dr Waahab ƙaraso mana"
A nutse ya ƙaraso ya zauna kan carpet kamar yadda ya ke yi a duk lokacin da yazo gaban iyayensa, cikin girmamawa ya gaida su
"Daddy, Alhaji barkan ku da safiya"
Alhaji ya amsa da
"Yauwa barka dai Likita ya aiki?"
"Sai godiya"
"Abdulwahab lafiya kalau, har zaka fita wajen aiki?"
Cewar mahaifinsa, a nutse Dr Waahab ya ce
"A'a Daddy aikin dare gare ni"
"Ok daman ma nemanka muke, yanzu zaman mu anan tattaunawa ne muke yi na yadda za mu sake fitar da Hajiya ƙasar waje a sake duba lafiyar ta, kamar jikin har yanzu babu sauƙi"
Gyara zama yayi sosai kan carpet ya ce
"A'a Daddy a ɗan dakata da kaita outside, akwai wasu magungunan da na ɗaurata akai bi'iznillahi zata samu sauƙi"
"To bari mu jira zuwa wani lokacin, to amma yaushe ne tafiyar naka? tun last week da kayi min zancen ban zauna mun sake tattaunawa ba"
A nutse ya ce da mahaifinsa
"Ai an ɗaga tafiyar ne sai next week in sha Allahu"
Alhaji ya ce
"Ah yayi kyau Allah ya ƙaro nasarori"
"Amin"
Cewar Dr Waahab, mahaifinsa ya ce
"Allah ya nuna mana lokacin"
"Amin"
Cewar Dr Waahab, Alhaji ya ce
"Alhaji Waseem yakamata mu aurar da waɗan nan samarin sai tasowa suke yi"
Murmushi Dr Waahab yayi ya sudda kai ƙasa, Alhaji Waseem KIRAWA ya ce
"Ai Alhaji Shereef da wannan abin nake kwana, amma kasan yaran yanzu akwai ra'ayi, amma za mu zauna mu tattauna akan wannan batun"
"Gaskiya yakamata"
Cewar Alhaji Shareef KIRAWA, Alhaji Waseem KIRAWA ya kalli ɗansa yana murmushi tare da cewa
"Abdulwaahab wane gari ma za ku tafi?"
"Daddy ƙasar Ghana ne"
"Oh za kayi nesa, ai nayi tunanin anan ƙasar ne"
"Da farko a nan ne to daga baya ne aka maida tafiyar ce"
"Da alamu za ka jima"
"Eh aikin 3 month ne"
"To Allah ya dafa"
"Amin"
Ya faɗa ya mik'e ya fito zuwa ɗakinsa......
Comments and share fisabilillah