BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 13

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA♥️* *Arewapen@ayshadansabo*

©️Ayshat Ɗansabo lemu ✍🏻

*Free page 13*

*ABUJA*

Tun safe da suka tashi Rasheeda ke lura da yadda Anty Sameera ke shirin tarbar Ya Hisham ɗin,ƙarfe 12pm ta shiga kitchen domin shirya masa abinci na musamman.Tare suke aikin da Rash ɗin kamar yadda ta saba tayata,Fauziyya kan taimaka musu da wasu abubuwan.Aiki suke cike da ƙwarewa domin dukkansu gwanaye ne a wannan fannin,daga Rash ɗin har Anty Sameeran.Sai da suka kammala komi aka zuba cikin tsadaddun wamas na alfarma,Fauziyya ta shiga kwasar wamas ɗin tana fita dasu zuwa dining.Yayin da Anty Sameera ta fice ta nufi upstair's domin faɗawa wanka,tabar Rash na mixing choculate chips Muffin,wanda taji tana sha'awar ci.Sai da ta kammala ta sakashi cikin oven bayan ta zuba kwaɓin a cikin baking tray,lemun coconut ta haɗa ta sanya a cikin fridge.Zuwa lokacin har Muffin's ɗinta sun gasu ta cire,ta zubasu a cikin bowl ta nufi ɗaki dashi bayan ta aje wa Fauziyya guda biyu.

Ta gaji matuƙa da gaske,hakan yasa ta shiga wanka.Koda ta fito sallah tayi ganin har 2 tayi ma,zafi ake sosai a garin Abuja hakan yasa ta ƙara ƙarfin AC dake aiki a ɗakin.Ta nufi gaban mirror ta murza turaren jikinta,sam bata buƙatar shafa komi a lallausar fatarta sabida zafin garin.Doguwar riga ta zaro mara nauyi cikin kayan data siyo a Dubai,ta sanya rigar yabi jikinta yayi mata kyau sosai.Sake fesa turare tayi tabi lafiyar gado,ta ɗauki wayarta ta shiga duniyar chat.Tun safe sukai waya da Ya Hisham ɗin ya sanar mata cewa jirgin 2pm zai sauka,tare da tabbatar mata da cewa lallai su haɗu a Sharaton hotel,domin ya sanar da Sameera sai biyar zai sauka.

Tayi niyyar sharesa ne ba za ta ba,domin a can ƙasan zuciyarta akwai tausayin matarsa sosai.Yadda tun jiya take kashe lokacin ta tana gyare+gyaren tarbarsa,gyara na jiki da muhallinsa amma shi sam zuciyarsa na kanta ne.Wayarta dake ringing take kallo sunan Hisham ɗin ne ke yawo,ta ɗaga wayar tana narke murya sosai.Magana yake mata wanda banji mai ya faɗi ba na dai ji Rash ɗin na faɗin,

"Alright gani nan ya Hisham,but gaskiya ba za mu jima ba domin matarka na tsananin buƙatarka wallahi,na rasa wace iriyar jarabace wannan."

Ta ƙare maganar tana sauke wayar daga kunni.Bata sauya komi ba illah abaya data ciro mara nauyi ta ɗaura akan rigar jikinta,rolling tayi da veil ɗin Abayar ta ɗauki ƙaramar jakarta na LV mai shegen tsada ta fito. Sama ta haura ɗakin Anty Sameeran,a zaune ta sameta tana tsara kwalliya a gaban mirror.Ɗauke kanta tayi daga gareta tana faɗin,

"Anty key ɗin motarki za ki bani in je in dawo please!"

"Ina kuma za ki Rash ba za ki jira Hisham Ya dawo ba? Ga mukullin can a saman drawer ai."

Ta ƙare maganar tana sharce gashinta da ya gama shan gyara,yana fidda ƙamshi mai daɗi yayin da Rash ta ɗauki key ɗin tana faɗin,

"Ai ba wani jimawa zanyi ba ɗinki za mu kai can loko goma ni da Ralsy,kin santa da wutar ciki duk ta isheni da kira."

