BURIN ZUCIYA(Short Story)

BURIN ZUCIYA Chapter 14

by @ayshadansabo

*BURIN ZUCIYA♥️* *Arewapen@ayshadansabo*

©️ _Ayshat Ɗansabo_ _lemu_ ✍🏻

*Free page 14*

Surayyah ce tsaye a cikin kitchen tana dafa indomie,domin shi kawai ta tashi tana son karyawa dashi.Sanye take cikin doguwar Riga na material,wanda akaiwa ɗinkin buba mai kama da babbar riga.Yabi jikinta sosai domin ita kanta tasan tayi ƴar ƙiba kwana biyu,sosai take son zama ƴar lukuta.Makeup tayi light a face ɗinta,ta saka red ɗin lipstick na oriflame ya zauna raɗau a saman cute lips ɗinta.Ƙamshinta mai sanyi da kwantar da hankali ke tashi a jikinta,cikin mintuna kaɗan ta juye indomie ɗin a plate bayan ta soya egg guda 2.Cup ta ɗauka ta haɗa tea,ta fito zuwa falo domin karyawa.

Bata jima sosai ba da fara cin abincin ba Hajiya Kaka ta fito daga ɗakinta,tana dogara sandar dake taimaka mata wajen tafiya sosai.Domin ciwon ƙafa ce kawai ke matsa mata a tsufan nata,zama tayi tana duban Surayyah take faɗin,

"Sai yanzu za ki karya ƙarfe sha ɗaya? Hmm! Yaran zamani kuna yadda kuke so,kinibibi salo-salo a wajenku dai."

Surayyah ta saki dariya tana faɗin,"To ya kika iya damu Hajiya Kaka,haka muka sabarwa kanmu.Ke dai yanzu barka da fitowa,da fatan mun tashi lafiya."

"Lafiya ƙalau ja'ira mai bakin surutu da shagwaɓa, Shi kawun naki bai shigo ba har yanzu?"

Hajiya Kaka tayi tambayar tana kallon Surayyah.Surry ta saki smile tana bata amsa da faɗin,"Bai shigo ba Kakansu,Nima shi nake jira so nake idan zai fita ya sauke ni a Kawo,za ni gidan wata friend ɗina da mukai skull tare."

Kafin ma Hajiya Kaka tace wani abu suka jiyo sallamar uncle B ɗin.Surayyah ce ta amsa sallamar nasa,idanunsa a kanta yana bin cute lips ɗinta da kallo.Zama yayi kusa da Hajiya kaka yana amsa gaisuwar Surayyah,kafin Shima ya gaida Granny din yana sake maida dubansa kan Surayyah yake faɗin,

"Surry baby wannan gayu haka,sai ina kenan da safen nan?"

Surayyah ta saki dariya kaɗan,cike da shagwaɓa take faɗin, "Sai Kawo mana,za ka sauke ni idan zaka fita.Za ni ziyara wajen friend ɗina Zarah ce."

"Ok yayi kyau,yanzu dai tashi ki soyamin Chips ki haɗo min da tea."

Cewar Uncle B idanunsa fes akan face ɗinta,shigarta Yai masa kyau matuƙa,shiyasa har ta shige kitchen ɗin idanunsa na binta da kallo.

Cikin lokaci kaɗan ta kammala ta kawo masa.Wayarta dake bisa kujera ta ɗauka ta nufi ɗaki,ko zama bata kai ga yi ba kiran Mum ya shigo mata.Ta ɗaga wayar tana gaida Mum ɗin,wacce ta shaidawa Surayyah cewa ta zama cikin shiri yau Abdallah zai zo nan gidan Hajiya Kaka su ga juna.Ta tabbatar wa Surryn cewa bata son taji wani matsala daga gareta,ta tabbatar tayi masa tarba ta mutunci.Basu wani jima ba sukai sallama da juna,jiki a sanyaye Surayyah ta sauke wayar daga kunninta tana mai kai hannu ta dafa goshinta. Zuciyarta na cigaba da bugawa a hankali,"Ko ya zai karɓeta? Wasu kalamai zai jefeta da su? Ya za ta ganshi a zahiri? Shin yayi na'am da ita ne da har ya amince zai zo ya ganta,ko kuwa duk cikin bin umurnin Hajiyarsa zai yi hakan?" Waɗannan sune tambayoyin da suka cika kan Surayyah.

Ƙarfe 12pm Uncle B ya gama kintsawa ya fito domin fita.Wayar Surry ya kira ya sanar mata cewa ta sameshi a mota idan za ta fitan ne,mayafi da hand bag ɗinta kawai ta ɗauka tai wa Hajiya Kaka sai ta dawo ta fice.

Ko da suka ɗauki hanya ba wani hira suke da Uncle B ɗin ba kamar yadda ta saba taita zuba masa hira,gabaki ɗaya zuciyarta naga tunanin yadda za ta ga Abdallah ne anjima.Ta rasa meyasa zuciyarta ke shiga ruɗu idan ta tuna shi,sauke ta Yai Yayi tafiyarsa yana kisima yadda zai bi domin cika BURIN ZUCIYARsa akan Surayyah.....

