19_20
SANADIN HIJIRA
Ummu Fadeela
19/20
Wani irin tsalle Daniel ya buga yana hantsilawa gefe sakamakon wani katon kumurcin maciji da ya gani gaf da kafarshi ya fasa kai zai kawo mishi sara, a daidai lokacin ne kuma bullet da Al'ameen ya harbowa snake din ta fasa kanshi take jini ya wanke wajen, da sassarfa Daniel ya koma inda ya taso koda ya fahimci Al'ameen ne yayi harbin just to save his wicked life, wani irin kunya ne ya mamayeshi, shi yana can yana shirin yadda zai kashe sa amma yaga abun da zai cutar dashi ya kareshi, am I that heartless? ya tambayi kansa sai dai shaidaniyar zuciyarshi tana kawata mishi wadannan makudan kudin da akayi mishi alk'awari tuni ya Koma ruwa...
*FANNE*...
Haka muka kwashe wannan dare mai cike da bakin ciki da tashin hankali mara misaltuwa, jama'a sun yi kuka har hawayen su ya daina fita.
Washegari da ya kasance jumma'a haka al'ummar annabi suka dinga bi gida gida ana karbar gaisuwa, ni dai ina sama wajen kula da Maahh wacce ke bukatar taimako itama na yi kuka har hawayena sun kafe sosai mutuwar Baba Abbagana ta dakeni, daga hawayen dake zirara saman fuskar Maahh lokaci zuwa lokaci zaka fahimci itama mutuwar ta shige ta, duk bala'i irin na Uwa wannan ranar shiru kake jinta batacewa ko uffan karara zaka ga tashin hankali rubuce saman fuskarta, gida ya cika ya batse damkam da mutane, har wayewar Garin kuwa matar Baba Abbagana bata daina suma tana farfadowa ba, daga karshe allurar bacci aka zurkuda mata.
Ana tsaka da karbar makoki Baba Modu da sauran kannenshi suka fado gidan a hargitse kusan kowa mikewa tsaye yayi dama a halin fargaba ake, "Kowa ya koma gida Allah ya jikan mamatanmu ya karbi shahadar su, mu kuma Allah ya kyautata namu zuwa, mun samu labarin yan bindigar nan suna bayan gari yanzu haka kowa ya koma gida dan tuni wasu sun fara barin garin nan suna hijira zuwa wasu yankunan,"
Cewar Baba Bamai cikin daga murya, dan su da abin ya faru a garin su har yaran suka yi nasarar karbar garin sukuma sukayo gudun hijira sune zasu bada labarin yadda lamarin yake.
Cikin kiftawar idanu kowa ya watse wasu ma takalmi a hannu wasu ko takalmar ma basu bi ta kansu ba, gida ya rage mu kadai.
Sulalewa Baban Fanne ya yi zuwa jikin bango cike da tashin hankali ya daga murya da karfi sosai yace, "Taya ne zamu zauna lafiya, tayaya ne zamu samu kwanciyar hankali ,tayaya ne kasarmu zata ci gaba alhali masu mulki da yan siyasa babu abun da suka sani sai kawunansu, taya Ubangiji zai dubemu alhali ana kashe mashi rayukan bayinshi muminai salihai da basu ji ba basu gani ba, shin ina shugabanni ne ana kashe mu kamar kiyashi amma sun yi shiru basa cewa komai, ana korarmu daga muhallanmu kamar dabbobi amma basa cewa komai..
Ina jami'an tsaro wadanda nauyin kare rayukanmu da dukiyoyinmu ke wuyar gwamnati su kuma gwamnati su samar mana jami'an tsaro da kayan aiki domin karemu, ina arzikin da Allah ya huwacewa karkashin kasarmu da babu wata kasa a wannan yanki da ta kaimu arzikin karkashin kasa, me ya sa ake kashemu amma sun yi shiru?!!!"
Ya fada idanunshi suna kadawa jajwur. Baba Aisami da baba Bamai suka karaso gareshi da hanzari har suna hada baki wajen fadin, "Yaya wannan ba lokacin tambayoyi bane, ko kayi tambayar ma baka da muryar da za'a jika har a saurareka a baka amsar su abun da ke gabanmu shine muma mu shiga ayarin yan gudun hijira dan wallahi summa tallahi abun nan ya wuce duk tunaninku wanda ya taba gani ne kawai zai baku shaidar yadda yake,
"Yakura, Iya, Uwani, Bintu, Falmata lallai kowa ya hada kan yayanshi da abun da za'a iya dauka muna saukowa Jumma'a zamu bar garin nan, bazamu zo muna tsere da rayuwa ba" Cewar Bamaina cikin bada Umarni yana kiran matanshi da matan yan uwansa
Amma Bamai ina zamu shiga, nan kawai muka sani, nan shi ne muhallinmu bamu taba sanin wani waje sabanin wannan ba ina muka nufa?. Baba Aisami ya fada cikin gigicewa.
