BABI NA SHIDA
by @maidambu41
KARFE DUKKA ƘARFE NE...!!!
{Zanen Ƙaddarar Falilah}
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai...
#Mai_Dambu
BABI NA SHIDA
mourning
Har yau bata san me yasa zuciyarta yaki aminta da Ya Nafi'u ba, duk da kuwa tasan babu wata alaƙa da zai nuna cewa ba wani mugun abu a kasa a tare dasu, tasan Falilah tayi rashin ji, amma kuma Allah yafi su sanin abin da yake boye. Duk da Ya Man da Hajja Mama sun kashe maganar, amma haka kawai jikinta yake bata wani abu, kuma da ace akwai wani abu a kasa da ya fito, Uba daya ba wasa ba, sannan kodan rikon da Hajja Mama tayi mishi Ya Nafi'u ba zai tab'a cutar da Falilalh ba.
A can dakin Hajja Mama kuwa, Ya Man kuka yake hawaye na zuba daga idanun shi. Tabbas yau ya kure Hajja Falmata tunda gashi tana gaya mishi abin da ya fito bakin ta, gara ta fada mishi gara ta fadi duk abinda yake ranta suddenly zai fahimci yadda take jin abin a ranta. "Mustapha me zan maka? Ni ba zanje ko ina ba, daga Yola ta wuce Abuja ta cigaba da zama da Nafi'u shi ya fi cancanta ya zama mahaifinta sama da kai Uban da ka haife ta." "Nayi nadama wallahi nayi danasani don Allah ki dawo min da ita kusa da ni" "Kai ai kana da kafa, ka tafi ka dawo da ita dole sai ni ce? Ko baka da halin da zaka iya dauko ta ne?" Ta tambaye shi, har lokacin yana kallonta tuno kuruciyar su yayi da irin zaman da suka yi bai tab'a saka abu ta tsalleke ba, tsabar biyayyar aure, har ya cika gidan da mata bata tab'a rigima da wata ba, sai dai su sune mata da rigima, idan har zai ce wacece waziriar shi tow Falmata ce, domin ƙoƙarin kiyaye hakkin shi, ko Yaran gidan ita ta koya musu yadda zasu girmama Ubansu, saboda ita ce Uwargidan shi.
Duk wanda ya shigo gidan daga cikin Yaranta da na kishiyoyinta turus suke, su juya da baya domin ba zasu iya ganin Malam cikin wannan yanayin ba. Baki daya suka taru a falon Hajja Jume suna kuka. "Don Allah Hajja Jume ki tafi ki bata hakuri." "Babu inda zani domin lokacin da tayi mishi dad'i har cewa yayi duk wacce ta kira mishi sunan Falilah a bakin auren ta. Ta gasa shi itama lokacinta ne" fita suka yi daga wajen ta,.suka nufi bangaren Hajja Warisah. Suna kuka domin tunda Hajja Jume ta ce bata zuwa wallahi ba zata din ba ne. Suna shiga ta gan su kamar an koro su. "Lafiya?" "Don Allah muje ki bawa Hajja Mama hakuri Ya Man sai kuka yake yana durkushe a gabanta." "Ikon Allah, ita kuwa me yayi zafi?" "Mijin Falilah ya rasu" "innalillahi wa'inna illahi raju'un, Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar, kai wannan Yar tana ganin Jarabawa muje" ta mike suka fito, nufar kofar Hajja Mama tayi, har lokacin Ya Man yana durkushe a gaban bata d'ago kai ta dube shi ba. Magana ce kuma ta gama shi, babu uban da zai sauya mata ra'ayin ta. Zuwan Hajja Warisah bai saka ta sauya ra'ayinta ba. Sai ma tashi da tayi ta bar falon. Dole suka kira Hajja Jume, ita ta shigo tare da Aunty Zahra'u.