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Zaune yake a office ɗinsa shi kaɗai,wayarsa ce riƙe a hannusa ya tsurawa pic ɗinta idanu.Croping pic ɗin Yayi ya cire Humaida,sai face ɗin Surryn ce kawai a jiki.Sosai kallon kyakykyawar fuskarta ke sanyashi cikin nishaɗi da tsananin begenta,duniyar tunani ya lula na yadda zai tinkareta a yau ɗin."Ko wata irin tarba zai samu daga gareta? Alhali dukkkaninsu zaɓa musu juna aka yi." Waɗannan sune tambayoyin dake addabar zuciyarsa,duk ya ƙosa a tashi office ya wuce gida domin yin shirin zuwa wajenta.Number ɗin Rayyan wanda yake aboki,kuma Amini na gaske a wajen sa ya kira.Bugu biyu ya ɗaga wayar,Abdallah yayi baya a jikin kujerar dake juyawa dashi yana mai saka wayar a hand's free,ba tare da ya kara wayar a kunni ba.Muryar Rayyan ne ya fito tar time ɗin da yake faɗin,

"Hello na Pretty,ya aka yi ne?"

Lumshe ido Abdallah yayi yana jin wani daɗi na ratsa zuciyarsa,da wannan sunan da Rayyan ya kirashi.Saɓanin da idan ya kirishi da na Pretty ɗin yake taɓa zuciyarsa sabida yadda ya kasa gano ta,amma a yau sai ya samu kansa da jin daɗin sunan.Kamar ba zai tanka ba sai kuma ya furta,

"Zuwa bayan isha'i muna da zuwa Unguwar Dosa,bisa umurnin Hajiya domin ganin Yarinyar da ta zaɓa mini."

Yayi maganar can ƙasan maƙoshi,yana sauraran yadda Rayyan ya kwashe da dariya.Kafin ya furta, "Wow! Turaki cemin za ka yi zan rakaka zuwa wajen Amarya."

"Mitsuww...! Kaifa Rayyan ba ƙaramin ɗan iska bane,sai anjima to."

Bai jira cewar Rayyan ɗin ba Yai cutting call ɗin,yana buɗe idanunsa tare da sakin smile.Gyara zamansa Yayi,yana cigaba da duba file ɗin n dake gabansa.

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

Ƙarfe huɗu da rabi na yamma Surayyah da Zarah Sharehu suka fito daga ceceniya market,ta raka Zaran yin siyayya a cikin motar Zarar.Wayar Surryn ce ta shiga ringing,ganin Humaida ce yasa ta ɗaga wayar da murmushi a face ɗinta.Bayan sun gaisa ne Humaida ta haɗata da Hajiya dake son yin magana da ita,cike da girmamawa Surayyah take gaida Hajiyar tana sauraran bayanin da Hajiyan ke mata.Tana sanar da ita zuwan su Abdallah wajen ta,ta amsa cikebda girmamawa kafin Humaida ta amshi wayar tana mata tsiyar cewa wai tayi kwalliya sosai ta yadda za ta sace zuciyar Yayan nata.Murmushi kawai Surayyah tayi ta sauke wayar a sanyaye,Zarah ta dubeta tana faɗin,

"Surry ya dai?"

"Lafiya lau wallahi Zarah,wai baƙo zanyi zuwa anjima shine duk nake tunanin yadda zan tarbesa."

Cewar Surayyah a shagwaɓe,hakan yasa Zarah sakin dariya tana faɗin,"Wallahi kina da abin dariya,sai kace yau kika saba tarbar Saurayi.Ko wannan shi special one ne?"

"Hmm! Zarah ba za ki gane bane."

Cewar Surayyah cikin son basar da zancen.Itama Zarah sai ta shareta domin sarai tasan halin Surryn ba a jin cikinta inba Mardiyya ba,har suka shiga Unguwar Dosa domin ta sauke Surayyah a gida babu wanda ya sake magana.Ita Surayyah hankalinta na kan waya suna chat da Busheera,yayin da Zaran ta maida hankali akan tuƙinta.Bayan ta tsaida motar a bakin gate ɗin gidan Hajiya Kaka ne Surry ta dubeta tana faɗin.

"Thank u Zarah Sharehu,but za ki shiga ku gaisa da Hajiya Kaka ko? "

"No Surry,bari dai na wuce zan zo na musamman kafin ki wuce Abuja ɗin,a gaida babban baƙon idan ya iso."

Cewar Zarah cike da tsokana,hakan yasa Surayyah sakin dariya tana faɗin,"To zai ji ƴar world kawai,bye."

Surayyah ta shige gida yayin da Zaran ta juya. Koda ta shiga a barandar waje ta samu Hajiya Kaka zaune a saman ƙaramin carfet,da aka shinfiɗa mata.Ita da Tabawa ne suna hirarsu cike da nishaɗi,gefe guda radio ne a kunne da Hajiya Kaka bata rabo da saurarensa.Sallamar Surayyah suka amsa Hajiya Kaka na faɗin,

"Ke kuma idonki kenan,sai yanzu kika dawo? To sannu da zuwa."