"YAN GUDUN HIJIRA,!! Yan gudun hijira zamu zama yaya, baza ku taba fahimtata ba yanzu, kuna gani dai yadda masu hankali suke kauracewa yankin nan, Ko a sansanin yan gudun hijira zamuyi rayuwa".
daga haka ya wuce yasan yan uwan nashi baza su fahimceshi ba, su Yakura da suka san abun da suka baro ai a dari da sittin kowacce ta fara hada kan yayanta, sauran matan gidan kuwa sai abun ya zamto musu bambarakwai yayin da ahalin Abbagana mutuwar ubansu ya dawo musu sabo filll.
Almuhajir da yayi sakato a gefe kwatakwata ma baya fahimtar abun da ake cewa tsabar yadda kwanyarshi ta toshe abubuwa sun mata yawa yana ganin dandazon mutanen sun fara watsewa ya faki idon sauran ya wuce saman mu da wani irin sauri, muna zaune jugum jugum kamar kurame duk mun fita a hayyacinmu, ba ga Maahh marar lafiyar ba hatta ni mai lafiyar zuwa yanzu na fara rasa garkuwar jikina, har yanzu rigar jiya ce sanye a jikina saidai na cire kayan dan kunnen, kamar wanda aka hankadoshi ya fado dakin, "Fanne, ki hada kayanki da na Maahh duka waje daya ana saukowa sallar jumma'a zamu bar garin nan gari babu lafiya, an ga yaran nan a can bayan gari kuma nan shine waje na gaba da suke hari dama ki hanzarta dan Allah." ya karishe fada yana haki ba tare da ya lura da yadda na koma jikin bango na makale ina makyarkyata kamar kyanwar da ta jike ba tun shigowarsa.
Har ya juya zai fita sai kuma ya dawo baya takowa yayi gab dani har ina iya jin fita da shakar numfashinsa, "Ka fita anan, ka fita na ce ni ba yar iska bace ka fita." na fada bakina yana rawa dan mun samu kusanci sosai, guiwarshi guda yakai kasa ya na dafe dayar kuma da guiwar hannunshi.
"Dan girman Allah Fanne ki tsaya kiji abun da zan fada miki, nima ba dan iska bane, a zatona kece mutum ta farko da zaki bada wannan shaidar sai gashi abun haushi ke ce kike min kallon hakan, dan Allah ki yafemin ba laifina bane nima bansan yadda akayi hakan ta kasance ba, ki koma min asalin Fannetun da na sani plsss"....."Ka fita nace ko in maka ihu ka fita".
Na kuma fada ina nuna mishi hanyar kofa, mikewa ya yi jikinshi a sage yace, "Zan fita fanne amma zakiyi nadama a lokacin da ni kuma zan miki dariya but ba zan dau irin matakin da kika dauka a kaina ba, kar ki manta ki hada kayanku kamar yadda nace" daga haka ya sa kai ya fice a dakin. Zaman yan bori na yi a wajen ina daura hannuna bisa kai zan kwada ihu sai kuma na fasa na fara tasbihi ina kiran sunan Allah gami da matsowa kusa da Maahh da ke binmu da idanu kawai amma babu bakin magana duk ta yi laushi, tun ina bata taimakon da karamar kwakwalwata ta nuna min har na koma kawai sai dai in riketa ina kuka.
Kamar wanda aka jefo haka Baba ma ya fado dakin yana haki, inda Maah take ya nufa gami da kamo hannunta "Aminatu kuyi hakuri haka Allah ya so damu, ki kara hakuri zaki ci jarabawarki, ban so abun ya kasnace haka ba amma haka Jallah ya tsara" sumbatar hannunta ya yi ya na mikewa a daidai lokacin da ake kwada kira karfe daya na ranar jumma'a a babban masallacin jumma'ar garinku "Fanne ki hada muku kaya idan mun sauko juma'a zamu bar garin nan, babu yacce zan yine kawai amma su bamai sun dage kuma bazan iya yi musa musu ba,
"Yana magana ya fita ba tare da ya yarda mun hada idanu ba, kamar ma kuka naga yanayi ban yi wata wata ba na kwasa a guje a karon farko na rayuwata na rungume Baba ina sakin kukan da ban san dalilinshi ba, cakkk ya tsaya shima a maimakon ya tureni kamar yadda na yi zato sai ji na yi ya janyoni jikinshi sosai yana bubbuga bayana.
"Yi shiru kar ki dagawa Ummarki hankali, In sha Allah kina tare da sanyawar Albarkata, ke din kece bangon zuriyata, a gare ki zan samu zuriyar da ban haifa ba, Allah yai miki albarka, Allah kuma ya baki karfin guiwa na jure.....
"kukan da yaji yana taho mishi ne ya sanyashi sakina da barin dakin da sauri kamar zai kifa. Sororo na yi a wajen ina kokarin digesting maganganun Baba amma na kasa hada komai, tuna abun da suka fada shi da Yaya ya sa na koma kusa da maahh, "Maahh sun ce wai zamu tafi, wai gari babu lafiya ban san ina muka nufa ba" ko uffan batace min ba nima nasan bazatace din ba. Kayayyakinmu na hada a akwati guda daya da shike ba wasu wadatar sutura garemu ba, yawanci ma duk sun jikata..!