"Had'a kayanta zamu tafi tare da ita." Haka suka shiga hada kayan Hajja Mama, d'ago kai tayi tana kallon Hajja Jume. "Duk wanda aka bashi hakuri tabbas an zalunce shi ne, amma fushi irin naki bai da amfani babu wacce zata iya tunkarar Falilah a wannan yanayin sai ke don Allah kiyi hakuri, a dawo da ita Zahra'u ki saka a gyara wancan dakin." "A'a ku bar min ita a kusa ba zata kuma nesa da ni ba in sha Allah"
Haka a Ya Man ya saka aka fito da babban motar shi sienna aka wanke ya Zabi mutane biyar domin sauran Yayunta maza sun tafi Yola, dan ma ance sai gobe jana'izar. Kafin kace me an hada tafiya Yola domin su tari Falilah duk da tafiyar dare ce amma yayi Addu'oin bayan ya dafa motar ya ce su tafi. A cikin yan tafiyan akwai Aunty Zahra'u, Hajja Mama da Hajja Jume, Aunty Sa'adatu da suka dauke ta a hanya, sai Ya Kabiru da Ya Hamza. Sai drive.
---
Falilah
Ina kwance nayi kuka har ina jin zafi a idanuna, na rasa meke min dadi. tunda nayi sallah Hanny ta kawo min abinci, bayan iya ci ba nasha kunu kawai, sannan na koma na kwanta, kwanafi ya dame ni dole na tashi na nufi kitchen.
"Ih, gobe in sha Allah zamu taso na gode da Alfarman da kuka mana. Ok Kai madalla Allah ya kara muku hakuri ya gafarta mishi." naji muryan Ya Nafi'u.
"Daddy ina wayata?" Na tambaye shi. Juyawa yayi ya zuba min idanu, kafin ya ce min. "Babu caji na saka miki ita a caji" yana fadar haka ya juya ya cigaba da kallon Sunnah tv. "Waye ya rasu?" Na tsinci bakina da tambyar shi. "Abokin aikina ne" ban san dalilin da yasa ni jin hawaye ya zubo min ba sai da na share na juya na nufi kitchen na dauki kanwa na fito, na jefa a bakina na koma dakina na kwanta, dakyar barci ya dauke ni, sai juyi nake a gadon. Wani irin kewar Ahmad nake ji kamar na tafi Yola a daren domin idan na same shi ba zan mishi ta wasa ba. Haka dakyar nayi barci.
Mafarki
A hankali nake takawa a cikin koran ciyawar da ta lullube wurin, hango shi nayi zaune a kujeran azurfa sai wani murmushi yake min, da sassarfa na isa wurin shi na durkusa a gaban shi. Dafe gwiwar shi nayi ina murmushi. "Kayi kyau yaushe zaka dawo?" Murmushi ya min, sannan ya ce min. "Ai tafiyar mu anan zata tsaya, ga shi can zaku cigaba da tafiyar da shi. " A hankali na juya yana tsaye kamar yadda na san shi a shekaru goma sha biyar da suka wuce. "Kasan Mr Aljani ne?" Tashi yayi ya nufi wata kofa da aka yi da wasu irin ganye. "Na gode sosai Falilah," daga haka ya shige kofar, ina ganin ganye ya rufe kofar rub, riko hannuna aka yi na d'ago kai zan yi magana.
Farkawa nayi cikin tashin hankali, zufa na karyo min. A duk lokacin da zan rasa aurena bayyanar Mr Aljani yake saka ni fahimtar zan rasa aurena, Ina son Ahmad don Allah kar ya rabani da shi. Sauka nayi a gadon jikina babu kwari, na nufi banɗaki nayi alolana fito na fara sallah, har aka yi sallah asuba, sai lokacin Hanny suka shigo da Aunty Amrah suka hada min kayana. "Lafiya?"
"Babu kome" suka fada min, sannan can suka ce min na fito, ko karyawa bamu yi ba,.muka nufi airport mu hudu ina dauke da Babyn Hanny, koda muka isa kamar mu ake jira, a kan lokaci muka bar Abuja. Wajen karfe tara na safe muka isa Yola, tunda naga Ya Bana jikina ya dauki rawa, ga Ya Kabiru da Hamza, duk sun zo haka yasa jin wani irin zazzaɓi ya sauko min.
.......
Mariyah Matar Ahmad.
"Nancy Allah ya tsine miki albarka, kun kashe min Yaro, Ahmad na ce zaku kashe kuka kashe min Yaro na, dama dan waye nake wannan faffutukar ba dan shi bane? "
"Ke Malama dakatar min, kashe Mijin kika yi bamu kashe miki Danki ba, don Allah Ahmad ya kashe miki danki" kuka take tana ji tana gani, ta rasa Ahmad da D'anta.