"Shikenan sai kun dawo,nima idan za ki amso akwai kayan da nake so a ɗinka min."

Cewar Sameera kenan,Rasheeda ta amsa da,"To shikenan na tafi."

Ta ƙare maganar tana fitowa abinta.Cikin sauri take sauka daga stair's ɗin,har ta gama sakkowa ta fice harabar adana motoci ta shiga motar Sameera ta fice. Cike da gwanancewa a tuƙi take murza kan motar,harta ɗauki hanyar da zai kaita sharaton hotel in da Hisham ke jiran ta kafin ya iso ga matarsa ta sunnah.

( _Allah ka shirya mazajen aure da ma samari da ƴan matan wannan zamanin baki ɗaya Ameen_ 👏🏻)

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*KADUNA*

Surayyah ce zaune a gaban Hajiya Kaka suna hira,tsohuwa mai shekaru 82 a duniya,mai cikakken ƙoshin lafiya.Tunda suka shigo garin Surayyah take bacci,sai a zuhur bayan ta tashi tai sallah shine ta fito falo wajen Hajiya Kaka suna sake gaisawa.

"Wai ke wannan Yarinyar sai yaushe za ki fidda miji ne,tunda bokon dai an kammalashi ina sha?"

Cewar Hajiya Kaka idanunta akan Surry wacce ta sauya kayan jikinta zuwa riga doguwa mara nauyi. Murmushi tayi tana zunɓure baki take faɗin.

"Bismillah za ki fara ba,shiyasa fa ni ban cika son zuwa gidanki ba.Duk ki ishi mutum da maganar aure,duka nawa nake Hajiya Kaka?"

Surayyah ta ƙare maganar tana dariya ganin yadda Hajiya Kaka ke mata wani irin kallo,kafin ta furta."Ke bera ce kam,baki ma fara ko irgan dangi ba.Ja'ira kawai,ganɗamemiyarki dake nono ya gama cika ƙirji kamar suyi magana,kike gayamin nawa kike? Ba laifinki bane,laifin Aisha da Mamudan ne da suka zuba miki ido su a dole ga Auta 'yar so,sabida sunga yanzu ke ɗaya ce tilo kika rage musu a duniyar,ai sai kuyi."

Sosai Surayyah ke dariya ganin yadda Hajiya Kaka ta dage,sai zuba magana take.Ana haka Uncle B ya shigo falon, Surayyah ta amsa sallamarsa tana faɗin,

"Yauwa Uncle B gara da ka shigo,ka jini da wannan Kakar taku daga zuwa za ta isheni da zancen aure koh."

Yadda tayi maganar a shagwaɓe yasa shi kafeta da ido,shi kaɗai yasan me yake ji idan tana masa wannan shagwaɓar tata.Murmushi ya saki yana zama cikin seater yake faɗin,

"Rabu da Granny kinji baby,nima haka take tasani gaba.Rigimar tsufa ce kawai."

Duka suka sa dariya,Hajiya Kaka na faɗin,"Kwadai ji da gafalewarku,kana Kawu ba za ka matsama Ƴarka tayi aure ba.Koda yake kaima ina kayi,ka tsaya ruwan ido da yawon ƙasashe duk akan bokon wofi."

Ta ƙare maganar tana sakin tsaki mai nuna ita tsakaninta da Allah haushi suke bata,hakan yasa Surayyah faɗin,"Easy mana sweety Hajiya Kaka,karki damu indai aure ne na kusa.Ke dai kimin addu'a,Allah ya bani mijin da zai kula muku dani."

Hajiya Kaka sai ta washe baki tana faɗin,"Ko ke fa Surayyatu,ai auren shine cikar mutuncinku.Allah Yai miki albarka yasa dai da gaske kike ja'ira."