A bangaren Uwa kam yau gidanmu ya samu salama sun kule a daki ita da yaganah dake ta kumbure kumburen ke nan baza'a daura aurenta da Almuhajir ba.
"Ke shegiya ana ta kai wake ta kaya, dan kaza kazan ki tashi ki hada kayan nan ko bakiga halin da ake ciki bane kasa duk ta dauki dumi ko ina ya rikice, to kadan daga cikin abun da zan iya ne in tafi in barki a gidan nan, yo to Allah na tuba dan na barki asara na yi" Cewar Uwa da ta hada uban zufa tana ta shirya kudi cikin wani katon bujen siket dinta yar ciki da aka dinkawa wani makeken aljihu..."
Karfe 1:30 na rana gabau sun yi wankan Jumma'a zasu wuce masallaci Baba ne ya leka dakin Uwa ya ganta tana ta shirya kaya, "Uwani mun wuce jumma'a ku gaggauta gama shiri kuma kuyi ta hakuri kin ji ko" dagowa ta yi da sauri, suka hada ido duk yadda ta saba masifeshi amma yau ta kasa, a dawo lafiya kawai ta fada ta cigaba da aikinta. Dakin mu baba ya shigo ina yiwa Maahh alwala lokacin kamar yadda ta kwatantamin da bakinta yana kare mana kallo ya ce, "Aminatu mun wuce ayi ta hakuri, Fannatah kema kiyi ta hakuri da rayuwa sannan ki dage ki zama jaruma mai karbar rayuwa a duk yadda yazo miki, Allah yai miki albarka ke da zuriyarki"
Da kallo kawai muka iya binshi, ina jiyo muryoyinsu a waje ta windownmu dake setin waje, dan haka na tashi da sauri na leka dukkansu suna kokarin shiga keke napep din Yaya Almuhajir, kamar wanda akace ya dago caraff muka hada idanu dashi, yasha wanka cikin wasu fararen kaya hannunshi rike da key na machine dinshi, samun kaina na yi da gaza janye idanuna shima haka, a hankali ya sakar min wani irin lallausan murmushi da naga ya sanya fuskarshi yin wata irin annuri kana ya min blowing kiss yana huro min saitin inda nake still da murmushi dauke a fuskarshi, turo baki na yi ina sakin labulen windon da karfi gami da yin zaman dirshan a wajen zuciyata tana gudu da karfi karfi,... Rashin sani yafi dare duhu, da na sani na mayar mishi martanin murmushin da yai min, danasani na mayar mishi martanin kiss din da yamin, da na sani na kalli kwayar idanunshi na ce mishi Yaya Almuhajir na san ba laifinka bane dan haka na yafemaka kuma ina sonka ina kaunarka. Sai dai kash....wannan ita ce nadamar da bana fatar in kuma maimata makamancinta...Dan bata fuska Muhajir ya yi ganin ta saki labulen. "Muje mana babana lokaci na tafiya" cewar Babanmu, gyara zaman rigarshi ya yi yana shiga machine din ya jata suka wuce masallacin jumma'a, karar dirin tashin machine din yayi daidai da wani faduwar gaba da ya ziyarceni a tare muka rumtse idanu ni da Maahh wacce ban san dalilinta na yin hakan ba.
Masallacin ya cika makil da al'umma kowa ya nutsu baka jin komai sai sautin muryar liman dake karanto huduba yana magana akan Imani da jin tsoron Allah, lokacin da ya gama ladan ne ya kuma kiran sallah kafun yace sahu sahu, nan kowa ya mike aka shiga sahu a jere gwanin sha'awa, ALLAHU AKBAR. Ladan ya fada bayan liman da karfi duk inda kake a fadin garin sai kajiyoshi. ALLAHU AKBAR ya kuma fada lokacinda aka kai ruku'u,"SAMI'ALLAHU LIMAN HAMIDAH"ya kuma fada lokacin da suka dago,"ALLAHU AKBAR" ya kuma fada lokacinda suka kai goshinansu sujjada suna mai mika addu'a ga Ubangijinmu wanda ya hallici dukkan komai da kowa, a dai dai lokacin al'amarin ya faru al'amarin da zuciyoyi baza su taba mancewa dashi ba, ALLAHU AKBAR fitar sautin muryar ladan da mamu dake biye yayi dai dai da tashin wani sauti mai cike da tashin hankali da rikitarwa da rudarwa da tsoratarwa ga duk wanda ya jishi a wannan lokacin ji kake DOOOOOUUUUOOOMMMMMM sautin ya bada na fashewar wani abu a take kasar garin ta jijjiga na tsawon second biyar da duk wani mahaluki mai rai sai da yajisa, a lokaci daya wani irin hayaki bakikkirin mai tafe da 'kura suka turnuke sararin samaniyar garin gabaki dayansa........😭😭😭😭