"Yauwa,sannu da hutawa ƴar Tsohuwa.Wallahi sai yanzu kam,mun biya kasuwa ne shiyasa.Ni bari in shiga daga ciki in ɗan miƙe ƙafa."

Cewar Surayyah tana wucewa zuwa cikin ɗaki.Aje jakarta tayi tana shirin shiga toilet taji ana kiran wayarta,sai ta dawo da baya ta ɗauki wayar.Sunan Ya Mubarak data gani yasa ta jan ƙaramin tsaki tana zama a bakin gado tare da amsa call ɗin,

"Don Allah Ya Mubarak mu aje maganar luv a gefe,nifa na riga na fidda miji ma,zai fi kyau mu cigaba da zumunci kawai."

Banji mai Mubarak ɗin yace mata ba,gani kawai nayi ta yanke kiran tana jan tsaki.Tashi tayi ta shige toilet abinta,bata jima ba ta fito ta cire rigar jikinta ta saka shirt mai laushi tare da ɗaura zanin Hajiya Kaka akai.Ta fito ta nufi kitchen,ƙaramin freezer ɗin dake girke a kitchen ɗin ta buɗe domin ganin me ke akwai.Domin wani abu take son sarrafawa kafin zuwan Abdallah ɗin,kaza ta ciro ƙatuwa ta barta domin ƙanƙarar ya narke.Sai ta nufi wajen fridge ta ciro pineapple da zata haɗa juice ɗinsa,aiki ta fara sosai cike da gwanancewa.Nan da nan ƙamshi ya fara cika ko'ina,dambun kaza tayi wanda Yai mugun kyau shar-shar dashi.Sai tayi chocolate swiss cake,tayi rafin a cikin foilpaper ta saka cikin fridge haɗe da lemun abarban.

Sai da ta gyara komi tsaf ta fito daga kitchen ɗin ta nufi ɗaki,lokacin anata kiran Sallar Magriba.Hakan yasa ta shige toilet,sai da tayo wanka sannan ta ɗauro alwala ta fito.Daidai da shigowar Hajiya Kaka cikin ɗakin,ta dubi Surayyah tana faɗin,"Ke kuma da kika cika gida da ƙamshi wa kikai wa girki haka? "

Surayyah ta saki dariya tana faɗin,"Mijin da zan aura mana,tunda kun matsa lamba sai nayi aure.Shine zai zo anjima ya ga Tsohuwa."

Surayyah ta ƙare maganar tana sakin murmushi.Hajiya kaka ta furta,"Au!Tuh,Yaron da Ayshatu ta kira ta waya ɗazu take sanarmin zancensa kenan,to Allah ya tabbatar da alkhairy ko ke fa Surayyah.Kada ki damu,so da yawa wani haɗin na Iyaye wallahi alkhairi ne matuƙar anyi da kyakykyawar zuciya ne,ba wai anyi ne da wani manufa ba.Allah Yai muku albarka."

"Ameen Hajiya. "Cewar Surayyah tana ɗaukar hijab ta saka.Hajiya Kaka ta shige toilet domin ɗaura alwala. Koda Surayyah ta idar da Sallah sai ta kasa tashi ta jira har akai Isha'i,ta miƙe ta gabatar tana addu'ar Allah ya bata ƙwarin guiwar yin biyayya domin ta faranta ran Mahaifiyarta.Duk da cewa ba dole za'ai mata ba,amma tunda maganar yazo ne a lokacin da bata da wani na kamawa.Ga yadda kwanakin da Baba ya bata suke ta tafiya,ba tare da ta samu wani tsayayye da zuciyarta ta gamsu da shi ba.Shiyasa take ji za ta amshi Abdallah,matuƙar Shima ya amshe ta a matsayin zaɓin Mahaifiyarsa.

A hankali ta ja ƙafa ta isa bakin akwatin kayanta,domin ciro kayan da za ta saka, zuciyarta na cigaba da tunanin isowarsa.Ƙarar wayarta data jiyo kawai sai ƙirjinta ya fara bugu da ƙarfi,da ƙyar taja ƙafa ta isa ga wayar.Ganin Humaida ce yasa ta sauke ajiyar zuciya,a nutse ta ɗaga call ɗin cikin sanyin murya.

"Surry Ya Abdallah na kan hanyar zuwa yanzu bada jimawa ba fa,please kiyi kwalliya mai kyau duk da naga alamun ke gwanace,so akula min da Yaya,bye."

Abinda Humaida ta faɗi kenan ta kashe wayar,ba tare da ta ba Surayyah damar cewa komi ba.Sauke wayar Surry tayi tana nufar gaban mirror bayan ta zari jakar kayan makeup ɗinta,ta a jima zaune shuru kafin ta fara murza mai a saman lallausar fatarta.... ✍🏻