Uncle B ne ya riga Surayyah magana yana faɗin."Ba wani Granny,bada gaske take ba."

"Dallah tafi can,wa ya sa da kai to? Kar dai ka maida hankali ka zaɓo mata ka tsaya shashanci da ruwan ido,zan haɗaka da Kawunka ne wallahi kuwa."

Ganin yadda Hajiya Kaka ta hau uncle B da faɗa yasa Surayyah tashi tsam,ta nufi bedroom ɗin Hajiya Kaka tana ƙunshe dariyar dake cinta.Uncle B ya bi bayanta da kallo yana haɗiye wani yawu da ya taru a maƙoshinsa,ya rasa wace iriyar fitina ce yake ji game da Surayyah.Tashi Yayi ya fice zuwa ɗakinsa dake can bayan flat ɗin Granny ɗin.

Surry bata sake fitowa ba sai ma ta baje bisa bed ɗin Hajiya Kaka,kiran Mardiyya tayi vedio call suna magana.Labarin maganar Hajiya Halima na son a haɗasu aure da tilon ɗan nata take baiwa Mardiyya,shawara ta ba Surayyah akan ta amsheshi matuƙar ya zo ya nuna amincewarsa.Ba a san inda za a dace ba,domin so da yawa sai zaɓin zuciyarka ya zamo ba alkhairi bane.Amma sai ayi auren haɗi kuma ya zama alkhairi,sosai Surayyah ke jin shawarwarin Mardiyya na ratsata,shiyasa kullum take sake godewa Allah da Ya haɗata da Aminiyar ƙwarai mai bata shawarwari na kirki.Ko da suka gama wayar sai Surayyah ta kira Mum,sun jima suna magana kafin ta kashe ta kira Busheera.

Misalin 9pm Surayyah da Hajiya Kaka ne a zaune,suna cin abinci a plate ɗaya.Surryn na sanye cikin Riga da wando na bacci masu taushi,kayan sosai sukai mata kyau duk da cewa bawai sun kama jikinta bane.Tuwan semo miyar ɗanyar kuɓewa suke ci,wanda aka wadatashi da busasshen kifi da naman saniya.Sosai Tabawa mai yiwa Hajiya Kaka girki da aikace-aikace ta iya abinci,musamman na gargajiya.

Uncle B ne Yayi sallama ya shigo hannunsa riƙe da ledoji guda biyu,ya zauna a cikin seater idanunsa akan Surayyah dake masa sannu da zuwa ya sauke yana faɗin,

"Surryn Uncle tuwo kuma wannan tsohuwarnan take ta cusa miki?"

Surayyah ta saki murmushi tana faɗin,"A'a Uncle,nice dai nayi sha'awar cinsa."

Ta ƙare maganar tana tsame hannunta domin ta ƙoshi.Hajiya Kaka ce ta watsa masa harara tana faɗin. "Ka dai ji da kinibibinka,yanzu me ka taho mata dashi tunda baka da aiki saina shagwaɓata."

Murmushi yayi idanunsa na bin bayan Surayyah da kallo,wacce ta suri plate ɗin da Hajiya Kaka ta gama cin abinci ta nufi kitchen.Sauke wani gwauron numfashi Yayi a lokacin da ta ɓacewa ganinsa,kafin ya samu bakin baiwa Hajiya Kaka amsa da faɗin,

"Granny kenan,nama da ice cream mana.shi na siyo mana,in kuma ke baki ci sai mu cinye kayanmu."

"Ina ko zanci tunda kasan Allah bai tsaga min bakin cin nama ba,sai Bashary da Surayyah."

Cewar Hajiya Kaka a ƙufule,dariya sosai Surayyah ke yi wacce ta ratso cikin falon.Ita dramar Hajiya Kaka da Uncle B dariya yake bata,gashi kuma son shi take sosai a cikin jikokinta,amma sam basa jimawa a inuwa guda ba a ji kansu ba.