Tsoro ya hanata fitowa domin bata san me zata ce musu ba, haka yasa ta cigaba da zaman dakin tana kuka. Wurin karfe sha daya na dare, tsoro ya hanata sakewa domin Basmah taki zama a wurin ta. Gani take itama zata saka a mata abin da tayiwa Baban su da Bassam. Tana kwance har barci ya fara fisgar ta, kamar a barci kamar a zahiri kofar ɗakinta ya bude, Ahmad ne sanye da fararren kayan shi da suka b'aci da jini. "Mariyah me na miki? Mariyah me na Miki?" Yana matsowa kusa da ita. Amma taki motsi, ai kuwa kafin kace me ya tako ya sheke wuyarta, Ihu take tana kokarin kwatar kanta. Dakyar ta farka ta samu ta fada can gefe kafin ta fita da mugun gudu. Tana ihu domin tana ganin Ahmad yana bin ta, haka gidan kowa ya fito tana ihu da tonawa kanta asiri.
Har su Hajja Mama suka iso wurin karfe hudu na asuba, ai kuwa take aka bude musu bangaren Falilah suka shi, a tsaye suka kwana akan Mariyah tana fadar abin da ta aikata. Wanda da alamun ya tab'a ƙwaƙwalwa ita.
Morning
......... Muna shigo layin su Ahmad gabana ya yanke. "Hanny ko Hajiyar su Ahmad ce ta rasu?" Dauke kai Hanny tayi tana share kwalla, har cikin gidan muka shiga daga can na hango Hajja Mama, sanye da Laffaya maroon color. Hannunta rike da counter, Jamal da Ya Babangida suka iso.
"Barkan ku da hanya, sannun ku da zuwa." Yawwa suka amsa, ni kan sai raba idanuna nake ina niman mijina. "Ina Baban Basmah Ya Jamal?" Kamar bai ji ni ba,.haka suka wuce da sauri, shi da ya Babangida, zan kuma magana Hajja Mama ta ce min. "Yarda da ƙaddara yana cikin rukunin imani, duk abin da zaki gani ko zaki ji,.ki yarda Allah ya baki ya kuma amsa lokacin da yaso, nasan ke me amsar ƙaddara ce, ki taimaka min ki amshi wannan ma a wannan lokacin, Allah yana ganin ki, kuma zai kara miki kyautar da ya baki ya amsa, ki zama me gode mishi ki zama me yarda da kyautar shi, kar ki zama me butulce mishi, Ubangiji yana madakata."
Tun bata gaya min ba, mafarkin jiya ya dawo min, a hankali nake d'aga kafana. Har falon Hajiyr su Ahmad, da sallama na shiga falon wanda ya dinke da mutane. Tasowa Fad'ime tayi ta rungume ni, wani iriin sanyi naji kamar an lullube ni da danyen nama, har cikina yana wani irin juyawa, makara ne a gaban mu wanda kasarta a ka saka tsumokara. "Allah ya baki hakuri ya sauke ki lafiya Falilah, Hamma Ahmad ya tafi ya bar mu"
Durkusawa nayi a gaban gawar Ahmad, na tsura mishi Idanu, hannuna yana rawa na bude mayafin da aka lulluba mishi. Fuskar nan ta cika tayi kyau, ga zatin nan ya karawa fuskar kyau, alamun rahama suna ga wanda ya mutu kaga fuskar shi dauke da murmushi da fara'a, komawa nayi na zauna. "Allah bai amshi Ahmad ba, sai da ya kawo miki sauki da sassauci rayuwar ki, don Allah ki yarda da Allah yana kaunarki da rahama ya jarabce ki." A hankali na juya jikin Hajja Mama na fada kanta, "Hajja Mama, daki bayana daki bayana wani abu ya cakke baya, don Allah daki bayana ko zai daina" na kasa kuka domin jin wani irin abu nake ji a bayana da kahon zuciyata. Tofa min Addu'oin take, kafin can na samu damar fashewa da kuka, "Innalillahi wa'inna illahi raju'un, a ina zan samu mijin da zai kaunace ni? " Na fada ina kuka na juya da sauri zan nufi wurin makarar, maza suka iso ai nan aka ga tashin hankali. Domin kamar mahaukaciya haka na koma naki su dauki makarar. "Wallahi baku daukar min Bobby na bai mutu ba, na rantse da Allah gashi nan zai tashi dalla ku sake min shi" Aunty Zahra'u da Aunty Amrah suka zo suka d'ago a jikin makarar, ina kuka ina kome aka fitar da gawar Ahmad, wallahi ba zan kuma samun nagartaccen miji irin shi ba,shi din na musamman ne shi daban ne, wani irin kuka nake me cin rai da tab'a zuciya. a hankali naji kamar ruwa me dumi yana bin kafana. "Hajja Jume! Rike min cikina kar ya zube".na fada ina zubewa a kasar wurin sumammiya. A yadda na samu labarin a tare da Hajiya Mahaifiyar Ahmad aka wuce da mu asibiti,domin ita ta samu pralazy, ni kuma sai da aka daure min mahaifana, domin kwana na biyar ina barci. Ban san waye a kaina ba.