"Hajiya Kaka me kuma ya faru kike ta sababi haka? "

Cewar Surayyah tana tsagaita dariyarta. Hajiya Kaka ta nuna Uncle B tana faɗin,"Ni da wannan Kawun naki ne mana,da ya gama rainani."

"Sorry Granny in dai akan nama ne gashi nan sai kici ki ture,Surry ɗakko plate ki zuba min nawa,ga ice cream nan ki ɗauki wanda za ki sha,sauran kisa a cikin fridge."

Uncle B yayi maganar yana turawa Surayyah ledojin gabanta,ta miƙe tana ɗaukar ledar ice cream ɗin tana faɗin,"Thank's Uncle B ɗinmu,kamar kasan ina jin shan Havilah kuwa."

Ta ƙare maganar tana sake komawa kitchen ɗin.Ice cream ɗin ta sanya a cikin fridge ta ɗakko plate ta fito,shi kawai ta ɗibarwa naman ta turawa Granny Hajiya Kaka sauran.Ita sai ta maida hankali akan shan ice cream ɗinta hankali kwance,suna hirarsu da Uncle B.Sai 10pm Ya bar sashin Hajiya Kaka,Surayyah na masa a tashi lafiya.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

*KADUNA*

"Abdallah maganar zuwa Zaria ta tashi,sauƙi ya samu ashe ma Surayyah ɗin yau ta zo nan Kaduna,sai da ka fita Humaida ke faɗi min."

Hajiya tayi maganar idanunta akan Abdallah dake danna waya,gama cin abinsu kenan suka dawo cikin falo suna tattaunawa.Daga gefe guda Humaida ne zaune tana chat tana sauraran hirar Hajiya da Ya Abdallah ɗin,zuciyarta cike yake da farin ciki da wannan haɗi da Hajiya ke son yi.Muryar Ya Abdallah ta jiyo yana faɗin,

"Ok Hajiya,amma dama Humaida ta san Yarinyar ne?"

Murmushi Hajiya tayi har haƙoranta suka bayyana,kafin ta furta.

"Ko ɗaya,kawai zuwan da mukai ne da suka ga juna Allah ya haɗa jininsu lokaci guda.Har hotuna sukai kafin mu taho a wayar Humaida,Humaida maza zo nuna masa zaɓin tawa ya fara ganin face ɗinta kafin ya ganta a zahiri. "

Hajiya ta ƙare maganar cike da raha,yayin da ƙirjin Abdallah ya buga da ƙarfi gaske wanda bai san dalilin jin hakan ba.Humaida cike da zumuɗi take fad'in."To Hajiya."

Ta taso ta kawo ma ya Abdallah wayar ta miƙa masa,cike da murmushi take faɗin,"Wallahi Ya Abdallah za ku dace da juna sosai da Surry."

Harara ya watsa mata yana karɓar wayar tare da ɗaura idanunsa bisa screen ɗin wayar,cikin tsananin razana yake kallon fuskar da gani ɗaya Yayi mata har yau ta kasa barin zuciya da idanunsa.Tsurawa pic ɗin idanu Yayi baya ko ƙiftawa,yayinbda zuciyarsa ke gaya masa kawai gizo take masa.Kama ce kawai yake hangowa amma ba Pretty ɗinsa bane,tsabar soyayyarta da yayi masa mugun kamu ne yasa take masa gizo.Humaida da Hajiya suka haɗa baki wajen faɗin.

"Ya kaga Surayyan? "

Sai yayi firgigit yana ɗauke ido akan wayar ya mayar kan Hajiya,yana son saita nutsuwarsa yake faɗin,"Hajiya tayi,tana da kyau ba laifi."

Yayi maganar cike da basarwa,can ƙasan zuciyarsa na cike da ruɗu da tsananin mamakin ina Hajiya ta samo masa pretty ɗinsa bayan ya shafe tsayin watanni yana bulayin nemanta? Cikin sauri yake cigaba da ganin sauran pics ɗin bugun zuciyarsa na sake gudu,cike da matsanancin ƙaunarta. Tura pic's ɗin Yayi ta chat tare da gogewa yadda Humaida ba za ta gane me yayi ba,miƙa mata wayar yayi cike da tsare gida yana faɗin,

"Oya take ur phone mara kunya,kinyi min tsaye aka."

Wayar ta amsa tana gimtse dariyar dake taso mata,domin tasan dai da wuya ya iya basar da wannan kyakykyawar halittar.

Hajiya data zuba masa ido ne ta furta."To yanzu yaushe za ku can aunguwar dosa ɗin ku ga juna? Don ɗazu na sanar da Hajiya Aishan cewa za ka je kaga Surayyan."

Duban Hajiya yayi yana faɗin."Ina ga zuwa gobe da dare sai Rayyan yamin rakiya Hajiya."

"Hakan yayi,Allah ya kaimu goben.Allah kuma ya tabbatar da alkhairy."

"Ameen Hajiya. "

Cewar Abdallah yana miƙewa tsaye domin barin sashin,sabida yadda zuciyarsa ke azalzalarsa akan pic's ɗin da ya ke ma kallon Pretty ɗinsa ce sak.So yake yaje ya kara pics ɗin da zanen da Yayi domin sake tantancewa.Duka bayan shi suka bi da kallo a lokacin da ya fita,Hajiya na faɗin,"Abdallahna kenan,Allah Yai maka albarka,ya kuma haɗa zuciyoyinku waje guda.Allah ya cika min BURIN ZUCIYAta inga aurenka da Surayyah."

Humaida ce ta amsa da,"Ameen" Tana barin falon,domin zuwa tayi shirin kwanciya.Itama Hajiya ɗaki ta nufa domin kwanciya.

A ɓangaren Abdallah kuwa bayan yayi shirin kwanciya ne,ya baje ƙaton hoton zanen fuskarta da yayi tare da buɗo pic's ɗin da ya tura ta wayar Humaida.Ƙirjinsa ke cigaba da bugawa sosai,domin tabbas pretty ɗinsa ce wannan.Wani daɗi yake ji na ratsa zuciyarsa,"To amma ya aka yi hakan ya faru? Ko dai Hajiya ta taɓa ganin hoton zananta ne har ta gano itace BURIN ZUCIYARsa,ta zaɓo masa ita domin ta cika masa BURINsa ya mallaki abinda yake so?" Waɗannan tambayoyin sune suka cika kansa,yana cigaba da jin soyayyarta na sake bin jinin jikinsa.

Sai dai bazai taɓa nuna wa Hajiya da ita kanta Yarinyar cewa itace BURIN ZUCIYARsa ba,zai bar abin a cikin zuciyarsa har zuwa lokacin da zai gama gwaji a kanta.Zai ɓoye komi a cikin ransa,har zuwa lokacin da zai barta ta koyawa zuciyarta sonshi.

Domin yana ji a zuciyarsa matuƙar ya bayyana dama ita ce BURIN ZUCIYARsa,Hajiya za ta ɗauka cewa ya amshi zaɓinta ne don dama itace yake so.Shi kuma sam baka yake so ba,yafi so taji a zuciyarta cewa ta isa dashi.Ta isa ta zaɓa masa koma miye ya kuma amsa da hannu bibiyu,don haka bazai taɓa nuna mata Surayyah ita ce Pretty ɗinsa da yake nema ba.

Pics ɗinsu da Humaida ya zubawa ido yana sake kallon kyakykyawar fuskanta,wani murmushi na suɓuce masa,kafin yakai baki yayi kissing pic ɗin yana lumshe idanu.

Ranar Abdallah Ya kwanta bacci ne cike da farin ciki,da kuma mafarkin Pretty ɗinsa...... ✍🏻