Ranar da na cika na shida na farka, na rame sosai. Duk me Imani sai ya zubda kwalla. Da taimakon Yayuna mata nayi wanka aka bani kayana sauya, doguwar riga ce ta Atamfa, Hajja Mama tana zaune hannunta rike da Mug ta mika min. "Sha naji ance kina son kunu?" Gyada kai nayi, ta cigaba da cewa. "Tow sha, kiyi hakuri kowa mutuwar yake jira, ki rungume ƙaddaran ki." "Tow" na kurbi kunun da nake jin shi kamar magani. Haka na mika mata kunun. "Ih baki sha ba" "Hajja na koshi" ganin ina hawaye yasa ta koma rarrashina tare da nasiha, da yarda da ƙaddara haka ya sani shiru na kwanta. Zuwa dare aka sallame ni.
Ba zance nasan meke faruwa ba, domin wasu abubuwan labari naji, haka washi gari aka yi addu'ar bakwai din shi dama tun ranar ukun shi aka kwashe kayana zuwa Yobe, ranar bakwai kuwa ana Addu'oi da yamma masu mota suka bar Yola, ni kuma washi gari da sassafe muka wuce ta jirgi saboda halin da nake ciki. Har abada ba zan daina yiwa Ahmad Addu'a ba, domin ya bani abubuwa dayawa.
A bakin Umamatu naji labarin wai ai an kai Mariyah kotu, domin danta Bassam shima ya rasu bayan Addu'oin bakwai, abin da na iya fada shi ya bata mamakin. "Ku kyale ta, bakin cikin mutuwar danta ya ishe ta" "baki son a hukuntatta" "hmm! Hukuncin Allah ya ishe ta." Na fada ina share kwalla, daga haka nayi shiru. Da wannan muka rabu. Koda muka isa Abuja sai da nayi kwana uku, haka hada kayana na can tass aka cire na Ahmad aka aika musu Yola, sannan ni kuma Ya Nafi'u da kanshi ya mai da ni Yobe, ko kafin mu isa gidan, duk da an bude get din da zamu shiga amma haka na fito na nufi zauren Ya Man, yana zaune akan kilishi ya kishingid'a. Na shiga zauren da zai kaika cikin gidan mu. Na zube a gaban shi, "Ya Man" bude idanun shi yayi ya zuba min. Hawaye suka zubo min. "Ya Man na shigo gidanka?" Zubur ya mike zaune, "Aishatu! Tashi ai gidan nan ko mutuwa nayi na mallaka miki balle kuma ina raye naki ne, shigo Albarka da Nasarar Ubangiji ya tabbatar a gare ki, shigo da kafar dama Falilah " haka kowa na gidan ya fito, tare da Yayuna maza da mata, a hankali na koma jikin Ya man ina kuka me cin rai, ina ji ina ma Asad bai shigo Rayuwata ba, Ina ma da hannun agogo zai juya na gyara kuskure daya tal da nayi, wai shin Laifina ne ko laifin wanda ya shigo domin lalata goben ka?..........
Kunji yarinya da sharri, shi kuma Asad din meye laifinsa😏🙄 salon ki ja mishi tsinuwar al'umma Chaii, ni bana son sharri
Kuyi min Uzri zuwa Sunday ko Monday Insha Allah #mourning#familyissues#Mistakes
#Mai_Dambu